NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Neehal yau tunda ta tashi take jin wata irin faduwar gaba na riskar ta, shi ya sa ma ta shirya ta tafi gurin aiki, ko idan tana cikin mutane za ta ji sauƙin abin da yake damunta, amma tunda ta je gurin aikin ta kasa tab’uka komai, wayar da su ka yi da Anwar ne ma da safen nan ta ɗan sanyaya mata rai, kowa ya ganta sai ya mata sannu, dan su duk ɗaukarsu rashin lafiyar da take ne. Haneefah na tsaka da aiki, Mama ta kira ta, ba ta d’aga ba ta bari idan ta gama sai ta kira ta, ganin kiran da Maman take mata ba k’ak’k’autawa ya sa ta ɗaukar excuse ta fita ta d’aga kiran,Mama cikin dauriya dan kar Haneefah ta fuskanci da wata matsalar tace “Haneefah ku taho gida yanzu ke da Neehal” ba ta jira amsar Hannefan ba ta katse wayar, duk da Mama ta yi ƙoƙarin b’oye damuwarta amma sai da Haneefah ta fuskanci akwai wani abu a Muryar Maman, office d’in da Neehal ta ke ta nufa da sauri, Neehal ta na zaune ta kwantar da kanta a kan table ɗin office Haneefah ta shigo, taɓa ta yi ta na faɗin “Neehal taso mu koma gida tunda ba ki da lafiya” Neehal ba ta yi musu ba dan ita ma ta na bukatar zuwan gidan, dan har wani jiri_jiri ta ke ji daga zaunen da take, d’ago da kanta ta yi a hankali, wayarta ta ɗauka jikinta a matukar sanyaye ta zira a cikin jakarta, ganin yanda take Haneefah ta kama ta suka fito daga office din, Manager d’in gidan TV Haneefah ta sama ta masa bayani, sannu ya yi wa Neehal sannan ya haɗa su da ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan TV’n ya kai su gida.

Mama ce kaɗai a falo tana zaune ta na hawaye, su Dad sun wuce gidansu Anwar harda Hajiya da ta dage sai ta bisu. Jin shigowar su Neehal ya sa tai saurin share hawayen fuskarta ta mik’e tsaye, ganin yanayin Neehal gabanta ya faɗi, dan ta yi tunanin ko ta ji mutuwar ne, Haneefah ta ce “Mama ga ta mun dawo, nima dama tun d’azu nake son na ce mata ta dawo gidan saboda jikinta, sai kuma gashi kin kira ni” Mama ta kama Neehal a jikinta ta rungume, ta na sakin ajiyar zuciya jin ba su ji mutuwar ba, Haneefah kallon Mama kawai take yi ganin yanayinta, hakan ya tabbatar mata da tabbas da akwai wata matsalar ba iya ciwon Neehal ɗinne ya maida Mama haka ba, Neehal kuwa luf ta yi a k’irjin Mama ta na sauke ajiyar zuciya, wayar Mama ce ta yi ƙara, hakan ya sa ta sakin Neehal da sauri ta zaunar da ita, Dad ne ke kiran ta, ɗagawa ta yi ta kara wayar a kunne, daga ɗaya ɓangaren Dad ya ce “Doctor, Neehal d’in sun dawo?” Mama ta ce “Eh.” Dad ya ce “To ku taho yanzu an kawo gawar.” Mama ta ce “Ohk ga mu nan.” Daga haka ta katse wayar, dama ta ce wa Dad idan ankawo gawar su kirata dan gawar ta na asibiti fiye da awa biyu Police na binkice a kanta, sai yanzu aka ba da ita. Mama da ma da hijabinta a jikinta, mukullin Motor kawai ta ɗauka ta dubesu ta ce “Ku taso mu je” Kallon ta Neehal ta yi cikin mamaki amma ba ta ce komai ba, sai Haneefah ce ta ce “Ina zamu Mama?” Mama ta ɓata rai ta ce “Siyar da ku zan yi” Haneefah ba ta ƙara cewa komai ba, ta kama hannun Neehal suka bi bayan Mama, a tunanin Haneefah asibiti za su itama Neehal haka. A bayan Motor suka tarar da Mama, sai driver a gaba, suma bayan suka shiga. Tunda suka shiga Motar idanun Neehal a lumshe suke, Haneefah ce ma take ɗan kallo hanya, a tunaninta Nasarawa Hospital za su sai ta ga sun yi hanyar Hotoro ba ta kawo komai a ranta ba, sai da ta ga sun shiga layinsu Anwar sannan ta fara tambayar kanta a kan mai kuma za su yi a gidan su Anwar d’in, gabanta ne ya yanke ya faɗi Lokacin da driver ya yi parking a ƙofar gate ɗin gidansu Anwar, ga mutane an taro a na ta d’aura rumfuna, duk wata alama da za nuna mutuwa a ka yi a gidan Haneefah ta gan ta, sai dai ko kaɗan ba ta yi tunanin Anwar ne ya mutu ba, ta yi tunanin dai wani dabanne a gidan, tunda mahaifinsu already ya rasu balle ta ce ko shine. Mama ta buɗe Motar ta fita, Neehal ta biyo ta itama ta fito, sai da ta fito ta gane inda suka zo, Mama ta kama hannunta kawai ganin yanda take jujjuya idanunta ta na bin layin da kallo kamar wata doluwa suka nufi cikin gidan, Haneefah jiki a sanyaye ta fito ta bi bayansu. Bin Mama kawai suke zuciyoyinsu na bugawa har suka shiga part ɗin Mahaifiyar Anwar inda suka tarar da Mutane damk’am a falon an yi jugum_jugum, masu kuka na yi masu salati na yi, Kakarsu Anwar ta na hango su Neehal ta rushe da kuka, cikin kukan ta ce, “Allah sarki, ga yarinyar da Anwar zai aura nan, Allah ya ji ƙanka Anwar, Anwar ya saka mana, ya tona asirin azzaluman da suka kashe ka” ta ci gaba da rizgar kukanta, wani irin wul Neehal ta ji a kanta kamar an ɗora mata dutse, k’wace hannunta ta yi daga na Mama ta yi baya za ta faɗi, cikin dauriya Mama ta ruk’ota da sauri, Haneefah kuwa tuni ta durk’ushe a ƙasa dan ƙafafuwanta ba za ta su iya ɗaukar ta ba, jin wai Anwar ne ya mutu.

Mama ta na riƙe da Neehal har suka ƙarasa gurin da Mahaifiyar Anwar take, Neehal ta kwace jikinta daga na Mama ta je ta tsugunna a gaban Maman Anwar ta ce “Ammi ke kaɗai ce za ki faɗa mun Anwar ya rasu in yarda, Ammi dan Allah ki faɗa mun dagaske Anwar ya mutu, dagaske wannan taron na rasuwar Anwar ne?” Ammi ta share hawayen fuskarta ta kama hannun Neehal cikin lallami da dangana ta ce, “Neehal, Allah shi ya bamu Anwar kuma ya fimu sonshi ya karbi abinsa, Addu’a kawai Anwar yake buƙata daga gurinmu” Tunda daga Allah ya karb’i ran Anwar da Ammi ta ce, Neehal ba ta ƙara fahimtar komai da yake wakana ba, sai farkawa ta yi ta ganta a jikin Mama ta na shafa mata ruwa a fuska, ga Haneefah a gefenta ta na kuka, dafe kanta da yay mata mugun nauyi ta yi, ga kirjinta ma kamar an ɗora mata dutse saboda nauyin da yay mata. Mahaifiyar Anwar ta na hawaye sosai ta zo ta d’aga Neehal ta na faɗin “Mu je ki ganshi kafin a fita dashi” Neehal ta bita kamar wani mutum_mutumi jiri na kwasarta su ka shiga wani ɗaki, gawar Anwar ta hango kwance samb’el an gama shiryashi har an sanya shi cikin makara, jini gaba-daya ya ɓata likafanin ta saitin k’irjinsa, wata ƙara Neehal ta k’walla ta ƙarasa inda gawar take a gigice ta fara faɗin, “Anwar dagaske ka mutu, kai ma za ka tafi ka barni, mutuwa me ya sa zaki mun haka, me ya sa za ki ɗauke mun Anwar ɗina, dan Allah Anwar ka tashi kar ka tafi ka barni, ka tashi ka ce musu ba ka mutu ba, ka…..” Mama da ta shigo ɗakin saboda ƙarar da Neehal ta k’walla, ta rufe mata baki, ta na hawaye ta ce “Addu’a za ki yi masa Neehal ba surutai da kuka ba, addu’arki ya fi buƙata a halin yanzu” Neehal ta ture hannun Mama daga bakinta ta ce “To..to, zan masa addu’ar” Ka na ganin yanayin Neehal ka san ba ta cikin hayyacinta a wannan lokacin. Mama ta dubi Ammi dake tsiyayar da hawaye kamar an buɗe famfo ta ce “Wuk’a aka soka masa ne?” Ammi ba ta iya ba ta amsa ba saboda halin da take ciki, sai wani k’anin mahaifin Anwar ne dake tsaye a ɗakin ya ce “Harbin sa aka yi da bindiga” Neehal ta kalli Mama a matuƙar firgice ta ce, “Mama shi ma harb’e mun shi a kai, kamar yadda a ka harb’e mun JAMIL ɗina da…..” Mama da ita ma kalmar Harbin ta firgita ta, ta rungume Neehal a jikinta ba ta ce komai ba, zuciyarta na wani irin bugu. Neehal kuka take a jikin Mama ta na sumbatu na fitar hayyaci. a haka a ka shigo a ka ɗauki gawar Anwar a ka fita da ita dan kai sa gidansa na gaskiya???? (Ya Allah ka sa mu cika da kyau da imani????.)………..✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button