NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

………”Ya…ya… Al…lah kasa mafarki nake ba gaske ba ne abun da yake faruwa.” Ta sauke hannunta tare da runtse idonta tana girgiza kai, cikin ranta tana addu’ar Allah yasa ta buɗe ido ta ga babu shi a gurin, Allah yasa idan ta buɗe idon ba shi zata gani ba wani daban zata gani idanunta ne ke mata gizo. Ta buɗe idonta a hankali kamar mai tsoron buɗewa bugun zuciyarta na ƙaruwa. Shi ɗin ne dai tsaye a gaban ta yana kallon ta. Ta sake nuna shi tana ƙoƙarin yin magana amma ta kasa sarrafa harshenta ta yi maganar, sai rawar baki kawai take. Ta juya cikin fitar hayyaci ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice da gudu, ƙofar dake kusa da dakin ta murd’a ta buɗe ta shiga, cikin ikon Allah kuma ƙofar a buɗe take. A cikin wani ɗan ƙaramin ɗaki da babu komai a cikinsa ta tsinci kanta, ta zube a bakin ƙofar cikin matsanancin tsoro da fargabar wanda ta gani, shirun sa da yanda ya tsaya yana kallon ta ya tabbatar mata da shine wanda yake ƙoƙarin keta mata haddi, me ya haɗa shi da wannan ƙungiyar wadda bata tantama ta matsafa ce? Ko shi ma member ne a cikinta? Ta tambayi kanta. “Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un.” Ta shiga maimaitawa a fili cikin sark’ewar numfashi. Addu’a da fatanta ɗaya Allah ya farkar da ita daga wannan mummunan mafarkin da take, dan ta kasa yarda a gaske ne wannan baƙin al’amarin yake faruwa da ita. Wanda take masa kallon jigon rayuwarta anya zai aikata mata haka? Wanda take kallo a matsayin bangon rayuwarta a ce da shi ake ƙoƙarin gurɓata mata rayuwa, wannan wacce irin ƙaddara ce ta kuma samun ta? Wacce irin rayuwa take yi ne a duniyar nan? A fili ta furta. “Ya Allah idan wani laifin nai maka kake jarabta ta Allah ka yafe mini ka sassauta mun wannan jarabawar, Ya Allah karka tabbatar da abun da nake zargi, Allah karka ɗora mun abun da ya fi ƙarfi na.” Ta zauna akan gwiwoyinta ta shiga bubbuga kanta a jikin kofar ɗakin cikin rashin sanin mafita da abun yi, ƙwaƙwalwarta_ta ta tushe gaba-d’aya ta ƙi bata space ɗin ma da zata yi tunani, idanunta kamas ko k’walla babu a cikinsu, kukan ma ya ƙi zuwar mata balle ta ji sauqin yaƙin wutar da ake a cikin zuciyarta…….

Tunda bayan fitar Daddy su Mama suke ta amsa kiran wayar mutane, ƴan’uwa da abokan arzik’i ana ta tambayar ko an ga Neehal. Mak’ota da wasu mutanen suna ta zuwa jaje. Ƙarfe sha ɗaya da mintuna Hajiya ta ƙaraso gidan, ta zube a falon ƙasa inda su Mama suke da Abba yayan Daddy wanda bai jima da zuwa gidan ba shi ma. Salati kawai Hajiya take yi tana hawaye. Mama tay mata sannu da zuwa cikin muryarta dake fita da ƙyar saboda tsananin damuwa. Su Aunty ma suka gaishe ta tare da bata baki akan ta yi haquri. Hajiya ta ce. “Wanne irin haquri zan yi? Ku daina bani wani haquri ni, ku bar ni in yi kukana, wannan wanne irin bala’i ne yake bibiyar yarinyar nan? Dan na tabbatar sace ta aka yi.” Mama ta jinjina kai tare da sauke numfashi. Dan itama zuwa yanzu ta fi zargin sace Neehal ɗin akay. Gashi Daddy shiru tunda ya fita bai dawo ba, ana ta trying Numbers ɗinsa basa tafiya.

Gajiya Neehal ta yi da bubbuga kan nata ta zauna dab’as tana sauke numfashi, sai ta ji kamar wani abu yana tokarinta a cinya. Ta kai hannu ta taɓa gurin sai ta ji abu a cikin aljihun rigarta. Cikin sauri ta dage hijabin jikinta ta zira hannu ta zaro ƙaramar wayarta da tashin hankali ya mantar da ita tana jikinta. Hannunta har rawa yake wajen kunna wayar, sai kuma ta kama waige_waige kamar mai tsoron kar wani ya gan ta. Numbern Mama ta lalubo da ƙyar saboda ko gani bata yi sosai ta yi dialing, amma sai kiran ya ƙi tafiya, tay ta trying kusan sau 20 amma ya ƙi tafiya, wayar ma gaba-d’aya emergency ta koma, sim ɗin ya ɗauke alamun babu network. Cillar wayar ta yi gefenta cikin takaici, ta zauna sosai ta jingina kanta dake barazanar fashewa saboda ciwo a jikin ƙofar ɗakin, bata san kuma mai zai faru da ita next ba, ko zasu biyo ta har nan ɗin ne su cimma buƙatarsu a kanta? Ko kuma wani sabon shirin muguntar suke kuma yi a kanta? Duk wannan ba shine abun da ya fi damunta ba a yanzu, damuwarta me ya kawo mutumin data gani a ɗakin da aka kaita? Ko fitar da ita ya zo yi daga gidan? Amma me yasa da ya gan ta ya ƙi magana? Ya ƙi ce mata komai? Me yasa data fito bai biyo ta ya kama hannunta sun fice daga gidan nan ba? Me yasa? A fili ta ce. “Dan Allah ka zo ka ce mun zuwa ka yi ka cece ni ba wai da kai ake ƙoƙarin cutar da ni ba, idan har hakan ta kasance ƙwaƙwalwarta baza ta ɗauki wannan al’amarin ba, zuciyata bugawa zata yi in mutu……!”

Tun daren jiya da Ameen ya bar gidan Mama ya koma gidansa ya kulle kansa a ɗakinsa dan a halin da yake ciki ba ya buƙatar takurar Hafsat. Wata ƴar ƙaramar laptop ya ɗauko ya shiga operating, ga dukkan alamu aikin da yake yi mai matuƙar mahimmanci ne duba da yanda ya bayar da hankalinsa duka a kan aikin, yana yi yana kiran Numbobin Neehal tare da addu’ar Allah yasa su shiga, ya ɗaukarwa kansa alƙawarin duk inda Neehal take sai ya nemo ta ko da zai rasa ransa a gurin yin hakan, saboda dalilai guda biyu. Na farko saboda Mahaifiyarsa, ba zai iya jurar ganin Mama cikin wannan tashin hankalin da take ciki ba, wanda bai taɓa ganin ta a cikin irinsa ba tsawon rayuwarsa, dan haka dole sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Na biyu kuma yana son sanin gaskiya akan wani al’amari da yake zargi, al’amarin da idan abun da yake zargi ya tabbata to tabbas da akwai babbar matsala, matsalar da zata girgiza rayukan mutane da yawa. Har asuba yana operating system, sai da aka kira sallah sannan ya tashi duk ya haɗa zufa duk da A.C dake ɗakin, sai da ya watsa ruwa sannan ya ɗaura alwala ya fito ya tafi masallaci. Hafsah ta cika ta yi fam akan shiga ɗaki da Ameen ya yi ya kulle, kishi ya cika ta dan ko tantama bata yi saboda ɓatan Neehal ya aikata hakan. Kwana ta yi tana jan tsaki da ƙwafa tare da addu’ar Allah yasa kar a ga Neehal ɗin shegiyar yarinya, ko kuma in an gan ta a gan ta a mace kowama ya huta. Dan tun gabatowar bikinta da Sadik ta rasa gane kan Ameen, har yanzu kuma bai dawo dai-dai ba, kullum cikin damuwa da shegen bincike_bincike yake, wanda ta san duk akan al’amarin Neehal ɗin ne. Bayan ya dawo daga Masallacin ɗakin Hafsat ya zarce, ya tarar da ita kwance lullub’e da bargo babu alamun ta tashi ta yi Sallah. Ya shiga tashin ta a hankali. Ta buɗe ido da yake baccin nata ba wani nisa yay ba, sai da aka shiga sallah ya ɗauke ta. Ta riƙe hannunsa idanunta ƙur a kansa, cikin kissa ta ce. “Baby.” Tana tashi zaune. Bai amsa mata ba sai zare hannunsa da ya yi daga cikin nata yana haɗe rai, ta kuma san dalilin hakan saboda bata tashi ta yi Sallah akan lokaci ba ne. Sai ta ƙara riƙe hannunsa cikin damuwa ta ce. “Baby a kwana ɗaya har ka faɗa, nima jiya kwata_kwata ban samu bacci ba, saboda damuwar ɓatan sister, sai yanzu gab da Asuba na ji ya ɗauke ni, dan Allah ka kira Mum ka tambaye ta ko an ga Neehal ɗin, ko kuma an samu labarin inda ta je, hankalina gaba-d’aya a tashe yake.” Ya saka ɗayan hannunsa ya shafi gashin kanta cikin sanyin murya ya ce. “Go and pray First.” Ta gyaɗa masa kai cikin nuna tsantsar damuwa. Ta sakar masa hannunsa ta sauka daga kan gadon ta shiga toilet zuciyarta fal da murna, dan yanda ta ga yanayin Ameen ta san babu wani daddaɗan labari, ta k’udurce a ranta tana idar da Sallah zata kira Mama dan jin ƙarin bayani, a zuwan da damuwar abun ta kwana kamar yadda ta nunawa Ameen. Shi kuwa da ya koma ɗakinsa ɗorawa ya yi daga inda ya tsaya a aikin da yake yi, babu alamun yana da niyyar fita yau…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button