NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Zuciyar Sadik Cike da farinciki ya koma gida, a main Parlour ya tarar da iyayensa da k’annensa kamar kodayaushe. Ya yiwa iyayen nasa sannu da gida ƙannansa kuma suka yi masa sannu da zuwa ya shige ɗakinsa. Bayan shigar sa ɗakin ba jimawa Batul ta zo ta ce ya je Abbansu yana kiran sa a part ɗinsa. Ya amsa tare da tashi ya biyo bayanta suka fito. Abba yana zaune shi da Umma da Maamah, kamar yadda tsarinsa yake idan zai yi magana da ƴaƴansa a gaban su Maamah yake yi. Sadik ya samu guri ya zauna a ƙasa bayan ya ƙarasa falon Abban. Abba ya dube shi cikin kulawa ya ce “Abubakar na kira ka ne akan maganar yarinyar da kake zuwa gurinta, kamar yadda na ce zan yi bincike akanta da iyayenta na yi, kuma Alhamdulillahi na samu kyakkyawan sakamako kamar yadda ake fata dama. An tabbatar mun yarinyar tana da tarbiyya, mahaifinta kuma mutumin kirki ne. Dan haka na yarje maka ka cigaba da zuwa gurin ta.” Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Maamah na farinciki. Sadik kuwa ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin bayanan Abba, daman ya san babu wata matsala da za’a samu a gurin Neehal. Maamah ta ce “Masha Allah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi.” Abba ya ce “Ameen.” Tare da mayar da duban sa ga Sadik wanda kansa ke ƙasa ya ce “Ashe ma yarinyar nan ce mai aiki a gidan TV na ASTV?” Sadik ya shafa kansa ya ce “Eh ita ce Abba.” Abba ya ce “Masha Allah, Allah ya yi mana jagoranci.” Umma da baƙin cikinta ya kasa b’oyuwa akan fuskarta ta tari numfashin Abba ta ce “Alhaji wacce yarinya na ji kana magana a kanta? Ba dai Neehal ɗin nan ba ta gidan Alh. Tafida?” Abba ya ce “Ita mana, ai yarinyar da mahaifinta sanannun mutane ne a ƙasar nan.” Umma ta jinjina kai irin ta ga mugun abun nan ta ce “To gaskiya Alhaji baka yi bincike yanda ya kamata ba, indai akan yarinyar nan ne?” Abba ya ɗan canza fuska ya ce “Kamar yaya kenan?” Umma ta tab’e baki ta ce “Ita yarinyar fa su Alhaji Tafidan ba su ne asalin iyayenta ba.” Sadik ya d’ago da sauri ya kalle ta, Maamah zata yi magana Abba ya riga ta da faɗin “Kamar ya ba su ne iyayenta ba Ruqayyah? Ban gane me kike son faɗa ba.” Umma ta ce “Ina nufin riqon ta suke Alhaji ba ƴarsu ce ta cikinsu ba, riqonta kawai suke amma ko dangi ba su haɗa ba.” Abba ya ce “Wannan ai ba wata matsala ba ce, indai tana da asalinta ai shikenan.” Umma ta ce “Hmm, hakane. Amma kuma akwai wata matsalar bayan wannan.” A harzuk’e Maamah ta ce “Wai ni Rukayya dan Allah me Yaron nan ya tsare miki a gidan nan ne, duk abun da zai yi sai kin san yanda kikai kika kawo masa cikas, akan wane dalili zaki takurawa ɗana? Me ya tsare miki?” Abba ya d’aga mata ya ce “Ya isa haka Kaltum, barta ta ƙarasa maganarta.” Umma ta harari Maamah sannan ta cigaba da magana. “Abu na biyu Alhaji, wanda na same sa daga majiya mai ƙarfi akan yarinyar, na so in ɓoye maka kar in faɗa a mun wata fassarar daban, amma na kasa saboda yanda ba zan bari a cutar da ɗan cikina ba, haka ba zan bari a cutar da naka ba. Ita yarinyar ce duk wanda zata aura sai an kashe shi…” A zabure Sadik ya miƙe tsaye yana duban Umman, zuciyarsa na wani irin bugu ba tare da ya ji ƙarshen zancen nata ba.” Abba ya haɗe rai sosai ya ce “Kin ga Rukayya, bana son shirme wannan wacce irin magana ce mara ma’ana?” Umma ta ce “Wlh Alhaji ba ƙarya ba ne, nima na girgiza da na ji zancen dan da farko ma ban yadda ba sai da aka tabbatar mun, samari har biyu sai an saka ranar Aurensu sai a wayi gari a tarar an kashe su idan…..” A fusace Abba ya katse ta da faɗin, “Wannan duk ba hujja ba ce Rukayya, Babu mai kashewa da rayawa face Ubangiji, suma waɗanda suka rasun kwanansu ne ya ƙare. Dan samarin yarinya guda biyu sun rasu baza a ce daga ita ba ne, Ubangiji ne ya karb’i abinsa. Dan haka kar na ƙara jin wannan maganar mara kai da tushe, kuma wannan dalilin ba zai sa na hana Sadik cigaba da neman Auren yarinyar ba.” Yana gama faɗar haka ya tashi ya shige ɗakin baccinsa. Maamah ta sauke ajiyar zuciya cikin jin daɗin yanda mai gidan nasu bai goyi bayan abokiyar zamantata ba a wannan karon. Miƙewa ta yi ta kama hannun Sadik dake tsaye kamar an dasa shi suka bar falon, ba tare da ta kuma kallon inda Umman take ba. Umma ta yi ƙwafa tare da raka su da harara, a fili ta furta “In kun san wata baku san wata ba ai, wallahi indai ina raye Sadik ba zai auri wannan yarinyar da Ubanta yake da arzik’i ba, mu zuba mu gani, shege ka fasa.”

Har ɗakin Sadike Maamah ta kai shi ta zaunar da shi a bakin gadonsa. Cikin tausasawa ta ce “Kar abun da Rukayya ta faɗa ya d’aga maka hankali Sadik, ka dai san halinta ba sai na faɗa maka, zata iya yin ko wanne irin sharrin dan ganin auran ka da yarinyar nan bai yiyu ba. Ka dogara da Allah, ka kuma dage da addu’ar neman zab’insa ka ji.” Sadik ya d’aga mata kai yana sakin ajiyar zuciya. Sai da kwantar masa da hankali sannan ta bar ɗakin. Kwanciya ya yi bayan fitar Maamah zuciyarsa na tariyo masa abun da Umma ta faɗa akan Neehal, tabbas ya san Sauratinta ya rasu kafin su haɗu, har Haneefah ma ta tabbatar masa da an kusa bikinsu lokacin da ya rasun. Amma bai san da wani ba bayan shi ba. Wani b’arin na zuciyarsa kuwa cike yake da mamakin cewa wai ba su Mama ne suka haifi Neehal ba, shi ko kaɗan ma bai yarda da wannan batun ba. A yanda yake jin Neehal a cikin ransa koma me za’a faɗa a kanta ba zai iya rabuwa da ita ba, ko yaya take yana son abarsa kuma a haka zai aure ta. Balle ma ya san bata da wani aibu. Tashi zaune ya yi a ransa yana faɗin ‘Dole ma ya yiwa Maamah magana ta faɗawa Abba ayi_ayi a saka ranar bikinsu kowa ma ya huta.’ Ko da suka yi waya da Neehal yau sai da ta gane kamar yana cikin damuwa har ta kasa shiru ta tambaye shi. Amma ya ce mata babu komai, dan Maamah ta gargad’e shi akan kar ya sake ya yiwa Neehal zancen. Umma kuwa bayan ta koma ɗaki Yayan Abban su Sadik wanda suke kira da Kawu ta kira ta sanar masa ƙarya da gaskiya akan yarinyar da Sadik yake nema. Kawu ya dinga masifa a waya kamar zai ari baki yana faɗin “Shi Surajon (Abba) ba shi da hankali ne yana ji yana gani zai salwantar da rayuwar ɗansa har zai da ce wannan abun ba wata matsala ba ce? To ina nan zuwa a cikin satin nan in same shi, domin kuwa wannan yarinyar dole Sadik ya rabu da ita.” Cikin jin daɗi Umma ta masa sallama, zuciyarta fari k’al kamar takarda.

Bayan kwana biyu Ranar Laraba Neehal ta dawo daga gurin aiki da Yamma, tana zaune a ɗakinta tana operating system Mama ta shigo ɗakin, bayan ta yi Sallama Neehal ɗin ta amsa mata ta ce “Neehal Ahmad ya zo, yana ƙasa.” Ta d’ago kanta da sauri ta ce “Uncle Ahmad kuma?” Mama ta ce “Ki yi sauri ki je kar ki bar shi yay ta jiran ki, na san ki da shiririta.” Neehal ta ce “Toh.” Sannan ta miƙe ta ɗauki Hijabi ta zira ta fito. Haka kawai ta ji zuciyarta na d’okin ganin sa, ko dan ta kwana biyu rabon ta da shi ko a waya ne. Yana zaune hannunsa tallafe da fuskarsa idanunsa akan steps, wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke jin takun tafiyarta. Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon. Ya miƙe tsaye da sauri kamar wanda aka tsikara ya ƙarasa gabanta ya tsaya daf da ita kamar zai rungume ta, cikin wata irin murya ya ce “Princess!” A hankali ta ce “Na’am Uncle.” Ya kamo hannunta tay saurin k’wacewa tare da yin baya ta zauna akan kujera. Ya ƙarasa ya tsugunna a gabanta ya ce “Princesss mai ya faru idan na kira wayarki bakya ɗauka, ko wani laifin na miki?” Ganin yanda yake magana cikin damuwa sai ta ji tausayinsa mai tsanani ya cika mata zuciya, har ta fara da na sanin abun da ta yi masa. Cikin raunin murya ta ce “I’m sorry Uncle, ka koma ka zauna akan kujera.” Ya girgiza mata kai tare da faɗin “No Princess, please tell me me ya faru.” Ta ce “Seriously babu komai Uncle ɗina.” Ajiyar zuciya ya ƙara saukewa jin yanayin da ta yi magana ya tabbatar masa babu komai ɗin. Ya koma ya zauna sosai tare da zuba mata idanunsa. Cikin marairaicewa ya ce “But Princess why? Na shiga damuwa sosai da ƙin d’aga kira na da kike, har na fara tunanin ko ba lafiya ba. Na karb’i Numbern Mama a gurin Ummi na kira ta, dan nasan in ma ba lafiya zata sanar mun, amma jin bata ce mun akwai matsalar komai ba sai hankalina ya ɗan kwanta, amma kewarki gaba-d’aya ta hana ni sukuni. Kwana ukun nan da ban ji muryarki ba gaba-ɗaya bana cikin nutsuwata, yau dai na kasa jurewa na ce sai na zo na gan ki.” Ta lumshe idonta cikin sanyin murya ta ce “Nima na yi kewar ka Uncle.” Ya ce “Sure?” Ta gyaɗa masa kai. Ya ce “To me yasa kika daina ɗaukar kira na.” Ta buɗe idonta tana kallon fuskarsa ta ce “Babu komai fa Uncle ka yarda da ni.” Ya ce “Uhm, salon ki tayar mun da hankali ne kawai ko?” Ta ce “A’a, i’m sorry ba zan kuma ba.” Ya ce “Shikenan Princess.” Ta ce “Ina yarana, me yasa baka zo mun da su ba?” Ya ce “Bari na yi sai next week idan sun yi hutun school sai na kawo miki su.” Ta ce “Allah ya kai mu, Ya su Ummi?” Ya ce “Duk suna nan lafiya lau.” Hira suka sha sosai yau, dan ita kanta sai yanzu ta tabbatar ta yi kewarsa ba kaɗan ba. Anan ya yi Sallar Magriba, yau kam ya ci abinci kaɗan a gidan saboda gudun ɓacin ran Princess ɗin tasa. Sai kusan isha’i ya tafi zuciyarsa cike da nishad’i, saɓanin kwana biyun da suka wuce wanda ya yi su cikin damuwa. Itama Neehal anata ɓangaren cike take da farincikin kasancewa da Uncle ɗin nata a yau. Bayan ya koma gidan Mamy tai ta tsokanarsa tana faɗin “Ai fa yanzu dole yay ta musu zarya a Kano tunda zuciyarsa tana nan.” Murmushi kawai yake mata baya cewa komai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button