NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

………..Ba ƙaramin kaɗuwa da firgita Neehal ta yi ba da ganin Uncle Umar, juya wa ta yi ta falfala a miliyan ta nufi gida. Ahmad dake tsaye yana kallonta ya cika da mamakin abun da yasa ta gudu da firgita lokaci ɗaya, bai gama mamakin ba ya ji tsayuwar babur a gabansa kamar yaƙi, kafin ya yi magana Uncle Umar ya sauko daga kan babur ɗin, yana ƙarasa wa kusa da shi bai yi wata_wata bae ya cakumi kwalar rigar Ahmad cikin zaro ido waje ya ce “Kai ne kake hure wa ƴata kunne dama, munufinki Allah yau Allah ya toni asirinka, kune irin mutanen nan masu ɓata ƴaƴan mutane wato, to ka sani wallahi sai na yi shari’a da kai, kotu ce zata raba mu.” Kallon shi kawai Ahmad yake yi cikin rashin fahimta, k’wace jikinsa ya yi ya ce “Malam lafiya zaka zo ka ci kwalata kana faɗar maganganun da ban gane musu ba tare da jifana da munanan kalamai.” Uncle Umar dake kallon gidansu Ahmad ganin gidan ƙato yasa ya yi baya dan ya san bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne. A harzuk’e yake faɗin “Zama ka gane ne, idan ka ga sammaci.” Babur ɗinsa ya hau a fusace ya tayar da shi ya nufi gida. Ahmad ya tab’e baki sannan ya juya ya shige gida, a zuciyarsa yana Addu’ar Allah ya kare Neehal daga muguntar waɗannan azzaluman mutanen ya kuma hana su cutar da Ita.

Da gudu Neehal ta shiga gida ta yi ɗaki dan neman gurin b’uya, domin ta san idan Uncle Umar ya kama ta yau mai k’watar ta a hannunsa sai Allah. Aunty Fauziyya jin motsinta ta fito daga ɗakinta, jijjiga kai ta hau yi ta ce “Sannunki, shegiya karuwar banza, ƴar ƙaramarki dake kin san bin maza, to yau zan yi maganinki dan Uwarki, gaban naki zan k’ona sannan in miki tsarki da jajjageggen attaruhu, sai in ga da abun da zaki yi iskancin gobe.” Ta ƙarasa zancen tare da fizgo Neehal da ƙarfi. Neehal ta fasa kuka ta ce “Dan Allah Aunty ki yi haquri, wallahi ba zan ƙara ba.” Wani wawan mari Aunty Fauziyya ta zabga wa Neehal. Neehal ta fasa ƙara ta ce “Wayyo Allah, Ummanah, Auntynah….” Wani marin Aunty Fauziyya ta ƙara kifa mata wanda yasa ta kifawa a ƙasa, Aunty Fauziyya ta ce “Uwarkin da Aunty’n su zo su cece mana shegiya mai kama da aljanu.” Tsakar gida Aunty Fauziyya ta fita ta ɗauko wata igiya ta ɗaura a jikin windon kitchen sannan ta dawo falo inda Neehal take durk’ushe har lokacin ta janyo ta kamar wata tinkiya ta ɗaure k’afarta da igiyar, Neehal ta ƙara volume d’in kukanta tana ba ta haquri, amma Fauziyya bata saurare ta ba ta shiga kitchen ta ɗauko wayoyin wutar data haɗa dan zane Neehal. Dai_dai lokacin Uncle Umar ya shigo gidan a babur ɗinsa, kafe babur ɗin ya yi a fusace tare da sauko wa, bai bi takan sannu da zuwan da Aunty Fauziyya take masa ba ya k’wace wayar hannunta ya zabgawa Neehal a ƙafa yana faɗin “Dan Ubanki dama ashe bin maza kike har gida kuna iskanci, tarbiyyar dana baki kenan, yaushe ma aka haife ki da har zaki lalace haka ehe!.” “Wayyo dan Allah Uncle ka yi haquri ba zan kuma ba, wayyo Allahna, Abbana…….” Magiyar da Neehal take ta masa kenan cikin kuka, amma ya rufe idonsa ya dinga tafkar ta da waya. Aunty Fauziyya daɗi kamar ya kashe ta, duk wani makusancin Neehal a duniya sai da ta kira shi sunansa dan ya neman taimakonsa saboda azabar duka, tun tana kuka da da ƙarfin murya har muyar ta dashe. Wata mak’ociyarsu mai suna Binta wadda ta taɓa yi wa Neehal kitso ce ta shigo gidan a guje saboda ihun Neehal da take jiyo wa, ganin yanda Uncle Umar yake tafkar ta kamar an aiko sa yasa ba ta san lokacin data ƙarasa ta hankad’e shi gefe ba. Uncle Umar ya taso a fusace ya ce “Ki ƙyale ni in kashe ta data jawo mun abun kunya.” Matar tana hawaye ta ce “Ba zan ƙyale ka ba, Kuma wallahi baza ka ƙara dukan yarinyar nan ba, sai dai ka haɗa ka dake mu tare.” Ta fashe da kuka ta ce “Wannan wanne irin zalunci ne da rashin imani? Me yarinyar nan ta muku kuke azabtar da ita haka? Idan baza ku iya roqon ta ba kukai ta gurin waɗan da zasu iya mana, wallahi da wannan muguntar da kuke mata gara ta gwammace a gidan marayu ta tashi.” Uncle Umar da sai huci yake kamar zaki ya yar da wayar hannunsa ya ja ƙwafa ya fice daga gidan. Aunty Fauziyya ta dubi Binta ta ce “Hmmm, Maman ikram dan baki san abun da yarinyar nan ta yi ba ne, da kin san abun da ta yi da kin bar Baban Iman ya cigaba da dukan ta.” Binta ta ce “Ko me ta yi bata cancanci wannan cin zalin ba, kuma wallahi sai Allah ya saka mata, haqqin yarinyar ba zai taɓa barin ku ba.” Aunty Fauziyya ta tab’e baki ta ce “Bin maza fa take dan….” “Sai dai ki gani akan ƴaƴanki Insha Allahu wannan alkaba’in ba dai akan marainiyar Allah ba, kuma ko wanne hali yarinyar ta shiga laifinku ne, kun quntata wa rayuwarta da izaya da matsi haka kawai saboda ba ku kuka haife ta ba. Me tay muku? Me ta tsare muku a rayuwa? Wallahi ku bi a hankali da duniya, kuma ku ma kun haifa indai ƴaƴa ne, kuma baƙu san hannun wanda ƴaƴan nawku za su faɗa ba tunda rayukanmu ba a hannunmu suke ba, inda iyayen yarinyar nan suka je kuma zaku je ne, ina jiye muku ranar nadama da dana sani akan cutar da yarinyar nan da ku kai, ku kiyaye gamuwarku da Ubangiji Fauziyya daga ke har mijin naki.” Aunty Fauziyya ta ɓata fuska ta ce “A’a, a’a Binta kar kuma ki yi wa ƴaƴana baki, ki faɗi duk abinda zaki faɗa amma kar ki kuma jawa ƴaƴana alkaba’i gaskiya ba zan ɗauka ba.” Binta ta bita da kallon tausayin bin rud’in shaid’an da take wanda har take ganin hakan kamar ba komai ba ne. Ba ta kuma cewa komai ba, ta juya ta tallafo Neehal jikinta tare da kiran sunanta, amma ko motsawa ba ta yi ba, balle ta amsa. A gigice Binta ta shiga jijjiga ta tare da kiran sunanta cikin bugawar zuciya ganin babu alamar numfashi a tattare da ita. Dai_dai lokacin Uncle Usman ya yi sallama tare da shigo wa gidan………..✍️

Da babu gwara ba daɗi

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:47] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

3️⃣2️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

……….Aunty Fauziyya ta amsa masa sallamar cikin mamakin ganin sa a dai-dai wannan lokacin, Uncle Usman da idansa ya sauka akan Neehal wadda Binta keta jijjiga ta a jikinta. Da sauri ya zubar da manyan ledodin dake hannunsa a ƙasa yana tambayar “Lafiya me ya same ta?” Binta tana hawaye ta ce “Dukan tsiya ya mata, wanda har ya kai ta ga suma.” Wani irin sarawa Uncle Usman ya ji kansa ya masa, yana ɗago Neehal daga jikin Binta ya ce “Duka kuma? Wa ya dake ta?” Binta ta ce “Babansu Aiman.” Uncle Usman ya yi shiru kawai yana bin jikin Neehal da kallo, ganin yanda shatin duka ya fito b’aro_b’aro a jikin lallausar fatarta, wadda wahala ta sa yanzu ta fara canzawa. Lokaci ɗaya idanunsa suka kad’a tsantsar ɓacin rai ya bayyana akan fuskarsa. Cikin rawar jiki ya miƙe da Neehal a jikinsa amma sai ya ji sun koma ƙasa, da mamaki ya kalli k’afarta wadda a zatonsa wani abun ne ya riƙe ƙasan kayanta amma sai ya ga ashe ɗaure mata ƙafar akay. Cikin sauri Binta ta kwance mata igiyar tana Allah wadaran hali irin na Uncle Umar da Aunty Fauziyya. Wani kallo Uncle Usman ya yi wa Aunty Fauziyya sannan ya fice daga gidan cikin k’unar zuci. Aunty Fauziyya ta dubi Binta rai a haɗe ta ce “Kin ji daɗi kin haɗa ƴan’uwa uwa ɗaya uba ɗaya.” Binta kamar zata tanka mata sai kuma ta fasa ta fice daga gidan. Aunty Fauziyya ta ja dogon tsaki ta shige ɗakinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button