NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Neehal tana nan zaune a bakin ƙofa ta ji ana taɓa handle ɗin ƙofar ta waje. Ta zabura ta miƙe tsaye ta manne a jikin bango jikinta na ƙyama, jin an turo ƙofar ɗakin ta runtse idanta a tunaninta sun biyo ta nan ne domin su far mata. Jin shiru har na wasu sakanni bayan turo ƙofar yasa ta buɗe ido, farin saurayin nan da ya kawo mata abinci d’azu ta gani yana kallon ta. Ya tako a hankali zuwa gaban ta ya kama hannunta ya ce. “Ki nutsu ƴan’mata, zan fitar dake daga gidan nan yanzu amma sai kin nutsu kin kuma yi komai cikin lura. Da sauri Neehal ta gyaɗa masa kai alamun gamsuwa. Ya ce. “Ki zauna anan, yanzu zan je na lalata wutar gidan haske ya ɗauke, kafin su gyara Insha Allahu zan fitar da ke. Cikin marainiyar murya Neehal ta ce. “Na gode, na gode sosai bawan Allah.” Ya jinjina mata kai sai kuma ya juya da niyyar fita idanunsa suka sauka akan wayarta dake tsakar ɗakin, ya waro Ido cikin alamun mamaki. Da sauri Neehal ta zo ta tattare wayar data tarwatse ganin yanda yake kallon ta, ta haɗa ta ta kunna ta. Bai ce komai ba ya juya ya fita. Neehal ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ƙara dialing Numbern Mama, amma still bata tafiya network is not available ake rubuta mata. Kamar ta yar da wayar sai kuma ta zira ta a cikin aljihun rigarta. Ta koma ta rakub’e a kusurwar ɗakin tare da rafka tagumi da hannu biyu. Bayan mintuna biyar ta ga hasken ɗakin ya ɗauke sai duhu dumɗum, ta ƙara mannewa a cikin bango jikinta na ƙyarma. Ko minti biyu ba’ai ba ta ji an turo ƙofar ɗakin an shigo, muryar saurayin ta ji yana faɗin. “Taso da sauri ba mu da ishashshen time.” Neehal ta tashi cikin sauri kamar yadda ya ce ta yi inda ta ji sautin muryarsa saboda bata ganin sa, sai da ta matso kusa da shi ne ma ta ga alamar duhun mutum a tsaye, ya kamo hannunta cikin raɗa ya ce. “Duk inda nasa ƙafata ki saka taki, amma sai kin yi sauri fa dan yanzu zasu gyara wutar, kuma gidan nan gaba-d’aya a zagaye yake da CCTV camera, duk inda muka gilma akwai masu kallon mu.” Neehal ta gyaɗa masa kai. Ya buɗe ƙofar suka fita yana jan ta, dan gudun ma gagarar ta ya yi ta kasa yin sa, sai faɗuwa take musamman idan suka zo gurin shan kwana, amma kuma sai ta miƙe zumbur saboda tamkar gudun ceton rai take. Suna fitowa daga corridor ɗin gidan wutar gidan ta dawo, saurayin ya waro ido waje cikin alamun tsoro, dan ya san kafin sukai bakin gate waɗanda suka gyara wutar sai sun gan su, ya tsaya ya fara tunanin mafita. Neehal ta shiga kalle_kalle a makeken harabar gidan. Bai gama tunanin ba ya ji alamun tafiya, ya yi saurin jan hannun Neehal suka zagaya baya, suna zuwa bayan ya hangi mutum uku suna tahowa, ya yi saurin yin ƙasa tare da jan Neehal suka b’uya a bayan wani gini. Ta daf da ginin mutanen ukun nan suka zo suka wuce, ɗaya daga cikinsu har da juyowa, ai kaɗan ya rage Neehal bata saki fitsari ba. A tare suka saki ajiyar zuciya bayan mutanen sun ɓace wa ganin su. Saurayin ya miƙe hannunsa cikin na Neehal ya ce. “Gudu zaki yi sosai mu samu ki fita daga gidan nan, dan na san zuwa yanzu sun fara nemanki, mintuna kaɗan kuma ya rage ragowar ƴan ƙungiya da sarauniya su ƙaraso gidan nan dan bikin murna.” Neehal da zuwa yanzu ta fara sarewa ta gyaɗa masa kai numfashinta na fita da ƙyar. Ya ja hannunta suka falfala da gudu yana yi yana waiwaye, cikin ikon Allah har suka ƙarasa gate ɗin gidan babu wanda ya gan su. Sai dai gate ɗin a kulle yake da gark’amemen ƙwado. Saurayin ya dafe kansa cikin takaici dan gaba-d’aya ya manta da akwai sauran rina akaba, wato ta yanda zasu fice daga gidan. Kallon ɗakin mai gadi ya yi sannan ya juyo ya kalli Neehal wadda ke ƙoƙarin sumewa. Ya ja ta dan tafiya ma neman gagarar ta take, a bakin ƙofar ɗakin mai gadi suka tsaya, ya zaunar da ita shi kuma ya tura ƙofar ya shiga. Mai gadin yana zaune kishingid’e, jin an shigo ya tashi zaune sosai. Saurayin ya ƙaƙaro murmushi ya ce. “Malam Buba ana hutawa ne?” Malam Buba ya washe baki ya ce. “A’aa, Malam sagiru kai ne, sannu da zuwa farin mutum ganin ka Alkhairi ne.” Sagir ya ce. “Yau an gama abinci da wuri, kuma baka zo ka kawo kwano ba.” Buba ya ce. “Ai na ga lokaci bai yi ba ne shi yasa.” Sagir ya ce. “Ka san yau muna da shgali fa shi yasa aka gama da wuri, yanzu dai ɗauko kwanan naka kar wanda ya fi maik’on ya ƙare.” Buba ya ƙyalƙyale da dariya ya tashi ya ɗauko flaks ɗin da ake zuba masa abinci ya miƙawa Sagir, Sagir ya karɓa ya buɗe ya ce “Dan daurayo shi dai a bayan gida Malam Buba, na ga da ɗan maik’o a cikinsa.” Buba ya ce. “Toh Sagiru daɗina da kai akwai tsafta.” Sagir ya yi murmushi kawai yana wurwurga idanunsa a ɗakin yana neman inda zai ga makullan gidan. Cikin sa’a ya ga malam Buba ya ajiye su akan wani ɗan table ya shige toilet. Jikinsa har rawa yake ya ɗauka tare da juyawa ya fice daga ɗakin da mugun gudu, inda ya bar Neehal anan ya tarar da ita. Ya kama hannunta suka nufi get ɗin da gudu, ya lalubo key ɗin ƙofar ya shiga bubbud’e makullan gidan kusan guda goma, yana yi yana waiwaye. Yana gama buɗewa ya hango Buba ya fito daga ɗakinsa a gigice, ya kama ƙaramar ƙofar gate ɗin ya buɗe ya tura Neehal waje sannan shi ma ya fita, ya damk’i hannunta suka falfala suka yi gabas da mugun gudu. Tafiya sosai suka yi sannan Neehal ta faɗi tana numfarfashi, cikin magana da ƙyar ta ce. “Ruwa, ruwa.” Sagir ya ce. “Ki yi haquri ban san inda zan samu ruwa in baki ba, kuma dole anan zan barki in koma gidan da muka fito in karɓi hukunci na.” Neehal ta ƙura masa ido ta ce. “Me yasa ka san za’a hukunta ka, ka taimake ni? Me yasa zaka koma gidan da da mutanen cikinsa babu Allah a ransu? Ka zo mu gudu tare mana.” Sadik ya girgiza mata kai ya ce. “Duk inda na shiga a faɗin duniyar nan sai sun nemo ni, idan ban koma ba a yanzu za su tsotse jinin mahaifiyata wadda ita kaɗai ta rage mun a duniya, ni kuma da haka ta faru gwara ni su kashe ni.” A ruɗe Neehal ta ce. “Tsotse jini kuma? Suna shan jini ne?” Sagir ya gyaɗa mata kai ya ce. “Eh suna shan jini, matsafa ne, kuma nima ina cikin su.” Neehal ta waro Ido ta ce. “Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, me ya kaika cikinsu? kuma gashi ba kai kala da marasa imani ba.” Sagir ya ce. “Baza ki gane ba ƴan’mata, amma abun da zan faɗa miki rashin imanin yan ƙungiyar nan ya wuce duk inda kike tunani, ni zan koma kafin azzaluman ƙungiyar da sarauniya su ƙaraso.” Neehal ta ce. “Me yasa ka taimake ni?” Ya ɗan yi shiru sannan ya ce. “Saboda Yayanki Al’ameen, ya taɓa mun wani taimako da bazan taɓa mantawa da shi ba a rayuwata, kalamanki na d’azu a lokacin da na kawo miki abinci su suka tunzura ni akan na taimake ki, domin na san kamar yadda kika faɗa da ƙanwata ce na ga ana ƙoƙarin keta mata haddi sai inda ƙarfina ya ƙare a ceton ta duk da bani da ƙanwar ban san daɗinta ba ni kaɗai iyayena suka haifa. Dan haka na yi amfani da wannan damar gurin sakawa Ameen da Alkhairin da yay mun na taimake ki, domin na san da zarar sauran ƴan ƙungiya sun zo babu abun da zai hana su aiwatar da ƙudirinsu a kanki sai dai wani ikon Allah. Ni ne na bar ƙofar ɗakin da kika shiga a buɗe saboda na san idan kin samu kin kub’uta nan zaki fara tunkara dan neman tsira.” Ta ce. “Ta ya ya ka san ni ƙanwar Ameen ce?” Sagir ya yi murmushi ya ce. “Na sani kawai.” Neehal ta ce. “Ya sunan ka?” Ya ce. “Sagir.” Ta ce. “Na gode sosai Yaya Sagir da taimakon da ka mun, amma ina tsoron kar su kashe ka saboda ka fito da ni.” Sagir ya ce. “Karki damu baza su taɓa kashe ni ba.” Neehal ta sauke ajiyar zuciya numfashinta na fita da sauri_sauri. Sagir ya miƙe da niyyar tafiya Neehal ta tsayar da shi da faɗin. “One more question.” Ya tsaya yana kallon ta bai ce komai ba. Ta ce “Wanda waɗannan mutanen suka kaini ɗakinsa shine wanda yake ƙoƙarin keta mun haddi? Shine wanda aka ce mun my virginity is for him? Shi ma ɗan ƙungiyar ne? Yana shan jini?” Sagir ya ce. “Kin ci sunanki ƴar jarida, Tamboyoyinki kuma amsar su gaba-d’aya Eh ce.” A razane Neehal ta ce. “Real him ɗin shi fa, not fake face maks ɗin daya saka, kasan kuwa matsayin shi a gurina?” Sagir na ce. “Na sani kuma shi ne.” Neehal ta dafe ƙirjinta da sauri saboda wata irin bugawa da zuciyarta ta yi a million. Hakan ya yi dai_dai da jin vibration ɗin wayarta da ta yi. Sagir ya juya ya tafi cikin sauri. Ta zaro wayar daga cikin aljihun rigarta da ƙyar saboda yanda kanta yake juya mata, ta danna gurin picking ba tare data duba mai kiran ba. Ameen wanda tun safe ya ɗora da kiran Numbobin Neehal sai yanzu cikin sa’a ya ji ɗaya ta shiga. A hanzarce ya ce. “Miemerh.” Cikin magana da ƙyar ta ce. “Yaya…!” Ya ce. “Where are you?” Ta ce. “I dont know, please Yaya ka zo ka ɗauke ni.” Ameen ya sauke doguwar ajiyar zuciya ya ce. “Okay I will come now Insha Allah, ki bar wayar a kunne.” Bai jira amsar ta ba ya katse kiran. Ya miƙe da sauri ya ɗauko wata laptop ɗinsa ya kunna ta ya shiga latsawa yana kwafar Numbern da suka yi waya da Neehal yanzu yana sakawa a ciki, sannan ya ɗauko wani abu mai kama da waya ya yi connecting ɗinsa da system ɗin, ya soka wani abu a jikin socket ya shiga lallatsa su a tare, in ya taɓa wannan sai ya taɓa wancan, a gaggauce yake yin komai. After 5 minutes ya sauke doguwar ajiyar zuciya a fili ya ce. “Alhamdulillah.” Sannan ya ɗauko wani abu a cikin takarcensa mai kamar agogon hannu ya ɗaura a damtsen hannunsa. Ya kwashi wayoyinsa ya dau key ɗin Mota ya fice daga gidan ko Hafsat bai yiwa Sallama ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button