NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:34] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

1️⃣4️⃣

……….. Neehal duk da ta ga irin kallon da Hafsat ta mata amma ta danne zuciyarta ta rungume ta, sai dai jikinta ya yi sanyi ba kaɗan ba. Kamar yadda ta rungume Hafsat haka ta rungume Fadeelah. Fadeelah da ba ta ji daɗin abun da Hafsat ta yi ba ta yi murmushin ƙarfin hali ta ce “Ai na yi fushi, tunda Aunty’nki kawai ki ka sani ita ki ka fara tarb’a.” Neehal ta yi murmushin yaƙe ta ce “Sorry ai kema Auntyna ce.” Fadeelah ta yi murmushi dan sosai ta ji ta na son Neehal, yarinyar ta burgeta daga gani ba ta da d’abi’ar wulak’anta mutane duk da kasancewar ta celebrity. Neehal ta ce “Mama ta na sama mu ƙarasa.” Fadeelah ce kawai ta amsa mata suka mik’e suka bi bayanta, Hafsat sai hararar bayan Neehal take. Neehal ta shiga d’akin Mama ta sanar mata da isowarsu sannan ta fito ta wuce ɗakinta. Kafin Mama ta fito Fadeelah ta ce wa Hafsat “Haba Hafsah, gaskiya ban ji daɗin abun da ki ka yi wa yarinyar nan ba ko kaɗan wlh.” Hafsat ta mata wani kallo ta ce “Yarinyar ba ta mun ba ne shi ya sa.” Fadeelah ta ce “Hmmmmm, me yarinyar nan ta yi da za ki ce ba ta miki ba? Yarinya ta taho da murnarta da ɗokin ganin ki ka amma ki mata wannan wulak’ancin, gaskiya ban ji dad’i ba.” Hafsat ta tab’e baki ba ta ce komai ba, domin ita kaɗai ta san baƙin cikin dake cin ranta na ganin Neehal, ashe duk kyawunta da mutane suke faɗa na ganin da suke mata a TV a fili tafi haka, yarinya ga dirin jiki kamar ita ta yi kanta, tafiyar ta ma kaɗai abun kallo ce ga zazzak’ar murya…. Fitowar Mama ya katse mata tunanin da take. Cikin girmamawa suka ɗan zamo daga kan kujerar da suke suna amsa sallamar da Mama ta musu. Mama ta zauna ta na faɗin “Sannun ku da zuwa.” Suka amsa da yawwa tare da gaisheta, Mama ta amsa musu cikin fara’a ta ƙara da faɗin. Ya mutanen gida.?” “Suna lafiya, suna gaishe ku.” Cewar Fadeelah. Mama ta ce “Masha Allah, muna amsawa.” Hafsat dai kanta na ƙasa ta na satar kallon Mama, domin Maman kamar ba ta tsufa, a ‘yan shekarun da ta yi ba ta ganta ba sai ta ga ta ƙara kyau da gayu, ba za ka taɓa cewa ta haifi Ameen ba. Mama ta mik’e ta na faɗin “Bismillah ku ƙarasa dinning ku ci abinci, bari na kira Neehal ta yi sarving ɗinku.”

Neehal ta na shiga ɗakinta ta zauna a bakin gado hannunta dafe da kanta, mamaki take sosai a kan abun da Hafsat ta mata, dan ta ji haushi ba kaɗan ba kawai ta danne zuciyarta ne, domin ita mutum ce wadda bata son wulak’anci ko kaɗan kuma ba ta son a yi mata, hakan ya sa itama ba ta yi. Kawar da tunanin Hafsah ta yi daga ranta ta na ƙoƙarin tashi kira ya shigo wayarta, ta daga tare da karawa a kunnenta. Cikin daddad’ar muryarshi ya mata sallama, Neehal ta amsa tare da faɗin “Ina yini Yaya.” Ameen ya ce “Lafiya k’alau, su Hafsat sun zo kuwa.?” Neehal ta ce “Ehh.” Ya ce “Ok” tare da kashe wayar, ya bar Neehal da mitar faɗin ya kira Hafsan mana ya tambaye ta.

Su Hafsat sun ɗan jima a gidan Mama kafin su tafi, sosai Neehal suka sha hirarsu ita da Fadeelah, dan da ta fito ma ko ƙara kallon inda Hafsat take ba ta yi ba, hakan kuwa ya burge Fadeelah dan ko ba komai Neehal ta nunawa Hafsah tafi ƙarfin raini. Da za su tafi Mama ta basu turaruka da kayan kwalliya. Suna Mota Hafsat ta dinga yi wa Fadeelah masifa a kan wai me yasa ta sakarwa Neehal fuska su ka yi ta hira kamar wata sa’arta salon ta jawo ta rainasu. Fadeelah kallon Hafsat kawai ta tsaya ta na yi cike da mamakinta, kawai daga ganin mutum sai ka ɗauki k’iyayya ka ɗora masa ba tare da wani dalili ba.?”

Bayan Magriba Mama ta na kitchen Dije ta zo ta sanar mata ta yi bak’o, Mama ta ce ta je ta shigo da shi gata nan zuwa. Ta na fitowa falon ta ga ashe Sadik ne. Ta na dubansa ta ce “Sadik ashe kai ne?” Ya ɗan sosa kai kansa na ƙasa ya ce “Ni ne Mama.” Mama ta ce “Shine kuma ka tsaya a waje ba za ka shigo ba, sai ka ce wani bak’o.? Sadik ya yi murmushi kawai tare da gaishe da Mama, Mama ta amsa cikin fara’a sannan ta mik’e ta hau sama dan ta kira masa Neehal. Neehal ta na duba abu a system Mama ta shigo d’akin ta ce “Ba ki gama abun da ki ke ba har yanzu?” Neehal ta ce “Ehh, amma na kusa.” Mama ta ce “To ki sauko ƙasa kin yi bak’o.” Neehal ta d’ago da sauri ta na duban Mama da mamaki ta ce “Mama bak’o kuma?” Mama ta ce “Eh, ya na ƙasa ya na jiran ki.” Ba ta jira amsar Neehal ɗin ba ta juya ta fice. Neehal ta mik’e ta na turo baki ta ɗauki Hijabinta ta zira ta sauka ƙasan. Babu kowa sai shi kaɗai ya na latsa wayarsa, Neehal ta ƙaraso cikin falon ta na kallonsa, a hankali ya d’ago kansa suka haɗa ido, gaban Neehal ya yanke ya fadi. Ƙasa ta yi da kanta da sauri bugun zuciyarta na sauyawa, dama tun da ta shigo falon ta ji kamar tasan baƙon k’amshin da ta ji a falon, ashe shine. Zama ta yi a kujerar dake fuskantar sa kanta na ƙasa ta ce “Ina yini.” Ba tare da ya ɗauke idonsa daga kanta ba ya ce “Lafiyar k’alau, ya aiki.” Neehal ta ce “Alhamdulillah.” Shiru suka yi na tsawon mintuna biyu, Sadiƙ ya katse shirun nasu da faɗin “Kun kusa komawa school ko?” Neehal ta ce “Ehh.” Ya ce “Yaushe.” Cikin k’osawa ta ce “This coming Monday.” Sadiƙ ya jinjina kai ya ce “Allah ya taimaka.” Suka ƙara yin shiru na wasu mintuna, Sadik ya na lura da Neehal gabad’aya a takure take sai turo baki gaba take. Neehal ganin bashi da niyyar tafiya ta ɗan d’ago kanta ta ce “Gashi kuma ka zo k’anwar taka ba ta nan.” Sadik ya yi murmushi ya ce “Ok, you mean Ke ba k’anwata ba ce.?” Neehal ta yi shiru tare da ƙara mai da kanta ƙasa, Sadik ya ƙara yin murmushi ya ce “Shikenan bari in tashi in tafi.” Neehal cikin shagwab’arta da ta zame jiki ta ce “Am sorry ba haka nake nufi ba.” Ya ce “To ya.?” Ta yi shiru ta na wasa da yatsun hannunta dan ba ta da abun cewa. Mama ce ta sakko ƙasa za ta ɗauki abu, da mamaki a kan fuskarta ta ce “Neehal ya ba a kawo masa ruwa da abinci ba.?” Kafin Neehal ta yi magana ya riga ta da faɗin “Ba komai Mama a k’oshe nake ma.” Mama ta ce “No, ba za a yi haka ba, Neehal tashi ki kawo masa abinci.” Neehal ta mik’e a hankali ta nufi kitchen, Mama kuma ta ɗauki abun da za ta ɗauka a falon ta koma sama. Neehal ta fito da k’aton tire a hannunta ta ajiye a gaban Sadik, sannan ta koma ta ɗakko drinks ta kawo masa. Shi dai kawai bin ta yake da ido. Neehal ta koma ta zauna, ganin bashi da niyyar taɓa abincin ta ce “Ka ci mana.” Ya ce “Na k’oshi.” Neehal ta marairaice ta ce “Dan Allah Ya Sadik ka ci, idan ba ka ci ba Mama faɗa za ta mun.” Ya yi murmushi a karo da yawa ya ce “Shikenan zan ci.” Neehal ta yi murmushin itama. Ruwa kawai ya tsayaya ya sha, Neehal tayi_tayi ya ci abincin amma ya ƙi, dole ta hak’ura ta k’yale shi. Jin an fara kiran Sallah ya mik’e ya na faɗin “Ni zan wuce.” Neehal ta ce “Bari na kira Mama ku yi sallama.” Ya ce “A’a ki ce mata na wuce kawai.” Neehal ta ce “Sai da safe ka gaida gida.” Daga haka ta wuce sama. Ɗakin Mama ta leƙa ta sanar mata ya tafi. Mama ta ce “Ok, zan kira shi, kema ya kamata later ki kira shi ki ji ya ya koma gida.” Neehal ta ce “To” kawai, amma ita Mama ba ta ma san ko Number’nsa ba ta da shi ba. Ɗakinta ta koma domin yin Sallah.

Bayan ta idar da Sallar, ta ɗakko wayarta da niyyar kiran Haneefah ta faɗa mata Sadik ya zo sai ta tarar da missed call d’in Ameen har 3, waro manyan idanunta ta yi cikin mamaki dan ta san ze yi wuya ka ga ya kira ka ba ka d’aga ba kuma ya ƙara kiran ka, amma gashi ita ya mata har 3 missed call. Bin bayan kiran ta yi, ringing biyu ya d’aga tare yin da sallama. Neehal ta amsa masa ta ƙara da faɗin “Ina yini Yaya.” Ameen bai amsa mata ba, sai cewa ya yi “Ina ki ka shiga.?” Neehal ta ce “Ina ƙasa wayar kuma ta na sama a ɗakina.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button