NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

I’m sorry, na san kuna ta jirana, tun rana na yi typing amma network ya ban matsala, sai yanzu na samu ya yi. Thank you so much masoyan Neehal, ina jin daɗin yanda kuke k’aunar book ɗin nan, masu mun magana a PC da masu kirana da masu magana a group suna cikiya ta ina godiya sosai da kulawa, alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke masoyana na.????????????

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

8️⃣1️⃣

Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.

……….Tana mita a ranta an saka ta wanka alhalin bata dad’e da yi ba sai ka ce wata kwad’uwa ta yi wankan ta gama. Sai kuma ta ji jikinta ya yi mata daɗi, ta ɗauki zanin data cire ta d’aura ta yafa d’ankwalin kayan akanta ta fito. Ganin baya nan ta saki sassanyar ajiyar zuciya tare yin sauri ta ƙarasa ta yi locked ƙofa. Ta dawo ta zauna a bakin gado ta janyo jakar da Haneefa ta ajiye mata ta buɗe dan duba abun da zata sakawa jikinta mara nauyi dan baza ta iya bacci da atamfa ba. Wasu kayan bacci ta fara cin karo da su riga da wando, rigar idan ta saka ta ko cibiya baza ta rufe mata ba, wandon kuwa ba shi da maraba da pant, ga kayan sharara, ta ɗaga su a hannunta tana kallon su cikin takaici, bata ma san time ɗin da Haneefah ta sako mata su ba, watsar da su ta yi a gefe tana jan tsaki. A fili ta ce. “Wa ake tunanin zai saka wannan kayan? Ba dai Neehal ba.” Ta cigaba da duba jakar, Allah ya taimake ta ta samo wata doguwar rigar bacci mai ɗan santsi. Ta ajiye ta a gefe sannan ta mayar da kayan data fito da su ta yi zipping jakar ta rufe. Cikin sauri ta zira rigar ta ɗaura zanin jikinta akai, sannan ta tashi ta kashe light ɗin ɗakin ta kwanta tare da lumshe idonta. A ranta tana mamakin yau ita ce zata yi bacci akan gadon gidan Aurenta, ta ƙara yarda komai yana da lokaci a rayuwa. Bacci ya ɗan fara fizgarta kamar a mafarki ta ji ya buɗe ƙofa ya shigo, ta buɗe idonta da sauri gabanta na faduwa amma bata motsa ba. Ya kunna light hakan yasa ta yi saurin mayar da idonta ta rufe. Da alama shi ma wanka ya yi, dan ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya ash colour. Ya ƙaraso bakin gadon ya zauna tare da ɗora hannunsa a goshinta ya ce. “Jikinki da zafi har yanzu, ki tashi ki sha magani.” Ta ƙudundune jikinta guri ɗaya tare da buɗe idonta kaɗan ta ce. “Bacci nake ji, idan na yi bacci zan ji ni normal.” Bai ce komai ba ya tashi ya fita ba tare da ya kashe mata light ɗin ba, ta bishi da kallo sannan ta lumshe ido ta koma baccin dake cin ta. Ya ɗan jima sannan ya dawo ɗauke da sabon duvet, ya lullub’a mata a jikinta sannan ya je ya rufe ƙofa ya dawo ya kashe light ya kunna bedside lamp. A hankali ya hau kan gadon ya kwanta ya shiga cikin bargon tare da janyo ta jikinsa, ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da lumshe idonsa yana ƙara cusa fuskarsa a jikinta dan sosai ƙamshin jikinta ya yi masa daɗi tare yin tasiri a gare sa. Ta motsa tare da buɗe idonta a tsorace saboda yadda ya ƙwaƙume ta a jikinsa, dama baccin ba wani nisa ya yi ba. Ta zare jikinta da sauri ƙirjinta na dokawa a million ta tashi zaune tana keɓe fuska kamar zata yi kuka. Ya ɗan ɗago yana kallon fuskarta ta cikin ɗan hasken bedside lamp, shi dariya ma ta bashi yanda ta yi da fuska kamar wadda ta ga dodo ko fatalwa saboda tsoro. Ya kama hannunta a hankali ya ce. “What happening?” A shagwabe ta ce. “Bacci fa nake ji sosai, dan Allah Yaya ka koma ɗakinka ni bazan iya bacci kana nan ba.” Ya janyo ta gaba-d’aya ta faɗa jikinsa ya saka hannunsa ya matse ta, yana jin yanda jikinta yake rawa saboda tsoro. Ɗayan hannun nasa ya kai kanta ya shiga shafa gyararren gashin kanta slowly. Dai-dai kunnanta ya kai bakinsa ya ce. “Relax, babu abun da zan miki.” Ta buɗe baki zata yi magana ya hana ta ta hanyar ɗora finger ɗinsa akan lips ɗinta ya ce. “Shiiiii…..Just sleep.” Ta turo baki tare da lumshe idonta tana sakin ajiyar zuciya a hankali. Mamakin Ameen take ba kaɗan ba, ko kaɗan bata yi tunanin zai kalli ɗakin da take ba ma a yau a yanda yake nuna mata a baya balle har ya shigo su kwana tare, shi yasa babu fargaban hakan ko kaɗan a ranta, amma yanzu ya dasa mata fargabar, sai faman mammatse jikinta take guri ɗaya kamar wacce take kwance kan a ƙaya, a matuƙar tsorace take sai faman jan numfashi take tana saukewa. Saboda tarin gajiya da ciwon kai da baccin dake kanta cikin mintuna ƙalilan bacci ya kuma ɗauke ta ba tare data sani ba. Ajiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta, ya ɗan rabata da jikinsa tare da gyara mata kwanciyarta, ta wani dunk’ule jiki kamar dafaffiyar kaza. Ya tsurawa fuskarta ido yana sakin murmushi shi kaɗai, yanda yake jin kansa a yau ba zai misaltu ba, sosai yake cikin farin ciki da nishad’i gami da annashuwa. Ya saka finger ɗinsa guda ɗaya yana zagaye lips ɗinta da shi, zabura ta yi amma bata farka ba, ya ƙara yin murmushi ganin gaba-d’ayanta a tsorace take. Imagine yanda bata jin daɗin jikinta a yanzu ya yi mata wani abu, ya san idan bata fasa masa kunne da ihunta ba to sai an jiyo kukanta a mak’wabta. Yanda take uwar raki, ko yaya ciwo yake ta yi ta kuka kenan, ina kuma ga ya yi mata abun da ya san dole sai ta ji jiki. Bai san tsawon lokacin da ya ɗauka yana kallon ta tare shafa kanta zuwa fuskarta ba cikin shauƙi, a haka dai bacci ya ɗauke shi.

Da asuba kusan makara suka yi saboda dukkan su da tarin gajiya a jikinsu. Ameen ne ya fara tashi lokacin har an shiga Sallah, ya tashe ta sannan ya shiga toilet ya yi alwala a gaggauce ya tafi masallaci. Daƙyar ta iya tashi dan ji ta yi kamar ta koma ta cigaba da baccin, dan bai ishe ta ba. Ta dai cize ta tashi ta shiga toilet ta yo alwalar ta fito ta ɗauko hijabi a cikin jakar kayanta ta zira ta tayar da Sallah. Bayan ta idar ta ɗauko wayarta a cikin hand bang ɗinta ta yi karatun Alkur’ani tare da azkar ɗin safe, Alhamdulillah ta ji sauƙin jikin nata da ciwon kan sosai. Har gari ya fara haske bai dawo daga Masallacin ba, ta miƙe ta yi locked ƙofa sannan ta kwanta ta koma baccinta. Bata jima da kwanciya ba ya dawo gidan, duk abun da ya san zata buƙata na toilet ya kwaso ya kawo mata, sannan ya cire jallabiyar jikinsa ya hau kan gadon ya jawo ta jikinsa suka cigaba da baccin tare. Wannan karon ta riga shi tashi. Ta buɗe idonta a hankali ta sauke su akan kyakkyawar fuskarsa, baccinsa yake yi hankali kwance. Ta zame jikinta daga nasa a hankali ta tashi zaune, a lokacin ta gane babu riga a jikinsa, ta ƙurawa faffaɗan ƙirjinsa dake ɗauke da farar fata da kwantaccen ƙananun gashi ido. Sai ta ji kamar ta kai hannu ta shafa su amma sai ta kasa. Jin ta take kamar a mafarki, wai yau ita ce kwance gado ɗaya da yayanta akan ƙirjinsa? Abun har yanzu bai daina bata mamaki ba. Ta yunkura da nufin ta sauka ta ji ya riƙo ta, ta kalli fuskarsa da sauri ta ga still idanunsa a rufe suke. Ta yi ƙoƙarin k’wace jikinta ya buɗe idanunsa dake lumshe saboda bacci ya ce. “Where are you going?” Ta yi ƙasa da kanta cikin kunya a ranta tana addu’ar Allah yasa bai san ta tsaya kallon shi ba. A hankali ta ce. “Toilet.” Ya jawo ta jikinsa ya ce. “Me zaki yi?” Ta yi shiru tana rarraba ido cikin tsoro kamar ace kyat ta ruga da gudu. Ya shafi saman idonta ya ce. “Matsoraciya.” Sannan ya sake ta. Ta ɓata fuska tare da sakin ajiyar zuciya ta sauka daga gadon. Tana mitar abubuwan da yake mata a ranta, fargaba fal a cikin ranta na kar abun ya wuce haka. Sai ta fara tambayar kanta ‘anya kuwa Yayanta data sani a da shine na yanzu? Wannan kamar ba Yayanta ba an canza mata wani’ ga abubuwan da yake mata ko kunya ba ya ji, ko dama haka mazan suke ba su da kunya ne? Ta yi mamakin ganin sabon toothpaste da brush da robar jower jel da takarcen sabulan wanke toilet na ruwa, sai kuma sabbun towels guda biyu an yi hanging ɗin su a cikin toilet ɗin. Brush kawai ta yi ta fito, tana son yin wanka amma bata san a yaya zata iya fitowa idan ta yi wankan yana ɗakin ba, sai kawai ta yi fitsari ta wanke toilet ɗin duk da babu dattin komai a cikinsa ta fito. Ta tarar baya ɗakin ya fita sai mayen ƙamshinsa mai kama guri, gaba-d’aya ya gama ɗakin. Cikin murna ta koma cikin toilet ɗin ta yi wanka tana addu’ar Allah kar ya dawo da shi ɗakin har sai ta gama shiryawa. Adduarta ta karɓu kuwa, har ta gama ta fito ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa bai dawo ba, tana cikin d’aura ɗankwali ya shigo ɗakin da sallama, ta amsa masa ba tare da ta juya ta kalle shi ba. Ya tsaya a kanta yana kallon ta har ta ƙarasa ɗaurin nata. Cikin sanyin murya ta ce “Ina kwana?” Bai amsa ba sai tsugunnawa da ya yi a gabanta tare da lek’a fuskarta ya ce. “Kwalliyar ce ba’a son in gani ake boye mun?” Ta rufe fuskarta da hannunta zuciyarta ta fara bugun da take yi mata a duk lokacin da suka yi over close. Ya cire hannun nata ya matsar da fuskarsa daf da tata ya ce. “Wai wannan wacce irin kunya ce da ta ƙi ƙarewa? Ko sai na yi maganinta ne?” Ta shagwab’e fuska tare da turo baki gaba. Ya ƙurawa lips ɗin nata ido, a hankali kuma ya ɗora nasa soft lips ɗin akan nata, bata yi aune ba ta ji ya haɗe bakunansu guri guda ya shiga bata hot kiss. Abun ya zo mata a bazata hakan yasa lokaci ɗaya jikinta ya d’auki rawa, gaba-d’aya ta ƙara firgicewa da al’amarin sa, amma duk da haka sai da sak’onsa ya ratsa dukkan jikinta, ta dinga jin wani irin abu tun daga kanta har tafin ƙafarta yana yawo a cikin jininta. Yanda yake kissing ɗin nata kamar zai cinye mata baki shi yake ƙara tsorata ta, ta yi ƙoƙarin k’wace kanta amma ta kasa, ƙara jawo ta jikinsa ma ya yi alamun ba shi da niyyar bari. Ƙarar knocking ƙofar parlour ce tasa ya sake ta a hankali yana sauke numfashi gami da ajiyar zuciya. Runtse idonta ta yi tana jin kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya, ita kam ta ga ta kanta Ameen zai kashe ta da wannan abubuwan da yake mata. A kasalance ya tashi ya fita daga ɗakin idanunsa har sun fara sauya kala. Ta buɗe idonta a hankali tana jin lips ɗinta kamar har yanzu suna cikin bakinsa, ta kai hannu ta shafa lips ɗin nata tare da lumshe idonta, tana jin jikinta kamar ba nata ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button