NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A haka Ameen ya dawo ya same ta. Ta ɗaga kai a hankali ta kalle shi tare da amsa masa sallamarsa. Ajiye kayan hannunsa ya yi ya tsaya yana murmushi, ta gane mai yake nufi amma sai ta kasa motsawa balle ta tashi ta yi masa abun da yake jira. Ya ƙaraso inda take ya tsugunna a gabanta yana kallon fuskarta ya ce. “What happened Baby?” Ta lumshe idonta kawai bata ce komai ba. With so worry ya ce. “Oh My God, Baby me ya faru? Ko baki da lafiya ne?” Ya shiga tattab’a wuyanta da fuskarta. Girgiza masa kai kawai ta yi. Ya kama hannunta ya ce. “Please Baby tell me abun da ya faru, hankalina ya fara tashi da ganin yanayinki, ko wani abu ya faru da bana nan?” Ta buɗe idonta tana kallon fuskarsa, damuwa ta hango ƙarara a cikinta, sai ta ji tausayinsa ya cika mata zuciya, daga dawowarsa ta saka shi cikin damuwa, haka yake ko yaya ya ga ta ɗan canza yanzu zai rud’e ya yi ta tambayar ta abun da yake damun ta, in ya gan ta a cikin damuwa kuwa rasa inda zai saka kansa ya ji daɗi yake. Hannu ta kai ta fara shafa fuskarsa ta ce. “Babu komai fa Mijina, kewar ka ce kawai take damu na.” Ya saki ajiyar zuciya a hankali yana kallon cikin idonta ya ce. “Kin tabbata? Dan Allah idan wani abu yana damun ki Baby ki faɗa mun.” Ta ce. “Da gaske fa Dear babu komai.” Ya shafi cikinta ya ce. “Sorry My Boy, da na ƙi kula welcoming ɗinka, rigarmar Mamanka ta saka, yau ka hana ta bacci ka rama mana, Daddy missed you too.” Murmushi ta yi tana jin yanda yake shafa cikin nata a dukkan jikinta, ta shafi lallausar sumar kansa ta ce. “Dama can ai ba baccin ake bari na in yi ba.” Ya ce. “Ban da sharri dai Baby.” Sannan ya yi kissing cikin nata, lumshe idonta ta yi tana sauke numfashi. Ya miƙe ya koma kusa da ita ya zauna ya janyo ta jikinsa ya ce. “Baby! Akwai abun da yake damunki wallahi, dan Allah ki faɗa mun, ganin ki a haka yasa gaba-d’aya na rasa nutsuwata.” Ta saka hannunta ta rungume shi sosai tana shaƙar ƙamshinsa tare da sakin ajiyar zuciya, tabbas akwai abun da yake damun ta, kuma ba komai ba ne face yanda ta ga su Kawu Sani da halin matsin rayuwar da suka ce mata suna ciki, amma bata san ta ina zata fara faɗa masa ba. Ta fara shafa kafaɗarsa da hannunta ɗaya ta ce. “Da gaske yaya babu komai, Just I’m not in the mood.” Ya ce. “Sorry, bari na yi wanka sai mu fita, na san zaki jin daɗin hakan, ina kike son mu je? Gidan Mama ko gidan Aunty ko gidan Aunty Sadiya ko gidansu little Neehal ko gidan Kawu ko wani gurin daban?” Ta ce. “Gidan Mama, daga nan sai mu biya inga namesake ɗina sannan mu je mu sha ice-cream, Gobe sai mu je gidansu Auntyn.” Ya shafi kuncinta ya ce. “An gama Gimbiya Sarautar Mata.” Ta ce. “Sarautar Ameen dai.” Ya ɗago ta ya ce. “Me kika ce?” Ta yi dariya kawai. Ya ce. “Ni ban taɓa jin kin faɗi sunana ba sai yau, ƙara faɗa mu ji ko kin iya.” Kafaɗa ta mak’e masa. Ya ce. “Shikenan mu je in yi waka.” Ya miƙar da ita sannan shi ma ya miƙe suka shiga ɗakinsa. Ta taimakonta ya cire kayan jikinsa, ya ɗaura towel a k’ugu Sannan ya fara ƙoƙarin cire mata abayar jikinta. Ta riƙe hannunsa tana ɓata fuska dan ta san me yake nufi ta ce. “Ni fa ban jima da yin wankana ba.” Ya langwab’e kai ya ce. “Yanzu kuma taya ni zaki yi.” Cikin shagwab’a ta ce. “Ai na san ba iya wankan zaka tsaya ba, sai ka saka ni jik’a gashina da yamman nan.” Bai ce komai ba ya cire mata abayar, ya janyo ta jikinsa ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ce. “To ai ke ce Baby kullum ƙara kyau kike da…….” Saurin rufe masa baki ta yi dan ta san me zai ce. Murmusawa ya yi ya ɗauke ta cak ya nufi toilet da ita…….Suna hanyar zuwa gidan Mama ne take sanar masa da zuwan su Kawu Salisu, anan ya gane dalilin damuwartata. Washegari ya tambaye ta address ɗin su Kawu Salisu, ta faɗa masa ba tare da tunanin komai ba. Yana fita ya aika yaransa suka siyo kayan abinci masu yawa ya haɗa musu da kuɗi ya ba su address ɗin su Kawu Sani ya ce sukai musu, bai faɗa mata ba sai daga baya take jin labari wataran ta kai musu ziyara suke faɗa mata, su ma suka ce bai ce a ce in ji shi ba, yaran da suka kawo kayan ne suka kwatanta musu shi anan suka gane shi ne.

Haka rayuwa ta yi ta tafiya, kwanaki na shud’ewa. Mama ta yi nacin Ameen ya mayar da Hafsah amma ya ƙi, ya ce idan ya dawo da ita ya san ba zai yi adalci a tsakanin su da Neehal ba, dan haka gara bai kwasarwa kansa zunubi ba, dan shi a yanzu babu gurbin wata ƴa mace a cikin zuciyarsa, Neehal ta kanainaye ko ina, dama can tun fil azal ita ce a ciki, ya Auri Hafsat ne kawai saboda matsawar da Mama ta yi masa a time ɗin akan ya yi Aure. Ita ma Neehal ɗin tana yawan yi masa maganar ya mayar da Hafsat ɗin ɗakinta, amma duk sanda ta yi masa maganar basa kwashewa ta daɗi, dan fushi yake yi sosai ya ce dama ya san ba son sa take yi ba. Daƙyar take samu ta lallab’a shi ya sauko. Lokacin da cikin Neehal ya shiga wata tara idan mutum ya gan ta sai ya tausaya mata saboda girman cikin, ƙafafuwanta duk sun kumbubbura. Hana ta aikin komai Ameen ya yi, shi yake komai na gidan kafin ya fita, daga baya kuma Aunty A’isha ta turo musu Maryam ɗinta take taya ta zama da aikace_aikace. E.d.d ɗinta saura one week Mama ta je ta ɗauko ta, ta dawo da ita gida. Ameen bai so haka ba amma babu yadda zai yi, sai dai kusan raba dare yake a gidan kafin ya tafi, a hakan ma sai Mama ta kora shi. Neehal tay ta yi masa dariya. Zuwa wannan lokacin Hafsah ta tabbatar Ameen ba zai taɓa dawowa gare ta ba, ta yi kuka ta yi dana sani mara iyaka, daga baya ta haqura ba dan ta daina son shi ba, sai dai fa har a yanzu tsanar Neehal na nan a cikin ranta, musamman da take ganin kamar ita ce silar rabuwar su da Ameen. An yi bikin Hameedah da wani abokin aikinta mai Mata da yake nacin son ta, a da ta ƙi shi sai da taga bata da kowa sai shi sannan ta amince masa, Tunda Ameen ɗin da take nacin so baya ta ita. Neehal bata je bikin ba saboda time ɗin ta yi nauyi sosai. Matar Ahmad ma ta haifi ɗanta Namiji watanni uku da suka wuce, su Afrah an yi k’ani sai murna, yanzu ma kullum cikin murna suke Auntinsu ta kusa ƙara haifo musu new Baby……..

Ranar wata Alhamis cikin dare Neehal ta fara jin ciwo a jikinta, kusan kwana uku kenan tana jin jikin nata babu daɗi, amma ciwon na yau ya fi na kullum. Tun tana yi tana daurewa har ta fara nurk’ususu tare da salati, Mama take Sallah ta sallame ta yi kanta. Ganin Haihuwa ce ta kira Daddy a waya ta sanar masa, cikin hanzari ya baro part ɗinsa suka ɗauke ta da su kai asibiti da ita bayan Mama ta ɗauki duk abun da ake buƙata, Asibitin Nasarawa suka je inda Maman take aiki, dama a can take yin awu. Haka kawai Ameen ya ji ya kasa bacci a daren ranar, sai tashi ya yi ya yo alwala ya shiga yin Sallah. Mama da kanta ta karb’i haihuwar Neehal, sai kusan asuba Allah ya sauke ta lafiya ta santalo Ƴaƴanta Maza guda biyu masu tsananin kama da mahaifinsu. Ba tare an goge musu jiki ba Mama ta rungume su idonta cike da ƙwallar farinciki, sannan ta ɗorawa Neehal su duka akan cinyarta. Neehal tana kallon su ta ji gaba-d’aya zafin wahalar labour da ta sha ta gushe daga cikin zuciyarta, wata zazzafar k’aunar yaran ta maye gurbin su. Mama ta lek’a ta faɗawa Daddy ta ce ya kira Ameen ya sanar masa. Kiran sa Daddy ya yi ya ce masa ya zo suna asibiti Neehal ta haihu, ba tare da ya faɗa masa abun da ta haifa ba. Ga mamakin Ameen sai ya ji hankalinsa ya tashi, mukullin Motor kawai ya ɗauka ya fice cikin sauri. Sam zuciyarsa bata ta Babyn da ka haifa tana ga Neehal, so yake kawai ya gan ta ya ga halin data ciki, ya ga lafiyar jikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button