NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

7️⃣6️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.

……….Idanunta suka sauka akan kyakkyawar kamilalliyar fuskarsa mai cike da kwarjini, ta yi ƙoƙarin ɗauke kallon ta daga fuskarsa amma ta kasa. Wani irin kallo yake mata wanda yasa ta ji wani irin abu yana yawo a cikin jinin jikinta, kamar yadda zuciyarta take bugawa da ƙarfi. Kallon sa take yi yau as husband to be not as brother before, tunanin hakan yasa ta ji gabanta ya yi wani irin mugun faɗuwa, ya sakar mata wani murmushi wanda zata iya cewa ba’a taɓa murmushin da ya kayatar da ita kamar shi ba. Ta lumshe idonta da sauri wani baƙon abu yana cika zuciyarta a kansa, like kunya ko tsoro. Ta yi baya da sauri tare da buɗe ido tana ɗan turo baki gaba, zuciyarta ta bata shawarar ta zura da gudu ta koma ɗakinta, har sai ya bar gidan sai ta fito. Ta juya cikin sauri amma ko ɗaga ƙafarta bata yi ba ya kamo hannunta, ta juyo kamar zata yi kuka dan abun da take ji a game shi ƙara yawa yake yana neman hautsina mata zuciya, kuma bata taɓa jin hakan a gare shi ba a rayuwarta sai yau. Ta saci kallon fuskarsa ta ga ya haɗe rai kamar ba shi ya yi murmushi yanzu ba, ya tsatstsare ta da kyawawan idanuwansa wanda suke ƙara mata yawan abun da take ji a kansa a cikin zuciyarta. Murya ƙasa_ƙasa ya ce. “Can’t you great me?” Ta shiga girgiza kai tsoronsa na ƙaruwa a ranta, cikin rawar murya ta ce. “Ina yini?” Bai ce komai sai kallon fuskarta da yake yi kamar mai neman wani important thing a fuskar. Ta yi ƙasa da kanta a ranta tana addu’ar Allah yasa Mama ta fito ko ta samu ya bar ta. Tana ji ya saki ajiyar zuciya a hankali sannan ya sakar mata hannu without saying anything ya nufi ɗakin Mama. Ta bi bayan shi da kallo tare da murgud’a baki, ganin kamar zai jiyo ta buɗe ƙofa ta fice da gudu. Ya juyo jin ƙarar buga ƙofa, ya girgiza kai kawai tare da yin murmushi sannan ya shige ɗakin Mama.

Mama tana shirya gogaggun kayanta a wardrobe ya shigo ɗakin da sallama. Ta amsa masa ba tare da juyo ta kalle shi ba. Ya zauna akan bedside drower tare da gaishe ta. Ta amsa masa tana rufe wardrobe ɗin sannan ta ƙaraso ta zauna a bakin gado. Tana duban sa cike da kulawa ta ce. “Ya su Hafsah?” Ya ce. “Lafiya k’alau.” Mama ta ce. “Dafatan dai lafiya, tun ranar Friday rabon ka da gidan nan.” Ya ce. “Lafiya k’alau Mum, weekend ɗin nan ban fita ba a gida nake wuni.” Mama ta ce. “Okay.” Sun taɓa hira kaɗan wadda majority akan aiki ne sannan ya yi mata sallama ya tafi. Bata yi masa zancen Neehal ba shi ma bai yi mata ba. Neehal kuwa tunda ta sauka ƙasa tana sauke numfashi ta shige ɗakin su Dije, ko abincin ma bata je ta ɗebo ba saboda tana tsoron kar Ameen ya sakko su ƙara haɗuwa, sai da ta ga fitarsa ta window’n ɗakin su Dije sannan ta fito. Da daddare Mama ta yi mata zancen Ameen akan jin ra’ayinta, dan Kawu Musa yau wayarsa biyu akan jin inda maganar ta kwana. Shiru ta yi ƙirjinta na luguden bugu. Mama dake kallon ta cikin nazari ta ce. “Neehal, ki kalle ni as your Mother ba mahaifiyar Ameen, ki faɗa mun abun da yake ranki kamar yadda kike faɗa mun a kodayaushe kin ji ƴar albarkata.” Ta gyaɗa kai a hankali sannan ta ce. “Na amince.” Mama ta ce. “Kin amince da me?” Ta kwantar da kanta a ƙafaɗar Mama ta ce. “Kin sani fa.” Mama tana murmushi ta shiga shafa bayanta ta ce. “Da gaske Daughter maganar da kike faɗa mun tun daga zuciyarki take, bana son ki yi abun da ba kya so, in ba kya so you are free to say, no body will force you.” Ta ƙara shigewa jikin Mama ta rufe fuskarta da hannunta ta ce. “Allah da gaske nake Mama.” Mama ta faɗaɗa fara’a akan kyakkyawar fuskarta cikin tsokana ta ce. “Kina son Ameen ɗin kenan?” Da sauri ta cusa fuskarta ta ɓoye a jikin Mama tare da turo baki gaba. Mama ta shafa kanta cikin tsananin farincikin data manta rabon da ta yi kamarsa ta ce. “Masha Allah Neehal, Allah ya yi miki albarka ya inganta rayuwarki, ya baki ƴaƴa masu ladabi da biyayya kamar ki, Allah ya baku zaman lafiya yasa haka shi ya fi Alkhairi.” Ta amsa da Amin a cikin zuciyarta. Ba ta kallon fuskar Mama amma a muryarta kaɗai tana jin irin farincikin da take ciki, kuma duk saboda ta amince da Auran Ameen ne, ina ga Daddy? Shi wanne irin farinciki zai ji idan ya ji wannan batun? Su saunawa suka saka ta a cikin farinciki a rayuwarsu? Babu adadi. Kenan data ƙi amincewa haka zasu ji babu daɗi a cikin ransu? Gwara da Allah yasa bata yi wannan gatobarar ba. Ta san bata son Auren Ameen ko kaɗan a cikin ranta, amma ta yiwa kanta alƙawari zata danne ta daure ko a fuska baza ta bari a gane ba, zata saka a ranta Allah ya yi Ameen ne mijinta, zata karb’i Auransa hannu bibbiyu idan Ubangiji ya yi hakan ta kasance. Amma tana mamaki da girmama abun a cikin zuciyarta ba kaɗan ba, YAYANTA MIJINTA, ko a mafarki bata taɓa tunanin hakan zata iya faru ba, ita mantawa ma take akwai aure a tsakaninsu da Ameen. As blood brother desame mother desame father take kallon shi. Wasu hawaye da bata san kona mene ba ta ji suna rige_rigen gudu akan kuncinta daga cikin idonta. Ta ƙara rungume Mama tare da fara kuka a hankali. Mama ta shiga bubbuga bayanta tare da faɗin. “Kunan na mene ne?” Ta ja majina bata ce komai ba. Mama ta d’ago da kanta tana kallon yanda take kukan ta ce. “Mene ne wai?” Ta girgiza mata kai kawai. Mama ta ce. “Iskanci ne kenan?” Cikin kukan ta ce. “Bana son na bar ki ne Mama.” Mama ta yi murmushi tana jin tausayinta na cika mata zuciya, ta shiga share mata hawayen fuskarta tana faɗin. “Wa ya ce miki zaki bar ni dan kin yi Aure? Duk sanda kike son gani na zaki zo ki ganni ai.” Cikin shagwab’a ta ce. “Ke baza ki zo ki dinga gani na ba?” Mama ta yi murmushi ta ce. “Zan zo mana, Amarya tun kafin a yi Aure har an fara zancen zuwa gida.” Ta cusa kanta a jikin Mama cikin tsananin jin kunya. Mama ta ƙara rungume ta a jikinta tana jin tsananin farinciki a ranta, tabbas kamar yadda Daddy ya faɗa bata jin akwai wanda zai kai ta farinciki idan wannan al’amarin ya kasance. Bayan Daddy ya dawo Mama ta sanar masa yanda suka yi da Neehal. Farincikin da ya nuna ba zai misaltu ba, ya kira Neehal ta zo part ɗinsa wadda gaba-d’aya yanzu ta ji tana jin kunyarsa, ya dinga saka mata albarka tare da tarin addu’oi, har da tambayarta me take so ya yi mata a rayuwar nan wanda zata ji daɗi? Ta ce masa babu komai ai ita ya gama yi mata komai a rayuwa. Ta kasa tantance tsakanin shi da Mama wa ya fi wani farinciki da amincewarta. Da daddaren Ameen ya kuma dawowa gidan, Neehal tana falon ƙasa tana kallon wani series firlm ɗin India da take matuƙar so, bata ji sallamarsa ba sai k’amshinsa ne ya sanar mata da zuwan sa. Ai kuwa da sauri ta miƙe ta nufi upstairs, ya bi ta da kallo kawai yana sakin wani munafukin murmushi. A balcony suka ci karo da Mama, garin saurin da take har da tuntube ta yi. Mama ta ce. “Subhallahi, ki dinga kallon gabanki mana kina tafiya a hankali, kuma lafiyarki kuwa na gan ki kamar a firgice?” Tana sassauke numfashi ta ce. “Babu komai.” Tare da shigewa falo. Mama ta tab’e baki ta sauka ƙasa abinta. Ta tarar Ameen ya zauna har lokacin bai bar murmushin da yake yi ba, ta yi masa wani kallo sannan ta zauna a kujerar dake facing ɗinsa. Suka ƙara gaisawa sannan Mama ta ce masa. “Ya na ga ka dawo?” Ya kama haɓa da hannunsa ɗaya ya ce. “Oh Mum, dan na dawo gidanmu laifi ne?” Mama ta ce. “Baka da gaskiya ne shi yasa na tambaya.” Ya waro ido ya ce. “Rashin gaskiya kuma Mum?” Mama ta ce. “Ka fi ni sanin me ka yi ai.” Ya yi murmushi ya ce. “I don’t know fa.” Mama ta ƙara ta tab’e baki ta ce. “Ai baza ka taɓa sani ba, wannan muskilancin naka yana k’ona mun rai, ka turo a sanar mana abu kuma ka san an sanar manan and still you can’t say anything about it.” Ya shafa kansa yana murmushi sosai ya ce. “Mum, what do you want me to say?” Mama ta ce. “Abun da ka je ka faɗa a zo a faɗa mana.” Ya yi shiru still yana murmushi bai ce komai ba. Mama ta shiga mitar abun da yake ranta, harda ce masa alfarma ta yi kawai ta ba shi Neehal amma ba dan halinsa ba, babu yanda zata yi da Kawu Musa ne kawai. Shi dai murmushi kawai yake yi. Daga baya kuma ta koma yi masa faɗa da faɗin. “Ga Neehal nan Ameen, idan Allah ya yi auranku na baka amanarta, ka riƙe ta da amana dan Allah, ka ga yarinyar nan bata da kowa sai Allah, marainiyar Allah ce, idan ka zalunce ta Ubangiji bazai bar ka ba.” Ji ya yi jikinsa ya yi sanyi, soyayyar Neehal da k’aunarta gami da tausayinta na ƙara narkar masa da zuciya. Daga nan part ɗin Daddy ya je wanda dama shi ya kira shi yana son ganin sa, shi ma faɗa da nasiha ya yi masa duk akan ya riƙe Neehal da amana ne. Neehal kam bata kuma fitowa ba tunda ta shige ɗaki dan bata san ta fito su haɗu kar ta je bai tafi ba. Wani irin tsoronsa da kunyarsa Ubangiji ya ɗoro mata tun daga lokacin data fara tursasawa zuciyarta karɓar sa a matsayin mijin da zata aura.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button