NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Sai bayan Azhar ta farka, lokacin Mama ta kikkira wayarta bata ma sani ba. Ta tashi ta ɗauke bedsheet ɗin dake gaban gadon ta kay toilet, sannan ta dawo ta ɗauko wani ta shimfid’a. Ta ɗauki wayarta ta bi bayan kiran Mama, ringing uku ta d’aga da sallama. Neehal ta amsa mata tare da turo baki gaba kamar tana ganin ta, ta ce “Mama nay ta kiran ki baki ɗauka ba, kuma ban da lafiya na kusa mutuwa.” Mama ta ce “Sorry dear, na shiga surgery ne, ciwon ciki ko? Ya jikin naki? Amma dai kin sha maganinki?” Ta ce “Ni ina kwance na kasa tashi, Aunty Zulai ta je ta duba ɗakin ki bata gani ba.” Cikin damuwa Mama ta ce “Subhallahi, amma dai ciwon bai wahalar dake sosai ba?” Ta ce “Na wahala sosai, sai da Uncle Ahmad ya zo yay mun allura sannan ya lafa mun.” Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Allah sarki Doctor ashe ya zo? Allah ya biya shi.” Ta ce “Amin.” Mama ta ce ta je ta ɗauki magungunanta duka dake ɗakinta, ta dawo da su nata ɗakin. Daga yanzu a nan zata na barin su, saboda gaba kar irin haka ta kuma faruwa. Bayan sun gama maganar ta k’waso magungunan ta dawo da su ɗakinta. Duk second ɗaya zuciyarta na bugawa da tsoron punishment ɗin da Ameen ya ce zai mata. Ta sauka upstairs ta tarar da su Afrah baje akan carpet suna bacci, ga chocolate ɗin da Ahmad ya siya musu da suka fita barbaje a kusa da su. Dije ta fito daga kitchen tana duban ta, ta ce “Har kin tashi? Ya jikin naki?” Ta ce “Alhamdulillah, waɗannan bacci su kai kenan.” Ta ce “Eh, da Babansu ya dawo da su zasu hau sama ya hana su, ya ce su zauna a nan kar su je su dame ki. Na kunna musu kallo, sun fara kuma bacci ya ɗauke su.” Ta ce “Ya daɗe da dawowa?” Dije ta ce “Eh, ga magani ma ya kawo ya ce in kin tashi a baki shi ya wuce Abuja.” Sai ta ji daɗin tafiyar tasa, dan idan suka ƙara haɗuwa a yau bata san da idon da zata kalle shi ba saboda kunya.

Sai la’asar Mama ta dawo gida, Neehal ta haye jikinta tay ta zuba mata shagwab’ar ita bata da lafiya, cikinta ciwo da ƙafarta da kanta. duk da ta ji sauqi sosai rigimarta ce kawai. Da Maman ta gaji da mitar ta_ta, sai ta ce bari ta ɗauko allura tay mata, zata ji sauqi. Sai ta bar jikin nata tana faɗin ta ita ta warke ai. Kafin Magriba ta ware abunta tana harkokin ta, sai ɗan abun da baza a rasa ba. Da yamma wasu daga cikin abokanan aikinta mata suka zo suka duba ta.

Bayan Magriba ta yi wanka ta shirya cikin wata brown abaya mai kyau, ta yi kyau amma fuskarta ta yi fayau saboda cutar ta da ta yi. Ta fesa sassanyan turarenta mai daɗin k’amshi. Su Afrah suka mak’ale mata dan a zaton su fita zata yi. Ta zauna tana latsa wayarta kafin Sadik ya ƙaraso. Amrah ta ce “Aunty Unguwa zamu?” Ta ce “A’a.” Bayan abun da bai fi mintuna biyu ba Sadik ya kira ta ya sanar mata ya ƙaraso. Ta miƙe ta kama hannun yaran suka fita. A falon sama ta tarar da Mama tana operating system. Ta saki hannun yaran tare da faɗin “Mama ga ƴan tayin aiki na kawo miki.” Mama ta d’ago ta dube ta, ta ce “Sadik ɗin ya zo ne?” Ta ce “Eh.” Mama ta ce “Sai ki ɗauki drinks ki tafi masa da shi, tunda ke ki shiga kitchen ki yi masa ko da snaks ne ma baza ki iya ba saboda ganda, sai dai mutum yay ta zuwa yana tafiya haka.” Ta turo baki ta ce “To Mama baki ga ban da lafiya ba.” Mama ta ce “Haka ne, duk watannin da ya yi yana zuwa ma a cutar kike ai? Wuce ki tafi ni kar yay ta jiran ki.” Ta ɓata fuska, Afrah ta ce “Aunty zan biki.” Mama ta ce “Ku zauna a nan, zata je gurin Uncle Sadik ne.” Suka koma suka zauna kusa da Mama ita kuma ta fice bayan ta ba su wayarta ta ce su yi game. Bayan ta ƙarasa inda suka saba zama, ta gaishe shi cikin mutuntawa ya amsa tare da tsokanarta kamar yadda ta saba har ta yi fushin wasa, shi kuma ya rarrashe ta. Sai da suka shirya sannan ya gyara zama yay mata tambayar dake damun sa a rai. “Neehal Please dan Allah karki ɗauki tambaya da wata manufa i want know something ne.” Ba tare da tunanin komai ba, ta ce “Karka damu Ya Sadik, ka tambaye ni ko me kake so, ni kuma indai na sani Insha Allahu zan baka amsa.” Ya sauke numfashi ya ce “Neehal kafin mu haɗu, na ga sanarwar rasuwar tsohon saurayinki wanda a lokacin ma an kusa bikinku, bayan mun haɗu da ku Haneefah ta ƙara tabbatar mun da hakan, lokacin dana nuna mata ina son ki. Already na riga na san wannan, amma kafin shi akwai wani saurayin naki da ya rasu ne?” Neehal ta ƙura masa ido cikin tsananin bugawar zuciya dan bata taɓa zaton tambayar da zai mata ba kenan. Hawaye masu d’umi suka fara zuba a kan kuncinta, cikin raunin murya mai haɗe da kuka ta ce. “Sadik! Har an kai maka wannan labarin? ko kuma in ce an kai muku kai da ƴan gidanku, har lokaci ya yi da za’a fara yawo da ni a gari ana duk wanda zai aure ni kashe shi ake, har lokacin ya yii?” Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi. Gaba-d’aya Sadik ya ruɗe cikin dana sanin tambayar tata ya shiga bata haquri da ban baki, amma ina kuka kawai take yi, dama ta san wannan ranar sai ta zo a rayuwarta, ranar da wani zai zo neman auranta a ce masa ya janye kar ya zama gawa. Da ƙyar Sadik ya rarrashe ta ta yi shiru, sai da ya yi kamar zai rungume ta sannan ta haqura. Cikin tsananin damuwa ya ce “Dan Allah Wifey ki yi haquri, wlh ba da niyyar ɓata miki rai na yi miki wannan tambayar ba, amma mu bar maganar kawai tunda har ta samun ke kuka haka.” Ta ce “Na sani Sadik, na sani kuma ko kaɗan ban ga laifinka ba, tun kafin yau na shirya tarb’ar wannan ranar a rayuwata dan na san dole zata zo. Sadik! Kafin Anwar Jameel ya kawo kuɗin aurena, sai da bikinmu ya rage saura watanni aka kashe shi, aka harbe shi and shima Anwar haka.” Sai ta kuma ta fashewa da kuka. Gaba-d’aya Sadik ya ruɗe ganin yanda take kukan da dukkan zuciyarta, kuka ne irin wanda an fama wa mutum wani gyambon ciwo a cikin zuciyarsa. At the first time a tarayyar su ya kama hannunta, tare da tsugunnawa a gabanta ya fara magana cikin rarrashi. “Dan Allah, Neehal ki yi shiru ki saurare ni.” Ta yi iya yinta ta ga ta bar kukan da take, ya zaro handkerchief ɗinsa ya shiga share mata hawayen fuskarta zuciyarsa cike da matsanancin tausayinta. Da yasan samarinta biyu ne kacal suka rasu Wlh ba zai tambaye ta ba, shi duk a tunaninsa sun kai irin biyar ɗin nan, amma saboda tsabar gulma irin ta mutane har an saka wa rayuwarta ido. Ba tare da ya saki hannunta ba ya ce “Neehal! Ina son ki fiye da yanda nake son kaina, komai rintsi komai wuya ba zan taɓa iya rabuwa dake ba, ki saka wannan a ranki.” Ta kalle shi cikin wadataccen hasken dake wurin, cikin raunin murya ta ce “Bana son na rasa ka Sadik, bana son kaima a kashe mun kai.” Ya ce “Allah ne mai rayawa da kashewa Neehal, kisa a ranki zamu yi aure kamar yanda kowanne masoya suke yin auransu, jikina yana bani zamu yi aure, mu rayu cikin farinciki da annashuwa, har ma da tuk’wucin kyawawan yara kamar ki da yardar Allah.” Ta sauke ajiyar zuciya tare da zare hannunta daga cikin nasa, tana jin sanyi ya fara ratsa zuciyarta. Sadik ya cigaba da faɗa mata daɗaɗan kalamai masu kwantar da zuciya, gami da ƴar nasiha. Lokaci ɗaya ta ji ta samu nutsuwar zuciya, ta kuma tabbatar Sadik ya cancanci zama miji a gare ta, ko dan tarin Alkhairinsa da k’aunarsa a gare ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button