NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Yana kwance akan gadon ɗakinsa ruf da ciki Maamah ta shiga ta same shi, idanunsa a lumshe sai faman sassauke numfashi yake. Maamah ta zauna a bakin gadon tare da ɗora hannunta a kansa cikin sanyin murya ta ce. “Ka yi haquri Sadik, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, ka miƙawa Allah komai zaka ga ya warware maka damuwar ka cikin sauƙi, ta hanyar da baka taɓa tsammani ba. Ka saka a ranka idan Neehal matar ka ce duk runtsi duk wuya sai ka aure ta, just pray hard my son everything will be Okay by the grace of God.” Sadik ya gyaɗawa mata kai tare da sauke ajiyar zuciya. Maamah ta ce. “Dan Allah karka damu kanka da tunani, ka kwantar da hankalinka, ka ga yau ka dawo kana murna muma muna murna, karka ɓata Mood ɗinka ka ɓata namu.” Ya gyaɗa mata kai. Maamah ta shafi sumar kansa ta ce. “Allah yay maka Albarka, ya baka ƴaƴa masu biyayya kamar yadda kake mana, ya zaɓa maka abun da yafi Alkhairi a rayuwarka.” Ya buɗe ido cikin daɗin addu’arta ya ce. “Amin Maamah ta, thank you so much.” Maamah ta yi murmushi ta miƙe ta fice. Ya bita da kallo cikin matsananciyar k’aunar ta, uwa uwa ce, mai sanya farinciki a zuciyar ƴaƴanta akodayaushe, dole duk wanda ya rasa uwa ya yi kuka. Ya lumshe ido a ransa yana faɗin, dole ya yiwa iyayensa biyayya ya rabu da Neehal, duk da ya san zai cutu, cutuwa ba kaɗan ba, bai ma san ya zai kwatanta rayuwarsa babu Neehal ba, bai sani ba ko zuciyarsa zata ɗauki rayuwa babu ita ko ba zata ɗauka ba? A fili ya furta. “I’m sorry Neehal, dole zan bar ki ba dan san raina ba.” Ya sauke ajiyar zuciya tare sakawa a ransa ya rabu da Neehal rabuwa ta har abada kamar yadda iyayensa suke zo, zai dage da addu’ar Allah ya rage masa soyayyarta a cikin zuciyarsa ko da rabi ce, dan ya san ba zai taɓa daina son ta ba har abada. Amma Neehal fa? Yaya zata ji idan ta ji ya bar ta akan ƙaddarar da ba ita ta ɗorawa kanta ba? me yasa mutane baza su yi mata uzuri ba? Me yasa za’a ƙyamace ta a hana a aure ta? Mene laifin ta a cikin ƙaddarar ta? Hawaye masu d’umi ne ya ji suna zarya akan kuncinsa, na tausayin kansa da tausayin abar k’aunarsa, masoyiyarsa, muradin ransa, wadda ya saka ran zata zamto matarsa uwar ƴaƴansa amma ƙaddara ta raba su, a lokacin da ba su taɓa tsammani ba, lokacin da suke gab da mallakar junan su, su zamto abu ɗaya. Ya share hawayen fuskarsa wanda ya manta rabon da ya gan su akan fuskarsa sai yau, shi musulmi ne ya yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, haɗuwar su da Neehal wani shafi ne a cikin shafin littafin ƙaddarar rayuwarsa da Ubangiji ya rubuta masa, haka ma rabuwa da ita, dan haka He accepted it, Rayuwar mumuni dole sai da jarrabawa daga Ubangijin sa. Fata kawai Allah yasa mu iya cinye dukkan jarrabawoyin rayuwar mu, wanda muke fatan hakan ya kai mu ga samun dacewa a duniya da lahira baki ɗaya……..✍️

Not edit, sorry for the typed errors.

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

6️⃣7️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

……….Tun ƙarfe biyar da ƴan mintuna Mama suka yi waya da Neehal ta sanar mata ta taho gida, amma har shida ta wuce bata dawo ba, abun ya bawa Mama mamaki dan daga ASTV zuwa gidansu bai fi tafiyar 10 minutes ba, indai ba mugun go slow mutum ya tarar a hanya ba, shi ma ba zai tsayar da kai har kusan 1 hour ba. kiran wayar Neehal Mama ta yi dan jin abun da ya tsayar da ita amma sai ta ji switch up. Ta kira another sim ɗinta shi ma ta ji shi a kashe, Numbobin Neehal huɗu gare ta amma duk ta kira abu ɗaya ake maimaita mata is switch up. Sai ta ji kawai hankalinta bai kwanta ba, ta miƙe daga zaunen da take gabanta na fad’uwa ta lulubo Numbern ɗaya cikin abokan aikin Neehal mai suna Rahama ta kira. Cikin sa’a wayar ta shiga ringing biyu ta ɗaya tare yin sallama. Mama ta amsa mata ta ƙara da faɗin. “An wuni lafiya Rahmah ya aiki?” Rahmah ta ce. “Alhamdulillah.” Mama ta ce. “Na ji kamar baki gane mai magana ba, Maman Neehal ce.” Da fara’a a muryar Rahmah ta ce. “Laa Mama ke ce, ina yini, wallahi ban gane ki ba, Numbern babu save da yake na canza waya ne.” Mama ta ce. “Babu komai, kin baro gurin aiki ne?” Rahmah ta ce. “Eh, tare ma muka fito da Neehal.” Mama ta sauke numfashi ta ce. “Mun yi waya da ita tun d’azu ta ce mun ta taho saboda bana son ta yi dare a waje tunda ba ishashshiyar lafiya ce da ita ba, to kuma har yanzu na ji ta shiru bata dawo ba, ga magriba ta kawo kai, na kira wayoyinta duka a kashe.” Rahmah ta ce. “Too, kuma bata ce miki zata biya ta wani gurin ba, saboda sai da ta shiga Mota sannan direbanmu ya zo ya ɗauke ni.” Mama ta ce. “Kina nufin ta ma riga ki fita?” Rahmah ta ce. “Eh, buɗe mata gate ɗin ma da akai ta fita kafin a rufe direbana ya shigo, da ya ɗauke ni muka fita daga cikin gidan TV’n babu ma motar ta a layin har ta ƙarasa titi.” Mama ta ce. “Toh shikenan Rahmah na gode, dama na yi tunanin ko ta yi mantawa ne ta koma.” Rahmah ta ce. “Gaskiya ban ga komawar ta ba, amma bari na kira wani a cikin masu night duty in ji ko bayan mun fito ta koma.” Mama ta ce. “Yawwa Rahmah na gode sosai, yanda kuka yi sai ki kira ni ki faɗa mun.” Rahmah ta ce. “Insha Allahu.” Mama ta ajiye wayar a hannun kujera bayan ta katse kiran ta shiga kaiwa da komowa a falon idanunta akan makeken agogon bangon dake manne a kusurwar Parlour’n, duk second ɗaya da yake tafiya akan idonta, haka kuma duk second ɗin yana tafiya ne da ƙaruwar bugun zuciyarta na tsoron kar wani mugun abun ne ya samu Neehal. Girki take a ƙasa amma ta kasa sauka ta ƙarasa, girki na musamman take shiryawa Neehal ɗinta dan ta ci abinci sosai in ta dawo, dan ta san mawuyacin abu ne ta ci a gurin aikin, amma kuma rashin dawowar Neehal ɗin akan lokaci ya sanya mata wani irin abu a zuciyarta, duk da ba yau Neehal ta saba ƙara lokaci ba idan ta fita amma yau ɗin sai ta ji hankalinta ya kasa kwanciya da hakan, ko dan yanayin damuwa da Neehal ɗin take ciki ne yasa take tsoron kar wani abu ya faru da ita? Like accident or something like that. Abun da yake ƙara d’aga mata hankali kuma jin wayoyinta gaba-d’aya a kashe, ta san ba zai yiyu a ce duka wayoyi ukun da Neehal take amfani da su babu charge ba, ta san kuma Neehal bata kashe wayoyinta haka kawai, dole sai da wani dalilin…….

Ringing ɗin wayarta ne ya katse mata tunanin da take, ta ƙarasa ta ɗauka cikin sauri tare da karawa a kunne ganin Rahmah ce take kiran. Rahmah ta ce. “Mama wai bata koma ba tunda ta fita.” Ƙirjin Mama na tsananta bugu ta ce. “Shikenan Rahmah, na gode.” Rahama ta ce. “Kuma bata ce zata biya ta wani gurin ba?” Mama ta ce. “Bata faɗa ba, amma bari na kira Auntie’s ɗinta na ji ko ta je gurin su.” Rahama ta ce. “Toh Mama, Insha Allah ma tana can ɗin.” Mama ta ce. “Allah yasa.” Sannan ta katse wayar ta kira Aunty A’isha. Cikin dabara yanda Aunty A’ishan baza ta gane da wata matsalar ba, Mama ta tambaye ta ko Neehal ɗin ta zo gidanta, Aunty A’isha ta ce bata zo ba, har take tambayar ta Neehal ɗin ta fara fita ne? Mama ta ce mata yau ta fara fita. Bayan sun gama wayar ta kira Aunty Sadiya ita ma ta tambaye ta, Aunty Sadiya ta ce bata zo ba, ita yanzu ma ta dawo daga gurin aiki. Mama ta zauna dab’as cikin tsananin tashin hankali, zuwa yanzu kam ta tabbatar da akwai matsala, gashi Haneefah bata nan suna Kogi state bare ta ce ko gidanta ta tafi. Ta yi tunanin ko gidan Ameen ta tafi, ko kuma gidan su wasu k’awayen nata. Duk wanda Mama take tunanin Neehal zata iya zuwa gidansa a cikin garin Kano sai da ta kira ta tambaya ko ta je, su Aunty matar Uncle Umar, da matar Kawu Musa, da k’awayen Maman da suke zuwa gidajensu da Neehal ɗin, da Maman Haneefah, har mak’ota sai da Mama ta kira amma ko ina babu labari. Ta kira few Freind’s ɗin Neehal da take da Numbern su, su ma babu labari. Data kira Ameen bai ɗauka ba sai ta kira Hafsat ta tambaye ta, and amasar duk ɗaya ce nan ma Neehal bata je ba. A gigice Mama ta sauko ƙasa ta shiga duba all Apartments ɗin gidan ko Neehal ta dawo ta wuce can, duk da wasu a kulle suke amma duk sai da Mama ta duba, su Zulai na taya ta suma hankali a tashe da Mama ta labarta musu abun da yake faruwa, duk bayan mintoci Mama tana ƙara kiran wayar Neehal ko za’a dace, amma still a kashe. Har parking space Mama ta duba ko zata ga Motar ta amma bata gani ba, Mama ta tambaye yi masu gadi ko Neehal ta shigo ta kuma fita suka ce tunda ta fita bata dawo ba. Har an fara kiran Sallar isha’i amma Mama bata yi Magriba ba saboda tashin hankali, ita da bata wasa da Sallah. Ta kira Daddy ta sanar masa Neehal fa bata dawo gida ba, kuma ta kira duk inda take tunanin zata iya zuwa amma an ce bata je ba. A gigice Daddy ya ce gashin nan zuwa gidan yanzu_yanzu. Sai da Mama ta ji ana kiran ishar sannan ta tuna bata yi Magriba ba, ta miƙe cikin sauri ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta tayar da Sallah. A kowacce sujjada tana roƙon Allah ya dawo mata da Neehal gida, tana cikin Sallar ta ji anata kiran wayarta. Tana idarwa ta ɗauko wayar cikin addu’ar Allah yasa Neehal ce take kiran ta ko kuma wani da zai ce mata ya ga Neehal ko kuma ya tsince ta, ita a yanda take ji ma ko ce mata aka yi Neehal tana asibiti ta yi accident zata fi jin daɗi fiye da rashin sanin inda take da halin da take ciki. Amma tana dubawa sai ta ga Ameen ne yake kiran ta. Ta yi pick cikin sanyi jiki ta saka wayar a speaker, muryar Ameen ta karede ɗakin da yin sallama a wayar, Mama ta amsa masa cikin raunin murya. Ya ce. “Mum, I saw your missed call, time ɗin ina yin abu, hope dai ba wata matsalar ba ce na ji muryarki with so concern.” Sai a lokacin Mama ta ji hawaye masu d’umi sun zubo daga cikin idanunta, muryarta da alamun kuka ta ce. “Ameen! Neehal has missed.” A ruɗe Ameen ya ce. “What? Kamar ya?” Mama ta labarta masa abin da yake faruwa. With so concern ya ce mata gashin nan zuwa gidan. Mama ta ajiye wayar tare da rafka tagumi tana hawaye tare da tunane_tunane. Ganin tunanin ba zai kai ta ba ta kira Aunty A’isha da Aunty Sadiya ta sanar musu halin da ake ciki. Ƙarshen rud’ewa su Aunty sun ruɗe, su ma suka sanar da Mama gasu nan zuwa gidan. Ameen ne ya fara zuwa gidan a gigice, ya tarar Mama tana kuka sosai abun da ba zai iya tuna ranar da ya ta yi ba, kasancewar ta mace mai juriya da dauriya. Ya kama hannunta ya ce. “Please Mum stop crying, Insha Allahu za’a gan ta.” Mama ta girgiza masa kai cikin kuka ta ce. “Ameen duba time ka gani har tara fa ta kusa, sai yaushe zata dawo? Ina tsoron yarinyar nan kar damuwa tay mata yawa ta yanke shawarar guduwa wani gurin.” Ameen ya ce. “Miemerh will never do that I know, tarbiyyar da kikai mata baza ta taɓa yanke shawarar guduwa ba, may be Gombe ta tafi ko kuma Abuja, ko dai wani gurin daban.” Mama ta kalle shi cikin sauri ta ce. “Abuja? Gombe? A daren nan zata ɗauki hanya ita kaɗai, amma kuwa idan haka ne yarinyar nan bata kyauta mun ba, ta san hankalina zai tashi sosai, kuma sannan ta kashe wayoyinta.” Ameen ya ce. “No Mum, hasashe na ne kawai ba wai na tabbatar da hakan ba, a halin da ake ciki everything will happen.” Mama ta sauke gwauron numfashi bata ce komai ba. Ameen ya ce. “Let me check har room, ko zan samu something like jotter da take rubuta Numbers a ciki, sai mu kira Freind’s ɗinta da baki da Numbers ɗinsu, mu ji ko suna tare.” Mama ta gyaɗa masa kai cikin gamsuwa da shawararsa. A dai-dai lokacin Daddy ya shigo ɗakin a gigice, hankalinsa a matuƙar tashe. Ameen ya gaishe shi amma ko iya amsawa bai yi ba ya shiga tambayar Mama ƙarin bayanin abun da ya faru. Ameen ya fice dan zuwa bedroom ɗin Neehal, Mama tana ƙara yiwa Daddy bayani tana trying Numbers ɗin Neehal, but still wayar a kashe. Daddy ya shiga maimaita Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un sannan ya ce. “Ina wannan yarinyar ta tafi a dai-dai lokacin da bata cikin normal mood? Bata tunanin wani abun ya faru da ita? Ko dai accident ta yi?” Mama ta ce. “Na yi tunanin haka nima Gen. Amma da haka ne da tuni an kira mu an sanar mana, kusan 4 hours fa da yin wayar mu.” Daddy ya jinjina kai with so concern ya ce. “Yanzu zan bayar da cikiyar ta a duk wata kafar sadarwa dake garin nan, sannan kuma zan baza yarana su bi asibiti_asibiti su duba mun ko an kai ta.” Mama ta ce. “Allah yasa a dace.” Ya ce. “Amin.” Tare da zaro wayarsa a aljihu ya shiga kiran mutane………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button