NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

4️⃣2️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

……….Lamo ta yi a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya tare da barin kukan da take. A hankali ya d’ago ta daga jikinsa yana dubanta da murmushi akan fuskarsa ya ce “Je ki wanke fuskarki ki zo ki raka ni unguwa.” Ta gyaɗa masa kai tare da miƙewa ta shige ɗakinta. Ya bita da kallo cikin sauke numfashi. Miƙewa ya yi shima ya shiga ɗakin Mama. Bayan ya yi sallama ta amsa sun gaisa ya zauna a gefenta tare da faɗin “Mum ki taya ni murna, next month zan dawo Kano da aiki Insha Allah.” Mama ta ce “Masha Allah, na ji daɗin hakan sosai, ka ga an huta da fargabar barin Hafsah ita kaɗai a gida.” Ya ce “Hakane, bari in je masallaci na ga lokacin Sallah ya gabato, idan na dawo zamu fita da ƴarki.” Mama ta ce “Fita kuma? Zuwa ina?” Ya ce “Unguwa.” Ta ce “Ita unguwar bata da suna?” Yana miƙewa ya ce “Sirri ne tsakanin Yaya da ƙanwarsa.” Mama ta tab’e baki ta ce “Kamar gaske.” Ya yi murmushi kawai tare da ficewa daga ɗakin. Itama Neehal data shiga toilet bayan ta wanke fuskarta ganin Magriba ta gabato sai ta ɗauro alwala ta fito. A gaban mudubi ta tsaya ta ɗan gyara fuskarta ta saka kwalli a idanunta saboda kukan da ta yi. Bata canza kaya ba, mayafi kawai ta ɗauko ta yafa ta ajiye hijabin da yake jikinta. Ɗakin Mama ta shiga dan sanar mata Ameen ya ce za su fita, zuciyarta cike da mamakinsa dan ta manta rabon da su je unguwa ko wani gurin tare da shi, dan tun da ko Mama ta ce ya kaita School ko gurin aiki sai ya haɗa ta driver, ya ce shi ba direbanta ba ne. Ta tarar Mama tana toilet tana alwala, ganin ƙofar toilet ɗin a buɗe ta ƙarasa bakin ƙofar ta ce “Mama Yaya ya ce zamu fita yanzu.” Mama ta ce “Ya faɗa mun, amma ai kya ci abinci kafin ku tafi.” Ta ce “Bana jin yunwa.” Mama ta ce “Shikenan ai, ki je ki yi sallah kafin ya dawo, shima ya je masallaci.” Neehal ta ce “Toh.” Ta dawo cikin ɗakin ta ɗauki darduma ta shimfid’a ta zira hijabin Mama ta tayar da Sallah. After some minutes Ameen ya shigo ɗakin, yana duban Neehal ya ce “Tashi mu je kar dare ya yi.” Mama ta ce “Allah ya tsare, saura kuma kafin ku dawo ka samun ita kuka, dan na san hali.” Ya yi ɗan murmushi bai ce komai ba. Neehal ta yiwa Mama Sallama suka fice a tare. Yanda ta bar Haj.saratu da Hameedah haka suka sauko suka same su, da alama ko tashi sun je sun yi sallah ba su yi ba. Ba suce musu ƙala ba suka fice, su kuma su Hameedan suka raka su dana mujiya. Bayan fitarsu Hameedah ta dubi Mahaifiyarta ta ce “Sabon salo b’arawo da sallama, ko ina kuma za su a daren nan?” Haj Saratu ta ce “Oho musu, amma ni fa na fuskanci take_taken Haj. Fatima so take ta aurawa Ameen shegiyar yarinyar can.” Hameedah ta lailayo ashariya ta ce “Tab’dijan, da kuwa an yi ƙaramin yaƙi a family wallahi, ta hana shi aure na sannan kuma ta aura masa wata can bare.” Haj Saratu ta ce “Hmmmm, ba dai tak’amarta ita ta haife shi ba, to ai ba ɗanta ba ne ita kaɗai, wallahi matuƙar ta ce zata aurawa Ameen yarinyar nan da taƙi auruwa sai na yi sanadin barinta gidan nan, mu zuba mu gani ni da ita.” Cikin damuwa Hameedah ta ce “Mommy ni duk ba wannan ba ma, wai ya batun aure na da Ya Ameen ne? kin ce mun wannan zuwan da mukai akan maganar auren ne, kuma ban ga wata alama data nuna hakan ba, ni fa gaskiya na gaji da gafara sa ban ga k’aho ba.” Ta ƙarashe maganar cikin botsarewa. Mommy ta ce “Me kike ci na baka na zuba ne? Ki bari ki ga me zan yi mana, akwai shirin da nake yi, da zarar ya kammala zaki sha mamaki, ke dai ki kwantar da hankalinki bana son kina damuwar nan.” Hameedah ta sauke numfashi cikin damuwa, ita yanda Ameen yake nuna halin ko in kula da ita yafi komai d’aga mata hankali, gashi ita babu wani wanda yake zuwa gurinta a yanzu da sunan saurayi. K’awayenta duk sun yi aure, ita ga kuɗin ga aiki tana yi amma babu mashinshini duk da uwar maganin farin jinin da uwarta take dirka mata.

Sai da suka shiga Mota sannan Neehal ta dubi Ameen ta ce “Yaya ina zamu?” Ba tare da ya kalle ta ba ya ce “Siyar dake zan yi.” Jin haka yasa ta ja bakinta ta tsuke. Har suka ƙarasa wani had’ad’d’en Bakery dake cikin Nasarawa babu wanda ya ce uffan. Ya yi parking ɗin Motar ya fito itama ta biyo bayan shi suka shiga gurin. K’amshin abinci irin me tsinka yawun nan ne ya fara musu welcome. Gurin ya haɗu sosai kuma babu hayaniya ko kaɗan. Suka zauna a kujerun dake zagaye da table suna fuskantar juna. Ameen ya ɗauko wayarsa ya shiga latsawa, ita kuma ba ta fito da waya ba ta baro ta a gida, kallon gurin kawai take cike da burgewa. Wani ma’akaicin gurin ya kawo musu takarda mai ɗauke da duk wani abu da suke siyarwa a gurin tare da price ɗinsa. Ameen ya karɓa ya duba tare da selected ɗin abun da za’a kawo musu. Bayan mintuna biyar ma’aikacin ya dawo ɗauke da madaidaitan plates guda biyu a hannunsa, a gaban Neehal ya ajiye su duka kamar yadda Ameen ya ce masa. Neehal ta kalli snacks ɗin yawunta na tsinkewa saboda k’amshin daya bugi hancinta. Plate na farko meatpie ne a ciki da Spring rolls da samosa. Plate na biyu kuma Pizza and shawarma ne a ciki. Sai kuma Juice and bottle water a gefe, sai tissue. Ba tare da Ameen ya kalle ta ba yana cigaba da latsa wayarsa ya ce “ki yi sauri ki ci.” Ta dube shi ta ce “Kai fa?” Ya girgiza mata kai alamar a’a. Ba ta kuma cewa komai ba, ta yi Bismillah ta fara ci cikin nutsuwa. Cin abincin Neehal babu sauri, kafin ta gama fiye da mintuna ashirin sun wuce, kuma bai fi rabin abun da aka ajiye mata ta ci ba. Bayan ta gama, ya je ya biya kuɗin tare siyan wasu snacks ɗin, a leda biyu aka masa packaged, ya karbo suka baro gurin. Daga nan gurin shan Ice cream da siyar da su chocolate ya kai ta, suka shiga ya ce ta ɗibi abun da take so. Neehal masoyiyar choculate da wafer ta diba son ranta ya biya kuɗin suka fito suka nufo gida, lokacin har an yi isha’i. Suna hanya Hafsah ta kira shi, da ya duba ya ga ita ce sai ya ƙi d’agawa. Sun kusa zuwa gida ta ji Muryarsa ba tare da ya juyo ba ya ce “Ko mu ƙara zuwa wani gurin?” Neehal ta ce “A’a dare ya yi.” Ya ɗan kalle ta ya ce “Ko dai wannan saurayin naki ne zai zo kike sauri ki koma gidan?” Ta ce “A’a wallahi, ka san idan muka daɗe Mama za ta yi faɗa.” Ya ce “Hmmm.” Kawai. A parking space ya ajiye ta bayan sun ƙarasa gida, ya bata ledodin ta ya ce ta gaishe da Mama shi ya wuce, ta yi masa godiya sannan ta nufi part ɗin Mama. Tana jin zuciyarta ta mata sanyi akan bata mata ran da Haj Saratu ta yi. Sosai ta ji daɗin fitar nan da sukai, ko dan ta daɗe bata fita irin guraren nan ba ne?

Bata tarar da su Hameedah a falo ba, da alama sun shige ɗaki, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi ya mata ba. Ɗakin Mama ta nufa ta tarar da ita tana shirya kaya a wardrobe. “Mama na dawo.” Ta faɗa tana zama a gefen gado. Mama ta ce “Sannunki da zuwa, ina Ameen ɗin?” Ta ce “Ya wuce gida.” Mama ta ce “Ina kuka je ne?” Neehal ta ce “Wani Bakery ya kai ni, sai kuma muka biya muka siyi Ice cream.” Mama ta ce “Shine dan wulaqanci ba zai je da Matarsa ba sai dai ya zo ya ɗauke ki.” Neehal ta yi dariya ta ce “Kai Mama, itafa ta zama cuss yanzu tunda matar Aure ce, da ƴan mata ake fita, kuma itama ya siya mata nata, kema ga naki ya ce na kawo miki.” Mama ta ce “Ko ma da jarirai ake fita daga yau ya dinga fita da matarsa.” Mama ta ƙarasa zancen tana duba ledar da Neehal ta ajiye. Neehal ta miƙe ta ce “Bari na je na yi sallah.” Mama ta ce “Alright.” Tana shiga bedroom ɗinta ta dauko wayarta, kamar yadda ta zata missed call ɗin Sadik ta gani har biyu. Tana ƙoƙarin bin bayan kiran nasa wani kiran ya shigo amma da new Number. Ta d’aga ba tare da ta ce komai ba. Muryar Amrah ta ji ta ce “Hello Aunty.” Neehal tana murmushi ta ce “Sweetheart, ke ce? ya kike?” Amrah ta ce “Lafiya k’alau Aunty, yaushe zaki zo?” Neehal ta ce “Soon Insha Allah, ina Afrah?” Ta ce “Tana toilet tana pupu.” Neehal ta ce “Ina Ummi da Aunty Zahra?” Amrah ta ce “Suna gida, mu kuma muna gidan Daddy.” Neehal ta ce “Anan zaku kwana?” Ta ce “A’a, idan Afrah ta fito daga toilet Daddy zai mayar da mu gidan Ummi.” Neehal ta ce “To ƴar gidan Daddy ina Daddy’n?” Amrah ta ce “Gashi nan, yana jinki.” Ta ce “To ki gaishe shi.” Muryarsa ta ji a maimakon ta Amrah, cikin marairaicewa ya ce “Uhm, ke baza ki gaishe ni da kanki ba kenan?” shiru ta yi, jin muryarsa a bazata yasa ta ji wani abu a cikin zuciyarta, har da lumshe idanunta ba tare data sani ba, tare da tunanin a ina kuma ya samu Numbern’ta? ‘A gurin Zahra.’ zuciyarta ta bata amsa. A kasalance gami da shagwab’arta ta ce “Ina yini.” Ya kwaikwayi muryarta ya ce “Lafiya k’alau Aunty, ya Mama.” Ta turo baki gaba kamar yana kallonta ta ce “Tana nan k’alau.” Ya ce “My regard to her.” Daga haka ya miƙawa Amrah wayar jin Afrah tana kwad’a masa kira daga toilet. Suka ci-gaba da hira da Amrah tana bata labarin school ɗin da aka mayar da su, har Afrah ta fito daga ta karb’i wayar tay ta mata surutun ta itama, ganin dare yana yi Ahmad ya ce su mata sallama zai mayar da su. Bayan sun gama wayar ta bi wayar da kallo kamar zata ga yaran a cikin wayar. Sosai take jin kewarsu a cikin ranta, musamman in ta zo bacci sai ta ji gadon ya mata faɗi ita kaɗai, ta saba da, da twins manne a jikinta. Tashi ta yi ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da dauro alwala ta fito ta yi Sallar isha’i. Bayan ta idar ta kira layin Sadik amma bai ɗauka ba, hakan yasa ta kunna data ta shiga yanar gizo. Jimawa kaɗan Sadik ya kira ta, ta d’aga da sauri dan yau gaba- ɗaya ba su yi waya ba, ta yi kewarsa ba kaɗan ba…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button