NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Daf da Magriba Hameedah ta dawo gidan daga gurin aiki a matuƙar gajiye kamar wadda ta yi aikin ƙarfi. Jakarta da mayafinta ta cillar a kan kujera sannan ta zauna tare da faɗin “Wash, Mommy na gaji.” A dak’ile Mommy ta ce “Sannu” Hameedah ta kalli mahaifiyarta ta, yanayin da ta mata magana ta gane ba k’alau ba, da mamaki ta ce “Mommy what happened na ga kamar ranki a ɓace?” Mommy ta ce “Akwai matsala ne Daughter babba ma kuwa.” A ɗan firgice Hameedah ta ce “Me ya faru Mommy? Har kin sa hankali na ya fara tashi.” Mommy ta ce “Hmmm, bari kawai Hameedah, ni da waccan matar ne Fateema matar Yaya…….” Labarin duk abun da ya faru Mommy ta faɗawa Hameedah. Wani irin ihu Hameedah ta yi tare da mik’ewa tsaye cikin tashin hankali ta ce. “Wallahi Momy ba zai yiyu ba, shekara nawa ina zaman jiran shi sai yanzu a ce ba ni ze Aura ba.” Ta ƙarashe zancen tare da fashewa da kuka. Mommy ta taso ta zo kusa Hameedah, dafa kafadunta ta yi cikin lallami ta ce “Share hawayenki Daughter, indai Ina raye babu abun da zai hana auranki da Ameen, ki kwantar da hankalinki.” Cikin kuka Hameedah ta ce “Mommy Dan Allah ki san abun yi, wlh ba zan iya rayuwa babu Ya Ameen” Mommy ta zaunar da ita a kan kujera ta ce “Ki kwantar da hankali kamar tsumma a cikin ruwa, ki sa a ranki ma auranku da Ameen tamkar an yi angama.”


Neehal ta na kitchen ta na girkin dare Mama ta dawo gidan, ta fito daga kitchen d’in ta yi hugging d’inta ta na faɗin “Welcome sweet Mom.” Mama ta yi murmushi ta ce “Thanks You Daughter, ya gida?” Neehal ta ce “Alhamdulillah, sai gajiyar aiki.” Ta ƙarashe maganar a ɗan shagwab’e. Mama ta ce “Sannu, me ake girka mana ne, na ji k’amshi duk ya baɗaɗe ko’ina?” Neehal ta murmusa ta ce “Sai kin zo ci za ki gani.” Mama ta yi murmushi ta wuce sama jin a na kiran sallar Magriba………✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:33] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

1️⃣3️⃣

……….Neehal ta koma kitchen ta cigaba da aikinta. Bayan Sallar Magriba Mama ta na zaune a ɗakinta a kan darduma ta na lazimi wayarta ta yi ƙara, ɗauka ta yi ta duba ta ga Mommy’n Hameedah ce ke kuma kiranta. Tsaki ta yi cikin takaici ta maida wayar ta ajiye, dama ta san Mommy’n Hameedah za ta yi abun da yafi haka ma indai ta ji maganar Ameen ba zai auri Hameedah ba. Kiran Mama Mommy ta yi_ta yi, amma Maman ta ƙi d’agawa. Hakan ba ƙaramin ƙara tunzura Mommy ya yi ba, ta yi ta masifa ta na kiraye_kirayen ‘yan’uwa ta na faɗa musu abun da ke faruwa. Hameedah kuwa kiran layin Ameen tayi_tayi amma shima be d’agawa ba, hakan ya ƙara ta da mata da hankali ta zauna tayi ta rufzar kuka.

Mama ce zaune a falon Dad dake shan fruits, Dad ya na duban ta da murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce “Kamar da magana a bakin nan naki Doctor.” Mama ta ce “Babu maganar komai Hubby, Idan ma da akwai ba ta wuce ta zancen bikin Ameen ba, yaushe za ku kai kuɗin ne.?” Dad ya ce “Ranar Sunday Insha Allah.” Mama ta ce “Allah ya kaimu.” Dad ya ce “Amin, ina Daughter ne?” Mama ta ce “Tana can ta na hutawa wai yau a gajiye take.” Dad ya ce “Bari na kirata a waya na yi missed ɗinta yau.” Neehal ta na kwance a kan luntsumemen gadonta ta yi nisa a cikin tunanin rayuwarta, wayarta dake gefenta ta fara vibrate, ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi tare da share hawayen da yake zirarowa daga idanunta, tashi zaune ta yi ta na cize lips d’inta zuciyarta na mata zafi. Duba wayar ta yi ta ga Dad ke kiranta, cikin sanyin jiki ta d’aga wayar tare da karawa a kunnanta. Dad ya ce “Daughter bacci ki ke ne?” Neehal ta ce “A’a, ina kwance dai.” Dad ya ce “Yau tun safe ban gan ki ba, na dawo kuma na jiki shiru, ko yau ba za ki zo mu yi hirar ba ne.” Neehal ta yi murmushi cikin daɗi da kuma k’aunar Dad d’in nata ta ce “Zan zo My Dad, gani nan.” Dad ya ce “Yawwa d’iyar albarka sai kin ƙaraso.” Neehal ta ajiye wayar bayan ya kashe kiran ta na sauke ajiyar zuciya, sosai take kewar Anwar a cikin zuciyarta, musamman idan ta kaɗaice ita kaɗai babu abun da take sai tay ta tunanin sa, addu’a ta masa ta samun dacewa sannan ta mik’e jiki a sanyaye ta fice ta nufi part d’in Dad. Da sallama ta shiga falon, Mama ta kalle ta tare da amsa mata, kusa da Dad ta je ta zauna ta na faɗin. “Abbunah barka da dare.” Dad ya shafi kuncinta ya ce “Yawwa Daughter, Mamanki ta ce kin gaji yau ni kuma na taso ki ko?” Neehal ta ce “A’a Dad ba komai ai na huta.” Dad ya ce “To ya aikin na ku? Dafatan dai babu wata matsala.? Neehal ta ce “Babu Dad.” Dad ya ce “Masha Allah.” Neehal ta Kalli Mama ta ce “Mama ina son na je gidansu Ammin Anwar gobe in gaishe ta.” Mama ta ce “Allah ya kai mu.” Dad ya ce “Ai ko ni yakamata na kai ki da kaina, daga nan sai ki rakani zance, gurin….” Ya ƙarashe zancen da kannewa Neehal ido. Neehal ta yi murmushi ta ce “Gurin wannan kyakkyawar matar mai kirkin nan ta unguwar da muke zuwa?” Dad ya ce “Ehh ita fa, kin san ta iya girki sosai na yi kewar abincinta.” Neehal ta yi dariya ta na kallon Mama. Mama ta tab’e baki domin ta saba da zolayar Dad da Neehal, sun maida ita kamar wata kakarsu, idan ‘yan nishad’in na kansu haka za su yi ta tsokanarta, idan ta ga dama wani lokacin ta biye musu idan kuma ta so sai ta yi musu shiru. Yau ma biye musu ta yi sukai ta yi, hakan ya rage wa Neehal damuwar da take ciki ba kaɗan ba, dan Dad akwai shi da barkwanci. Sai wajen 10:30 Mama ta raka Neehal ta koma part ɗinsu.

Dad ya na zira kayan bacci bayan fitowarsa daga wanka ya ce “Doctor ban faɗa miki yanda muka yi da Suwaiba ba a kan batun su Ameen.” Mama ta ce “Ya ku ka yi.” Dad ya ce “Ai ko maganata ba ta gama saurara ba ta kashe wayarta, ina idar da Sallar Magriba kuwa sai ga kiran Yaya na Abuja, na d’aga muka gaisa ya ce mun wai ya ji wata magana a bakin Suwaiba, na ce masa dama ina shirin kiran shi a kan maganar, jibi Insha Allahu zan je har Abujan.” Mama ta ce “Allah ya kyauta ya kaɗe fitina.” Dad ya ce “Amin.” Mama ba ta faɗawa Dad Mommy’n Hameedah ta kira ta ba saboda gudun Fitina, dan tasan halin Dad bai iya ɓacin rai ba, yanzu sai ya kira ta ya ɓata rai. Neehal ta na fitowa daga wanka ta ga a na kiranta a waya, d’agawa ta yi da sauri ganin Yayanta ne. “Hello Yaya!” Neehal ta faɗa bayan ta d’aga. “Sallamar kenan ko?” Shima ya faɗa cikin daddadar muryarshi mai cike da nutsuwa. Neehal ta ce “Sorry duk murnar ka kira ni ce fa Yaya.” Ameen ya ce “Ba ki yi bacci ba?” Neehal ta ce “Uhm”

“Me ki ka tsaya yi?”

“Ina part d’in Dad muna hira, yanzu na dawo zan kwanta.”

Ameen ya ce,

“Ya yi kyau.” Cikin shagwab’a Neehal ta ce “Yaya ina Aunty Hafsat?” Ya ce “Wacece haka?” Neehal ta ce “Aunty Hafsat d’inka fa.” Cikin basarwarshi ya ce “Oh tananan k’lu.” Neehal ta ce “My regard please.” Ya ce “Insha Allah, Bye.” Neehal ta ce “Gud night.” Daga haka suka yi sallama ya kashe wayar. Neehal ta shirya cikin kayan baccinta masu taushi white color sannan ta rage light d’in ɗakin ta kwanta, hotunan Anwar ta lalubo a wayarta ta shiga kalla, saboda gajiyar dake addabar jikinta ba ta san sanda bacci ya yi awon gaba da ita ba.

Washegari ya kama Talata Neehal ba ta da aiki ranar, bayan sallar la’asar ta fito cikin shirinta na fita. Ɗakin Mama ta je domin yi mata sallama. Mama ta ce “Har kin shirya kuma Haneefan ba ta zo ba.” Neehal ta ce “Yaya Faruq ya na gari fa, shi yasa yanzu ganin ta sai an cike Form.” Mama ta ce “Shi yasa 2 days na ji ta shiru, yanzu ke kaɗai za ki tafi.?” Neehal ta ce “A’a zan biya na ɗauke ta mu wuce.” Mama ta ce “Shikenan amma kar ku yi dare fa, kin ga ke za ki yi driving, ban san ki na hawa manyan titi da daddare.” Neehal ta ce “Insha Allah Mama ba za mu jima ba.” Mama ta ce “Allah ya kiyaye, kar ki manta da addu’a dai idan za ki fita da kuma hawa Mota.” Neehal ta ce “Ba zan manta ba Mama.” Mama ta ce “Yawwa, sai kun dawo, ki ɗauki saƙon fa, a gaishe su.” Neehal ta amsa da “Toh” tare da ficewa daga d’akin. Sun je gidansu Anwar lafiya, tarb’a sosai Ammi ta musu kamar yadda ta saba. Su na zaune a falo bayan sun gama gaisawa da Ammi Najwa k’anwar Anwar ta shigo falon hannunta ɗauke da tire, ta dire a gaban su Neehal ta na faɗin “Aunty Neehal ku sha ruwa.” Neehal ta ce “Toh mun gode.” Hira suka shiga yi da su Najma da Ammi, can Haneefah ta dubi Ammi ta ce “Ni ko Ammi ya batun mutanen da suka kashe Anwar, an gano su kuwa.?” Ammi ta ce “Har yau dai shiru babu labari ba’a gano ko suwaye ba.” Haneefah ta ce “Allah ya bayyana su cikin gaggawa.” Suka amsa Amin gabad’aya. Kafin Magriba suka musu sallama suka tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button