NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Tun bayan isha’i Neehal take saka ran ganin kiran Sadik a wayarta amma ta ji shiru, tun tana jira har bacci ya ɗauke ta. Data tashi da asuba ta ɗauka zata ga text ɗinsa ko missed call ɗin sa, amma ko ɗaya bata gani ba. Bata yi tunanin komai ba sai ta yi tunanin ko yana cikin dangi ne anata murnar ganin sa, ko kuma a gajiye ya dawo ya yi bacci da wuri. Kafin ƙarfe goma na safe sun gama shirin su na zuwa gidansu Sadik dukan su, Aunty Sadiya ma ta zo, Aunty A’isha ce dai tunda a unguwar take sai dai su biya gidanta su ɗauke ta.

Mama da Daddy da driver a Mota ɗaya, Neehal da Hajiya kuma suna Motar Aunty Sadiya. Sun fara tafiya Mama ta dubi Daddy ya ce. “Jiya Ameen bai zo gida ba, yanzu kuma na kira shi ya zo mu je gidansu Sadik da shi wai ba zai samu damar zuwa ba, sun fita operating tun safe wani ƙauye.” Daddy ya ce. “Allah sarki Son ba dai jajircewa a aiki ba.” Mama ta tab’e baki ta ce. “Ni ban ma yarda da sun fita wani aiki ba, yau fa Saturday.” Daddy ya ce. “Ina ruwan aikin tsaro da weekend Doctor, ko kin manta yanda na yi da ne, sai kina kira na kina Hamma Tafida wai baza ka dawo gida ba, idan ma kin same ni a wayar kenan.” Mama ta yi murmushi tana tuna lokacin farkon Auren su ita da Daddy, lokacin suna faman yawon gari_gari a Nigeria idan an yi posted ɗinsa, wani gurin ma ba zai yiwu ya tafi da ita ba sai dai ya bar ta a gida. Cikin mintuna ashirin suka ƙarasa gidansu Sadik. A compound ɗin gidan suka tarar da Abban Sadik shi da Kawu. Suka gaisa cikin mutuntawa tare da yi musu murnar bayyanar Sadik da addu’ar Allah ya tsare gaba, Sannan su Neehal suka shige cikin gidan suka bar Daddy a gurin su Abba. Da fara’a sosai Maamah da ƴan’uwanta suka tarb’e su, suka gaisa cikin mutunta juna tare da ƙara jajanta abun da ya faru, su Mama sukay musu murnar bayyanar Sadik. Neehal dai tana ƙasa zaune akan carpet kanta a ƙasa, Hajja tana ta tsokanar ta, sai dai ta yi murmushi kawai, wata ƙanwar Maamah na tare mata. Ƴan’uwan Maamah suna da kirki sosai, kuma suna son Neehal da ɗansu, kawai babu yadda zasu yi dan su kansu al’amarin na ba su tsoro. Batul ƙanwar Sadik ce ta shigo falon, ta gaishe da su Mama sannan ta zauna a kusa da Neehal ta gaishe ta. Murya ƙasa_ƙasa yadda Neehal ɗin ce kaɗai zata ji ta, ta ce. “Aunty Neehal Yaya ya ce ki zo.” Cikin d’oki Neehal ta ce. “Yana ina?” Batul ta ce. “Yana bayan gida nan.” Neehal ta yi shiru dan bata san ta yanda zata iya tashi ta tsallake su Maamah da Mama ta tafi gurin Sadik ba. Maamah data fahimci abun da ke faruwa sai ta cewa Neehal. “Ƴata ku je da Batul ki ga jikin Sadik ɗin.” Cikin jin kunya ta ce. “Toh.” Sannan ta miƙe a hankali ba tare da ta kalli kowa ba ta bi bayan Batul wadda ta riga ta tashi. A wata rumfa dake bayan part ɗin Maamah suka same shi zaune akan ɗaya daga cikin kujerun robar dake gurin. Ta ƙura masa ido kamar yadda shi ma ya zuba mata nasa, sai ta ga ya rame ya ƙara haske. Ta zauna a kujerar dake fuskantar wadda yake kai, Batul kuma ta juya ta koma cikin gida. Sadik ya yi murmushi ya ce. “Neehal!” Ta mayar masa da matarnin murmushin ta ce. “Sadik!” Ya ce. “Na’am da fatan kina lafiya?” Ta ce. “Lafiya k’alau, Alhamdulillah Yaya Sadik, na gan ka cikin k’oshin lafiya ba kamar yadda muka yi zato ba, na ji daɗin hakan sosai sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba.” Sadik ya ce. “Amin ya Allah, Are you sick?” Ta ce. “Lafiya ta k’alau, me ka gani?” Ya ce. “Duk kin rame Neehal.” Ta ce. “Tashin hankalin ɓatan ka ne kawai amma yanzu ai komai ya wuce, tunda Allah ya dawo mana da kai lafiya.” Sadik ya danne duk wata damuwa dake cikin ransa suka cigaba da hira da Neehal, har yake bata labarin yanda aka sace shi da inda aka kai shi.

A Parlour’n Maamah kuwa bayan fitar su Neehal ba jimawa Hajiyarsu Sadik ta shigo Parlour’n. Bacci take a part ɗin Umma aka taso ta aka ce mata iyayen Neehal sun zo. Su Mama suka gaishe ta cikin girmamawa. Ta amsa ba yabo ba fallasa sannan ta ce. “To Alhamdulillah, yaron mu ya dawo lafiya, mun gode da zuwar mana murna da kuka yi, amma ku sani babu batun Aure yanzu a tsakanin sa da ƴarku.” Cikin mamaki Hajiya ta ce. “Saboda da me kuma?” Ta ce. “Saboda mu tsiratar da rayuwarsa daga faɗawa halaka mana, dan wannan yar taku ba matar aure ba ce, yawwa, dan haka baza mu ɗauki ɗanmu mu aura masa ita watarana kawai mu wayi gari mu ga an kashe mana shi ba.” Mama ta kalli Aunty A’isha dake gefen ta da sauri suka haɗa ido. Cikin rashin jin daɗin abun da Hajiyarsu Sadik ta faɗa, Hajja ta ce. “Haba Hajiya, wannan wacce irin magana ce?” Hajiya data saki baki tana kallon ta, ta ce. “Ko mutuwa tana kunyar idon iyaye, amma ke matar nan ki dubi tsabar idon mu ki faɗa mana haka? Saboda mun zo inda kike.” Maamah ko kaɗan bata ji daɗin abun da Hajiyar ta ce ba, ta dubi su Mama ta ce. “Dan Allah ku yi haquri.” Hajiyarsu Sadik ta ce. “Haqurin me zaki ba su, kar ma su yi haqurin gaskiya ce dole a faɗe ta, ƴarsu annoba ce wadda zaman ta ma a cikin al’aumma bala’i ne, wa ya sani ma ko mayya ce take lashe kurwar samarin nata.” Wannan kalmar ta maita da Hajiya ta danganta Neehal da ita ta bala’in k’ona ran su Mama ta yi ba. Hajiya ta ce. “Insha Allahu sai dai ki ga maita a zuri’arki ba dai a tamu ba, kuma Allah sai ya sakawa yarinyar nan k’azafin maita da kikai mata, ɗanku kuma ku kwad’anta shi ku cinye ko ɗan gold ne Neehal baza ta aure shi ba.” Ganin abun yana neman ya zama babban faɗa Maamah ta yiwa Abba text akan ya zo, dan duk haqurin da Hajja take ba su akan ɗan Allah su bar maganar haka amma sun ƙi saurarar ta. Aunty Sadiya da baza ta iya jure cigaba da sauraren munanan kalaman Hajiyarsu Sadik akan Neehal ba ta miƙe tana duban Hajiyar ta ce. “Yarinyar nan ƙaddara ce Allah ya ɗora mata wadda babu wanda ya fi ƙarfin ya ɗora masa ita, ita ma ba yin kanta ba ne. Dan haka karki sake danganta ta da maita, idan kin manta bari in tuna miki shari’ar maita ba ƙaramin abu ba ne, wallahi idan kika sake alaƙanta Neehal da maita zaki sha mamaki.” Tana gama faɗar haka ta ɗauki jakarta a fusace, ta cewa su Mama su tashi su tafi. Kafin su kai ga tashin Abban Sadik ya shigo falon a ruɗe, bai tambayi ba’asi ba dan ya san halin mahaifiyarsa ya shiga ba su haquri. Hajiyarsu Sadik kuma sai ta saka kuka wai ƴar cikinta wadda ta yi jika da ita ta zage ta amma ya zo yana ba su haquri.

Su Neehal suna can suna hira ba su san me yake faruwa ba, ita Neehal kanta gaba-d’aya ya kulle da labarin da Sadik ya bata, a yanda ta fuskanta waɗanda suke kawo masa abinci a inda aka ajiye shi su suka fito da shi suka dawo da shi gida. Kenan wanda yasa aka ɗauke sa shi ya saka aka dawo da shi, sai ta shiga tambayar kanta ta yaya Ameen ya fito da Sadik? Ko kuɗi ya bawa masu tsaron nasa fiye da yadda wanda ya saka su aikin ya ba su suka fito da Sadik ɗin? Ko kuma ƙarfi ya nuna musu ya tsoratar da su? Ko da hukuma ya haɗa su? Amma idan da hukuma ya haɗa su ai hukumar ce zata fito da shi su kuma a kama su. To ko dai ya san wanda ya sace Sadik ɗin ne? Sai ta girgiza kai a ranta tana cewa hakan ma ba zai taɓa faruwa ba, ta bar yiwa kanta tambayoyin tun kafin ta fara rubbish ɗin tunani akan Yayan nata wanda ta san ba za’a taɓa haɗa baki da shi a satar Sadik ba, ta k’udurce a ranta zata tambaye shi ya warware mata yanda abun ya kasance, duk da ta san halinsa da ƙyar ya bata amsa. Sadik yana ƙoƙarin faɗa mata abun da yake ransa na raba sun da aka yi dan kar ta ga lefin sa ta ga kamar ya zalunce ta ya yaudare ta, amma zuwan Batul kiran Neehal ɗin ya hana shi yi mata zancen, Batul ta ce ta zo su Mama suna jiran ta za su tafi. Neehal ta miƙe suka yi sallama da Sadik, ta lura da yanda jikinsa ya yi sanyi k’alau da kuma yanda yake bin ta da wani irin kallo. Ta tafi tana jin ba daɗi a zuciyarta kamar kar su rabu, sai ta tarar su Mama har sun shishshiga Mota zuciyoyinsu babu daɗi. Ta buɗe Motar Aunty Sadiya ta shiga, bata lura da yanayin da suke ciki ba saboda bata bari sun haɗa ido da kowa ba, har suka je gida babu wanda ya ce k’ala, sun yi shiru kowa da tunanin da yake a cikin ransa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button