NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ta zo dai_dai layin da suka haɗu da mutumin jiya wanda ta rad’a masa suna Uncle mai kirki , har ta wuce gidan ta dawo ta tsaya a ƙofar gidan tana kallon gidan, a hankali ta ƙarasa jikin ƙofar ta fara knocking, 2 minutes tana tsaye sannan aka buɗe ƙofar. Faɗaɗa fara’a ta yi sosai kamar yadda shi ma yake fara’ar cike da mamakin ganin ta, yana sanye cikin ƙananan kaya wanda suka masa kyau sosai, sai tashi daddad’an k’amshinsa yake. Neehal ta ce “Ina yini.” Yana murmushi ya ce “Lafiya k’alau.” Juya wa ya yi ya ce “Come in.” Neehal ta tsaya ba tare data bishi ba, ya juyo ya ce “Ya kika tsaya? Ki shigo mana.” Neehal ta girgiza masa kai alamun a’a, ya ce “Why?” Ta ce “Ina jin tsoro.” Da ƙyar ya lallaɓa ta ta shiga gidan, a BQ yake har ciki ta shiga ta zauna a falo a d’arare, haɗadd’iyar pride rice ya kawo mata a plate da bottle water da juice, da murna Neehal ta karb’a ta fara ci. Zama ya yi yana kallonta cikin tausayinta. Sai da ta ci ta yi ƙat sannan ta ce “Uncle ina Mamanka?” Ya ce “Tana cikin gida.” Ta ce “Nan part ɗinka ne?” Ya ce “Ehh.” Shiru ta yi tana ƙarewa falon kallo, cikin kulawa ya ce “What is your name?” Neehal ta ce “Neehal.” Ya ce “Wow Nice name, real name ɗinki fa?” Ta ce “Fateemah.” Ya ce “Wow! My mother’s name.” Neehal ta ce “And you?” Ya yi murmushi ya ce “Ahmad.” gyaɗa kai ta yi tare da tashi da sauri ta ce “Zan tafi Uncle, zan siyo wa Aunty kayan miya, idan na daɗe zata zane Ni.” Ya ce “To Princess, gobe ma zaki zo ko?” Neehal ta yi shiru can kuma ta ce “Ehh.” Har bakin titi ya raka ta sannan ya dawo gida. Yau ma data koma gida sai da ta sha bala’in Aunty Fauziyya. Tun daga wannan ranar kullum sai aka aike ta sai ta biya gidansu AHMAD, ya bata lafiyayyen abinci ta ci da drinks, wataran kuma ice cream da snacks yake bata, choculate da sweet kam kullum sai tasha su ta more, idan ta koma gida kuma Aunty Fauziyya tay ta mata masifa, wataran har da duka akan dad’ewar da take, amma ko sau ɗaya bata taɓa tambayarta inda take zuwa ba. Idan ta bawa Neehal abinci sai ta k’ulle a leda ta faki idon Aunty Fauziyya ta fita ta bawa almajiri, tunda yanzu kullum a k’oshe take wuni, abincin dare ma kullum sai ta rage kaɗan take ci. Breakfast kawai take yi full a gidan. A hankali shak’uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Neehal da Ahmad, kullum ta zo yana mata tambayoyi a game da rayuwarta, a haka ya gane marainiya ce kuma bata haɗu da uwar riƙo ta gari ba, hakan ya ƙara masa tausayinta a zuciyarsa sosai, kullum yana mata ƙarin haddarta na Alqur’ani tunda Uncle Umar ya ƙi saka ta a Islamiyya da School, haka karatun boko kullum yana mata lesson, sai ta yi fiye da awa biyu a gidansu, ta koma gida kuma ta ci duka, amma duk da haka gobe sai ta karsi zuwa.

Yau Sunday da misalin ƙarfe biyu na rana Neehal tana zaune ita kaɗai a ɗaki tana bitar haddarta, su Aiman kuma sun tafi Islamiyya. Uncle Umar ma baya nan, duk da yau Sunday amma ya fita tun safe shagonsa da yake sayar da kayan masarufi, kuma ba ya dawowa sai dare, kullum haka yake dama, Monday to Friday ma bayan sun tashi daga School ɗin da yake koyarwa can shagon yake wuce wa. Aunty Fauziyya ta tak’wala wa Neehal kira, Neehal ta miƙe da sauri ta fito waje. Aunty Fauziyya tana mata wani mugun kallo ta cilla mata kuɗi ta ce “Ɗauki kuɗin nan, ki je ki siyo mun kayan miya, kuma yau ma ki biya yawon naki da kika saba, wallahi dukan dana miki jiya Nafila ne akan wanda zan miki yau idan kika daɗe. Neehal ta ɗauki kuɗin ta koma ɗaki ta ɗauko Hijab da hula ta saka sannan ta fito ta tafi. Duk da gargadi’n da Aunty Fauziyya ta mata sai da ta biya gidansu Ahmad, dan dukan Aunty Fauziyya zuwa yanzu har jikinta ya saba da shi. Kamar kullum bayan ta yi knocking ya zo ya buɗe mata ƙofa ta shiga. Yau ba BQ ya kai ta ba, ainihin cikin gidan ya nufa da ita. A falon gidan ya zaunar da ita sannan ya nufi kitchen yana kiran sunan Mamy, Mamy wadda takasance ƙanwar mahaifiyar Ahmad ta fito daga kitchen tana amsa masa. Ya tsaya tare da faɗin “Sannu da aiki Mamy.” Mamy ta ce “Yawwa son.” Nuna mata Neehal ya yi ya ce “Ga yarinyar da nake baki labarinta na kawo miki ita.” Mamy ta washe baki tana duban inda Neehal take ta ce “Ita ce wannan, Masha Allah, ga ta kyakkyawa da ita.” Ta ƙarasa kusa da Neehal ɗin, Neehal ta durqusa ta ce “Ina yini Mama.” Mamy ta ce “Lafiya k’alau, sannunki yarinya ya sunanki?” Ta ce “Neehal.” Mamy ta ce “Masha Allah, Allah ya miki albarka ya inganta rayuwarki.” Ahmad dake tsaye yana fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa da “Ameen.” Mamy ta kawo wa Neehal lafiyayyen abinci da ruwa da juice, Neehal ta mata godiya sannan ta zauna ta ci. Mamy sai kallonta take cike da tausayawa, dan Ahmad ya tsakura mata labarin Neehal. Bayan Neehal ta gama cin abinci ta dubi Mamy ta ce “Please Mama ki tsefe mun kaina, na ce Aunty ta tsefe mun ta ce inyi da kaina, ni kuma ban iya ba.” Mamy ta yi murmushi ta tashi ta ɗauko kibiya ta ce Neehal ta cire hijabin jikinta ta tsefe mata, Neehal tana cire Hijab sai ga shatin bulalar jiya ruɗu_ruɗu a jikinta, kasancewar hannun rigar jikinta k’arami ne. Mamy tay salati ta ce “Neehal wa ya dake ki haka?” Neehal ta ce “Aunty ce.” Mamy cikin tsananin ɓacin rai ta ce “Amma kuwa wannan matar bata da imani ko kaɗan, yanzu wannan yar yarinyar ita akewa irin wannan dukan kamar wani qaton gard’in? Wai duniya ina zaki da mu ne, dan bake kika haifi ‘ya ba sai ki dinga zaluntar ta, menene abun damuwa a riqon ƴar wannan yarinyar da za’a dinga azabtar da ita haka?” Cikin takaici Ahmad ya ce “Hmm, kin ga wannan dukan kullum sai an mata shi, kuma Mamy wanke wanke, shara, mopping, wanki ta ce mun kullum ita take yi, sannan tai aike, kuma sun ƙi sata boko da islamiyya.” Mamy ta ce “To kuwa wannan mata ta kiyayi duniya, dan wallahi cutar da Maraya ba ƙaramin abu ba ne, ta kiyayi randa Hakkin yarinyar nan zai kamata, kuma itama uwa ce ta haifa ko zata haifa nan gaba, kuma ba ta san inda ƴaƴanta zasu ƙare rayuwarsu ba, tunda ba’a mata alƙawari zata rayu da su har abada ba.” Sosai ran Mamy ya ɓaci tai ta faɗa kamar zata ari baki, da gidan Fauziyyan ma ta ce zata je ta mata tatas duk da bata san ta ba, da ƙyar Ahmad ya taushe ta ta haqura ta fasa zuwan. Tass ta tsefe wa Neehal daddaud’an kanta da tunda ta dawo gidan Uncle Umar kusan 2 months Sau ɗaya wata mak’ociyarsu ta taɓa mata kitso. Mamy ta wanke mata kan tass ta busar da shi ta shafa wa gashin mai, ta mata wanka ta shafe mata jiki da mai, har yankan farce da cire dattin kunne sai da Mamy ta mata ranar. Tana yi tana mitar baƙin ciki Aunty Fauziyya take dan ta ga Neehal kyakkyawa ce shi yasa bata kula da ita. Ahmad kam daga baya dariya Mamy’n ta fara ba shi da mitartata, sai ga Neehal ta fito fess da ita sai k’amshin turaren da mamy ta saka mata take. Sai wajen ƙarfe biyar Ahmad ya raka Neehal ta siyo kayan miyan, suna tafe yana ta aikin maimaita mata “Ta yi kyau sosai.” Dan har cikin zuciyarsa ta masa kyau ba kaɗan ba. Ita kam Neehal sai dai tay masa murmushi kawai. Har kusa da layinsu ya rakata sannan ya juyo, ita kuma ta ƙarasa gida……….✍️

Yau ban yi edit ba, sorry for the typed error.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button