NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Kamar yadda Neehal bata iya runtsawa ba yau haka ma Su Mama ba su runtsa ba, dan Ameen ma sai ɗaya saura na dare ya bar gidan. Tashin hankalin da Mama take ciki ba zai misaltu ba, kwana ta yi tana kuka Daddy da Aunty Sadiya suna kanta suna bata baki, Aunty A’isha kuma tana gefe tana Sallah da roƙon Allah ya kare Neehal a duk inda take. Da yake su Auntie’s ɗin a gidan suka kwana ganin halin da Mama take ciki. Jiya har ɗaya na dare suna buge_bugen wayar mutane suna tambaya ko Neehal ta je gurin su, duk wata Number da Neehal ta rubuta a cikin jotter data rubuta Numbers da Ameen ya yi nasarar gani a ɗakinta, ya kira amma babu wanda ya ce ta je gurinsa, kafin ƙarfe goma na daren kuwa cikiyar Neehal ta baza garin Kano kamar yadda Daddy ya bayar da sanarwa a kowacce kafar yaɗa labarai dake garin Kano. Sai da asuba sannan Mama suka kira mutanen Gombe da na Abuja ko Neehal ɗin ta je can, nan ma aka sanar musu bata je ba. Da sassafe Uncle Mahmud ya haɗo Hajiya da driver zuwa Kano wadda ta matuƙar gigice jin ɓatan Neehal, Yayan Dad ma asubanci ya yi ya taho hankali a tashe. Duk gidan ƴan’uwa da kawu Musa yake tunanin Neehal zata je ya kira an ce bata je ba, har Gabasawa sai da ya kira nan ma babu wani labari. Wajen ƙarfe shida Mama ta kira Wayar Uncle Usman ta ji ko Niger ɗin Neehal ta je, ko kuma tana hanyar zuwa idan ta ƙarasa ya kira su ya sanar musu amma sai ta ji wayar tasa bata shiga. Ta kira Haneefah ko Kogin Neehal ta je amma Ita ma ta ce bata zo ba. Idan ka ga Mama sai ka tausaya mata ko ka zubar mata da k’walla, saboda yanda duk ta fita hayyacinta lokaci ɗaya. Ƙarfe bakwai na safe Daddy ya bar gidan dan zuwa Hospital’s da kansa duba Neehal, gani yake kamar yaran da ya saka aikin basa dubawa da kyau shi yasa tun jiya har yau ba’a gan ta ba……….

Neehal tana rakub’e a gurin da ta yi Sallar Asuba har gari ya waye, ta rafka tagumi tana jiran ganin ikon Allah, bata taɓa riskar ranar data tsinci kanta a cikin tsoro da fargaba irin na yau ba, ta sadaqar ta karaya yau sai yanda Allah ya yi da ita tunda ya nufa ta wayi garin yau da ranta, ita kaɗai a cikin wannan gida tare da waɗannan azzaluman mutanen ai sai yanda suka yi da ita, amma bata daina addu’ar neman ɗauki a gurin Ubangijin ta ba. Wajen ƙarfe takwas aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, ta runtse idanta cikin matsananciyar fad’uwar gaba da murd’awar ciki, a hankali ta ce. “Shikenan, sun zo ida mummunan baƙin nufinsu a kaina, shikenan rayuwata ta zo ƙarshe.” Jin an ajiye abu a gabanta yasa ta buɗe ido tare da d’ago kanta zuciyarta fal tsoro, wani farin saurayi ta gani tsaye yana kallon ta, gabanta kuma tire ne mai ɗauke da abinci, da alamun shi ya ajiye mata. Hawaye ya taru a cikin idonta ta fara kuka ta ce masa. “Fuskarka bata yi kala data masu cutarwa ba, ta yi kala data masu imani, dan Allah bawan Allah ka fitar da ni daga gidan nan kafin su gurɓata mun rayuwata, ni marainiya ce bani da kowa sai Allah, ka taimake ni dan Allah, na san baza ka so a wayi gari ka ga an ɓata rayuwar ƙanwarka ba, to ka ɗauke ni kamar haka ka fitar da ni daga gidan nan.” Saurayin ya lumshe ido a hankali ya buɗe, kamar zai yi magana sai ya tuna ba’a ba su umarnin hakan ba, kuma akwai CCTV camera a ɗakin, sai ya juya cikin wani irin yanayi ya fice daga ɗakin. Neehal ta fashe kuka tare da saka ƙafa ta yi ball da abincin gabanta. Cikin kukan take faɗin. “Yaya where are you? Ka zo ka fitar da ni daga gidan nan kar su cutar da ni, kar su yi abun da zai sa zuciyar Mama ta buga, Daddy…….” Haka ta dinga kiran sunan duk wani makusancinta tare da neman taimakon su, abun tausayi ta zama kamar wata zararriya. Ƙarfe goma saura wasu maza majiya ƙarfi guda biyu suka shigo ɗakin, Neehal ta tashi da gudu ta haye kan gado ta koma can ƙarshen gadon ta takure jikinta dake karkarwa kamar ana kad’a mata mazari. Gifd’a_gifd’an mutanen nan guda biyu suka bi ta gadon suka kamo ta tana ihun su sake ta har su kai ta inda za’a keta mata haddi amma kamar da dutse take magana abun da aka saka su kawai sukay. Fitar da ita suka yi daga ɗakin, wata ƙofa dake ƙarshen corridor ɗin gidan suka buɗe suka shiga, steps ɗin bene ne ya bayyana suka fara hawa da ita. K’ofofi uku ne a upstairs ɗin da suka hau, ta farko suka buɗe suka tura ta tana tirjewa sannan suka ja ƙofar suka fice. Ta d’ago kanta ta kalli mutumin dake tsaye a gaban gado yana saka face maks ta bogi a fuskarsa, sai dai kafin ya gama zirawa ta ga ainihin fuskar tasa, kuma ta gane shi. Ta miƙe cikin matuƙar dimaucewa daga fad’uwar da ta yi lokacin da mutanen nan suka yarda da ita. Dai-dai lokacin mutumin ya gama saka fake face maks ɗin, suka haɗa ido da shi ta cikin face maks ɗin da ya saka. Ko a cikin magagin bacci take ta ga mutumin nan sai ta gane shi, ko makancewa ta yi ta shafa fuskarsa sai ta gane shi, tsayuwarsa da siffar jikinsa kaɗai idan ta gani sai ta gane shi ko da ya juya mata baya ne, ko a cikin duhu ne, balle yanzu da yake tsaye a gabanta cikin haske suna pacing ɗin juna, ba fuskar bogi ba ko jikinsa duka ya ɓoye a cikin kayan ƙarfe sai ta gane shi, balle kuma ta riga ta ga fuskarsa ba tare da ya sani ba, ga kuma k’amshinsa da ba baƙo ba ne a gurin ta da ya mamaye ɗakin. Amma ita duk ba wannan ne damuwarta ba, damuwarta me ya kawo shi gidan? Me yake yi a cikin gidan da ake ƙoƙarin keta mata haddi? Me yasa k’artan mazan can suka kawo ta inda yake? Ko shine wanda mutumin da suka yi waya jiya ya ce zai aiwatar da mummunan ƙudirinsu a kanta? Ta d’aga hannunta dake karkarwa kamar an jona masa shock da ƙyar kamar yadda zuciyarta take fat fat fat kamar zata faso ƙirjinta ta fito ta nuna shi, cikin rawar murya numfashinta na fita da ƙyar kamar ana zarar ranta ta ce. “Ya……….✍️

(???????? Neehal wa kika gani ne!? )

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

6️⃣6️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

………..Sai kusan ƙarfe goma na dare Daddy ya dawo gidan, Yana cikin cire kaya Mama ta shigo ɗakinsa. Ta zauna akan stoll tana duban shi ta ce. “Daddy yau ina ka je ka daɗe haka? Gashi ina ta kiran wayarka bata shiga?” Daddy ya ce. “Au har kin manta inda na ce miki zan je da safe kenan?” Mama ta ce. “Sorry na sha’afa, sannu da zuwa da fatan kun dawo lafiya kuma an dace da abun da aka je nema?” Daddy ya ce. “An dace kam, bari na ci abinci nay wanka sai nay miki bayani.” Mama ta yi murmushi ta ce. “Ga dukkan alamu dai baka da labarin an ga Sadik.” Daddy ya ce. “What? Yaushe? Wallahi ban sani ba.” Mama ta ce. “Tun yamma aka gan shi ko in ce ya dawo, dan Mamansa ta ce mun da kansa ya shigo gida cikin k’oshin lafiya.” Daddy ya ce. “Alhamdulillah, kai Masha Allah for this nice story, to ya akai ya dawo?” Mama ta ce. “Bata faɗa mun ba, da zamu je gidan kuma rashin dawowar ka da wuri yasa bamu je ba, su Sadiya ma duk sun zo d’azun, amma gobe da safe Insha Allah zamu je gaba-d’ayan mu.” Daddy ya zauna yana murmushin farinciki. Mama ta ce. “Kwanan masallaci ana sauka ya ƙare, yau sai ka more bacci ko zaka ciko, dan ba ƙaramar rama ka yi ba a Ƴan kwanakin nan.” Daddy ya yi murmushin dake bayyanar da farin cikinsa ya ce. “Dole ai, bari na kira baban yaron na fara yi masa murna.” Mama ta ce. “Toh, bari na kawo maka abincin ka nan ka ci.” Daddy ya ce. “Ina Daughter ɗin ne da Hajiya?” Mama ta ce. “Sun kwanta tuntuni, Neehal ta sha kuka kanta sai ciwo yake mata.” Daddy ya ce. “Sarkin kuka kenan, ta cancanci award ta wannan fannin.” Mama ta ce. “Rashin duka ne da iskancin banza, abun kuka da bana kuka ba ita duk kuka take musu.” Daddy ya yi dariya ya ce. “Duka kuma Doctor? Tab’ ai ba me taɓa mun ƴa ya kwana lafiya, saurin kukanta kuma ai halitta ce, da yawan mutane haka suke musamman ku mata.” Mama ta ce. “To Allah ya yaye mata.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button