NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Washegari ma fitar safe ta yi zuwa gurin aiki, data dawo kamar time ɗin jiya ta shirya ta tafi gidan Aunty A’isha, sai bayan Magriba ta dawo gida. Tana cikin yin Sallar isha’i ta ji wayarta na ringing, bayan ta idar ta yi lazimi ta ɗauko wayar domin ta duba mai  kiran nata. Wani kiran ne ya ƙara shigowa, ‘Uncle Ahmad’ sunan data gani yana yawo akan screen ɗin kenan. Ta d’aga tare karawa wayar a kunne, muryar su Afrah ta ji kowa na rige_rigen kiran sunan ta, “Aunty! Aunty!” Cikin farinciki ta ce “Na’am my kids ya kuke?” Suka haɗa baki gurin faɗin “Lafiya k’alau.” Neehal ta ce “Ya school da Islamiyya? Kuna dai karatu sosai ko yaran kirki?” Afrah ta ce “Eh Aunty, exam ma zamu fara next week.” Ta ce “Allah ya ba da sa’a Daughter, ina Ummi da Aunty Zahra?” Ta ce “Suna gida.” Neehal ta ce “Ki ce ina gaishe su.” Amrah ta zo ta karɓe wayar daga hannun Afrah tana faɗin “Aunty ki yi hirar da ni nima, ai kin gama da ita ko?” Neehal ta ce “Toh Daughter ina Daddy?” Amrah ta kalli Ahmad dake zaune yana sauraren hirar da suke, da yake a handsfree ya saka wayar. Ya gyaɗa mata kai, Amrah ta ce “Gashi nan.” Ahmad ya ɗauki wayar ya ce musu su je su cigaba da Assignment ɗinsu. Ya kara wayar a kunnensa bai ce komai ba. Neehal ta ce “Ina yini.” Ya ce “Bana amsawa.” Tun ma kafin ya faɗa mata abun da ta masa ta san laifinta, dan haka ta ce “I’m sorry bazan kuma Uncle, ya ka je gida?” Ya ce “Lafiya k’alau, ya Mama da Daddy?” Ta ce “Suna nan k’alau.” Ya ce “Masha Allah.” Tare da kwanciya akan gadon da yake kai, murya ƙasa_ƙasa ya ce “Princess ki bani labari mai daɗi mana.” Ta ce “Uhm, kasan me Uncle?” Ya ce “A’a.” Ta yi shiru, ya ce “Uhm? ina jin ki?” Ta ce “Ka fasa kawo mun su Afrah, ka bar su a gurin Ummi ta cigaba da riƙe su kawai.” Ya ce “Why?” Ta ce “Mama ta ce, kun fi mu buƙatar su a kusa da ku.” Ta faɗa masa duk yanda suka yi da Maman. Ya yi murmushi ya ce “Allah sarki Mama, ta hango abun da mu ba mu hango ba, kuma ta fi mu gaskiya.” Neehal ta ce “Amma idan sun yi hutu zaka na kawo mun su.” Ya ce “Insha Allah Princess, kafin kuma mu yi aurenmu su dawo hannunki da zama gaba-ɗaya.” Ta yi shiru tana maimaita kalmar Auren daya ambata a cikin ranta, gabanta na fad’uwa. Ya ce “Hello Princess!” Ta sauke numfashi ta ce “Na’am Uncle.” Ya ce “Kin yi shiru.” Ta ce “Ba komai.” Sun ɗan taɓa hira sannan suka yi sallama…..

SAFEENAH

Tun ranar da su Afrah suka gida anata murnar ganin su yan’uwa da abokan arziki, yayin da a ɓangaren Safeenah kuwa akasin haka ne. Dan wani irin tashin hankali mara misaltuwa ta tsinci kanta a ciki, lokacin ɗaya cikinta ya kaɗa ta tsure sai toilet. Da yake sai a washegarin ranar da su Ahmad suka koma da safe sannan suka samu labarin bayyanar su Afran. Ranar wuni ta yi a ɗaki cikin zullumi da fargaba, lokacin ɗaya ta zabge ta rame ta fita daga cikin hayyacinta. Gashi tana ta kiran wayar ƙanwarta Saudart bata shiga wayar a kashe. Ranar da su Afrah suka zo gidan ta ja su ɗaki ta tambaye su cikin bugar ciki, yanda aka ɗauke su. Afrah data fi surutu ta ce mata “Suna falo suna kallo, wasu suka zo fuskokinsu a rufe suka ɗauke su.” Tashin hankalin ta ne ya ƙaru, tunda gashi yaran za su iya bayanin yadda aka sace su idan an tambaye su, hakan yasa a washegarin ranar ta yi sammako ta tafi Zariya bayan ta yiwa mahaifiyarta ƙaryar Saudat ɗin ce bata da lafiya zata je duba ta. Tana zuwa Zariya ta ƙara tarar da wani tashin hankalin, domin kuwa kwance a gadon asibiti ta tarar da Saudat cikin mummunan yanayi, bata ma san waye a kanta ba. Ƙanwar Saudat ɗin ce take sanar mata wasu ƴan_daba ne suka mata duka ba tare da an san me ta yi musu ba. Amma ana ta bincike ana ce ƙoƙarin gano ko su waye. Cikin fitar hayyaci Safeenah ta dawo gida da daddare, tana zuwa ta kwanta zazzaɓi rigijib ya rufe ta saboda tsananin tashin hankali. Tana tsoron kar ta yi biyu babu, ita bata samu soyayyar Ahmad da take bala’in son sa ba gashi kuma Ƴaƴansa sun dawo gare sa cikin k’oshin lafiya. Ta yi da na sani da nadama mara amfani data biyewa rud’in shaid’an da zugar ƙawa har ta kaita ta baro ta, yau gashi ta barta a ciki, duk da itama gata can kwance cikin mawuyacin hali, amma ita ta san idan asirinta ya tonu kashe ta za’a yi. Tunda kwangilar kisan kai ta bayar a yi. Ta kira Gaye wanda yasa yaransa suka masa aikin ɗauke su Afrah amma wayar ta shiga bai ɗauka ba. Sai bayan kwana biyu ta ga text ɗinsa ya turo mata, inda yake sanar mata. Shine yasa yaransa suka yiwa Saudat dukan mutuwa, saboda ta yi masa barazanar zata tona masa asiri tunda ya ci amanar su a aikin da suka ba shi. Itama matuƙar ta yi ƙoƙarin aikata gangancin da Saudat ta aikata sai ya mata abun da ya fi wanda ya yiwa Saudat. Ƙarshen tashin hankali da damuwa Safeenah ta shiga da ganin wannan text ɗin, amma ta yiwa Allah godiya da ba’a kashe su Afrah ba, may be in an tashi yi mata hukunci a mata da sassauci. J inya sosai ta kwanta har sai da ta kaita ga kwanciya a gadon asibiti…….

A cikin week ɗin nan Neehal ta je gidan Aunty Sadiya kamar yadda Mama ta umarce ta, ta kai mata ziyara. Aunty Sadiya ta yi amfani da wannan damar ta ƙara yiwa Neehal tambayoyi a game da binkicen da take na kisan su Anwar, kuma Alhamdulillahi ta ƙara samun wasu evidence ɗin. Ranar Friday kamar yadda Sadik ya ce suka dawo lafiya daga Ibadan. Delicious sosai Neehal ta haɗawa masa na tarb’ar sa, ta bayar aka kai masa har gida, tunda bai samu zuwa gurinta ba saboda sai yamma lik’is suka dawo. Sai washegari Saturday ya zo suka sha hirar su. A kwanakin nan da suka wuce kullum Neehal sai sun yi waya da Ahmad every Morning and Night. Ranar Sunday tun ƙarfe goma sha ɗaya na safe ta shirya dan zuwa gidan Uncle Umar bisa tilastawar Mama. Tana aikin turo baki gaba ta shiga ɗakin Mama dan yi mata sallama. Mama ta dube ta, ta ce “To Haka zaki je musu hannu Rabbana.” Ta ƙara ɓata fuska ta ce “Toh Mama me zan kai musu, ni fa dak’yar ma idan zan gane gidan.” Mama ta ce “In kin je kar ki gane ɗin, ki ɓata, da duk da muke zuwa wani ne yake raka mu ai.” Neehal ta ce “Toh Mama ai yanzu na daɗe ban je ba.” Mama ta ce “Ko me zaki yi fa sai kin je, gwara ma ki bar wani kame_kame. Ki duba cikin drower ɗin can zaki ga kuɗi ki ɗauki 10k, sai ki biya ta Mall kafin ki tafi ki yiwa yaransu tsaraba.” Ta ƙarasa ta ɗauki kuɗin tana faɗin “An gode.” Mama ta ce “Kin haɗa kayan wankin da na ce ki haɗa?” Ta gyaɗa mata kai alamar eh. Mama ta ce “Har su bedsheet da labulayen?” Ta ce “Eh duk na haɗa.” Mama ta ce “Shikenan ki wuce ki tafi, Allah ya kiyaye, ki gaishe su.” Ta amsa tare da ficewa daga ɗakin. Two days bata ga Motar da take bin bayanta ba, ta yiwa Allah godiya tare da addu’ar Allah ya yi mata iyaka da koma su waye. Sai da ta biya ta siya musu kayan su chocolate duk da ta san yanzu su Iman sun girma, ta haɗa musu da turaruka da sabulan wanka, dan rasa me zata yi musu tsarabar da shi ta yi. Sha biyu da ƴan mutuna ta ƙarasa ƙofar gidan, ita kanta ta yi mamaki data iya gane layin, ko da yake layin ba shi da wahalar ganewa tunda miƙa ɗaya za kai daga titi har gidan. Da shagon wani mai aune_aune take gane gidan Uncle Umar da yake pacing ɗin gidan . Tabbas inda ta tsaya nan ne gidan, amma abun da ya bata mamaki ganin yanda gidan ya ƙara girma da kyau, filin kusa da gidan aka haɗe da gidan aka gine. A ranta ta ce “Ko sun tashi daga gidan ne? Ta day yi k’undunbala ta fito daga cikin Motarta hannunta ɗauke da ledar data musu shopping ta ƙarasa ta fara knocking ƙofar gidan. Muryar da ba za ta taɓa mantawa da ita ba a rayuwarta ta ji ta ce “Waye?” Ta sauke numfashi ta ce “Ni ce.” Aunty Fauziyya ta ce “Turo ki shigo.” Kanta a ƙasa ta tura ƙofar ta shiga tare da yin Sallama. Aunty Fauziyya da wata bak’uwar murya a gurinta suka amsa mata. Ta d’ago karaf suka haɗa ido da Aunty Fauziyya. Cikin mamaki Aunty Fauziyya ta ce “Neehal!” Ta ƙirƙiro murmushi ta ce “Na’am Aunty.” Tare da bin ta da kallo ganin yanda ta zabge ta rame ta yi wani uban baƙi. Ɗayar matar da Neehal bata san ta ba cikin fara’a ta ce “Sannu da zuwa, ki ƙaraso mana.” Neehal ta ƙarasa ta inda suke sannan ta ɗan tsugunna ta gaishe su. Ɗayar ce kawai ta amsa, Aunty Fauziyya kuwa mamaki ne ya sandarar da ita. Matar wadda ke sanye cikin atamfa doguwar riga tayi shar abunta ta ci d’aurinta ta kamo hannun Neehal ta yi hanyar sabon ginin da Neehal taga an yi a gidan tana mata lale marhabin. Sai a lokacin Aunty Fauziyya ta yi magana ta ce “To ai ba gurinki ta zo ba, tunda ba ma sanin ki ta yi ba, zaki wani janye ta daki.” Matar ta juyo ta yiwa Aunty Fauziyya wani kallo sannan ta juya hannunta still riƙe dana Neehal suka shiga ƙofar part ɗin nata bayan ta buɗe. Ta nunawa Neehal guri a falon ta ce “Bismillah ki zauna bari in kawo miki ruwa.” Neehal ta ɗan murmusa sannan ta zauna zuciyarta cike da tarin tambayoyi, ko shakka bata yi Uncle Umar ne ya ƙara aure, dan kwanaki suna waya da Uncle Usman ya fara mata zancen kuma sai wayar ta katse, data bi bayan shi kuma wayar ta ƙi shiga. Ita kuma bata wani riƙe zancen a ranta ba saboda a ganinta ba sabgarta ba ce. To an ma auren da Uncle Umar ya ƙara shine ya mayar da Aunty Fauziyya haka ta lalace ta zama kamar wata tsohuwa, ko kuma cuta ta yi… Dawowar matar falon ya katsewa Neehal tunaninta. Matar ta ajiye mata ruwa da juice a gabanta, sannan ta ƙara shiga kitchen ta dawo hannunta ɗauke da abinci. Neehal ta ce “Na gode.” Matar ta ce “Babu komai, dan ma bamu san da zuwanki ba kawai ganinki mu kai, ai da an tanadar miki ko ɗan wani abu ne.” Neehal ta ce “Babu komai, hakan ma Na gode sosai.” Matar ta ce “Neehal ko Yar gidan Yayar Umar?” Bata jira amsar Neehal ba ta cigaba da faɗin “Ai na ji labarin ki a bakin Binta mak’ociyarmu da kuma shi kansa mai gidan namu.” Neehal ta yi shiru cikin mamakin jin Uncle Umar ne har yake na zancen ta, ashe yana sane da ita kenan. Neehal ta ce “Ina su Iman fa ko basa nan?” Matar ta ce “Suna islamiyya, amma sun kusa dawowa, ɗaya tana yi zaki gan su sun dawo.” Ta jinjina kai ta ce “Uncle fa? Sai dare yake dawowa shi ko?” Matar ta ce “Zaki iya ganinsa ya dawo anjima da yamma.” Neehal ta yi shiru dan ba ma ta so su haɗu da shi. Haka matar ta yi ta jan Neehal da hira cikin fara’a da karamci, ta takurawa Neehal ta ci abinci tana mata tsiyar kamar ba gidansu ba ta ƙi sakin jikinta. Bayan ta ci abincin kaɗan ta yi Sallah sannan ta bawa Matar ledar data shigo da ita. Matar ta karɓa ta mata godiya ta debi abubuwan cikin ledar kaɗan ta bawa Neehal ta ce ta kaiwa Aunty Fauziyya sauran. Neehal ta fito ta tarar har lokacin Aunty Fauziyya tana tsakar gidan a zaune akan kujera yar tsugunne. Kallo ɗaya zaka mata ka fuskanci tana cikin damuwa. Aunty Fauziyya Ta shigar da Neehal ɗakinta cikin fara’ar data bawa Neehal mamaki. Bayan sun ƙara gaisawa ta ce “Neehal kin ƙara girma da kyau Masha Allah.” Neehal ta yi murmushi kawai. Aunty Fauziyya ta cigaba da bin ta da kallo cike da sha’awa, a ranta tana faɗin kamar ba’a Nigeria take rayuwa ba saboda kyawun fatar ta da hasken ta, ga k’amshin ta mai daɗi daya cika mata hanci irin na ƴan gayu. Ta sauke ajiyar zuciya ta fara bawa Neehal labarin abubuwan da Uncle Umar yake mata yanzu dan ya ƙara aure. Wai wulaqancin yau daban na gobe daban suke mata shi da matar tasa, har da k’wallar ta. Neehal ta ce “Ta yi haquri kawai.” Dan bata san me zata ce mata ba, bayan haqurin. Daga ƙarshe kuma ta fashe da kuka wai Neehal ta yafe mata ko alhakin ta ne yake bibiyar ta. Ta ce ita ta yafe mata, dama can bata riƙe ta ba. Sai kuma ta bata labarin ɓacin da Iman ta yi, wai yarinyar bata ji har bin maza take. Haka dai tay ta yiwa Neehal zance kamar wadda aka tambaya. Ita kuma duk sai ta ji tausayinta ya kamata har da zubar mata da hawaye. Suna cikin hirar su Iman suka dawo daga islamiyya, kallo ɗaya Neehal ta mata ta tabbatar da abun da mahaifiyarta ta faɗa. Yarinyar ta ci uban bleaching har da b’ular hanci, sai taunar cingum take ƙas_ƙas. Neehal tay ta mamakin ta a cikin ranta, yarinyar da bata fi 16 years ba amma ita ta yi wannan budewar idon haka. Ta ji ba daɗi sosai akan halin yarinyar, ko ba komai jininta ce bata so ta yi wannan lalacewar haka ba. Addu’ar shiriya ta mata a gurin Ubangiji, domin ita ce kawai mafita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button