NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan Sallar isha’i Mama suna falon Daddy ita da su Aunty, cikin ɓacin rai da takaici ta dube su ta ce. “Wai ashe Hafsah bata gidan Ameen ta yi yaji?” Aunty A’isha ta ce. “Yaji kuma kamar ya?” Mama ta ce. “D’azu Doctor Rahina wadda muka yi aiki da ita a asibiti take faɗa mun, ashe ƙanwarta ƙawar ƙanwar mahaifiyar Hafsat ɗin ce.” Aunty Sadiya ta ce. “To akan me ta yi yajin? Ko dan zai ƙara Aure ne?” Mama ta ce. “Hmm, ina zan sani, amma Ameen bai taɓa faɗa mun, a yanda Rahinan take faɗa mun zata yi sati uku fa a gida.” Aunty Sadiya ta ce. “Subhallahi, wannan abu bai yi daɗi ba, amma bari na kira Ameen ɗin na ji asalin maganar.” Ta kira shi bai d’aga ba. Mama ta ce. “Gaskiya Ameen bai kyauta mun ba, akan me zai bar yarinya ta daɗe a gida haka? Shi yasa shekaran jiya da nake tambayar sa zata yi taro ya ce mun ta ce baza ta yi ba, ashe yasan tsiyar da ya shuka kenan.” Aunty A’isha ta ce. “Baki san me ta yi masa ba Yaya, kar ki ga laifinsa.” Mama ta ce. “Koma me ta yi masa dai ai haquri ake tunda a da bata taɓa yi masa ba, yanzun ma da dalili ai, duk matar da za’a yi mata kishiya ai sai an yi haquri da ita.” Ta miƙe tana faɗin. “Zai zo ya same ni ne.” Ta shiga ɗakin Daddy ta tarar da Neehal ta zubawa hannunta da ya sha ƙunshi ido tana kalla. A zahiri zaka yi tunanin hannun take kallo, amma a badini tunani take, tunani take daga gobe fa shikenan ta zama matar Ameen, wataƙila ma i yanzu an kaita gidansa. Mama ta ce. “Kina nan ashe inata neman ki ki ci abinci.” Ta sauke numfashi tare yin ƙasa da kanta hawaye ya zubo daga idonta. Mama ta ce. “Kukan ne dai Neehal? Allah ya nuna mun ranar da zaki daina wannan kukan naki.” Kamar zuga ta Maman ta yi sai hawaye sharr kamar an buɗe fanfo. Mama ta ƙarasa ta zauna a gefenta tare da janyo ta jikinta ta ce. “To ya isa haka kukan, ki yi shiru kar kanki ya yi ciwo.” Maimakon ta yi shirun sai ta ƙara fashewa da kuka tana shigewa jikin Maman. Mama ta shiga bubbuga bayanta cikin danne zuciyarta, dan itama idan ta tuno few days idan ta tashi baza ta ga gilmawarta a gidan ba sai ta ji babu daɗi a ranta. Ganin ta ƙi yin shiru ta d’ago fuskarta ta ce. “Haba Neehal ki yi shiru haka mana, ko a akwai wani abun da yake damunki?” Ta girgiza kai cikin kuka ta ce. “Ni bana son barin ki Mama.” Mama ta ce. “Oh Neehal rigima, sau nawa zan faɗa miki dan kin yi aure hakan ba yana nufin kin barni ba ne, kuma ai haka rayuwar take tunda aure ya zama dole, kowa da haka yake sabawa, ki yi haquri kin ji.” Ta ƙarashe zancen tana share mata hawaye. Mama ta ce. “Ina nan ina murna na kusa samun ƴan jikoki daga gurin autata, ita kuma tana damun kanta.” Neehal ta rufe fuskarta da hannunta tare da juyawa Mama baya. Mama ta yi murmushi ta miƙe ta kama hannunta ta ce. “Mu je ki ci abinci, na san baki ci ba.”…….. Yau kam bacci rabi da rabi Neehal ta yi, ƙarshe ma sai tashi ta yi ta ɗauro alwala ta shiga yin nafilfili tana roƙon Allah ya kawo musu komai cikin sauƙi a rayuwar Auransu.

Washegari ranar D’aurin Aure, gida ya ƙara ɗinkewa da jama’a maza da mata. Sai ƙarfe biyu za’a d’aura auren a babban masallacin juma’a na unguwar. Da safe su Ummi suka zo harda matar Ahmad Khadijah da Ahmad ɗin. Neehal bata taɓa tunanin shi kanshi zai zo ba balle matarsa, Khadijan kuwa mai kirki da faran_faran ba ruwanta ta shiga cikin su Haneefah ana ta hira da ita. Batul ƙanwar Sadik ma wajen sha biyu na rana ta zo, ta ce su Maamah ma suna hanya. Sai da Neehal ta gan ta sannan ta tuna da kuɗin da Sadik ya turo mata ta account a matsayin gudunmawa ta manta bata faɗawa Mama ba, sai a lokacin ta faɗa mata, Mama ta ce zata kira shi bayan biki ta yi masa godiya. Tsoro da fargabar Neehal yau ya fi na kullum, dan da mutum zai yi close da ita sosai zai iya jin yanda zuciyarta take bugawa da sauri da sauri. Ta dai daure tunda garin Allah ya waye yau bata yi kuka ba, amma ta kasa cin komai dak’yar ta iya shan ruwan tea kaɗan. Ita da Haneefah da wata Freind ɗinta Zee suka je aka yi mata make up. Ta yi kyau sosai ta fito tsaf a amaryata sai baza k’amshi take. Ƙarfe biyu na rana kamar yadda aka tsara Ubangiji ya nufa aka ɗaura Auren AL’AMEEN MUHAMMAD TAFIDA da FATEEMAH MUHAMMAD GABASAWA. A lokacin Neehal ba su jima da dawowa daga gurin kwalliya ba, ta ji Aunty Sadiya tana an ɗaura, yanzu Uncle Ahmad ya kira ta ya faɗa mata. Bugun zuciyarta ne ya ƙaru ta ji ta a cikin wani irin yanayi da bazai misaltu ba, shikenan ta zama matar Aure matar Ameen. Ta lumshe idonta tana sauraren yanda zuciyarta take bugawa. “Finally an ɗaura, yarinya ta zama matar Aure…” Ta ji muryar Haneefah cikin dariya a kanta tana faɗar haka. Duk yanda taso mayar da hawayen idonta kasawa ta yi sai da suka zubo.

Wajen ƙarfe uku na rana suna part ɗin Ameen na gidan da yake anan ƴan’mata da k’awayen Amarya suka tare tunda aka fara bikin. Afrah ta zo da murnarta ta ɗane jikin Neehal da fara’arta ta ce. “Aunty Uncle ya zo, ya yi kyau sosai.” Amrah ta ce. “Aunty wai shine Ango ke kuma Amarya?” Wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarci Neehal, ta san yanzu za’a ce ta zo su je a yi musu hoto tare da shi, ita kuma gaskiya bata san da idon da zata kalle shi a matsayin Mijinta ba, wani irin feeling na daman take ji a kansa, kunyarsa da tsoronsa sun ƙara cika zuciyarta. Ta janye Afrah daga jikinta da sauri ta miƙe ta shige toilet duk da bata da abun yi a toilet ɗin. Tana ji Aunty Sadiya ta shigo tana neman ta amma ta ƙi fitowa har ta gaji ta fice. Mutun sama da biyar sun shigo neman ta sai a ce musu tana toilet, ita kuma ta ƙi fitowa dan ta san dalilin kiran nata, sai haqura aka yi aka ƙyale ta. Aka cigaba da shagalin biki cikin nishad’i da farin ciki. Hada_hadar mutane yasa Neehal ta ɗan saki ranta, dan da biki ya yi biki ko lokacin Kaɗaita bata samu ba, daga a gaisa da wannan sai a gaisa da wancan. Ga k’awayenta da ƴan gurin aikinsu sun zo mata sosai. Sai can yamma da Aunty A’isha ta zo ta jata part ɗin Daddy zata yi wanka a kaita gidanta ta fara kuka sosai, tana kukan ta yi wanka aka taimaka mata ta shirya. Zuwa lokacin har an fara ɗibar mutane ƴan kai Amarya. Ta zauna a gefen gadon Daddy tana ta kuka a cikin mayafi. Daddy ne da kansa zai kai ta gidanta, ya shigo ya tarar da ita tana kuka su Aunty suna aikin ban baki da ƙara yi mata ƴan nasihohi. Mama kuwa dama ko ɗakin bata tunkara ba, dan ta san idan Neehal ta gan ta kukan da zata yi sai Allah. Shi ma Daddy zama ya yi ya ƙara ɗora mata da nasiha akan zaman aure. Sai bayan ya gama yi mata faɗan za’a fita da ita Mama ta shigo ɗakin. Neehal ta tashi da sauri ta rungume ta tare da ƙara volume ɗin kukanta, duk dauriyar Mama sai da zuciyarta ta karye ta yi hawaye. Da ƙyar Daddy ya janye Neehal daga jikinta ya kama hannunta suka fice tana gunjin kuka.

Gidan Neehal babu nisa sosai, anan cikin Nasarawan ne unguwar badawa. Kafin a ƙarasa da ita wasu har sun fara dawowa. Har ɗakinta har kan gadonta Daddy ya kai ta bayan ya ce ta shiga da ƙafar dama tare da yin Bismillah. Gidanta ya yi kyau ya tsaru sosai, madaidaici ne ba ƙato sosai ba, amma an ƙawata shi da kayan ado da alatu dan har ya fi gidan Hafsat kyau da tsaruwa. Mama da Daddy kuma sun zuba mata kaya na alfarma, kowa sai Masha Allah da sam barka yake. Daddy ya kama hannunta a cikin nasa ya shiga yi musu addu’ar fatan Alkhairi da zaman lafiya a zaman auransu. Mutanen ɗakin na amsawa da Ameen, abun gwanin burgewa. Bayan ya gama ya ɗan bubbuga bayanta ya ce. “Kukan ya isa haka Daughter, ki yi haquri kin ji.” Ta zame daga kan gadon ta durk’usa a ƙasa ta rungume ƙafafunsa tana kuka sosai ta ce. “Na gode, na gode, na gode sosai Daddy, Allah ya biya ku da Aljannah maɗaukakiya, Allah ya saka muku da Alkhairi kai da Mama, bani da bakin godiya a gare ku.” Cikin karayar zuci Daddy ya ce. “Amin Daughter, Allah ya sanya miki albarka ya baki ƴaƴa masu albarka.” Ya ƙarashe zancen tare da d’ago ta ya mayar da ita kan gadon ya zaunar. Ta riƙe hannunshi gam tana hawaye, da ƙyar ya samu ya zare hannunsa ya fice yana jin zuciyarsa babu daɗi sosai. Haneefah ta ajiyewa Neehal ƙaramar jakar akwatin da aka zubo mata kayan da zata yi amfani da su a kusa da ita, tana hawaye ita ma, domin Neehal ta bawa mutanen ɗakin tausayi sosai. Aunty Sadiya ta zo ta rungume ta tana rarrashinta. Da wayo da dabara su Aunty da su Haneefah suka samu suka bar gidan, aka bar ta ita kaɗai k’wal daga ita sai halinta……….✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button