NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:33] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

1️⃣0️⃣

………… Ameen ya yi shiru tare da sunkuyar da kansa ƙasa. Mama ta na duban Dad ta ce “Kai ka biye masa ai, ban da haka mene aibun Hameedan da zai ce ba ya sonta?” Dad ya ce “Haba Doctor, kin san dai ba zan yi masa auren dole ba tunda ba ya sonta Shikenan.” Dad ya maida dubansa ga Ameen ya ce “Kai muke sauraro.” Ameen cikin dakiyarsa ya ce “Hafsah!” “Hafsat kuma?” Mama ta tambaya cikin mamaki. Ameen ya gyad’a mata kai. Mama ta ce “Dama har yanzu ku na tare da ita ?” Nan ma kan ya kuma gyad’a mata. Dad ya na murmushi ya ce “Masha Allah, A Ina ita Hafsan take? ‘Yar waye?” Mama ta ce “Hafsat fa ‘yar gidan Alhaji Nuhu Ɗan gaske” Dad ya ce “Allah sarki, to Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, Insha Allahu a satinnan zan samu shi Mahaifinnata mu yi magana, a san abun yi.” Mama ta ce “To Allah ya tabbatar da Alkhairi” Dad ya ce “Amin” Ameen ya mik’e kansa a ƙasa ya fice daga falon, Mama ta bishi da kallo cikin mamakin shi, maida kallonta ta yi ga Dad bayan ya fice ta ce “Al’ameen halinsa sai shi, yarinyar nan Hafsat ba irin son da ba ta nuwa masa ba a baya, amma ya nuna ba ya son ta, yanzu kuma da bakin shi ya dawo ya ce ya na sonta” Dad ya ce “Haka Al’amarin Allah yake, kin san matar mutum kabarinsa, wata ƙila duk wannan abun da ake itace matar tasa” Mama ta ce “Hakane, Allah ya sa Albarka ya sa da mu za’a yi.” Dad da fara’a ta ƙi bacewa daga fuskarsa ya ce “Amin.” Mama ta ce “Um, sai wata fara’a kake kamar an maka wani albishir ɗin.” Dad ya yi ‘yar ƙaramar dariya ya ce “Wlh ba ki ji yanda farin ciki ya lullub’e ni ba da Ameen yau ya furta mun ya fidda mata, dama ni tsoro na kar mu bashi mata a zo a samu matsala zumuncinmu ya ɓaci.” Mama ta ce “Gaskiya kam, amma Ni na so Ameen ya auri Hameedah, ko dan yanda take k’aunarsa, ga ta kuma jininsa ce, yanzu idan Family suka ji zancen nan ya kake ganin za su ɗauki maganar, tunda kowa ya na tunanin Ameen Hameedah zai aura, ita kanta Hameedan ban san wanne hali za ta shiga ba idan ta ji wannan zancen.” Dad ya gyad’a kai ya ce “Nima na so hakan Doctor, Amma kin san yaran yanzu ba’a musu dole, ni ba na so a samu matsala ne, shi ya sa ban tursasawa Ameen a kan lallai sai ya Auri Hameedah ba, itama Allah ya fito mata da miji na gari ta yi auranta.” Mama ta ce “Amin ya Allah.” Wayar Dad ce ta fara ringing, dubawa ya yi sai kuma ya saci kallon Mama, ƙin d’aga wayar ya yi har ta katse, aka kuma kira ya kuma ƙin d’agawa. Mama ta ɗauke kai kamar ba ta gani ba, kiran da aka kuma yi ya sa Mama mik’ewa tsam ta zagaya ta ɗauki wayar ta duba, Dad ya yi murmushi ya na kallonta ya ce “Ba wata ce take kirana ba sarkin kishi.” Mama ta haɗe rai ta ce “Hubby! Har yanzu dama ka na tarayya da Alhaji Kabir Ginyau ?”  Dad ya riko hannun Mama tare da zaunar da ita a gefensa ya ce “Ehh, amma ba tarayya irin wadda muka yi da ba, kawai dai mu na gaisawa ne sama_sama.” Mama ta ce “Amma…” Dad ya d’aga mata hannu cikin lallami ya ce “Kin ga Doctor, Dan Allah kar ki tada hankalinki a kan dan Kabir ya kira ni, yanda kike tunanin abun kwata_kwata ba haka yake ba.” Mama ta yi shiru kawai ta na kallonsa.

Washegari da safe Neehal ta na kitchen ta na yin breakfast Ameen ya shigo part d’in, ganinta a kitchen d’in ya sashi shiga kitchen d’in. Neehal ta juyo ta na kallonsa jin k’amshin turarensa, a hankali ta ce “Ina kwana Yaya?” Ameen ya ce “Lafiya k’alau, ina Mama fa?” “Ta na d’akinta” Neehal ta bashi amsa ta na satar kallonsa, shima kallon nata yake yi hakan ya sa suka haɗa ido. Neehal ta ɗauke idonta da sauri ta na turo bakinta gaba. “Idan kin gama ki kawo mun nawa breakfast d’in part d’ina.” Ya fadi haka tare da juyawa ya fice, Neehal ta bishi da kallo kawai.
Mama ta na zaune a kan darduma ta na karatun Alkur’ani mai girma ya shigo d’akin, sai da ta kai ƙarshen aya sannan ta rufe ta d’ago tare da amsa masa sallamar da ya yi. Ameen ya zauna a gefenta ya ce “Ina kwana Mom, dafatan kin tashi lafiya?” Mama ta ce “Lafiya k’alau, and you?” Ya ce “I’m fine.” Mama ta ce “Masha Allah, am Ameen dama ina son na tambayeka.” Ameen ya dubi Mama amma bai ce komai ba. Mama ta ajiye Kur’anin hannunta a kan bedside locker, sannan ta fuskance shi da kyau ta ce “Me ya sa ka ce ba ka son Hameedah?” Ameen cikin nutsuwarsa da sanyin muryarsa ya ce “Mama! Kin san wace Hameedah kuma kin san halinta, kwata_kwata ba ta da qualities d’in matar da zan iya aura.” Mama ta ce “Na san da haka Ameen, amma ba ka tunanin yanda Family’n Dad d’inka za su ɗauki abun? Kowa zai yi tunanin Ni na hanaka auren Hameedah saboda ba ma shiri da Mahaifiyarta.” Ameen ya tab’e ɗan ƙaramin bakinsa sannan ya ce “Kar ki damu kanki Mama da su, su faɗi duk abun da za su faɗa.” Mama ta tsura masa ido kawai ba ta ce komai ba. Kawar da zancen ya yi ta hanyar faɗin “Yaushe wacce old Woman d’in za ta tafi?” Mama ta ce “Bansani ba, tunda uwar tawa ce Old Woman.” Ameen ya mik’e ya na faɗin “Tunda ba za ki faɗa mun ba zan tambaye ta da kaina.” Ya ƙarashe maganar tare da ficewa daga d’akin. D’akin Hajiya ya leƙa ya tarar da ita a kan darduma ta na lazimi ta na gyangyad’i, ya yi murmushi kawai ya juya ya fice. Neehal ta na gab da kammala aikin da take Mama ta shigo kitchen, Neehal ta kwab’e fuska tare da turo baki gaba. Mama ta dube ta, ta ce “Sannu Daughter.” Neehal ta ce “Yawwa Mama, kin fito.” Mama ta ce “Eh, amma ba yanzu zan fita ba, kawo na ƙarasa aikin ki je ki yi azkar ɗin safe dan nasan ba ki yi ba.” Neehal ta ce “Toh Mama.” Harta fita daga kitchen d’in sai kuma ta dawo, Mama ta kalleta da alamun mamaki amma ba ta ce komai ba, Neehal kanta na ƙasa ta ce “Yaya ya ce in kai masa break ɗinsa part ɗinsa.” Mama ta ce “Yanzu dawowa ki kai masa?” Neehal ta ce “Ehh.” Mama ta ce”Ki wuce ki yi abin da na ce miki, zan bayar a kai masa.” Neehal ta turo baki sannan ta juya ta fice. Bayan ta gama azkar ɗin ta sakko ƙasa ta na break Mama ta ce mata, “Za ki aiki ne yau?” “A’a.” Neehal ta bata amsa. Mama ta ce “Idan kin gama ki shirya ki je gidan Sadiya, daga nan sai ki biya gidan A’isha, su na ta complain kin dena zuwar musu 2 days.” Neehal ta yi murmushi ta ce “To Mama, bari na kira besty mu je tare.”

Kafin azhar su Neehal sun je gidan Aunty Sadiya, Aunty Sadiya ta tare su da fara’a sosai, bayan sun gaisa ta kawo musu drinks su na zaune a falo Aunty Sadiya ta dubi Neehal ta ce “Ni kuwa Daughter Ina son in miki wata tambaya.” Neehal ta maida hankalin ta duka a kan Aunty Sadiya ta ce “Ina jin ki Aunty.” Aunty Sadiya ta ce “Ki na da saurayi bayan Anwar ne?” Neehal ta ce “A’a, dan gaskiya ba na kula duk masu nuna suna so na, tun daga lokacin da a ka yi Engagement ɗinmu da Anwar.” Aunty Sadiya ta ce “Babu wani wanda yake son ki tun da dad’ewa kafin haɗuwar ki da Jameel, kuma har yanzu ya na nuna ya na sonki?” Neehal ta ce “Ban gane ba Aunty?” Aunty Sadiya ta ce “Ina nufin kamar shekaru Biyar da suka wuce, ba ki yi wani saurayi da ya nuna ya na sonki ba, kuma har yanzu bai daina son ki ba.?” Neehal ta yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce “Gaskiya ba na jin akwai, idanma da akwai na manta.” Aunty Sadiya ta gyad’a kai sannan ta maida dubanta ga Haneefah da take saurararsu ta ce “Ke fa Haneefah ko kin sani?” Haneefah ta ce “Gaskiya samarin Neehal na baya duk sun hak’ura da ita, wasu ma sun yi Aurensu.” Aunty Sadiya ta ce “Alright.” Neehal ta ce “Amma me yasa ki ka mun wannan tambayar Aunty?” Aunty Sadiya ta ce “Kawai.” Daga haka suka shiga wata hirar. Sai bayan la’asar suka bar gidan Aunty Sadiya, wadda cikin hikima take yi wa su Neehal tambayoyi domin samun wani information d’in da zai taimake ta gurin binkicen da take. Kamar yadda Mama ta ce gidan Aunty A’isha suka wuce, nanma sun sha hira da Aunty A’isha sai bayan sallar Magriba suka yi haramar tafiya, shima sai da Mama ta kira su ta ce “Ko kwana za su yi a nan ɗin ne?” . Neehal ta na ɗaukar hand bag d’inta ta ce “Toh Aunty mun tafi sai gani na biyu.” Aunty A’isha ta ce “Yanzu ba za ku jira driver’n ya dawo ya kai ku ba tafiya za ku yi?” Neehal ta ce “Gwara mu tafi Aunty, tunda ba mu sani ba ko ba zai dawo da wuri ba, gashi kin kira wayarshi ta ƙi shiga balle mu ji in ya na kusa mu jira shi.” Aunty A’isha ta ce “Toh Shikenan, ku gaida gida, ku gaida su Hajiya da Yaya Fatimah.” Neehal ta ce “Za su ji Insha Allah.” Haneefah ta yi wa Aunty A’isha sallama, Aunty A’isha ta ce ta gaida Mamanta sannan suka tafi. Suna fitowa daga gidan Haneefah ta dubi Neehal ta ce “Wai me ya sa ba za ki kira driver’nki ya ɗauke mu ba?” Neehal ta ce “Kawai yau Napep nake so mu hau.” Haneefah ta ce “Kin shiga uku da tsurfa, ko mai ciki haka ta ganki ta k’yale.” Neehal ta ce “Na ji ɗin.” Suna tafiya suna hirarsu, sun zo dai_dai ƙarshen layinsu Aunty A’isha za su fita titi wata had’ad’d’iyar Mota ta shigo layin, kamar ance Neehal ta kalli Motar suka haɗa ido da ma mallakin motar wanda ya kasance saurayi, kuma a ka yi sa’a ya zuge glass d’in Motar, wata irin fad’uwar gaba Neehal ta ji dalilin haɗa ido da suka yi da shi, da sauri ta ɗauke kallonta daga gurin Motar bugun zuciyarta na sauyawa………..✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page