NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:43] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL ⚡

By
Zeey Kumurya

2️⃣2️⃣

………A ɓangaren Ango da Amarya kuwa komai ya tafi yadda ya kamata a daren da aka kaita, sai dai Ameen ya sha rawar kai a gurin Hafsat, daga baya kuma ta koma raki da shagwab’a. Sai dai abu na farko da Ameen ya fuskanta dangane da Hafsat tana da ƙarancin ilimin Addini da shi kanshi addinin ma, dan Sallah ma da asuba har ya je masallaci ya dawo ba ta yi ba tana kwance, da ƙyar ya tashe ta ta yi, duk ya san bata jin dad’i amma ai ba cutar da zata hanata Sallah take ba. Haka ɓangaren gyaran gida ma babu abun da ta taɓa da sunan gyara,duk da jikin nata ya warware, sai da ƴan’uwanta suka zo da yamma ne ma suka gyara mata gidan. Da daddare Mama ta aiko musu da dinner, bayan sun gama ci ta tashi ta bar kayan a wurin, Ameen ya bita da kallo cikin mamaki zuciyarsa cike da takaicinta, amma ya danne bai nuna ba ya kwashe kayan ya kai kitchen, wurin da suka ci abincin kuwa ko arzik’in tattarewa bai samu ba haka ya kwana.

Washegari misalin ƙarfe Takwas da ƴan mutuna na safe Mama tana zaune a falonta tana karatun Alkur’ani da bata samu ta yi ba sai da ta gama haɗa musu breakfast saboda fitar da za su yi, Neehal ce ta shigon falon, tana ɓata fuska wai ita a dole fushi take ta zauna a kusa da Mama tana jiran ta gama karatun. Mama ta kai ƙarshen aya ta d’ago tana dubanta. A hankali Neehal ta ce “Ina kwana.” Mama ta ce “Lafiya k’alau, Ina yaran?” Neehal ta ce “Bacci suke.” Mama ta ce “Bacci kuma har yanzu? Kin san fa za mu fita.” ta ce “Yanzu za su tashi sai na musu wanka.” Mama ta ce “Ki sauka ƙasa ki yi break.” Neehal ta miƙe ta ce “Bari na fara musu wankan sai mu yi tare.” Tana komawa ɗaki ta tarar sun tashi duka suna zauna, ta ƙarasa gadon da sauri tana dubansu. Afrah ta ce “Aunty yau za mu gurin Daddy ko?” Neehal ta ce “Insha Allah.” Amrah ta ce “Zaki bi mu ko Aunty?” Neehal ta ce “Ehh.” Tana cire musu kaya ta ce “Wa yake muku wanka a gida?” Amrah ta ce “Baaba talatu, idan mun je gidan Mommy kuma Aunty zahrah.” Neehal ta gyaɗa kai ta ce “Ku da wa kuke bacci.” Amrah ta ce “Mu da Baaba Talatu.” Neehal ta ce “A gidanku take itama?” Suka haɗa baki suka ce “Ehh.” Bayan ta musu wanka tana shafa musu lotion Afrah ta ce “Aunty ba mu yi karatu ba, kuma kullum Daddy yana mana idan mun tashi.” Neehal ta ce karatun me?” Afrah ta ce “Qur’an.” Neehal ta ce “Ku biya mun naji to.” Suka haɗa baki sukai basmala cikin karatun yara suka fara karanto Suratul Nas.” Harta gama shirya su ba su gama karatun ba. Neehal ta jinjina wa yaran sosai a ƙananun shekarun su amma sun iya karatun, sai da ɗan gyararraki da ba za a rasa ba. Neehal ta kamo hannunsu suka sakko ƙasa suka yi break, suna gamawa ta haye sama dan yin wanka su kuma ta barsu a falon suna kallo tare da su Dije. Wajen ƙarfe tara Ameen ya kira Mama, ya gaisheta ta tambaye shi lafiyar Hafsah ya ce tanan k’lu. Kafin ƙarfe goma sun fita, duk inda ya kamata su je sun je dan bayar da cikiyar su Afrah, Neehal dai kamar ta zunduma ihu haka take ji, a hanyarsu ta dawowa kuwa suna Mota ta saka kuka, dan ji take kamar har anga ƴan’uwan su Afrah sun karɓe su, Mama ta mata tsawa ta ce “Ta rufe musu baki kar ranta ya ɓaci.” Daddy kuma ya rarrashe ta. Wajen 1 suka koma gida, ɗakinta ta yi wucewarta da Twins ta kulle suka kwanta, hakan yasa baccin dole ya ɗauke su dukan su. Sai da 3 ta wuce Mama ta buga mata ƙofa dan su tashi su ci abinci. Bayan Sallar la’asar ma ta ƙara jan su daki ta samu game a wayarta ita kuma ta kwanta, Mama dai kallonta kawai take duk abun da take ba ta kuta ba. Har Ameen ya zo gidan da Yamma ya tafi ba ta sani ba tana ɗaki. Wunin yau ko kiranta aka yi a waya sai gabanta ya faɗi saboda tunanin ko ƴan’uwan su Afrah ne, dan Numbern’ta aka bada idan iyayen yaran sun ji cikiyar su kira. Bayan Magriba Mama ta kwankwasa mata ƙofa, ta taso ta buɗe, Mama ta ce mata “Ki sauka ƙasa Sadik yana jiranki, ya kira wayarki dan iskanci kika ƙi d’agawa.” Neehal ta ce “Ban gani ba wayar na silent.” Mama ta ce “Ke kika sani, kuma ki fito da Yara su shaƙata in ke kin zaɓi zaman ɗaki su ba za su yi ba.” ta ce “Toh.” Mama ta yi wucewarta. Hijabi ta zira ta kamo hannunsu suka fito, suna ta murna sun ɗauka fita za su ta yi. Sadik yana zaune yana latsa waya, k’amshinsa ya cika falon gaba-d’aya, Mama ta sa su Dije sun kawo masa drinks da abinci. Neehal ta yi masa sallama tare da zama a kujerar dake gefen ta sa, ya amsa mata yana kallonta. Su Afrah kuwa suna can gefe sun samu kallo. Sadik ya ce “Ya gajiyar biki kuma?” Neehal da ta ƙi d’agowa ta ce “Babu gajiya, ya kaje gida.?” Ya ce “Lafiya k’alau.” Suka yi shiru, ita tana wasa da yatsun hannunta shi kuma yana danna waya, can dai ya katse shirun da faɗin “Na yi tunanin ma bakya nan dana kira wayarki ba ki ɗauka ba, shigowa na yi in gaida Mama sai ta ce kina ciki.” Neehal ta ce “Uhm ina kwance ne.” Ya ce “Ba ki da lafiya ne?” Ta ce “,Lafiyata k’alau.” Ya yi shiru yana kallonta na wasu sakanni, duk ta ƙi d’ago kanta amma ya fahimci tana cikin damuwa. Murya ƙasa_ƙasa seriously ya ce “Me ke damunki to?” Numfashi ta ja jin yadda ya yi maganar ta girgiza masa kai, ya ce “Neehal!.” Ta d’ago da kanta a hankali ta ce “Na’am.” Ya ce “Har yanzu baki saki jikinki da ni ba, baki ɗauke ni a matsayin brother ɗinki ba kamar yadda na ɗauke ki as my sister.” Neehal ta yi shiru, Sadik ya ce “Okay thank you.” Ganin yana ƙoƙarin miƙewa ta marairaice ta ce “I’m sorry ya Sadik, dan Allah kar kace haka, wlh ba haka ba ne.” Ya ce “Ya ya ne?” Ta sauke numfashi cikin rashin sanin ta ina zata fara masa bayanin damuwarta, dan tabbas tana buƙatar share problem ɗinta da wani ko zata ji sauƙi a ranta, ita kanta tana mamakin yanda aka yi take son yaran haka.” Sadik ganin ta yi shiru ya ce “Kar ki damu ba sai kin faɗa mun abunda ke damunki ba, but i promise you zan taya ki da addu’a.” Neehal ta ce “No I will tell you now.” A hankali ta shiga bawa Sadik labari tun daga time ɗin data tsinci su Afrah har zuwa yau. Sadik dake kallon ta ya ce “Gaskiya Mama take faɗa Neehal, ki yi imagine ace yaran nan yanda suke hannunki yanzu kawai ki tashi ki neme su ki rasa, na san hankalinki zai tashi ba kaɗan ba, to duk tashin hankalin da zaki yi ba za ki kai iyayensu ba, dan haka Mama ta fiki gaskiya. And please kuma ki dena damuwa akan hakan, yaran nan ko da sun koma gurin iyayensu ai hakan ba yana nufin kun rabu ba kenan, duk time ɗin da kike son ganinsu zaki je ki gan su kin ji.” Neehal ta jinjina kai cikin gamsuwa da bayaninsa, ya ce “Yawwa sisina, ki kuma je ki bawa Mama hak’uri.” Neehal ta ce “Insha Allah, na gode.” Ya yi mata murmushi mai taushi yana jin sonta tamkar zai fasa masa zuciya. Cikin kankanin lokaci Neehal ta saki jikinta suka shiga hira da Sadik, sai gata tana ƙyalƙyala dariya kamar ba ita ce take ta k’unci ba d’azu.” Har kusan Tara da rabi Sadik bai tafi ba, duban agogon hannunsa ya yi da waro ido cikin mamaki ya ce “Haka dare ya yi ba mu yi Sallah ba, lallai yau hira ta yi daɗi.” Neehal ta turo baki gaba ta ce “Yanzu sai ka ce zaka tafi ko?” Ya ce “Ehh mana, ko so kike Maamah ta rufe mun gida.” Neehal ta ce “Sai ka kwana anan.” Ya mata wani kallo ya miƙe ya ce “Wataran zan kwana not now.” Miƙewa ta yi itama ta ce “Allah ya kai mu wataran ɗin, mu je in raka ka.” A bakin part ɗin Mama suka tsaya suka yi sallama, har cikin ranta take jin dama kar ya tafi, dan yana ɗebe mata kewa ba kaɗan ba.” Tana dawowa falo ta lek’a ɗakin su Dije ta ga ba su yi bacci ba hirarsu suke yi hakan yasa ta ce musu su kawo mata su Afrah sama, wanda tuni sun yi bacci. Ɗakin Mama ta shiga ta tarar da ita tana operating system. “Sannu da aiki Mama.” Ta faɗa lokacin da take zama a kusa da ita, Mama ta ce “Yawwa sai yanzu ya tafi?” Ta ce “Eh.” Mama ta ce “Ina yaran?” “Sun yi bacci.” Neehal ta amsa, Mama ta ce “Sun dai ci abinci ko?” Neehal ta ce “Na basu popcorn kafin mu fito.” Mama ta ce “Popcorn abinci ne?” Neehal ta ce “Da yawa suka ci ai, kuma da suna jin yunwa za su faɗa mun.” Mama ta ce “Alright.” Neehal ta ɗan yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce “Mama ki yi haquri akan abin da na yi, na gane gaskiya kika faɗa.” Mama ta ce “Shikenan na ji dad’i da kika gane haka, wai har yanzu ba’a kira ki ba akan Yaran nan? tun d’azu nake so na tambaye ki kuma sai na sha’afa.” Neehal ta ce “Ba a kira ba.” Mama ta d’ago ta dube ta karon farko tun shigowar ta ɗakin ta ce “Bana son ƙarya fa Neehal kin sani, ki faɗa mun gaskiya ko sun kira.” Neehal ta ce “Allah Mama ba’a kira ba, sai dai ko yanzu da na sauka ƙasa.” Mama ta ce “Amma na yi mamaki, more than five Radios banda Televisions amma a ce ba’a samu wanda ya san su ba, Sadiya ma ta kira ni ta tambaye ni, Dad ma haka.” Neehal ta ce “Nima Mama na yi mamaki, dan ko kirana akai sai na yi tunanin ko su ne.” Mama ta jinjina kai kawai, Neehal ta ce “Mama kun yi waya da Yaya kuwa?” Mama ta ce “Ya zo ma d’azu.” Neehal ta waro Ido ta ce “Amma shine bai neme ni ba.” Mama ta ce “Ya tambaye ki na ce kina ɗaki a kwance, ko kina ta k’uncin zan je in kira ki ne.” Neehal ba ta ce komai ba ta tashi ta fice tana turo baki gaba, cikin takaicin Ameen ya zo amma ba su haɗu ba, shima kuma ko ya shigo ɗakin ya ganta. Gyarawa su Amrah kwanciya ta yi ta cire Hijab ɗin jikinta ta shiga toilet dan ɗauro alwala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button