NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Sabuwar rayuwa Neehal ta buɗe a shafin rayuwarta, a ƙoƙarin ta na ganin ta manta da dukkan abubuwan da suka faru da ita a baya a rayuwarta. Ta yi ƙoƙari sosai wajen cire Sadik daga cikin zuciyarta tare da dagewa da addu’a. Ta koma shiru_shiru a rana bai fi ta furta kalmomin daza a iya irgawa ba. Kafin ka ga murmushi a fuskarta kam za’a daɗe. Alkur’ani da azkar su suka zamto abokan hirar ta, wani lokacin kuma takan taɓa karatun Hausa novels wanda Aunty Sadiya ta tuttura mata dan su ɗebe mata kewa. Tana kuwa jin daɗin karatun littafan sosai. Bata fita ko’ina, saboda a ganin ta tana fita za’a fara nuna ta ana gata nan ita ce duk wanda zata aura sai an kashe shi. Mama da Daddy sun yi sun yi ta koma gurin aikinta amma ta ƙi, da suka takura mata sai ta saka musu kuka, dole suka haqura suka ƙyale ta. Duk wani abu da Mama ta san zai sata farinciki shi take yi, haka zata fita da kanta ta jido mata su sweets wanda ada ita take hanata shan su, amma yanzu duk dan ta yi farinciki take siyo mata. Tun ranar da aka mayar wa da Sadik kayansa gidansu ya turo mata text ɗin ban haquri da nuna mata ba laifinsa ba ne ba su ƙara magana ba. Ahmad ya zo tun cikin week ɗin da ya samu labarin bayyanar Sadik, yay mata murna ya sanar mata bikinsa watan malaudi. Bata sanar masa an fasa bikinsu da Sadik ba dan ta san tsaf zai iya dawowa cikin rayuwarta a matsayin masoyi, ita kuma bata son hakan, ta riga ta cire babin soyayya a rayuwarta. Kuma baza ta so yabar yarinyar da zai aura saboda ita ba, dan ko ita akaywa haka baza ta ji daɗi ba. Ameen kuwa sai ya zo gidan ya tafi ma ba su haɗu ba saboda wunin ɗaki take, babban dalili ne yake fito da ita falo ko ya saukar da ita ƙasa.
Yau ta kama Monday, wanda ya yi dai-dai da wata ɗaya da fasa Auren su da Sadik. A jiya ne kuma ƙawarta Zee ta Bayero ta sanar mata result ɗinsu na last semester is on the corner. Hakan yasa ta shirya yau zata je gurin aikin su, saboda ta ciccike wasu takardu na promotion ɗin da za’ai mata, tunda yanzu zata bar aiki da k’walin Deplomer ne ta koma da na Degree, kafin result ɗin ya fito komai ya yi ready sai ta haɗa ta yi linking ɗinsu. Dama zaman gidan ya fara isar ta, kuma wannan aikin shine gatan ta a duniyar nan, baza ta so ta rasa shi ba.Ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa, ta yi kwalliya sama_sama a ƙoƙarin ta na ganin kar mutane su gane halin damuwar da take ciki. Sai dai a fuska ne kawai ta iya pretended amma damuwar na nan kwance a cikin zuciyarta. Ta tsaya tana kallon kanta a mudubi, sai ta ga ta rame musamman ta wuya da saman ƙirjinta. Hakan yasa ta cire mayafin jikinta ta ɗauko hijabin da zai shiga da kayan jikinta ta saka. Ta ɗauki jakarta wadda wayoyinta ke ciki ta nufi ƙofa, har ta buɗe ƙofar zata fita ta dawo ta ɗauki wata ƙaramar wayarta keypad wanda bata fiya amfani da ita sosai ba, ta saka ta a cikin aljihun rigar jikinta sannan ta fita. A falo suka ci karo da Mama, Mama ta yi murmushin jin daɗin yanda ta gan ta. Ta kama hannunta ta ce. “Kin tashi lafiya Daughter.” Neehal ta ce. “Lafiya k’alau Mamana, ina kwana.” Mama ta ce. “Lafiya k’alau, ko kefa Neehal har na ji daɗi da zaki koma aikin nan, zai ɗebe miki kewa ba kaɗan ba, jiya da Ameen ya zo kin yi bacci yay ta faɗa wai iskancin me ya hana ki komawa aiki.” Neehal ta yi murmushi ta ce. “Mama ɗan nan naki halinsa sai shi, Yaushe ya daina masifar zuwa na aikin, amma yanzu dan bana zuwa zai ce in koma.” Mama ta ce. “Nima na yi mamakinsa, wai zama guri ɗaya babu fita gara kina fita kina ganin jama’a hakan zai rage miki damuwa.” Neehal ta ce. “Haka ne, shi yasa yau na shirya komawa, Daddy ya fita ne?” Mama ta ce. “Yana nan yanzu dai zai fitan.” Neehal ta ce. “Bari na je na gaishe shi.” Mama ta ce. “Okay.” A falo ta tarar da Daddy zaune yana waya, ta zauna a ƙasan kujerar da yake a zaune, sai ya katse wayar ya dube ta da murmushi ya ce. “Daughter an fito? Ta ce “Eh Daddy ina kwana?” Ya ce. “Lafiya k’alau ƴar albarka, dafatan kin yi breakfast?” Ta ce. “Na yi Daddy.” Ya ce. “To Masha Allah, sai yaushe zaki dawo?” Ta ce. “Zan kai yamma saboda cike_ciken da zan yi.” Daddy ya ce. “To Allah ya taimaka, ki kula fa sosai kin ji.” Ta ce. “Insha Allah Daddy.” Sannan ta miƙe tay masa sallma ta fita, ta koma ta yiwa Mama Sallama ta tafi.
Ta ji daɗin fitar da ta yi yau sosai, sai ta ji duk rabin damuwarta ta kau, tana ta hada_hada cikin jama’a ko time ɗin tunani bata samu ba, balle ta tunano abun da zai dame ta. Duk inda ta gilma ma’aikata na yi mata magana, wasu na tsokanarta da wata sabon gani wasu kuma suna yi mata ya jiki, saboda abun da ta cewa Manager ɗinsu kenan da bata zuwa bata da lafiya ne. Sai yanzu ta ƙara tabbatar da abun da Mama take faɗa mata kullum akan ta dinga fita zata ji sauƙin damuwar dake ranta. Sai yamma ta baro gurin aikin tana jin zuciyarta wasai. Ta shigo farkon layin su ta ga wata Mota tana tahowa daga cikin layin, ta yi b’arin left inda masu shiga suke bi, masu fita kuma right side suke bi, amma sai ta ga Motar saitin da take bi nan ita ma take bi, kuma layin nasu yana da faɗi sosai, three motors zasu iya wucewa a lokaci ɗaya ba tare da sun takura ba, kuma babu kowa a layin balle ta ce an tsare masa hanya ne. Ta cigaba da tafiya slowly tana kallon ikon Allah, sai ta koma right side ta bar masa left side ɗin, sai ta ga shi ma ya canza ya koma inda ta koma. Ta yi tsaki ta cigaba da tafiyar ta, a ranta tana faɗin baza ta kuma matsawa ba, sai dai shi in ya ga zasu yi karo ya matsa. Amma me, sai kawai ganin Motar ta yi ta sha gaban ta kamar zata buge ta. Ta taka burki cikin sauri gabanta na fad’uwa. Kafin ta yi wani yunkurin ta ga maza guda biyu sun fito daga cikin Motar cikin sauri, ta yi looked Motar ta_ta da sauri cikin mamakin dalilin da yasa waɗan nan mutanen zasu tare mata hanya, ta shiga ambaton Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un a cikin zuciyarta. Suka ƙaraso inda take suka yi mata knocking glass ɗin Motar. Da farko ta tsorata sai ta ƙi buɗe musu, amma daga baya kuma da ta ga suna bata mata time sai ta zuge glass ɗin Motar ƙasa ta dube su cikin dakiya da son ɓoye tsoron da take ciki ta ce. “Me kuke buƙata a gurina, da zaku taren hanya and then ku zo kuna mun knocking?” Ɗaya daga cikin su ya juya yana kallon layin da babu kowa sai su kaɗai, ɗayan kuma ya bata amsar tambayar ta da watsa mata wani abu a fuska. Ta rufe idanunta tare kare fuskarta_ta da hannunta tana jujjuya kanta saboda juyawar da ta ji ya fara mata, cikin wasu sakanni kanta ya langwab’e a jikin kujerar da take. Da sauri wanda ya watsa mata abun ya zira hannunsa ta saman glass ɗin ya yi unlocked ɗin Motar, sannan ya ja murfin ya buɗe ya shiga, ya mayar da Neehal kujerar mai zaman banza sannan ya zauna a driver seat ya rufe Motar ya tayar da ita ya yi reverse ya fice daga layin da mugun gudu. Ɗayan wanda ya kasance kamar mai yi masa gadi ya juya cikin gudu ya shiga Motar da suka fito daga ciki ya kunna ta ya bi bayan ɗan’uwansa a guje………✍️
By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
6️⃣8️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price