NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Long page, amma ban yi edit ba, a yi haquri da typing errors.

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

5️⃣0️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

……….Falo ya koma ya zauna, ya lumshe idonsa hannunsa ɗaya dafe da kansa. Sai aikin taune lip ɗinsa na ƙasa yake alamun something is hurting his heart cikin sauke numfashi kaɗan_kaɗan. Ya fi mintuna goma a zaune ba tare da ya motsa ba, jin an buɗe ƙofar falon yasa ya ɗan buɗe idanunsa kaɗan. Mama ce ta shigo, cikin sanyin jiki ta ce “Ina Neehal ɗin.” Ya d’ago ya dube tare da nuna mata ƙofar ɗakin Neehal ba tare da ya yi magana ba. Bata ce komai ba ta shige ɗakin. Bacci ta tarar Neehal ɗin tana yi wanda ga dukkan alamu bana daɗi ba ne. Ta yaye mata bargon data lullub’a ganin yanda take zufa ga jikinta ya yi zafi zau. Cire mata hijabin jikinta ta yi ta ɗan goge mata gumin fuskarta sannan ta juya ta koma falo. Ta dubi Ameen ta ce “Ka bata Magani ne?” Ya ce “Eh, na ɗauko mata a dakinki.” Mama ta ce “Ashe ka je court? ban ma ga zuwanka ba.” Ya ce “Ina ciki ma kuka zo.” Mama ta jinjina kai ta ce “Ina Hafsat fa, me yasa baku zo tare ba?” Ya ce “Bata jin daɗi ne.” Mama ta ce “Ayya, Allah ya bata lafiya.” Kafin ya amsa Hajiya ta shigo falon tana faɗin “Ina Neehal ɗin ta shiga ne? ko ba gida Aminun ya kawo ta ba?” Mama ta ce “Tana ɗakinta, zazzaɓi mai zafi ne a jikinta, allura ma zan haɗa in mata yanzu.” Hajiya ta ce “Subhallahi, dama jikin nata bai gama warware wa ba, gashi ta je ta jiyo wannan abun tashin hankalin ai dole zazzaɓi ya dawo baya.” Mama ta ce “Allah ya bata lafiya kawai.” Sannan ta nufi ɗakinta. Hajiya ta dubi Ameen ta ce “Au Aminu, ina matar taka ne? Ban ganta a kotu ba, ai yanzu an zama ɗaya ya kamata ace ta zo, duk abun da ya samu Neehal ai ya shafe ka, ko ma ince kamar kai ya sama, tunda ba ka da kamarta a duniyar nan. Koda yake ba zan yi mamakin ƙin zuwan nata ba dan ba wani son mutane take ba. Dan ranar da na je dubo ka….. “Allah ya kawo ki zaki cika mun kunne.” Ameen ya katse ta da faɗin haka fuskar nan a haɗe.” A zafafe Hajiya ta zauna ta ce “An cika maka kunnen, na ce an cika maka kunnen, dan k’wal uba kawai, laifin matarka ne baka son a faɗa kuma sai na faɗa ɗin!” Hajiya ta cigaba da mitarta tana faɗar Abun da Hafsat ta mata na rashin kyautawa da ta je gidan. Idan kujerar da take kai a zaune ta tanka mata to Ameen ma ya tanka mata. Mama ce ma data fito ta ji tana mitar ta sanar mata Hafsan ce bata jin daɗi shi yasa bata zo ba. Kiran sallar Azhar da akai yasa ya miƙe dan tafiya masallaci. Hajiya ta ce “Idan ka dawo sai ka kai ni na dubo jikin Hafsan.” Ko juyowa bai yi ya kalle ta ba ya fice abinsa.” Ya bar Hajiya tana faɗin, “Dan Allah zani ba don halinta ba.”

Har wajen la’asar su Aunty Sadiya suna gidan Mama suna cigaba da tattaunawa akan al’amarin. Yayinda a ɓangaren al’ummar gari ba’a wani yayata zancen ba, saboda ba’a lokacin akai kisan ba. Kafafen watsa labarai ma ba su yaɗa labarin sosai ba, saboda gargadi’n da akay wa kowacce kafar yaɗa labarai daga sama, musamman waɗanda suke zaune a ƙarƙashin gwamnati. Masu zaman kansu ne suka faɗi hukuncin da akaywa su Bilyaminu, amma suma an gargad’e su akan kar sunan Senator Na_kowa ya fito a cikin al’amarin. Alhaji Ali kuwa bayan ya koma gida ko ruwa kasa kurb’a ya yi balle akay ga cin abinci, saboda tsananin al’ajabi da ɗimauta shi da al’amarin ya yi.

Sai bayan la’asar ta farka daga baccin, a hankali ta yunƙura ta tashi zaune, kanta ta dafe da hannunta saboda yanda ta ji yay mata dimm, amma babu ciwo kamar ɗazu. Jikin nata ma ta ji sauƙin sa babu zafi sosai kamar ɗazu, sai dai rashin k’warin jiki da kuma abun da baza a rasa ba. Ta ja ƙafa ta sakko daga kan gadon tana yamutsa fuska ta miƙe, taune lip ɗinta ta yi saboda yanda ta ji saman cinyarta ta hagu a ɗan daure, alamun Mama ta mata allura kenan da tana baccin. Toilet ta nufa cikin rashin k’warin jiki ta yi wanka da brush tare da dauro alwala ta fito. Tana fitowa Mama na shigowa ɗakin, dama ta shigo ta tashe ta ne ganin yamma ta yi sai kuma ta ga ta ma tashin. Mama tay sauri ta ƙarasa ta kamata ta kai ta kan gado ta zaunar. Mama ta ce “Sannu Daughter ya jikin?” Cikin muryar marasa lafiya ta ce “Da sauqi.” Mama ta ce “Allah ya ƙara sauƙi, bari na shimfid’a miki darduma ki yi sallah sai ki ci abinci ki ƙara shan magani.” Ta jinjina mata kai kawai. Mama ta ɗauko mata lotion ta shafa mata a hannu da ƙafafuwanta, sannan ta ɗauko mata wata gown mara nauyi ta bata ta saka a jikinta. Mama tana shimfid’a mata dardumar ta ce “Me zaki ci a dafa miki?” Ta yi shiru alamun nazari sannan ta ce “Babu komai, bakina babu daɗi.” Cikin lallami Mama ta ce “Ai dole sai kin daure kin ci wani abun, cuta ba cin abinci ai bazai yiyu ba. Ga abubuwan da Ameen ya siyo miki can a dawnstairs, bari na ɗauki miki na san ba’a rasa abun da zaki iya ci ba.” A hankali ta ce “Yayan ya tafi?” Mama ta ce “Eh, yakai Hajiya gidansa zata dubo Hafsah, itama bata jin daɗi.” Ta ce “Su Aunty ma sun tafi?” Mama ta ce “Duk sun wuce tun d’azu.” Bata kuma magana ba, dan wadda ta yi ma cikin dauriya ta yi ta, ta miƙe ta ɗauki hijabin da Mama ta ajiye mata ta saka ta tayar da Sallah. Kafin ta idar Mama ta je ta ɗauko siyyayar da Ameen ya yo mata ta kawo mata. Ledoji ne guda biyu, ɗaya kayan fruits ne cike a cikinta, ɗayar kuma Popcorn ne da wafer da shawarma da yoghurt. Ta yi murmushi lokacin da Mama take fito da su daga cikin ledar, gaba-d’aya favourites things d’inta ya siyo mata, sai dai yanda take jin bakinta babu daɗi da ƙyar zata iya ci. Yoghurt d’in ta ce Mama ta bata, shima kaɗan ta sha ta ajiye. Sai ta ɗauki wafer ɗaya ta koma kan gado tana gutsira kaɗan kaɗan tana ci. Mama ta miƙo mata wayoyinta ta ce “Anata kiranki tun d’azu, Haneefah ma ta kira, amma na d’aga nata kiran.” Ta karb’i wayoyin tare da faɗin “To bari na bi bayan missed calls ɗin.” Mama ta juya ta fice daga ɗakin. Ta latsa wayar ta duba ta ga Sadik da Ahmad ne suka kira ta, sai wasu daga cikin abokan aikinta sai kuma Uncle Usman.

Ahmad ta fara kira saboda missed call ɗinsa ya fi yawa. Kamar jira yake ringing ɗaya ya yi rejected ya kira ta. Ta d’aga tare da yi masa sallama. Ya amsa tare da faɗin “Princess!” cikin sauke ajiyar zuciya da jan numfashi. Ta ce “Na’am Uncle, ina yini?” Ya ce “lafiya lau, jikin naki ne har yanzu?” Ya yi maganar cikin damuwa. Ta ce “Na ji sauƙi Uncle.” Ya ce “Um,um Princess, sound ɗin muryarki ya tabbatar mun da baki da lafiya har yanzu, ko jikin ne ma nay ta kira baki pick ba.” Ta ce “Ciwon kai ne, kuma na sha magani, time ɗin da ka kira ni kuma bacci nake.” Ya ce “Oh God! Allah ya baki lafiya Princess sannu kin ji.” Ta ce “Amin na gode Uncle, ina twins ɗina?” Ya ce “Suna nan k’alau, suna ta missing Auntinsu, da a cikin week ɗin nan zan kawo miki su, to kuma baki da lafiya, sai kin warke zan kawo su.” Ta ce “Dan bani da lafiya baza ka kawo mun su ba.” Ya ce “Eh mana, kar su zo su damar min ke.” Cikin shagwab’a ta ce “Ni dai na warke, ka kawo mun su.” Ya ce “Shikenan Princess zan kawo miki su, suna dawowa daga gidan Ammi, sun je can zasu kwanar mata biyu ne.” Neehal ta yi murmushi cikin murna ta ce “Thank you.” Ya ce “Uhm, ni fa na gane kin fi son yaranki da ni, da ni na ce zan zo baza ki yi wannan murnar ba.” Ta yi murmushi mai sauti bata ce komai ba. Ya ce “Insha Allahu, inna samu chance gobe zan zo na ƙara duba jikinki.” Ta ce “Uncle, Jiya fa ka zo, ka yi zamanka Please na ji sauƙi fa.” Ya ce “In bakya son gani na ni ina son ganinki.” Ta ce “I’m sorry ba haka nake nufi ba Uncle, na ga kana ta wahala….” Ya katse ta da faɗin “Babu wata wahala a zuwa ganin ki Princess, don’t worry kin ji.” Ta ce “Toh Shikenan Allah ya kawo ka lafiya.” Ya ce “Ameen, sai ma in duba jikin naki da kaina in ga me yake damar mun ke haka.” Ta ce “Kafin ma ka zo na warke Insha Allah.” Ya ce “Allah ya amsa Princess.” Daga haka suka yi sallama ya ce bari ya barta ta huta tunda bata jin daɗi. Bayan ya katse kiran ta kira Sadik amma bai ɗauka ba, ta san dama by now yana gurin aiki. Uncle Usman ta kira, yay mata ya jiki da nuna jin daɗin sa akan hukuncin da kotu ta yanke akan su Bilyaminu, dan sun yi waya da Uncle Umar ya sanar masa da komai. Bayan sun gama wayar da shi ta bibbi bayan sauran missed calls ɗin da akay mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button