NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

……….A falon gidan suka tarar da matarsa Aunty Fauziyya hakimce akan kujera suna kallo, yaranta guda biyu mace da Namiji suna ta wasansu akan doguwar kujera. A hankali Neehal ta shiga Falon tana goge hawayen fuskarta dan kar Uncle Umar ya gani, kan kujera ta nufa zata zauna Aunty Fauziyya ta buga mata wata uwar tsawa tana faɗin “Kar ki kuskura ki zauna mun akan kujera zauna nan ƙasa.” Ba musu Neehal ta zauna a ƙasan cikin mamaki, dan ta saba ita a gidansu da gidan Mama akan kujera take zama. Uncle Umar ya zauna yana hararar Neehal ya ce “Hmmmm, yarinyar nan ai sai an dage mata, gaba-d’aya waccan matar da Ƴan’uwanta sun ɓata mata tarbiyya, Ni wlh Yaaya ta ban mamaki da ta yarda suke riƙe mata ƴa.” Fauziyya ta tab’e baki ta ce “Kai kwa kuɗii, kuɗi fa aka ce maka, ta ga suna da kuɗi ne shi yasa, ka ga in an ɗan yi Zakka a dinga tunawa da ita ai.” Shiru Uncle Umar ya yi jin abun ya fara komawa cin fuska. Yaran su Aiman da iman suna wasa suka fado tim akan Neehal, Uncle Umar ya ce “Subahanallah, Aiman ban hana ku wasan banza ba? gashi nan kun faɗo wa Aunty’nku akai.” Aunty Fauziyya dake ta aika wa Neehal harara ta ce “Kamar ya sun faɗo mata? Ita bata gani ne, makauniya ce ita, ai tana kallonsu zasu faɗo ɗin dan baƙin hali ta ƙi matsawa, salon ace daga zuwanta an fara cutar da ita.” Neehal dai ba ta ce komai ba, kanta na ƙasa tana ta hawaye. Su Aiman suka kwantar da trolley ɗinta suka buɗe suka fara zak’ulo mata kaya suna yar wa a dakin, Uncle Umar cikin tsawa ya ce musu “Wai wanne iskanci haka, ko kun mata ajiya a cikin kaya ne.?” Cikin tarar numfashi Aunty Fauziyya ta ce “Ka ga, ka dena dakawa ƴaƴana tsawa irin haka, nan gidan ubansu ne ba cin arziki suka zo ba, dan haka dole su sakata su wala san ransu.” Tsaki Uncle Umar yay ya ce wa Neehal ta tashi ta tattara kayanta ta shiga ɗakin yaran. Aunty Fauziyya ta ce “Kar kuma ki hau mun kan katifar ƴaƴa, a ƙasa zaki zauna, anan kuma zaki dinga kwana.” Neehal dai ba ta ce komai ba ta tashi ta shiga ɗakin tana janye da trolley ɗinta da ƙyar. A ƙasan ta zauna kamar yadda Fauziyya ta ce ta rafka tagumi, kanta ne ke mata wani irin ciwo hakan yasa ta kwanta a ƙasan, amma gaba-d’aya sai ta ji kwanciyar bata mata daɗi ba, ita data saba kwana akan luntsumemiyar katifa da lallausan bed sheet ta lullub’a da lallausan bargo, ta yaya zata iya kwanciya akan dandaryar
ƙasa kan tayis? A hankali ta miƙe dak’yar ta buɗe trolley ɗinta ta ɗauko kayanta ta shimfid’a a ƙasan ta kwanta akai, amma duk da haka bata wani ji daɗin kwanciyar ba, ya dai fi ta kwanta a ƙasan ne kawai. Allah ya so ma Aunty A’isha ta saka mata bargo acikin kayan nata, da yake ita ta haɗa mata kayan. Amma saboda garin da ɗan zafi shi yasa bata lullub’a ba, ɗakin kuma da fanka amma bata wani ba da iska, ko dan ta saba da Ac ne a gida. Tafi awa da kwanciya amma ta kasa bacci sai juyi take, idanunta dai a lumshe suke kamar mai bacci, tana jin Aunty Fauziyya ta shigo ta kwantar da ƴaƴanta akan katifa ta daura musu Net sannan ta kashe musu light ɗin ɗakin, nan fa sauro ganin duhu ya ce wa Neehal salamu alaikum, ita kuwa bata saba da sauro ba, nan da nan ya gigita ta, ta tashi zaune tana hawaye, ga ciwon kai tamkar ana ƙara mata ake, lallaɓawa ta yi ta shige Net ɗin su Aiman dan bata da wata mafita, katifar ma zata ishe su amma ɗan baƙin halin Aunty Fauziyya ta hanata kwanciya akai. Tana shiga ta sauke ajiyar zuciya, ba jimawa baccin wahala ya kwashe ta. Sanyin asuba ne ya tashe ta, cizon sauron da tasha jiya da kukan da tay ya haifar mata da zazzaɓi, cikin rawar ɗari ta sauko daga kan katifar ta dunk’ule a waje ɗaya tana numfarfashi, kayanta data shimfid’a a ƙasa ta rarumo ta rufe jikinta saboda sanyin da take ji. Sai wajen ƙarfe 7 su Iman suka tashi daga bacci, kamar wasu ƴaƴan karnuka da faɗa suka tashi, gashi sun tsutstsula fitsarinsu a kwance, Allah ya taimaki Neehal ba su ɓata ta ba. Da ƙyar Neehal ta iya tashi ta ƙarasa toilet ɗin dake ɗakin ta yi fitsarin da ya matseta, da ƙyar take tafiya saboda jiri, ga yunwa dake nuk’urk’usar hanjin cikinta, rabonta da abincin tun lunch ɗin jiya da ta yi a gida.

Aunty Fauziyya kamar kullum tana jiyo hayaniyar yaranta ta shigo ɗakin  da sauri, dan kullum da hakan take gane tashinsu, Neehal na rakub’e jikin kayanta tana ta rawar sanyi, cikin muryar marasa lafiya ta ce “Ina kwana Aunty.” Wani mugun kallo Aunty Fauziyya ta watsa mata, a harzuk’e tana zazzaro ido kamar sabuwar kamu ta ce “Yana gidan Ubanki shi kwanan.” Neehal bata kuma cewa komai ba, ita kuma Fauziyya ta ja ƴaƴanta sukai toilet, wanka ta musu ta shirya su cikin uniform ɗinsu, sannan suka fita falo dan karyawa. Uncle Umar ya ce wa Fauziyya “Ina Neehal ɗin, itama ta fito ta karya mana.” A fusace Aunty Fauziyya ta ce masa “Ka san yar gold ce bata tashi ba har yanzu.” Sai wajen ƙarfe tara Aunty Fauziyya ta ƙwalawa Neehal kira lokacin Uncle Umar ya fita, cikin hanzari Neehal ta taso dan wani bala’in tsoron matar take ji, k’osan Talatin ta bata da wani ɗan bread da ruwan bunu rabin ƙaramin cup a matsayin breakfast. Neehal ta bi abun da aka bata da kallo sannan ta fara ci tana yamutsa fuska saboda bakinta babu daɗi, yunwa ce kawai ta sa take ci, ga shi ita k’osai ba mutuminta ba ne, gara ma bread ɗin. Ruwan bunun kuwa ko kurb’a ba ta yi ba, dan tasan baza ta iya sha ba. Bayan ta gama cikin faɗa Aunty Fauziyya ta ce “Tunda ciki ya ɗauka, sai ki tashi ki haɗa kayan nan, ki kai tsakar gida ki wanke, sannan ki dawo ki share mun falo ki yi mopping, ɗakin da kika kwana ma haka.” Cikin sanyi Neehal ta ce “Aunty ban da lafiya, kuma ban iya b…….” “Ai ko cutar mutuwa kike yau sai kin mun aikin nan, dan Ubanki Jakar uwarki ce ni zan dafa miki ki ci kina daga kwance, zaki tashi ko sai na miki dukan mutuwa a gidan nan.” Jiki na b’ari Neehal ta tashi ta fara haɗa kayan, duk da zazzaɓin dake damunta, amma saboda tsoron Fauziyya da take ji dole ta yi. Ba ta taɓa wanke_wanke ba a rayuwarta, sai a gidan Mama ne ma idan ta ci abinci Mama take sata ta dauraye flate ɗin da taci abincin. Ai kuwa Fauziyya ta sha asarar omo, gashi kafin ta gama ta jik’a jikinta jagab da ruwa, a haka ta yi share_sharen da mopping, Fauziyya kuwa tuni ta fice yawon mak’ota. Tana gama aikin ta yi daki ta kwanta akan tiles, zazzaɓi mai zafi ne ya rufe ta. Da Fauziyya ta dawo ta ga b’arnar Omon da Neehal ta mata, ta dinga surfa mata ashariya da masifa, da dukanta ma zata yi wata makociyarta data shigo ta hanata, ganin yanda Neehal ɗin take rawar sanyi. Da rana ma kiranta Aunty Fauziyya ta yi ta bata wata shinkafa da wake ƴar kaɗan a roba, ko man kirki babu a ciki. Lauma ɗaya Neehal ta yi ta ture ta koma ɗaki ta kwanta, Fauziyya ranar wuni ta yi tana zagin Neehal. Da daddare Uncle Umar ya lek’a ɗakin da Neehal take ganin Shiru_shiru bai ji motsinta ba tunda ya dawo, ganin ba ta da lafiya ya bata panadol da Paracetamol ta sha, ya kuma kawo mata lemo da ayaban daya shigo gidan da su har ɗaki, ta kuwa ci ayabar ba laifi dan tana sonta sosai. Fauziyya tayta kumbure_kumbure tana huci kamar zata naushi iska ganin abun da Uncle Umar ya yi wa Neehal. Washegari ma Neehal ce ta yi wanke_wanke da shara, jikin nata ya yi sauƙi tunda ta sha magani, sai dai bata warke sumul ba, ranar kam sai da Fauziyya ta mare ta akan ta’adin omon data mata. A daren Ranar Uncle Usman ya zo gidan yi musu sallama dan zai koma garin da yake aiki ne. Tsaraba sosai yayo wa Neehal da su Aiman ta sweet da chocolate, da zai tafi Neehal tai ta Kuka, Aunty Fauziyya ta tab’e baki a ranta ta ce ‘Munafurcin banza.’

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button