NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Na karb’i riƙon Neehal a lokacin da Fateemah ta zo mun da shi gidana saboda Allah ba dan wani abu ba, kuma Allah ne shaidata akan hakan. Tun kafin nan dama ta saba zuwa mana hutu tun iyayenta suna da rai, haka kawai na ji ina son yarinyar tamkar ƴar cikina dana haifa haka nake kallon ta. Da zuciya ɗaya nake riqonta kuma nake yi mata komai. Watarana lokacin Neehal ta kusa shekara da dawowa hannunmu gaba-d’aya da zama Kabir ya zo gidana. Ban shigar da shi ciki ba saboda bana son Fateemah ta san muna tare sai muka zaune a farfajiyar gidan. Muna zaune sai ga Neehal an dauko ta daga makaranta ta dawo, tana hango ni ta taho da gudu ta rungume ni kamar yadda ta saba, nay mata Welcome sannan ta gaishe da Kabir ta wuce cikin gida. Kabir ya bita da kallo sannan ya dube ni ya ce wannan yarinyar fa? Na haɗe rai dan na san halinsa da maitar mace komai ƙanƙantarta nay masa bayanin yanda take a gurina. Ya jinjina kai bai ce komai ba, ashe shi ya k’udurce abun a ransa, washegari muna zuwa ƙungiya ya ce ai ina da ‘ya mace budurwa ƙarya nake na ce ban da ita. Cikin mamaki na ce musu da gaske ban da ƴa mace ta cikina, ɗana ɗaya ne tal a duniya kuma namiji ne, kuma Kabir ya fi kowa sanin haka. Kabir ya bayar da labarin ganin da yaywa Neehal jiya a gidana. Sarauniya ta yi bincike a ƙwaryar tsafinta sai ga fuskar Neehal ta bayyana. Ta dube ni ta ce. Tunda ni nake ciyar da Neehal nake shayar da ita nake tufatar da ita kamar ƴar cikina take a yanzu, dan haka ƙungiya tana buƙatar budurcinta. Na ce gaskiya ba zan iya cutar da ƴar amana ba marainiyar Allah. A fusace Sarauniya ta ce mun. Dole in yi, in ba haka ba su kashe iyalina su kashe ni kuma sannan wani a cikin ƙungiya ya karb’i budurcin Neehal ɗin. Hankalina idan ya yi dubu ya tashi a ranar, dan na san duk abun da sarauniya ta faɗa zata iya aikata fiye da hakan ma. Ba zan so in rasa matata da ɗana ba, kuma ba zan so a ɓata rayuwar Neehal ba. Dan haka na yanke wata shawara, na nuna musu na amince zan yi abun da suke so, amma a lokacin Neehal ta yi yarinta su ɗan bari ta ƙara girma. Da ƙyar suka amince da abun da na faɗa, dan a cewar su wanda ba su kaita ba ma ana musu fyaɗen. Na dawo gida hankali a tashe cikin rashin sanin mafita, ni ba’a abun in ce Fateemah ta mayar da Neehal gurin ƴan’uwanta ba dan tserayar da rayuwarta ba, ta ce mun akan me? Na dai ƙudurce a raina komai zai faru sai dai ya faru amma ba zan taɓa haikewa Neehal ba har abada, gwara na rasa raina dana aikata wannan abun kunyar. Ni babban tashin hankalina da suka ce ko ban aikata mata da kaina ba wani zai aikata mata. Ban taɓa sanin ina son Neehal sosai ba sai a wannan lokacin, Na saka ido sosai akanta saboda na san tsaf zasu iya ɓullo mata ta wata hanyar, musamman Kabir da kodayaushe cikin zancen ta yake. Haka shekaru suka shud’e ina ƙara bawa ƙungiya excuse akan Neehal, na rasa me yasa su kuma suka damu da ita over, kodayaushe cikin yi mun nacin in yi in far mata suke, wai hakan ba ƙaramin cigaba zai ƙarawa ƙungiya ba, yarinyar ta musamman ce gashi nima ban taɓa yiwa ƙungiya irin wannan aikin ba shi yasa suka damu da abun. Lokacin da na yi released soyayyar Neehal da Jameel sai na ce ya turo a yi auransu idan dagaske yake, Fateemah ta ce, na bari ta ɗan yi karatu mana tunda time ɗin candy kawai ta yi. Amma na ce a’a, dan so nake kawai na aurar da ita na huta da fargaba a kanta, a ganina idan ta yi aure ai dole su haqura da batun. Ban san a inda Kabir ya samu labarin Engage ɗinsu ba dan ban faɗa masa ba saboda bana son ya sani. Amma sai tsintar maganar na yi a ƙungiya, aka dinga zazzaga mun masifa wai ina son cin amanar ƙungiya ne, na ce musu danginta ne suke son aurar da ita ba ni ba ne. Sai suka ce to duk yadda za’a yi a yi a fasa batun bikin nan, ko kuma in karɓo musu abun da suke so kafin lokacin bikin. Na amsa musu kawai amma ban aiwatar ba. Wallahi ban san ya aka yi ba, ban kuma san ta yanda aka kashe Jameel ba, kuma bani da masaniya a lokacin da suka shirya kisan. Sai da aka yi sannan nake ji a ƙungiya Kabir ne ya shirya komai. Sarauniya ta tabbatar mun da cewar haka zasu yi ta yiwa duk wanda zai auri Neehal, tunda ni taurin kai gare ni na ƙi yi musu abun da suke so. Manyan ƙungiya sun so hukuntani amma Sarauniya ta hana, ni kaina ina mamakin yanda Sarauniya bata iya hukunta ni duk laifin da zan yi, ita da bata da tausayi da imani ko kaɗan. Duk uwar bautar da kake mata kana mata laifi na rana ɗaya zata rufe idonta ta azabtar da kai.
Abun da ya taimake ni akan Neehal ƙa’ida ne kowa shi zai yi amfani da ƴarsa, wani ba zai taɓa replace ɗinsa ba a ƙungiya, wannan dalilin ne yasa ba’a bawa wani damar keta wa Neehal haddi ba sai ni. Ban taɓa tunanin zasu kuma kashe Anwar ba a lokacin dana bashi auran Neehal, na yarda Ubangiji ne ke rayawa da kashewa rayuwar kowa a hannunsa take, dan haka sai kwanan mutum ya ƙare zai mutu. Ga dukkan alamu ba su samu labarin auren Neehal da Anwar da wuri ba sai gab da za’a kawo lefen ta, wallahi shi ma kamar kisan Jameel ban san sanda aka shirya kisan aka kashe shi ba. A lokacin hankalina yay matuƙar tashi domin na san idan aka cigaba da tafiya a haka akwai matsala, tunda dole hankalin mutane zai dawo kan abun, za’a fara zargin lallai da wata a ƙasa. Na rasa ya zan yi, na rasa hanyar neman mafita. Challenges da barazanar dana samu a ƙungiya baza su faɗu ba akan wannan al’amarin, wai ina ta raina musu hankali shekara da shekaru na ƙi yin abu. Ni kuma na ƙudurce a raina gara na mutu dana aikatawa Neehal wannan mummunan abun. Lokacin da Fateemah ta zo mun da batun tattaunawar da suka yi da su Sadiya akan suna zargin da akwai wanda yake aikata kisan su Anwar hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin na san tabbas idan tafiya ta yi tafiya asirina zai iya tonuwa. Ban tabbatar da hakan ba sai lokacin auransu da Sadik. Domin ƙungiya ba su san da bikin ba sakamakon ɓoye zancen bikin da kay sai da ya zo daf sannan aka bayyana, ana i gobe d’aurin Aure cikin dare sun tura a kashe Sadik aka tarar baya nan an sace shi. Hankalin ƙungiya ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin sun gane da alamun akwai wanda yake bibiyar al’amuransu kenan, nima hankalina ya tashi ba kaɗan ba dan bana son asirina ya tonu duniya ta san halin da nake ciki. Duk zuwa masallacin da na ce ina yi mu yi karatu ba can nake zuwa ba, gidan ƙungiya nake zuwa mu kwana muna bincike dan gano waye yake bibiyar al’amuranmu amma har yau mun kasa ganowa. Gidan da aka kai Neehal nan nake zuwa kullum muna aikin ƙungiya tun bayan dawowar mu Kano da zama. Wancan ɗayan gidan sai idan za’ai gagarumin aiki nake zuwan sa. Da Sadiya take cewa akwai wanda take zargi bayan an sace Sadik ko kaɗan ban yi tunanin ni take zargi ba, dan duk wata kafa ko alama da zata saka ayi zargi na akan al’amarin Neehal na toshe ta, duk binciken mutum bai isa ya gane ina cikin wannan mummunar harkar ba, dan takatsantsan nake bana wasa ba. Lokacin dana bawa Neehal Mota na saka yarana suna bin bayanta duk inda zata je, saboda kaɗan daga sharrin yan ƙungiya su saka a sace ta su tsare ta, su kira ni su ce dole sai na aikata abun da suke so a gaban su. Ni kuma idan su kay hakan bani da wata sauran mafita dole na aikata. Allah ya taimaka ya dubi maraicinta ba su yi hakan ba sai a wannan karon. Wallahi ban san time ɗin da suka shirya sace Neehal ba, sai bayan sun ɗauke tan nake sani. Kuma wannan duk shirin Kabir ne, shi yake shirya komai akan Neehal. Sarauniya kuma ta yi farinciki da hakan har da ƙarin matsayi tay masa na yanda duk wata hanyar mugunta ya san ta. Suka kuma shirya gagarumin shagali dan murnar mallakar BUDURCIN NEEHAL. Abun da suka daɗe suna fata da burin samu, domin bincikensu ya tabbatar musu ba ƙaramin cigaba ƙungiya zata samu ba idan member ɗin cikinta ya mallaki Neehal. Sun riga sun saka ni a tasku da tsaka mai wuya, dole na je na aikata abun da suke so, domin sun ce idan ma ban yi ba zasu saka wani ya yi, kuma bayan sun mata fyaɗen zasu kashe ta, su yanka ta su sha jininta. Shi yasa na amince za ni amma har ga Allah ba dan na aikata ɗin ba ne, sai dan na fito da ita daga wannan gidan, in yaso ni su kashe ni a matsayin hukuncin fitar da itan da na yi. Taimakon ta da Sagir ya yi ma nina saka shi, na san dole zata tambaye shi dalilin da yasa ya taimake ta, sai na ce masa ya ce mata saboda Ameen ya taimake ta idan ta tambaye shi.” Daddy ya yi shiru yana mayar da numfashi, ɗakin ya yi tsit kamar babu halitta a ciki. Ya fara hawaye sannan ya cigaba da magana cikin raunin murya. “Wallahi bani da niyyar cutar da Neehal a rayuwata, ku yarda da ni. Tamkar ƴar cikina haka na ɗauke ta. Da ace ina son cutar da ita da tuni na yi abun da suke so an wuce gurin, tunda ina da opportunities ɗin hakan da dama. A gidana take kwana take tashi, zan iya yin komai da ita a duk sanda naso ba tare da an gane ni na yi ba, ko kuma na saka a sace mun ita in yi duk abun da nake so da ita a wani gurin sannan in dawo da ita ba tare da an gane nina aikata hakan ba. Amma kuma sai ban yi ba saboda ba zan iya ba, ba zan iya cutar da ita ba. Lokacin da ta je gidan Ameen ni na je gidan na fesa mata abu a fuska, a lokacin na gaji da ƙwarzabar da ƙungiya take mun gami da barazanar kashe iyalina akan ƙin yi musu abun da suka umarce ni, a lokacin na saduda kawai zan aikata ɗin. Amma ina zuwa sai na kasa aikatawa saboda wasu dalilai, na farko idan har na yi rape ɗinta a gidan Ameen za’a ce shi ne ya aikata, domin babu wanda zai yarda ba shi ba ne, tunda babu alamar da zata nuna wani ya shigo gidan daga waje, Nima na yi amfani da spare keys ɗin kowacce ƙofa dake gidan na gurina kasancewar gidan nawa ne na mallakawa Ameen. Kuma ta ƙofar baya na shiga balle mai gadi ko wani ya ga lokacin dana shiga, shi yasa na fasa dan ba zan iya bari a k’ullawa ɗana sharri ta sanadiyya ta ba. Na biyu kuma wani tsoron Allah ne ya dirar mun a zuciyata a lokacin, na ji ba zan iya farantawa ƙungiyar mutane ƴan’uwana na sabawa Ubangijin da ya halicce ni da laifika biyu ba, laifin zina da kuma laifin cutar da ita, na ji kawai koma me zai faru sai dai ya faru amma ba zan iya ba, sai kawai na fasa na fice na bar gidan. A lokacin ni addu’a nay ta yi dama ƙin aikatawar tawa yasa su kashe ni, amma ba su yi hakan ba sai faɗa da fatar baki kawai da sukay mun. A ranar har na je na dawo Fateemah bata san na fita ba, sakamakon maganin bacci dana zuba mata a lemo ta sha. Kuma ranar da wuri na kwanta na nuna mata a gajiye nake bacci zan yi, ina ganin bacci ya ɗauke ta na tashi na fice. A yau na ɗauka Sarauniya zata fille kaina ne saboda tsananin takaici da baƙin ciki, domin ba ƙaramin buri ta ci ba na mallakar BUDURCIN NEEHAL. Amma sai naga ba tay hakan ba, ta ce zamana a cikin ƙungiya ba ƙaramin cigaba yake ƙarawa ƙungiya ba, dan haka baza ta so su rasa ni a cikinta ba, sannan kuma tana sona ba zata iya cutar da ni ba, amma duk da haka sai ta hukunta ni, hukunci mai tsanani, kuma dole sai na aikata abun da suke so akan Neehal baza su haqura ba. Ban san dame zata hukunta ni ba dan bata faɗa ba. Amma ina fatan dama ta kashe ni in huta da wannan asararriyar bak’ar rayuwar da nake mara amfani. Wannan shine gaskiyar abun da yake faruwa.” Sai ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro.