NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Bayan Magriba Neehal na zaune a gaban madubin ɗakinta ta na d’aura ɗankwalin atamfar da ke jikinta, dawowarta kenan daga gidansu Haneefah ta sauya kaya ta fara shiryawa kafin Anwar ya ƙaraso. Wayarta dake kan mudubinne ta fara ringing cikin amon sautin wak’a mai daɗi irin ta masoya, murmusawa ta yi ta kai hannu ta ɗauki wayar dan tasan Anwar ne ya ƙaraso tun da shi kaɗai ta sawa wannan ringintone ɗin, ta ɗaga kiran tare yin sallama cikin siririyar muryarta, Anwar ya amsa tare da faɗin “Gimbiyata na ƙaraso” ta yi murmushin jin daɗi mai sauti ta ce “You Are Welcome Sir” shima murmushin ya yi tare da katse wayar, Neehal ta ƙarasa daurinta ta feshe jikinta da da daɗaɗan turarukanta masu sanyin ƙamshi, wanda idan mutum ba matsowa kusa da ita ya yi ba, ba zai ji k’amshin ba. Ɗakin Mama ta lek’a ta sanar mata Anwar ya zo ta fita, Mama ta ce sai ta dawo, ta kuma gaishe da Anwar ɗin, a falon ƙasa ta tarar da su Dije su na kallo, ta dube su ta ce “Aunty Dije dan Allah idan babu damuwa ki ɗan biyo ni da cake ɗin can, zan ɗau drinks ne” Dije ta je “Haba uwar ɗakina babu damuwar komai” Neehal ta yi murmushi ta ce “Toh Nagode” Zulai ta ce “Kawai ki wuce zamu kawo miki har ruwanma, kar yay ta jiranki” Neehal ta ce “Toh Nagode sosai”
Ya na zaune a kan fararen kujerun da suke zama koyaushe dan yin zancen, ya na latsa wayarsa, ya na sanye cikin wata shadda light blue, da ta haska choculate colour ɗin fatarsa wadda ta nuna zallar jin daɗin da yake ciki, Anwar Kyakkyawane a jin farko a sahun kyawawa, dogo ne amma bashi da jiki sosai. Neehal ta ƙaraso gurin tare da yin sallama, Anwar ya d’ago ya na bin ta da wani kallo k’auna, wadda ya sata saurin sunkuyar da kanta ƙasa cikin jin kunya, ya amsa mata sallamar ya na ƙara k’ura mata ido, Neehal ta turo baki gaba cikin shagwab’arta ta ce “Ina yini” ya yi murmushi ganin yanda ta yi, kasancewar gidansu Neehal akwai wadatuwar haske sosai komun dare, shiyasa ya ke kallonta tar” ya ce “Lafiya k’alau, ya Mama” ta ce “Tananan k’alau ta na gaisheka” ya ce “Ina amsawa tare da ajiye wayarsa a kan ɗan table ɗin robar da ke gabansu, cike da soyayya da kulawa ya ce “Me ya faru ne, na ga kamar Queen na fushi da Ni” Neehal ta ƙara shagwab’e fuska ta ce “Nothing, kawai kai ne na ga ka na ta kallo na” murmushi Anwar ya yi me sauti ya ce “Dan mutum ya kalli matarsa laifine, ni fa gaskiya kunyar nan ta ki ta na cutata, dan ma kwanaki kaɗan suka rage ki zama mallakina na cire miki ita gabad’aya” Neehal ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa ba ta ce komai ba, saboda fad’uwar da gabanta ya yi, a dalilin zancen auransu da Anwar ya yi, ta rasa me ya sa tun da auransu ya matso take jin hakan a tattare da ita, a da kuma farkon soyayyarsu ba ta jin komai, burinta kawai a lokacin a ce sun mallaki juna, saboda tarin k’aunar da take masa, amma yanzu duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi da auran. Anwar bai yi tunanin wani abu a shirun da Neehal ta masa, dan ya riga ya saba da halinta na jin kunya idan suna tare, saɓanin idan suna waya ko chat da take zagewa ta na rattabo masa kalaman soyayya, amma idan ya zo gurinta sai dai ya yi ta hirarsa shi kaɗai, ita daga um sai um’um, in kuma ta so wani lokacin ta zage su sha hirarsu. Anwar ya ƙara cewa “Yau ko um ɗinma ba zan samu ba Queen, sai dai shiru?” Neehal ta yi murmushi a ƙoƙarin ta na ganin Anwar din kar ya yi tunanin wani abu ta d’ago kanta tana kallonshi amma ba ido cikin ido ba ta ce “Za ka samu mana, harma fiye da haka” ƙarasowar su Dije gurin ya hana Anwar maganar da yake son yi, su ka yi sallama Neehal da Anwar suka amsa musu a tare, gaishesa suka yi tare da ajiye kayan hannunsu a gaban Anwar din, Anwar ya amsa musu tare musu godiya suka juya suka tafi. Neehal ta mik’e ta tsiyaya masa ruwa da lemo a glass cup, sannan ta koma ta zauna suka cigaba da hirarsu ya na shan drink d’in kaɗan_kaɗan. Can Anwar ya dubeta ya ce “Queen ni fa yau na zo miki da babbar tsaraba” Neehal ta ce “Ta me kenan?” Bai ba ta amsa ba sai hannunsa da ya zira a aljihun rigarsa ya ɗakko wani abu da Neehal ba ta gane mene ba, buɗe ɗan ƙaramin case ɗin ya yi wani zobe mai kyau ya bayyana, Neehal ta waro manyan idanunta ta ce “Wow ya Anwar ring ɗin nan ya yi kyau sosai fa” ya ce “Sai ma kin san a wannan kyakkyawan finger ɗin naki, na san sai ya ƙarawa zoben kyau” Neehal ta yi murmushi, Anwar ya ɗakko zoben dake ta k’yalk’yali ya ce “Kawo Hannunki in saka miki, na ki ne na kawo miki” Neehal ta ce “Nagode sosai Ya Anwar, amma Ni dai ka ba ni in saka da kaina” Anwar ya ce “A’a my Queen ni dai ki barni na sa miki” Neehal ta yi shiru ba ta ce komai ba, domin ba za ta iya musu da Anwar ɗin ba, hannun damanta ta kalla, a hankali ta sa hannun hagunta ta cire zoben dake babban ɗanyatsanta ta ajiye, sannan ta miƙa masa ɗanyatsan, murmushi Anwar ya yi ya matso ya zira mata zoben, hakan ya yi dai_dai da fitowar Ameen daga part ɗinsa domin tafiya Masallaci dan anfara kiran sallar isha’i, karaf a idanunsa Anwar ya zirawa Neehal zobe………..✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
0️⃣6️⃣
…………Doctor an..an…an ka..kashe An…Anwarrrr!’ ta fad’i maganar a rarrabe saboda tsananin tashin hankali. Mama suman zaune ta yi zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu, Ammi ba ta jira amsar Mama ba ta katse wayar. Ita kuwa Mama wayar ma sakin ta ta yi ta fad’i ƙasa. Ganin yanda Mama ta k’ame kamar gunki ga kuma wayarta da ta saka ta faɗi ya sa Hajiya a ruɗe ta ce “Ke lafiyar ki kuwa, ki ka zuba mana na mujiya ga waya kin saki ta fad’i ƙasa?” Uncle Mahmud da ya fuskanci da akwai wata matsalar ya taso ya dawo kusa da Mama, ganin yanda ta sandare sai ya ɗan girgiza ta, wani nannauyen numfashi Mama ta ja ta sauke, saitin zuciyarta ta dafe da hannunta jin yanda ta ke bugawa tamkar za ta yi tsalle ta fito daga k’irjinta, sai a sannan wani uban gumi ya fara tsatstsafo mata ta ko wanne k’ofofin gashi na jikinta, duk da sanyin Ac’n dake falon. Kallo ɗaya za ka yiwa Mama a wannan lokacin ka hango zallar tashin hankali da ɗimuwar da take ciki, gabad’aya ta rasa a duniyar da take jinin jikinta ya tsaya, ƙwaƙwalwarta ta cak da aiki. Ganin yanayin Mama Uncle Mahmud ya ƙara tabbatar da ba k’alau ba, a ɗan ruɗe ya ce “Doctor lafiya kuwa, me ke faruwa ne?” Mama ba ta bashi amsa ba, numfarfashi kawai take sauke wa. A ruɗe Hajiya ta ce “Na shiga uku Ni Zainaba, Fatima ki faɗa mana me ya faru mana, yanayin da ki ka koma Lokaci ɗaya ya tada mana hankali” Mama ta runtse idanunta ta ce “Anwar ya rasu” A gigice Hajiya ta mik’e tsaye ba tare da ta shirya wa hakan ba, ta ce “Innalillahi_wa’inna’ilaihirraji’un, wanne Anwar d’in?, kar dai ki ce mun na Neehal” Uncle Mahmud innalillahi kawai ya shiga maimaitawa a fili domin mutuwar ta bige shi ba kaɗan ba, Hajiya ta saka kuka ta na salati ta ce “Allah ya ji ƙanka Anwar yaron kirki, mai biyayya, Allah ya sa aljannah ta zamo makoma a gareka, Ni Zainabu yaya Neehal za ta ji mutuwarnan?” Dai_dai nan Dad ya shigo falon a firgice, ganin yanayin su Mama ya tabbatar masa da suma sun ji mutuwar.
Mama ta shafe wasu mintuna a zaune a gurin, abu biyu ne yake ƙara dugunzuma mata hankali a kan mutuwar Anwar, na farko cewa da Ammi ta yi an kashe shi, na biyu kuma halin da Neehal za ta shiga idan wannan mummunan labarin ya riske ta. Hajiya kuwa ban da kuka babu abin da take, Dad ma kallo ɗaya mutum zai masa ya gane ya na cikin tsananin tashin hankalin mutuwar Anwar ɗin, musamman idan ya tuna halin da daughter d’insa za ta shiga idan ta ji mutuwar, Uncle Mahmud ne ma mai dauriyar cikin su, amma babu ƙarya wannan ahali mutuwar Anwar ya dake su ba kaɗan ba. Da k’yar Mama ta yi ƙarfin halin kiran Aunty Sadiya da Aunty A’isha ta sanar musu, suma sun shiga tashin hankali da jin mutuwar Anwar d’in ba kaɗan ba, Ameen kuwa ta yi ta neman Number’nsa amma ba ta shiga, kuma duka layikansa ta yi ta gwadawa amma sun ƙi tafiya, dole sai haƙura ta yi ta ajiye wayar ta fara tunanin hanyar da za ta sanar da Neehal.