NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya

ELEGANT ONLINE WRITER’S

8️⃣8️⃣

……….Hafsat tana zaune a ɗakinta tana tunanin Ameen data mayar da shi sana’arta, tun safe take tsammanin zuwansa dan jiya kusan kwana ta yi tana bankad’a magani da turara jikinta. Ɗaya daga cikin masu aikin gidansu ta yi knocking ƙofar ɗakinta, ta bayar da umarnin a shigo. Cikin ladabi Mai aikin ta sanar mata saqo aka bayar aka kawo mata ɗan aiken yana falo. Jikin Hafsat ya bata saqon daga gurin Ameen yake amma mai makon ta yi farinciki sai ta ji gabanta ya faɗi. Miƙewa ta yi suka fito tare da Mai aikin, a main parlour ta tarar da Mom da Aunty Jamila wadda ta zo yiwa Dad sannu da zuwa. Mai gadi dake tsaye ya risina ya gaishe ta sannan ya miƙa mata takardar tare da shaida mata in ji Ameen. Ta karɓa fuskarta da alamun mamaki. Duban Mum ta yi ta ce. “Kin ga wai takarda ce in ji Ameen.” Mom ta ce. “Lallai Yaron nan, ya cika shegen miskilancin tsiya, may be ta ban haquri ce ya yo, dan girman kai ba zai zo ya bayar da bakinsa ba sai dai ya rubuto miki a takarda.” Hafsah bata kuma magana ba ta buɗe takardar ta fara karantawa. Aunty Jamila dai kallo reaction ɗinta kawai take yi. Wani uban ihu Hafsat ta kurma da ya saka su Mom toshe kunnuwansu ba shiri. Lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya sauya gumi ya fara tsatstsafo mata. Ta nufi mahaifiyarta a gigice tana nuna mata takardar da hannunta dake faman karkawa kamar yadda duk jikinta yake yi. Cikin rawar Muryar ta ce. “Mo..Mom..wai ya sake ni, saki ya rubuto mun, Mom ki duba ko idona ne bai gane mun dai-dai ba.” Sai ta fashe da kuka. A razane Mom ta karb’i takardar ta duba. Aunty Jamila innalillahi….. kawai take maimaita cikin tsananin al’alabi. Durk’ushewa Hafsat ta yi ta shiga zunduma ihu tana faɗin. “Ameen kar ki yi mun haka Please, ka san ina son ka bazan iya rayuwa babu kai ba, Please ka ce mun wannan takardar bakai ka rubuta ta ba, wani ne ya copy note ɗinka ya rubuta dan ya raba mu. Na shiga uku….” Wani uban ashar Mom ta lailaya ta miƙe tana faɗin. “Lallai wannan yaron ya cika cikakken butulu, shegen yaro ni zai tozarta a idon duniya ya mayar mun da Ƴa ƙaramar bazawara? Lallai zai gane kuren sa a ƙasar nan, sai ya san ya taɓo mu wallahi.” Aunty Jamila dake karanta takardar sakin da Mom ta yada a ƙasa ta ce mata. “A’a Yaya mu bi komai a sannu, ai saki ɗaya ne ma, insha Allahu za’a dai-daita su.” Mom ta yi mata wani mugun kallo sannan ta juya ta ɗauki wayarta, jikinta na tsuma ta kira Aunty Safiyya ta ce ta zo gida yanzu_yanzu tana son ganin ta. Aunty Jamila ta koma kusa da Hafsah wadda haukan lokaci ɗaya ya kama ta, janyo ta jikinta ta yi ta shiga rarrashinta tana faɗa mata ta kasance musulmar k’warai mana mai yarda da ƙaddararta a duk yanda ta zo mata. Hafsah ko fahimtar abun da take cewa bata yi balle ta saurara. Mom da take jin kamar ta zunduma ihun ita ma irin na Hafsah ko zata ji daɗi a cikin ranta ta yi k’wafa sannan ta latsa wayarta ta lalubo numbern Mama ta yi dialing. Mama tana toilet a lokacin tana alwalar Sallar Magriba kiran ya shigo, ta ƙarasa alwalar ta fito sannan ta yi picking cikin mamakin ganin mai kiran nata, dan kiran farko har ya katse wani ya ƙara shigowa. Mama ta yi mata sallama. Mom bata bi ta kan sallamar ba ta ce. “Hajiya Fateemah kin aura wa ɗanki ƴarki ni kuma ya sakar mun tawa.” Cikin shock Mama ta ce. “Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un, Ameen ɗin? Yaushe?” Mom ta ce. “Ki riƙe sallallaminki zai miki amfani wani lokacin ba’a nan ba, munafurcin banza munafurcin wofi, amma ki sani wallahi Ameen sai ya san ni ya wulaqanta.” Ta ja tsaki sannan ta katse kiran. Aunty Jamila ta dube ta, ta ce. “Haba Yaya, ya zaki kira……..” A zazafe Mom ta katse ta, ɗaga mata hannu ta yi ta ce. “Dahalla Jamila saurara mun, bana son wani dogon jawabinki na banza, ko dan ba ƴarki aka saka ba ne.” Girgiza kai kawai Aunty Jamila ta yi. Mama kuwa bin wayar ta yi da kallo bayan ta katse, ta zauna a bakin gado tana jin zuciyarta babu daɗi sosai akan sakin Hafsah da Ameen ya yi, ba ta ji daɗin kalaman mahaifiyar Hafsah ba, amma duk da haka ta fi jin zafin sakin Hafsah da Ameen ya yi. Numbern sa ta lalubo ta yi dialing, komawarsa gida kenan ya tarar Neehal tana bacci a falo, da alama bata ma san lokacin da baccin ya ɗauke ta ba. Ya ɗaga wayar ya kara a kunne. Mama ta ce masa “Ameen where are you?” Ya ce. “Ina gida.” Ta ce. “To ka zo yanzu ina son ganin ka.” Ya ce. “Gani nan insha Allah.” Ɗakinsa ya shiga ya yo alwala ya fito ya fice ba tare da ya tashi Neehal ba, tunda ya san ba Sallah zata yi ba.

Zaune yake a gaban Mama yana sauraren faɗan da take yi masa. Ta ce. “Ban ji daɗi ba ko kaɗan Ameen, gaskiya baka kyauta ba, duk tausar kan dana dinga yi jiya amma sai da ka aikata wannan d’anyen aikin? Bana son ka kasance cikin mazan da dan sun samu wata matar su rabu da wadda suke tare da ita.” Cikin ladabi ya ce. “Mum ba haka ba ne kema kin sani, dan na samu Neehal haka kawai bazan rabu da Hafsah ba, halinta ne ya janyo mata. Kuma ina son hakan ya zama kamar jan kunne a gare ta. Mama ta sauke numfashi ta ce. “Saki nawa ka yi mata?” A hankali ya ce. “Ɗaya ne.” Mama ta ce. “Shikenan, Allah ya dai-daita ku, ya kiyaye faruwar hakan a gaba.” Ya amsa da Amin sannan ya tashi ya yi mata sallama ya tafi. Har kusan isha’i su Hafsat suna falo, mahaifiyarta na faman kumfar baki Aunty Safiyya data zo gidan tana taya ta, Hafsat kuma tana ta aikin kuka. Ko sallar Magriba ba su yi ba, ba su ma da niyyar yi, Aunty Jamila ce kawai ta yi. A haka mahaifin Hafsah ya shigo ya same su, ya zauna tare da tambayar ba’asi. Mom ta kora masa bayani, ta ƙara da faɗin. “Yanzu Alhaji sai ka san matakin da zaka ɗauka ga Ameen da iyayensa na wulaqanta maka ƴa da suka yi.” Dad ya haɗe rai ya ce. “Hafsah ‘yata ce wadda nake k’aunarta kamar raina, bana jin bayan iyayena akwai abun da nake so a duniyar nan sama da ita. Na san halinta na san abun da zata yi, haka na san mijinta Ameen yaron kirki ne shi da iyayensa, ya samu ingantacciyar tarbiyyar da nake da tabbacin bai saki Hafsat haka kawai ba tare da wani dalili ba, face ta yi masa wani abun. Dan haka i will never blame him akan abun da ya yi, balle har na ɗauki wani mataki kuma ban bawa kowa ikon ɗauka ba. Ban da ma hauka daga mutum ya saki mace sai a ce za’a ɗauki mataki a kansa? Duk matan duniya da ake sakin su fa? Ko ma ba haka Ameen ya wuce matakin da za’a ce za’a ɗauki wani mataki a kansa, irin matakin da kuke nufi na a wulaqanta shi ko something like that.” Ya nuna Mun da hannu ya ce. “Wannan ya ishe ki ishara, a da idan ina faɗa miki ɓata Hafsah kike yi ba gata kike yi mata ba sai kina ganin kamar k’arya ne, yau gashi nan ta yi aure Mijinta ya kasa ɗaukar halayenta ya sako ta. Ba fina son ta kika yi ba Amina, kuma nima ina nuna mata gata dai-dai gwargwado, amma ba irin naki ba, naki ya yi yawa. Kasancewar ni ba mazauni ba ne kullum ina tafe neman halak ɗina shi yasa tarbiyyar da kika yiwa Hafsah ta fi tasiri a gare ta akan tawa. Amma yanzu tunda ta dawo gidan, zan yi iya yina wajen ganin na gyara rayuwarta, duk da an ce ice tun yana d’anye ake iya tank’wara shi.” Ya mayar da kallonsa ga Aunty Jamila ya ce. “Idan zaki tafi gidanki ki tafi da Hafsan ta yi zaman iddarta a can, domin ki koya mata ilimin zaman duniya da kuma yanda zata samu lahirarta, da rayuwar zaman Aure da haqqokinsa dan ganin ta gina rayuwarta ko dan gaba. Sannan kuma duk lokacin da Ameen ya zo domin mayar da ita ɗakinsa zan yi masa maraba in kuma bashi ita.” Yana gama faɗin hakan ya miƙe ya nufi sashensa. Gaba-d’aya suka bi shi da kallo baki a sake, Aunty Jamila ce kawai ta ji daɗin maganganunsa ta kuma yaba masa. Mom ta saka kuka tare da surutan shiga tsakaninsu aka yi da Daddyn Hafsah, amma da ba zai faɗi haka ba. Bayan Daddy ya dawo gida Mama ta sanar masa da abun da ya faru, ya ji ba daɗi shi ma amma ya ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button