NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Gudu na fitar hankali waɗanda suka ɗauke Neehal suka dinga shararawa akan titi, duk inda suka gilma sai an yi maganar su da irin gudun gangancin da suke yi kamar basa san rayukansu. Tafiya suka yi takai ta mintuna hamsin sannan suka tsaya a wata unguwa mai kama da jeji, saboda babu gidaje sosai kuma tsit take babu mutane. A gaban wani ƙaton gida wanda shi kaɗai ne a layin ba gida gabansa babu a bayansa suka tsaya, suka danna horn, ba jimawa wani buzu da ya sha rawani ya zo ya wangale musu gate ɗin gidan suka kutsa kai ciki. Girman compound ɗin gidan ya ninka na gidan Mama sau biyu saboda girman sa, sai da suka je har bakin ƙofar da zata sada su da ainihin cikin gidan sannan suka yi parking. Wanda yake cikin Motar Neehal ya ɗauki jakarta cikin sauri ya buɗe ya ciro wayoyinta duka ya kashe su, duk da kafin su tafi farautar Neehal sun katse network ɗin gidan, amma saboda tsaro kuma sun san ogansu zai yi magana anjima da Neehal ta waya, to za’a iya dawo da network ɗin akodayaushe shi yasa ya kashe wayoyin nata kamar yadda aka ba shi umarni. Ya buɗe Motar ya fita ya tarar already har ɗan’uwansa ya fita ya tafi buɗe musu kofofin gidan. Ya ciccibi Neehal ita da jakarta kamar wata yaririya ya nufi cikin gidan da ita. Corridor mai ɗan tsayi zaka tarar kana shiga ciki mai ɗauke da k’ofofi a jejjere, sai da suka kusa zuwa ƙarshen sa sannan suka buɗe wata ƙofa suka shiga da Neehal dake kwance tamkar gawa. Madaidaicin d’aki ne da ya ji komai na buƙatar rayuwa, akan k’aton gadon dake ɗakin suka shimfid’e ta. sannan wanda ya ɗauko ta ya kwashe wayoyinta suka fice daga ɗakin suka kulle ta.

Bata farka ba sai kusan goma na dare, a hankali ta buɗe idonta da ƙyar ta shiga bin ɗakin da kallo, tana jin kanta yay mata wani irin dumm, ga warin wani abu a hancinta. So take ta tuno inda take da abun da ya faru da ita amma ta kasa, ƙwaƙwalwarta gaba-ɗaya ta cunkushe ta ƙi yin tunanin da take son tay mata, sai kayataccen ɗakin data gan ta a ciki wanda ya ji komai take bi da kallo, ta dai gane dare ne lokacin duk da wadataccen hasken dake ɗakin. A hankali cikin ikon Allah ƙwaƙwalwarta ta dawo dai-dai, ta fara tariyo mata last thing da ya faru da ita. Ta k’walla razananniyar ƙara tare miƙewa zaune a matuƙar hanzarce ƙirjinta na bugawa a million. Ta sauko daga kan gadon kamar zata kifa tana magana a fili cikin matuƙar rud’ewa da razana. “Ina ne nan? A ina nake? Wa ya kawo ni? Me na zo yi a nan? Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un.” Ta ƙarashe maganar tare da ɗora hannayenta duka a kanta. Ta fashe da kuka tare da faɗin. “Su waye ku da kuka kawo ni nan? Me nay muku? Me kuke so da ni? Nan kuma ƙaddarata ta kawo ni? Ya Allah ka fitar da ni daga gurin nan, Allah karka ba su ikon cutar da ni.” Sai ta nufi gurin da take tabbacin nan ne ƙofar shigowa ta kama handle ɗin ƙofar tana murd’awa da ƙarfi tare da bubbuga ƙofar da ɗayan hannunta tana kuka tana faɗin su zo su mayar da ita gida. Ganin babu alamun akwai ma me jin ta balle ya taimake ta, ta zube a bakin ƙofar tana ƙara volume d’in kukanta. Tana jin zuciyarta kamar zata tarwatse saboda tension, tana jin dama Ubangiji ya zare ranta a yanzu ta huta da wannan masifar da bala’in da yake riskar ta daga wannan sai wannan. Nan kuma ina ne waɗannan mutanen suka kawo ta? Ta d’ago kanta a fili ta ce. “Why Neehal? Why? Me yasa na buɗe my car na yi magana da mutanen nan? Da na yi zama na a cikin Motar har Allah ya taimake ni ya kawo wanda zai iya taimako na, ko kuma Daddy ko one of our staff soldiers sun zo sun kori mutanen. Wanne ganganci ne ya kai ni zuge glass ɗina?” Zuciyarta ta bata amsa da faɗin. ‘Tsautsayi da rashin sani.’ Tabbas tsautsayi ne wanda ba ya kaucewa ranar sa. Da kuma wata sabuwar ƙaddarar a cikin jerin ƙaddararorin rayuwarta. Jin ana buɗe ƙofar ɗakin ta waje ta tashi da gudu ta nufi kan gadon ta faɗa ta kudundune jikinta guri ɗaya tana cigaba da kukanta. Aka turo ƙofar ɗakin aka shigo aka mayar aka rufe, ɗaya daga cikin wanda suka kawo ta gidan ne, Neehal ta bi shi da kallo da jajajen idonta tsoro mai tsanani na ƙara lullub’e ta, ta ƙara makurewa a jikin gadon bugun zuciyarta na ƙaruwa kamar zata faso  ƙirjinta ta fito. Abinci ne a hannunsa ya ajiye mata a kan bedside locker, yana duban ta da wani shegen murmushi ya ce. “Ki ci abinci ƴan’mata.” A zafafe ta ce. “Ba zan ci ɗin ba, ku mayar da ni gida, me yasa zaku kawo ni nan, ku mayar da ni gurin Mamata, me nay muku? Me kuke so a wajena?” Ta fashe da kuka mai ban tausayi. Bai ce komai ba ya juya da niyyar fita, ta tashi ta biyo shi ta riƙe hannunsa ta fara ihu da ƙarajin ya mayar da ita gida ita dai. Ya hankad’a ta, ta faɗi a ƙasa, kafin ta yi yunƙurin tashi ya buɗe ƙofar ya fice. Ta ƙurawa ƙofar ido kamar idanun nata ne za su buɗe mata ƙofar. Ta tashi da ƙyar ta faɗa kan gado cikin rashin sanin mafita, “Mama.” Ta furta a fili. Ta san tana can hankalinta a tashe, tana can cikin damuwar rashin dawowar ta gida. Ta tashi zaune da sauri ta janyo hand bag ɗinta dake tsakiyar gadon ta buɗe da niyyar ɗauko wayoyinta ta kira ta, amma sai ta ga babu ko ɗaya. Ta zazzage jakar hoping ko zata ga wayoyin sun mak’ale a wani gurin, amma kuɗi da earpiece da i.d card ɗinta na gurin aiki ne kawai suka fado. Ta yi cilli da jakar ƙasa ta kuma fashewa da wani sabon kukun, tana ambaton sunan Allah a ranta tare da neman taimakonsa. Tunawa ta yi bata yi Sallah ba hakan yasa ta d’ago kanta, idanunta suka sauka akan agogon bangon dake ɗakin wanda ya nuna sha ɗaya da rabi na dare. Ta miƙe ta sauko kamar zata fadi ta nufi ƙofar da take da tabbacin toilet ne, tana turawa ta ga ta buɗe, kuma kamar yadda ta zata toilet ɗin ne mai matuƙar kyau a tsabtace, ba ta shi take ba abun da ya shigo da ita kawai ta yi ta fito, ta gyara hijabin jikinta ta tayar da Sallah. Bayan ta idar ta rafka tagumi a gurin, tana tunanin ko kidnappers ne suka sace ta, ko kuma gidan masu yankan kai aka kawo ta. Tana nan zaune aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, bata ko motsa ba balle ta d’ago ta kalli mai shigowar, ta fawwalawa Allah komai, ta san duk abun da ya rubuta zai same ta babu makawa sai ya same ta, kuma shi kaɗai ne zai iya kare ta daga dukkan wani sharri da mutanen nan suke nufi da ita. Mutumin d’azu ne ya ƙara dawowa da waya a hannunsa, ya tsugunna a kusa da ita tare da miƙa mata wayar yana faɗin. “Oga zai yi magana da ke.” Wata uwar harara ta zabga masa sannan ta ce. “Bazan yi maganar ba, ku mayar da ni gida na faɗa muku, ku kai ni gurin Mamata.” Bai ce komai ba ya saka wayar a handsfree, wata murya mai kaushi ta karaɗe kunnen Neehal da dariya, daga baya kuma aka daina dariyar ya fara magana da faɗin. “Fateemah Zahra! Neehal! ƴar Mamanta. Ki kwantar da hankalinki zaki koma gurin Mama nan kusa, amma kafin nan zai mun amshi abun da muka kusa shekara goma muna dakon sa a gurinki, abun da ƘUNGIYA Mai daraja take da buƙatar sa shekara da shekaru, abun da bata taɓa shan wahala gurin mallakar wani abu kamar sa ba, yau gashi lokaci ya yi, dama an ce komai nisan dare gari zai waye. Yau ƙungiya tana cikin farincikin da bata taɓa kasancewa a cikin irin sa ba, yau zata kwana tana shan shagalin da murnar mallakar BUDURCIN NEEHAL. Tun da ya fara magana babu abun da Neehal ta fahimta sai kalmar virginity ɗinta, ta ji dai yana ambatar ƙungiya. Cikin rud’ewa ta ce. “What? Wacce ƙungiyar? Me kuke so a gurina?” Mutumin ya kuma ƙyalƙyalewa da dariya cikin ƙatuwar muryarsa sannan ya ce. “Zaki gane komai daga daren yau zuwa safiyar gobe, zan so ace ni ne zan ratsa kyakkyawar yarinya ƴar hutu wadda ƙungiya take girmamawa da tattalin budurcin ta, sai dai kash dole sai mamallakin budurcin ne zai amshi abun sa.” Zuwa yanzu Neehal ta soma gane inda maganganun sa suka dosa, sun ɗauko ta nan ne domin yi mata fyade akan wata buƙatar su ta banza. Cikin ƙaraji da rashin tsaro ta ce. “Ƙarya kake munafukin Allah, Ubangiji ba zai taɓa baku nasarar cutar da ni ba, mushrikai kawai!” Mutumin ya ƙyalƙyale da wata muguwar dariya sannan ya ce. “Yaro man kaza, yaro baka san wuta ba sai ka taka. Dole a gobe ɗaya cikin ƴan ƙungiya ya mallaki budurcin ki, dole a gobe sarauniya ta sha sperm ɗinki da take ta ƙwadayin shi shekara da shekaru, ƙungiya bata taɓa neman abu ta rasa ba, ki hutawarki ƴan’mata.” Daga haka wayar ta yi ɗil alamun an yanke. Neehal ta shiga jujjuya kanta dake barazanar fashewa, ta ɗora hannunta a ƙirjinta da yay mata wani irin nauyi tana ambaton sunan Allah cikin fitar hayyaci. Bata ma san time ɗin da baƙin mutumin nan ya fice daga ɗakin ba. Ta d’au tsawon lokacin da bata san yawansa ba a cikin wannan halin, a hankali cikin Ikon Allah ta fara dawowa cikin nutsuwarta. K’azaman maganganun mutumin da sukay waya na yi mata kuwwa a cikin kanta tamkar yanzu yake faɗa mata, ta shiga auna maganganun nasa a mizanin hankali, idan ta fahimta wannan kungiyar da yake magana akai ta matsafa ce masu asiri dan neman duniya, idan ta fahimta mitumin da suka yi magana ba shi zai amshi budurcin nata ba kamar yadda suke so, wani ne daban wanda ya alaƙanta shi da mamallakin budurcin nata. “To waye wannan?” Ta tambayi kanta a fili, bata da amsa ba kuma ta san inda zata samo ta ba, hakan yasa ta tafi point na gaba. Wanda ya ce kusan shekara goma suna d’akon virginity ɗinta, idan ta fahimta su ne suka kashe su Jameel kenan dan sun san idan ta yi aure zata rabu da abun da suke dakon shi a gurin ta? Me tay musu da zafi haka to suke bibiyar ta da wannan mummunar manufar? Su waye ƴan ƙungiyar da sarauniyar su? A ina suka san ta da har suke son cutar da ita? Tambayoyi barkatai ta shiga yiwa kanta, daga baya ta fara addu’ar kar Allah ya basu ikon cimma mummunan kudirin su a kanta. Sai kuma ta koma tunanin abun da Mama tay ta tambayar ta a cikin kwanakin nan, ko ta taɓa samun saɓani da wani shine yake ta bibiyarta rayuwarta dan ɗaukar fansa, amma kuma ta kasa tunowa tunda babu, bata jin ta taɓa samun babban saɓani da wani a rayuwarta. Ta kawar da wannan tunanin ta koma tunanin samarinta da ba su ji ba, ba su gani ba an kashe su saboda ita, ta tuno Jameel wanda da an yi auransu da tuni yanzu sun yi 6 years da aure yanzu, Anwar kuma 3 years da watanni, sai Sadik da sun kusa wata biyu. Idan har waɗan nan mutanen suka samu nasarar cimma burinsu a Kanta rayuwarta ta zo ƙarshe, bata ga amfanin sauran rayuwarta_ta ba, tunda an raba ta da abu mai kima da martaba da daraja a tare da ita. Ta girgiza kanta tare da addu’ar Allah ya ɗauki ranta kafin safiya, ko ta huta da wannan bala’in. A tak’aice yanda ta ga rana yau haka ta ga dare……….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button