NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Gudu yake shararawa sosai akan titi, cikin 1 hour ya ƙarasa inda Neehal take da taimakon abun da ke ɗaure a hannunsa wanda shi yake masa pointing hanyoyin da zai bi zuwa inda Neehal take. Ya yi parking a gabanta inda wayarta take yashe a ƙasa wanda da sim ɗin ciki ya iya gano inda take. Ya fito cikin sauri yana kiran sunanta. Ta buɗe ido da ƙyar ta ƙura masa ido amma ko hannunta ta kasa d’agawa, ta kai maƙura a galabaita. Dan ma lokacin ƙarshen damuna ne ba’a rana mai zafi sosai, amma rashin cin abinci da ƙishirwa su suka taimaka gurin galabaitar ta_ta over. Ameen ya tsugunna a gabanta tare da riƙe hannunta, yana sakin ajiyar zuciyar farinciki ya ce. “Miemerh wa ya kawo ki nan?” Ta girgiza masa kai tana son ta yi magana amma ta kasa. Da ƙyar ta iya cewa “Ya..ya..!” Ya ce “Na’am, I’m here with you.” Ta yi luuu da idanunta ta lumshe su, daga gan bata ƙara sanin inda kanta yake ba ta sume. Ameen ya ciccib’e ta fahimtar da ya yi ta suma ya kai ta cikin Mota ya kwantar da ita a bayan Motar. Shi kuma ya shiga gaba ya ja motar a guje suka bar gurin bayan ya dauko mata wayarta dake yashe a ƙasa. Ya so ya yi binciken abun da yake neman sanin gaskiyar sa, amma halin da Neehal take ciki yasa ba zai iya tsayawa ba, ya ji jikinta da zafi sosai alamun akwai zazzaɓi a jikinta. 50 minutes ce ta kai su gidan Mama, a ƙofar part ɗin Mama ya yi parking ya fito ya ɗauko ta, har lokacin tana nan kamar yadda ya ɗauko ta. Babu kowa a falon ƙasa sai su Dije dake kitchen suna girki, su Mama tunda suka hau sama yin Sallah ba su sakkowa ba. A kan carpet ɗin Parlour’n ya shimfid’e ta. Ya zauna a gurin kanta yana kallon kumburarriyar fuskarta da ta ci kuka ta k’oshi, ta yi jajawur kamar ka latsa jini ya fito. Zulai ce ta fito daga kitchen ta ci karo da su, ta zaro ido waje cikin tsananin kaɗuwa, da gudu ta yi hanyar steps ta hau upstairs ta sanar da su Mama dake zaune jigum_jigum a Parlour’n sama Ameen ya dawo da Neehal. A tare suka taho cikin sauri dan tabbatarwa. Mama ta ƙaraso da gudu ta rungume Neehal a jikinta tare da sakin kuka ta ce. “Alhamdulillah, Allah na gode maka daka dawo mun da d’iyata.” Su Aunty A’isha kuwa har rige_rigen tambayar Ameen inda ya gan ta suke. Shi dai bai ce komai ba, dan abun da yake damun sa ya fi ƙarfin sa. Yana kallon su suka gama murnar bayyanar Neehal da godiya ga Allah, sai ya ji daɗi ko ba komai ya saka Mama da ahalinta farinciki. Hajiya sai shafa kan Neehal da har lokacin bata farfaɗo ba take. Mama ta dubi Ameen ta ce. “A ina ka gan ta?” Ya lumshe idonsa ya buɗe ya ce. “Ban san sunan gurin ba, amma is looks like Bush ko kuma sabuwar unguwa, amma dai wajen gari ne ba cikin mutane ba, na yi amfani da sim ɗin da mu kai waya da ita ne na yi tracked.” Aunty Sadiya ta ce. “Ita ta kira ka?” Ya ce. “No.” Sannan ya ba su labarin wayar da suka yi da Neehal da yadda ya ɗauko ta. Hajiya ta ce. “Allah ya yi da rabon shan ruwanta a gaba, dan wataƙila ƴan yankan kai ne suka sace ta Addu’a ta ci su suka yarda da ita.” Aunty A’isha ta ce. “Ko ma su waye Allah ya toni asirinsu.” Mama ta ce. “Amin.” sannan ta dubi Ameen ta ce. “Kira Dad ka faɗa masa, bawan Allah nan ko ruwa bai sa a cikinsa ba ya fita.” Ameen ya zaro wayarsa ya yi dialing Numbern Daddy amma bata shiga ba. “Mama ta ce. “Lafiya kuwa yake, kar ya je ya sawa kansa wata matsalar fa saboda damuwa, tun d’azu nake kiran shi nima amma bata shiga.” Aunty Sadiya ta ce. “Ina ya ce miki zai je?” Mama ta ce. “Hospital’s ya duba wai ko Neehal accident ta yi an kai ta can.” Aunty Sadiya ta jinjina kai kawai. Ameen ya miƙe ya ce zai je ya yi Sallah, Mama ta ce Ya sanar da Abba an ga Neehal yana masallaci tunda ya tafi Sallah bai dawo ba. Sai a lokacin su Mama suka fara damuwa da halin da Neehal take ciki, murna fa ta koma ciki. Mama duk ta ruɗe ta shiga jijjiga ta. Aunty Sadiya ta ɗebo ruwa mai sanyi a fridge ta cire hijabin jikin Neehal ta shiga shafa mata ruwan a fuska zuwa wuyanta. Cikin ikon Allah ta sauke dogon numfashi tare da buɗe idonta, suka haɗa ido da Mama. Mama shafa fuskarta ta ce. “Sannu Daughter.” Neehal bata iya amsa mata ba sai mayar da idon ta yi ta rufe. Gaba-ɗaya suka sauke ajiyar zuciya. Ta yi luf a jikin Mama cikin sakanni baccin wahala ya ɗauke ta. Dije ta ɗauko filo Mama ta kwantar da kanta akai. Nan fa suka shiga kiraye_kirayen mutane suna sanar musu an ga Neehal. Haneefah mai kuka hankali ya kwanta, dan ita Mama ta fara kira ta sanarwa saboda halin damuwar da ta shiga. Duk bayan mintuna sai Neehal ta zabura a cikin bacci tana faɗin, “Me nay muku kuke son cutar da ni? Karku ɓata mun rayuwa dan Allah, ni marainiya ce.” “Mama! Mama! ki zo ki ceci ni karki bari su keta mun haddi za su ɓata mun rayuwa.” Ko kuma ta ce. “Harda kai ake ƙoƙarin cutar da ni? Me yasa kake cikin azzaluman nan?” Kalaman da take yi kenan wanda ya tayar da hankalin su Mama matuƙa.” Aunty A’isha ta ɗora kanta akan cinyarta ta shiga tofa mata addu’a, Aunty Sadiya kuma towel ta sakawa a ruwa tana matsa mata a jikinta saboda yanda jikin nata ya yi zafi zau.” Mama kuka take tana faɗin “Na shiga uku, fyaɗe aka so yi mata kenan, they want to rape my daughter? Su waye waɗannan azzaluman? Ku duba mun yarinya kar na je sun cutar mun da ita.” Aunty Sadiya ta ce. “Insha Allahu babu abun da su kay mata.” Hajiya ta ce. “To waye take cewa harda kai a ciki? Kenan ta ga idon sani a cikin waɗanda suke ƙoƙarin yi mata fyaɗen?” Aunty A’isha ta ce. “Nima abun da na fahimta kenan, mu jira ta tashi sai mu ji ƙarin bayani daga bakinta.”

Sai bayan La’asar Neehal ta farka, ta buɗe idonta ta sauke su akan Aunty A’isha dake zaune a kusa da kanta. Aunty A’isha ta kama hannunta ta ce. “Sannu Neehal!” Ta gyaɗa mata kai a hankali tare da ƙoƙarin tashi. Aunty A’isha ta taimaka mata ta tashi zaune. A hankali ta ce. “Aunty zan sha ruwa.” Aunty A’isha ta miƙo mata ruwan da aka tanada already saboda ita, ta karɓa ta sha sosai sannan ta shiga sauke ajiyar zuciya. Mama ta ce. “Daughter kin tashi? Sannu, ina ne yake miki ciwo a jikinki yanzu?” Ta nuna mata kanta da ƙirjinta. Mama ta ce. “Sannu kin ji, Allah ya sauwaqe.” Cikin dashashshiyar murya ta ce. “Amin, zan yi wanka Mama.” Mama ta taso ta kamata ta miƙe tsaye dak’yar tana yatsina fuska gami da taune lips ɗinta. A hankali suke tafiya Mama na riƙe da ita har suka hau upstairs. Bedroom ɗinta Mama ta kai ta rage kayan jikinta ta shiga toilet ta yi wanka ta fito, sai ta ji jikin nata ya yi mata daɗi. Ta zira doguwar riga mara nauyi ta saka hijabi ta yi Sallar Azhar da la’asar dake kanta. Kafin ta idar su Mama sun shigo ɗakin dukan su. Tana idarwa suka shiga yi mata sannu. Mama ta dawo kusa da ita ta janyo ta jikinta, Neehal ta saki ajiyar zuciya a hankali ta ce. “Mama ina Yaya da Daddy?” Mama ta shafa fuskarta ta ce. “Ameen tunda ya kawo ki bai dawo ba, Har Hafsat ma ta zo ta tafi, ta ce ba ya jin daɗi ne, Dad kuma tun d’azu wayarsa bata shiga, sai yanzu ba jimawa ya kira ni ya ce yana hanyar zuwa gida.” Neehal ta gyaɗa kanta kawai bata ce komai ba. Mama ta cigaba da magana. “Sadik ya zo shi da Abbansa d’azu, Ahmad ma ya kira ni wai zai taho yanzu na ce masa ai an gan ki ma, amma ya ce cikin week ɗin nan Insha Allahu zai zo.” Hajiya dake jan carbi ta ce. “Ai mutane suna ta zuwa ko ta ina jaje da taya mu murna, sai abun kuka ya sameka kake gane mai k’aunarka.” Aunty Sadiya ta ce. “Haka ne kam.” Aunty A’isha ta kawo wa Neehal tea ɗin data haɗa mata a cup ta ce. “Ta so ki sha.” Neehal ta girgiza mata kai alamun baza ta sha ba. Mama ta ce. “Ki daure ki sha ko kaɗan ne, na san babu abun da kika ci tun jiya.” Kamar zata yi kuka ta ce. “Ƙirjina ciwo yake mun, ba zan iya sha ba.” Cikin damuwa Mama ta ce. “Tsoro nake Neehal kar su saka miki ciwon zuciya da wannan tashin hankalin da suke jefe ci a jiki.” Aunty A’isha ta ce. “Insha Allahu haka baza ta faru ba, ta daure dai ta sha tea ɗin zata ji daɗi.” Neehal ta bar jikin Mama ta ɗauki cup ɗin ta kafa a baki ta runtse ido ta k’ukk’uta tana jin sa kamar ruwan mad’aci, da ƙyar take iya had’iyewa, bata son tay musu musu ne kawai. Ta ajiye cup ɗin tana jin kamar zata yi amai saboda yanda tea ɗin yake mata juyi a cikinta. Cikin ikon Allah kuma sai ya zauna bata yi aman nasa ba. Aunty Sadiya ta ce. “Neehal ki faɗa mana yanda aka yi aka sace ki da kuma abun da ya faru. Neehal ta runtse ido kamar bata son tuno wani abu ta fara ba su labari turyan_turyan tun daga farko har ƙarshe. Salati suka saka gaba-d’ayan su cikin d’imuwa da al’ajabin wannan al’amari. Mama tana hawaye ta ce. “Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, wacce irin ƙungiya ce wannan kuma? A ina suke a ina suka san ki?” Hajiya ta ce. “Ai wannan daga ji matsafa ne masu shan jinin mutane.” Aunty A’isha tana kuka ta ce. “Wai me mutane suka ɗauki wannan duniyar nan ne? Me yasa suke manta cewar za su mutu su koma ga mahaliccin su? Rayuwar duniya fa tamkar kifta ido ne ka buɗe zaka neme ka ka rasa a cikinta? Me yasa muke manta kwanciyar kabari da azabar Ubangiji?” Aunty Sadiya ta ce. “Ke da Allah ya nufa da rahama ya baki imanin tunanin abun da kika faɗa, su kam waɗannan mutanen sam babu haka a ransu, duniyar kawai suke nema suna ganin kamar ba za su mutu ba.” Hajiya ta ce. “Hasbunallahu’wani’imal’wakil, Astagfirullah wa’atubu ilaihi, Allah ka kashe mu cikin imani da kai, wannan wacce irin rayuwa muke ciki? da mutane suke neman duniya su manta da k’iyama.” Mama ta ce. “Yanzu duk wannan abubuwan da suke faruwa da Neehal saboda wannan banzan ƙudirin nasu ne, Allah ya fi su kuma shi zai mana maganinsu.” Ita dai Neehal hawaye kawai take, domin ita kaɗai ta san me yake damunta.” Aunty Sadiya ta dafa ƙafaɗarta ta ce. “Neehal! Wa kika gani a cikin waɗanda suke son cutar da ke wanda kika sani?” A tsorace Neehal ta kalle ta, Aunty Sadiya ta gyaɗa mata kai alamun tabbatarwa. Ta girgiza kai cikin tsoro ta ce. “Ban san kowa ba a cikin su, ban taɓa ganin su ba dukan su sai yau.” Aunty Sadiya ta ce. “Nutsu Neehal ki faɗa mana, kina da sama da wanda ya fi mu ne a duniyar nan? Muna son mu kawo ƙarshen matsalar ki ne.” Neehal ta saci kallon Mama ta ce. “Da gaske ban san kowa ba.” Aunty A’isha ta kama hannunta ta ce. “Haba Neehal, dama akwai abun da zaki ɓoye mana a cikin duniyar nan, d’azu kina bacci kina zabura kina cewa harda kai a cikin wanda za’a cutar da ni, ki faɗa mana wanene?” Neehal ta saka kuka ta ce. “Babu kowa fa.” Hajiya ta ce. “Ka ji yarinya da iskancin banza, rayuwarki fa ake son taimakawa.” Aunty Sadiya ta ce. “Say it Neehal, ina son tabbatar da zargi na ne.” Mama da gabanta ke dukan tara_tara cikin sanyin murya ta ce. “Please Neehal ki faɗa mana, ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru, ko da wata bazaranar su kay miki sai abun da Ubangiji ya rubuta sannan zai faru da ke.” Neehal ta ƙurawa Mama ido a ranta tana cewa. ‘Ba zan iya faɗa muku wanda na gani a matsayin wanda zai keta mun haddi ba saboda ke Mama, karamcinki da halaccinki a gare ni ba zai bar ni in faɗi abun da zai saka zuciyarki ta buga ba Mama, ba zan iya ba, ba zan iya faɗar wannan mummunan baƙin labarin ba. Na yiwa kaina alƙawarin wannan maganar da ita zan mutu a cikin cikina, ba zan iya faɗawa kowa ba.’ Mama ta riƙe hab’ar Neehal ta saka idanunta a cikin nata na ce. “Idan har kin ɗauke ni uwa ki faɗa mana Neehal, gabana sai faɗuwa yake dan Allah ki faɗa.” ‘Matar data riƙe ni riqon gaskiya da amana ba tare da mun haɗa wata dangantaka ta jini da ita ba, ta nuna mun k’auna fiye ɗan data haifa a cikinta, take fifita farincikina akan nata, take shiga damuwa a duk lokacin da na shiga, ɗan da ta haifa a cikinta bai jefa ta cikin damuwa ba sai ni, ta yaya zata ce in mata abu in ƙi yi? Ta riga ta ɗaure ni da jijiyoyin jikina, amma ina fata abun da zan sanar musu ya zama maganata ta biyun ƙarshe a duniya, ya Allah kasa ina faɗa ka nufe ni da yin kalmar shahada, daga nan ka ɗauki raina, dan ba zan iya jurar ganin Mama cikin tashin hankali ba.’ Neehal ta faɗi haka a ranta. Aunty Sadiya ta bubbuga ƙafaɗarta ta ce. “Neehal please Talk, kin bar mu cikin zullumi da fargabar zuci.” Neehal ta runtse idanta da ƙarfi cikin rawar murya kamar yadda zuciyarta da jikinta suke rawa ta ce. “Da..da… Daddy!……….✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button