NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Soyayya sosai Neehal da Sadik suke, Haneefah kuwa ta samu abun tsokanarta, matar Barrister ma ta koma ce mata. Mama ma tana lura da ita a kwanakin nan Sadik ya bar Friend or brother ya koma Habibi. Ta kuwa ji daɗin hakan sosai, sai ta ƙara dagewa da k’aimi gurin yi musu addu’a akan Allah yasa Sadik shine mijin Neehal. Sadik ya iya tafiyar da mace yanda ya kamata, ga tarin kyautatawa da daɗaɗan kalamai wanda suke ƙara dulmiyar da Neehal a kogin k’aunarsa. Ranar Asabar ta kasance ranar farin ciki ga kowane musulmin duniya, saboda tashi da azumin watan Ramadana mai girma da ɗaukaka da akai. Ranar da aka ɗauki azumi na Shida su Mama suka tashi zuwa ƙasa mai tsarki ita da Aunty Sadiya dan yin Umrah. Gidan Aunty A’isha su Neehal suka koma kafin Mama ta dawo, wannan karon har da su Dije suka tafi. Mama ta yi addu’a sosai a gaban ka’aba akan Allah ya kawo ƙarshen ƙaddarar Neehal gami da tona asirin duk masu hannu a kisan su Anwar…………

THREE MONTHS LATER

Neehal ce ta fito cikin shirinta na tafiya school, a kitchen ta tarar da Mama tana yin lunch, ta cewa Maman. “Mama zan tafi school.” Mama ta ce “Har kin gama karatun?” Da yake Neehal ɗin sun fara exam ɗin second semester level three. Ta ce “Eh, na ga 2 ta wuce, kuma ƙarfe 3 zamu shiga exam ɗin. Mama ta ce “Allah ya kiyaye ya ba da sa’a, ki biya fa ki dubo Yayanki kar ki manta.” Neehal ta ce “Zan je Insha Allah, zan kira Haneefah ma idan tana free sai mu je tare, idan ma tana School ɗin sai mu wuce ta can kawai.” Mama ta ce “Shikenan ki masa sannu.” Neehal ta ce “Zai ji.” sannan ta juya ta tafi. Kamar kodayaushe tsawon watanni ukun nan da suka wuce kullum Neehal ta fita sai Motar nan ta bita a baya, idan zata school,aiki,shopping da unguwa duk tana biye da ita a baya. Ita har mamakin ma yanda mai Motar yake sanin time ɗin fitarta dana dawowarta take sai ka ce aljani. Kuma har yau bata taɓa faɗa wa kowa ana bin ta ba, Ubangijinta kawai take faɗawa, dan babu mai bata kariya sama da tasa. Bata son kuma ta d’agawa Mama hankali shi yasa bata faɗa mata ba, duk da a zahirin gaskiya a tsorace take da bin ta da ake yi ɗin. Watarana ta kai su Afrah shopping a hanyarsu ta dawowa motar tana bin ta sai ta ce a ranta bari ta gwada wani abu. Parking ta yi a gefen titi ta kulle su Afrah a cikin motar sannan ta shiga wani shago da ake sayar da zobuna da agogo, ta ɗauki zobe ɗaya ta siya duk da bata fito da niyyar hakan ba. Bayan ta fito daga shagon ta kalli titi ta bayanta ko zata ga motar nan amma bata ganta ba. Amma abun mamaki bayan ta shiga tata motar bata fi 3 minutes da fara tafiya ba ta hango motar tana bin ta a baya. Hakan ya tabbatar mata da abun da take tunaninta akan wani ne yake bibiyarta, kuma koma waye Allah ya fi shi.

Ƙarfe huɗu ta fito daga exam ɗin kuma Alhamdulillahi ta mata sauƙi, masallaci ta nufa ta yi sallah sannan ta kira Haneefah dan su je su dubo Ameen dake fama da zazzaɓi. Haneefah ta sanar mata bata gida sun fita kasuwa da ƙanwar Mommy, kasancewar bikinta ya gabato saura sati uku, dan ma exam ɗin da suka fara ne da tuni an yi bikin. Yanzu sai bayan Babbar Sallah da sati biyu za’ayi. Sallama Neehal ta yiwa k’awayenta ta tafi. Sai wajen biyar ta ƙarasa gidan. Babu kowa a falon ƙasa hakan yasa ta nufi sama, a nan ta tarar da k’awayen Hafsat su uku zaune a falo. Ta musu sallama ta shiga, suka amsa suna bin ta da kallo. Ta zauna a kujera sannan ta gaishe su. Cikin fara’a Fadeelah ta ce “Laa Neehal ke ce, ai ban gane ki ba da farko sai yanzu.” Neehal ta yi murmushi ta ce “Aunty Hafsan tana ciki ne?” Fadeelah ta ce “Eh wanka take, ki shiga Yayan naki yana cikin ɗakinsa.” Neehal ta ce “Toh.” Tare da miƙewa ta shiga ɗakin. Ɗaya daga cikin k’awayen Hafsat ta ce “Wannan yarinyar kamar mai aiki a ASTV ko?” Fadeelah ta ce “Ita ce, ƙanwar Ameen ce fa.” Wadda tai maganar ta ce “Allah sarki, Ni kam tana burgeni, yarinyar a nutse take bata da rawar kai.” Fadeelah ta ce “Ga ta da kirki wallahi so friendly babu ruwanta.”

Neehal ta tura ƙofar ɗakin Ameen a hankali bakinta ɗauke da Sallama, k’amshinsa ne ya fara mata Welcome. Yana kwance akan gado jikinsa sanye da jallabiya brown colour idanunsa a lumshe. Neehal ta ƙarasa ta zauna akan bedside locker tana kallonsa cikin tausayawa, ya ƙara haske kuma ya ɗan faɗa. Hannunta ta kai a hankali ta taɓa wuyansa ta ji jikin nasa da zafi, a tunaninta bacci yake. Ta zare hannunta a hankali daga jikinsa ta ce “Allah ya baka lafiya Yayana.” A hankali ya buɗe lumshashshun idonsa ya sauke su a kanta. Ta ce “Yaya! Sannu, ya jikin?” Bai amsa mata sai tashi zaune da ya yi yana taune lips ɗinsa. Cikin murya mara sa lafiya ya ce “Yaushe kika zo?” Neehal ta ce “Yanzu na zo, ya jikin naka?” Ya ce “Da sauƙi, ina Mum?” Ta ce “Tana gida daga school na biyo ta nan.” Ya jinjina kansa tare da lumshe idonsa, daga gani babu tambaya ka san yana jin jiki. Neehal ta ji duk hankalinta ya tashi dan baza ta iya tuna sanda ya kwanta ciwo irin haka ba, hannun damansa ta kalla ta ga abun ƙarin ruwa alamun ya sha drips. Kamar zata yi kuka ta ce “Yaya me yake damunka? Mama ta ce mun zazzaɓi kake, kuma na ga kamar ba iya zazzaɓin ba ne kawai.” Kafin Ameen ya bata amsa wayarta dake cikin jakarta ta fara vibrate, ta zuge jakar ta ɗauko wayar tare da d’agawa ganin Sadik ne. “Hello Yaya Sadik.” Jin haka yasa Ameen ya juyo da sauri ya kalle ta, ta ce “Eh na dawo, ina gidan Yaya na je duba shi.” Ta ɗan yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce “Tom sai ka zo.” Tare da kashe wayar. Ameen ya mayar da idansa ya lumshe a hankali ya ce mata “Bani ruwa.” Da sauri ta ɗauko ruwan dake gaban gadon ta buɗe sannan ta tashi ta miƙa masa tare da faɗin “Sannu Yaya Allah ya sauwaqe.” Ya d’aga mata kai tare da karɓar ruwan ya sha. Ganin yanda ta damu sai ya kamo hannunta a cikin nasa yana kallon fuskarta ya ce “Menene?” Ta yi ƙasa da idonta ba ta ce komai ba, ya d’ago hab’arta da ɗayan hannunsa ya ce “Don’t cry.” Dan ya san halinta, ai ko kamar zugata ya yi sai ta fara hawaye, ita haka Allah ya halicce ta idan ta ga mutum ba shi da lafiya duk sai ta ji ta damu sosai, musamman ma Yayan nata da take jin kamar ta mayar da ciwon nasa jikinta. Ya ɗan tauna lips ɗinsa murya ƙasa_ƙasa ya ce “Kukan na mene?” Ta ce “Yaya baka da lafiya, na ga duk ka rame.” Ya ce “Ai na ji sauƙi, kuma soon zan warke Insha Allah.” Ta gyaɗa masa kanta. Ya yi ɗan murmushi sannan ya shiga goge mata hawayen fuskarta da tattausan tafin hannunsa ɗaya, ɗayan kuma yana riƙe da hannunta har lokacin. Dai_dai time ɗin Hafsah ta turo ƙofar ɗakin ta shigo………✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:52] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

3️⃣8️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

……….Turus ta tsaya a bakin ƙofar cikin shock, wani abu mai tsananin ɗaci ya tsaya mata a mak’oshi, dama a fusace ta taho saboda Fadeelah ta sanar mata Neehal ta zo tana cikin ɗakin, sai da ta mata masifar me yasa zata bar wata ta shigar mata ɗakin miji sannan ta taho ɗakin. Neehal ta yi ƙoƙarin zame hannunta daga cikin na Ameen jin ƙarar buɗe ƙofar ɗakin, kuma ko tantama ba ta yi Hafsat ce, amma ya ƙi bata damar hakan, sai ma ƙara matse hannunta yake a cikin nasa duk da shim ya ji shigowar Hafsan. Sai da ya goge mata hawayen fuskarta tass sannan ya saki hannunta yana murmushi ya ce “Mommy’s girl, rigimammiya kawai.” Neehal ta koma kan bedside locker ta zauna ta turo ɗan bakinta gaba. Duk yanda Hafsah taso daurewa kasawa ta yi, sosai fuskarta ta nuna ɓacin ranta. Ta janyo ƙafarta data ji ta mata wani iri tana bankawa Neehal harara ta ƙaraso cikin ɗakin, ji take kamar ta janyo ta ta shak’e ta dan tsananin ƙiyayyarta da take ji a ranta. Neehal ta dube ta da murmushi akan fuskarta ta ce “Ina yini Aunty Hafsah.” Kamar an mata dole ta amsa da faɗin “Lafiya.” Neehal ta ce “Ya mai jiki?” A ranta ta ce ”Gashi nan a gabanki ai, kin ga jikin nasa munafuka’  Amma a fili sai ta ce “Da sauqi.” Daga haka Neehal ta ja bakinta ta tsuke sai ma ƙoƙarin tashi da ta yi dan ta ba su guri. Hafsah ta ɗan saki fuska ta zauna a kan gadon ta kai hannunta jikin Ameen wanda idanunsa ke lumshe ta ce “Baby ya jikin naka?” Ameen ya buɗe idanunsa ya kalli Neehal ba tare da ya amsa mata ba, ya ce “Ki bata abinci, daga school take.” Neehal ta miƙe ta ce “No Yaya am full.” Wani kallo ya wurga mata wanda yasa ta yin ƙasa da kanta. Hafsah ta had’iye wani malolon baƙin cikin da ya tsaya mata a mak’oshi, ‘wato ba ma zai amsa mata magana ba, sai ma bata umarnin da bawa wata banzar yarinya abinci. Amma da yake makira ce sai ta dake kamar ba ta ji komai ba. Cikin kissarta ta ce “Ayya, ai ban sani ba sisina, mu je na baki abinci ki ci” Neehal zata yi magana wayarta dake hannunta ta hau vibrate, ta duba tare da d’agawa ganin Mama ce. Mama ta ce “Kin je gidan Ameen ɗin.” Neehal ta ce “Ehh.” Mama ta ce “Ya jikin nasa.” Ta ce “Da sauqi.” Mama ta ce “Is he sleeping?” Neehal ta ce “A’a, idonsa biyu yana ma zaune.” Mama ta ce “Okay, bashi wayar.” Neehal ta miƙa masa ba tare da ta yi magana ba, ya karb’a tare da kara wayar a kunnensa, ko da ba’a faɗa masa ba ya san Mama ce. Gaisawa suka yi, Mama ya masa ya jiki? Sannan ya bawa Neehal wayar. Ameen ya dubi Hafsah wadda ke kallonsa ya ce “Ina kika ajiye mun my phone’s? Mum said ta kira ni ban yi picking ba.” Hafsah ta ce ,”Suna Bedroom dina, bari na ɗauko maka.” Sai kuma ta marairaice fuska ta dafa kafaɗunsa tare da faɗin “Babyna duk ka rame, ciwon nan yana wahalar mun da kai, nice mai cikin amma kai ne da laulayin.” Neehal ta ɗan tab’e baki tare da fita daga ɗakin. Ameen bai cewa Hafsah komai ba, sai idanunsa da ya mayar ya lumshe. Neehal ta fito falo ta zauna ta ɗauko wayarta ta shiga latsawa, su Fadeelah kuwa sai hirarsu suke. Hafsah ta fito ta shiga bedroom ɗinta ta ɗauko wayoyin Ameen ta kai masa, sannan ta fito ta zauna kusa da k’awayenta ba ta ko kalli inda Neehal take ba. Fadeelah ce ma take ɗan sako ta a cikin hirar tasu, ita kuma sai dai ta yi murmushi kawai. Ganin Magriba ta kusa ta miƙe ta dube su ta ce “Aunty Hafsah zan wuce Allah ya ƙara sauƙi.” Bata jira amsarta ba ta mai da dubanta ga su Fadeelah tana murmushi ta ce “Sai anjimanku.” Fadeelah ta ce “Har zaki tafi Neehal? To ki gai da gida da Mama.” Neehal ta ce “Mama zata ji.” Sannan ta juya ta fice daga falon. Hafsah ta bita da harara tare da jan dogon tsaki bayan ta fita. Fadeelah ta kalle ta ba ta ce komai ba, a ranta tana mamakin wannan hali na ƙawartata. Neehal tana koma wa gida Mama ta kalle ta, ta ce “Kuka kika yi ko Neehal?” Neehal ta yi shiru, Mama ta ce “Allah ya shirye ki, ya jikin nasa?” Kamar zata kuma wani kukan ta ce “Da sauqi, amma Mama daga gani Yaya yana jin jiki sosai, duk ya rame.” Mama ta ce “Ki masa addu’a, ba kuka ba.” Ganin idanunta har sun fara ƙyallin k’walla. Da daddare Sadik ya zo suka sha zancensu, sun daɗe suna hira wanda kusan gaba-ɗaya hirar a kan bikin Haneefah suka yi ta. Lokacin da Sadik ya koma gida kamar kodayaushe idan mahaifinsu yana gari, iyayensa duka suna zaune a main Parlour, sai dai yau babu k’annensa. Ya shigo da sallama kan sa a ƙasa, suka amsa masa baki ɗaya. Umma ta ce “Um su Sadik yanzu kullum sai an je zancen ne?” Ran Maamah ya ɓaci amma ba ta ce komai ba. Abbansa ya ce “Idan ya je zance laifi ne?” Cikin kissarta da son ɓata Sadik ɗin a idon mahaifinsa ta ce “Ba laifi ba ne Abbansu, kawai dai na ga ya kamata a san inda yake zuwa zancen ne, domin a tabbatar da tarbiyyar yarinyar.” Abba ya kalli Sadik dake tsugunne ya ce “A ina gidansu yarinyar da kake zuwa yake?” Cikin ladabi Sadik ya ce “A Nasarawa gidansu yake, sunan mahaifinta Alh. Muhammad Tafida.” Abba ya maimaita sunan kamar mai son tuno wani abu “Alh. Muhammad TAFIDA? kamar na san sunan nan, amma dai zan bincika, dan kamar Yadda Ummanku ta faɗa ya kamata mu san inda kake zuwa ɗin, idan gidansu yarinyar gidan tarbiyya ne sai ka cigaba da zuwa, idan kuma akasin haka ne kasan sauran.” Ya ƙarashe zancen yana kallon Sadik. Sadik ya gyaɗa masa kai zuciyarsa babu fargabar komai, dan yasan babu wani abu bad da za a samu a gurin Neehal ko iyayenta Insha Allahu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button