NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Manage please ????
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:31] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
0️⃣7️⃣
……….Neehal ta k’wace jikinta daga jikin Mama ta yi falo da gudu a matuƙar gigice ganin dagaske dai Anwar ɗin ya mutu har za’a tafi da shi, riƙe ta a ka yi ganin ta na ƙoƙarin bin masu ɗauke da gawar, bin gawar kawai ta yi da ido hawayen idanunta ya ƙafe ƙaf kukanma ta kasa yi, kawai gani a ka yi ta yi ƙasa ta fad’i sumammiya. Farkawa kawai ta yi ta ganta a cikin wani d’aki kwance a kan gado, ƙoƙarin tashi zaune ta yi amma ta kasa saboda nauyin da kanta ya yi mata. Muryar Mama ta ji ta na faɗin, “Sannu Neehal kin tashi?” Neehal ta gyad’a mata kai ta na bin d’akin da take da kallo, ƙoƙarin ƙara tashi ta yi Mama ta taimaka mata ta sa mata filo a baya ta jingina da shi, ta na sauke Numfashi, Aunty Sadiya ce ta shigo ɗakin ita da Maman Haneefah, Aunty Sadiya ta ce “Sannu Neehal” Neehal ta ɗaga mata kai kawai, Mommy ma sannu mata. Neehal ta dubi Mama ta ce “Zan yi Sallah Mama” Mama ta taimaka mata ta kaita toilet ta yi alwala, kafin su fito Mahaifiyar Anwar da ta ci kuka ta k’oshi ta shigo ɗakin, sannu ta yi wa Neehal sannan ta shimfid’a mata darduma ta yi Sallah. Bayan ta idar Haneefah ta kawo mata wayarta da’ake ta zuba mata uban kira, ajiye wayar kawai ta yi ba tare da ko dubawa ta yi ba, domin ba ta ita take ba a wannan lokacin, rashin Anwar ba ƙaramin rashi ba ne a gare ta, wayar da su ka yi da safiyar yau ta shiga tunawa bayan sun gaisa ya mata ya jiki sai ya ce mata. Neehal kwana biyun nan na lura kamar akwai wani abun da yake damun ki, ba zan matsa miki a kan dole sai na ji ba, Amma ki sani, ita rayuwa ba ta taɓa tafiya dole sai ka na fuskantar wani K’abule ko kuma jarrabawa daga Ubangiji, kuma komai ya same ka muk’addari ne daga Ubangiji kuma babu mai yaye maka sai shi a kuma lokacin da ya so, dan haka a kodayaushe ki zama mai kaiwa Allah kukanki, kuma ki zama mai haƙuri a kan dukkan wata jarabawa da ta same ki, domin dukkan mai haƙuri ya na tare da Nasara a rayuwarsa. Hawaye mai dumi ne ya zubo daga idon Neehal cikin ranta ta fara faɗin “Ashe dama Anwar mutuwa zai yi, shiyasa ya mata yar gajeriyar nasiha a zantawarsu ta ƙarshe da shi a duniya, Ya Allah ka ji k’an Anwar, ka gafarta masa zunubansa kasa Aljannah ta zama makoma a garesa.”
Kafin Yamma labarin Mutuwar Anwar ya karad’e ko’ina a garin Kano, dama jahohin Nigeria da wasu ƙasashen, kasancewar harbeshi a ka yi, kuma gashi ya na shirin angoncewa nan da wata ɗaya, gashi kuma shahararriyar ‘ƴar jaridar da duniya ta santa zai aura, hakan ya ƙarawa labarin armashin yayatawa. Sosai mutuwar Anwar ta girgiza Mama, musamman idan ta tuna mutane masu Mahimmanci a rayuwar Neehal duk kashe su akai ta hanyar harbin su, zuwa yanzu Mama ta tabbatarwa da kanta akwai wata a ƙasa a rayuwar Neehal ɗin, tausayin ɗiyarta ta ne ya ƙara cika mata zuciya, tun ta na ‘yar ƙaramar ta za’a ɗora mata abin da ya fi ƙarfinta. A ɓangaren su Aunty Sadiya da Aunty Aisha, suma tunanin da suka wuni da shi kenan a ransu, musamman Aunty Sadiya da ta kasance Barrister, tunanin abun take cike da nazari, Maman Haneefah ma haka. Har wannan time ɗin Mama ta na ta trying number’n Ameen, amma ba ta sameshi, abun ya bata mamaki ba kaɗan ba, domin Ameen ko cikin dare ka kira shi sai ka same shi ba ya taɓa kashe wayoyinsa. Neehal kuwa ta na zaune kawai ta na bin mutane da ido, amma ita ko tunanin ma ta kasa, Mutanenta maza da mata ana ta zuwa yi mata gaisuwa, amma abun da ya bata mamaki rashin ganin Yayanta har zuwa wannan lokaci da yamma ta yi Magriba ta gabato. Bayan isha’i su Mama suka tattara suka koma gida, duk da Neehal ta so a barta ta kwana amma Mama ta ce ta bari gobe da sassafe sai su dawo, tunda yanzu gidan damk’am yake da mutane ‘yan’uwan Mahaifin Anwar da na Mahaifiyarsa. Neehal har dare ko ruwa bata kai bakinta ba, ga ciwon mara da yake murd’a mata kaɗan_kaɗan, ta na daga zaune ma jiri take ji. Gabad’aya gidan Mama suka wuce, su Haneefah dai gidansu suka wuce. Neehal ta na kwance akan gadonta Mama ta shigo ɗakin da cup a hannunta, ajiye shi ta yi akan bedside locker sannan ta zauna a gefen gado, a hankali ta ce “Daughter!” Neehal ta buɗe idanunta a hankali ta sauke akan Mamanta, Mama ta ce “Tashi ki sha tea” Neehal ta girgiza mata kai alamar a’a, Mama ta ce “Haba Neehal ki tashi kisha ko kaɗan ne, ko haka za ki kwanta da yunwa” cikin raunin murya Neehal ta ce “Ba zan iya sha ba ne” Mama ta ce “Ki daure ki gwada dai” ƙoƙarin tashi Neehal ta yi Mama ta taimaka mata ta shi, kanta ta dafe da sauri alamun ya na mata ciwo, Mama ta ce “Sannu” sannan ta tashi ta ɗauko tea d’in ta fara bata a baki, Neehal shan tea ɗin kawai take yi amma babu test ko ɗaya a bakinta, tamkar ruwan mad’aci haka take jin sa, tasha kusan rabi kafin ta ture cup d’in daga bakinta har ruwan tea d’in ya d’an zuba a jikinta, Mama ta na shirin yi mata magana, amma ganin ta tashi da gudu ta nufi toilet ya sa Maman ajiye cup d’in ta bi ta, amai take k’wararawa sosai, hankalin Mama a tashe ta shiga yi mata sannu, bayan ta gama ta wanke mata bakinta sannan ta kamata ta mayar da ita ɗaki, ta kwantar. Sosai hankalin Mama ya tashi ganin yanayin jikin Neehal ɗin, ga zazzaɓi mai zafi da ya rufe ta, lullub’a mata duvet Mama ta yi, sannan ta fita ta haɗo allura ta mata, duk rashin son Allura irin ta Neehal wannan kam ba ta ma sam an yi ta ba, ba jimawa kuwa bacci ya ɗauke ta. Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta ƙara gyara mata kwanciya gami da tofa mata addu’a, cike da tsananin tausayinta, ta san a daren yau Neehal ba za ta taɓa rintsawa ba shiyasa ta mata allurar bacci dan ta samu ta rintsa. Falo ta koma inda su Aunty Sadiya suke, Hajiya kuwa ta na ɗakinta itama baccin ya ɗauke ta, ba tare da ta shirya masa ba. Aunty Sadiya ta na duban Mama ta ce “Yaya Fateemah me ki ka fahimta a kan kisan Anwar?” Mama ta sauke Numfashi ta ce “Sadiya na Fahimci kamar yadda a ka kashe Jamil haka a ka kashe Anwar, kuma idan har hakane to saboda Neehal ake kisan” Aunty Sadiya ta jinjina kai ta ce “Hakane, amma shi Jamil ɗin an gano waɗanda suka kashe shin?” Mama ta ce “A’a, dan ko last week mun haɗu da Mahaifiyarsa a asibiti mun daɗe ma, har nake faɗa mata bikin Neehal ya kusa, kuma na tambayeta ya maganar kisan Jamil ta ce mun, an yi binkicen, an yi binkicen amma shiru har yanzu babu wani labari, shiyasa su sun ma haƙura sai addu’a kawai suke, koma waye ya yi kisan Allah ya bi musu hakkinsu” Aunty Sadiya ta ce “Tabɗijan, ni tsoro na ɗaya idan har aka cigaba da bincike a kan mutuwar Anwar, za’a gano a baya Neehal an taɓa kashe mata wanda za ta aura, dan haka gabad’aya binkicen kanta zai koma fa.” Mama ta yi shiru dan ta ma rasa me za ta ce, Aunty Aisha dake saurarensu ta ce “To wai abun tambayar ma a nan Sadiya, idan har saboda Neehal ake wannan kisan waye ya ke yi?” Aunty Sadiya ta ce “Ba mu da amsa Ya A’isha” Mama ta ce “Wannan abun shine babbar damuwata, yau tunanin da na wuni kenan ina yi, akan waye ya kashe wa Neehal duk mijin da za ta aura, kuma me ta yi masa yake mata hakan, me ne ribarshi na yi mata Hakan?” Aunty Sadiya ta ce “Hmmm sai Allah, amma na yi wa kaina alƙawari daga yau zan fara zurfaffen binkice akan wannan abun, insha Allahu ko ma waye yake bibiyar rayuwar Neehal sai mun binciko shi” Mama ta ce “Ba na jin ki a kan aikin ki Sadiya, na san ki na da k’warewa da kuma Sa’a gami da jajircewa, amma kuma sai na ji zuciyata ta na tsoron ki yi aikin nan, kar su gano ki na binkice akan su su yi miki wani abun.” Aunty Sadiya ta yi wani guntun Murmushi ta ce “Kar ki damu Ya Fateemah, insha Allahu babu abin da zai faru da ni, kuma da ma harkar Shari’a a ƙasar nan indai kai me gaskiya ne, sai addu’a kawai, ku dai kawai ku taya mu da addu’a.” Mama ta yi shiru kawai, dan ita kaɗai ta san me yake damun zuciyarta akan wannan baƙon al’amari da ya shigo cikin rayuwarsu yake ƙoƙarin tarwatsa masu farin cikinsu, ita fatan ta ma a ce kisan ba saboda Neehal ake ba, duk da tasan hakan da wuya, domin Neehal ba iya samarinta kawai aka kashe mata ba har da…… Shigowar uncle Ahmad mijin Aunty Sadiya ya katse wa Mama tunaninta, amsa masa sallamar da ya yi suka yi. Ya zauna suka gaisa, sannan suka ƙara tattaunawa a kan al’amarin kasancewar shima Barrister ne, kamar matar tasa, Dad ma ya shigo falon aka cigaba da tattaunawar da shi.