NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
6️⃣9️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#
………Cikin matuƙar gigita Mama ta saki fuskar Neehal da ƙarfi ta kalli Aunty Sadiya tana so ta yi magana amma ta kasa. Gaba-ɗaya suka waro Ido waje kamar zai faɗo ƙasa amma aka rasa mai magana a cikinsu. Kuka mai tsananin taɓa zuciya Neehal ta fashe da shi, tana jin anya kuwa ta yiwa kanta adalci data faɗawa Mama wannan maganar? Sai ta ji dama ta ƙi faɗa, ta san dole za su haqura su ƙyale ta da tambayar, amma ta riga ta furta bakin alqalami ya bushe. Aunty A’isha ta runtse idanta tana karanto Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un a fili. Sannan ta samu yar nutsuwa ta dubi Neehal ta ce. “Neehal! Wanne Daddy’n kike nufi?” Mama ta shiga girgiza kai ta ce. “Sadiya da gaske Neehal sunan Daddy ta ambata ba kunnena bai ji mun dai-dai ba?” Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. “Shi ta ce.” Mama ta dafa gado da hannunta ɗaya tana ambato duk addu’ar da ta zo bakinta jin kanta na wani irin juyawa. Sai a lokacin Hajiya data ƙame baki buɗe ta iya magana, ta dubi Neehal ta ce. “Ƙarya ne, wannan abun sharri ne ba Muhammadu kika gani ba, wani ne ya yi kama da shi saboda yana son ya k’ulla masa sharri, na san Muhammadu ba zai taɓa aikata hakan ba.” Aunty Sadiya ta miƙe tsaye ta ce. “Ba ƙarya ba ne, ba kuma wani ne ya yi kama da shi ba, shine da kansa, kuma na daɗe da gano hakan.” Aunty A’isha ta ce. “Subhallahi, Sadiya kin san wa ake magana akai kuwa? Gen. Fa, mijin Yaya Fateemah mahaifin Ameen.” Aunty Sadiya ta ce. “Shi ɗin fa.” Mama tana numfashi da ƙyar ta ce. “Sadiya, kina nufin Muhammad Tafida dama shine wanda kike zargi akan al’amuran Neehal?” Aunty Sadiya ta dafe kanta na wasu sakanni sannan ta tsugunna ta ɗora hannunta akan ƙafaɗar Mama wadda jikinta yake rawa ta ce. “Na yi mamaki a yadda na san ki mutum ce ke mai saurin fahimtar abu amma kika kasa gane wasu sauye_sauye a tattare da Yaya Tafida. Abu na farko da yasa na fara dasa zargina a kansa shine, a yanda yake sanannen mutum mai kuɗi wanda ya san manyan ƙasar nan da yan siyasa amma ace ana aikatawa Neehal wannan abubuwan ya kasa binciko masu aikata hakan a matsayin sa na babban soja. Talaka mara gata shi yake shan wahala a shari’a a ƙasar nan, amma ban da irin su Yaya Tafida, a yanda yake tun lokacin da akay kisan Jameel a rana ɗaya idan ya so sai yasa an gano masa waɗanda suka yi kisan, amma bai yi hakan ba. Kuma tunda aka fara abun nan ban taɓa jin ya ce yau yana yin wani bincike akan abun ba ko kuma yasa a yi masa. Secondary kuma, idan ban manta ba Yaya Tafida ya yi shekara bakwai da yin retired, Amma kullum sai ya fita tun safe sai dare yake dawowa. Ina yake zuwa? Kin taɓa tambayar sa akan haka? Idan baki manta ba farko dana fara zargin sa na taɓa tambayar ki cikin hikima ina yake zuwa yanzu shi da ya yi retired? Kika ce mun gurin kasuwancinsa yake zuwa dubawa sai kuma Mall ɗinsa da yake lek’awa time to time. Kuma ɗan wannan abun ba zai saka mutum ya wuni a waje ba, tunda daga kasuwancin har Mall ɗin nasa akwai masu kula da su, babu abun da zai yi idan ya je, ko kina tunanin zai je ya zauna a cikin yaransa ne? Abu na uku kuma Yaushe rabon da ki ga wani abokinsa ya zo gidan nan alhalin kuma kafin ya shiga wannan ƙungiyar suna zuwa sosai? Duk da ba a gidan nan nake kwana ba amma na san wannan kuma na sa an bincika mun. Tun daga lokacin dana fara zargin sa na saka ido sosai akan duk wani motsinsa, amma da yake shi ma da shirinsa yake tafe na sha bak’ar wahala kafin na gano wasu abubuwan, su ma ba sukai cikakkiyar hujjar da zan iya cewa direct shi ba ne, shi yasa ban bayyana ba. Sannan sai labarin abun da ya faru da Neehal a gidan Ameen, shi ma ya ƙara tabbatar mun da zargi na. Na girgiza ba kaɗan ba a lokacin dana gane da saka hannu Yaya Tafida a duk abubuwan da suke faruwa da Neehal, domin ban taɓa zaton haka daga gare shi ba, Yaya Tafida mutumin kirki ne kowa ya san da haka, na yi mamaki matuƙa da yakasance dan cikin ƙungiyar matsafa duk da ban san ta yanda aka yi ya shiga ba amma na san tabbas ba’a san ran shi ba ne ƙaddarar sa ce ta zo a haka. Lokuta da dama ina kulle kaina a ɗaki in yi kukan takaici da baƙin cikin wannan al’amari, gami da tausayin ku ke da Ameen da Neehal da shi kan shi Yaya Tafidan, idan zaki lura har gidan nan na rage zuwa, saboda watarana kar na yi subutar baki na faɗa miki wannan mummunan labarin, ko kuma mu haɗu da Yaya Tafida in kasa jurewa in masa wata maganar da zai gane na san abun da yake. Dalilin da yasa kullum al’amarin Neehal yake ƙara tab’arb’arewa tare da ƙara yin gaba saboda wanda yake aikata abun da shi a ake zama a tattauna akan matsalar da kuma hanyoyin da za’a magance abun yana cikin mu, the way da zamu kawo mafita duk ya sani, shi kuma sai ya canza salo yanda zai ƙara kawar da tunanin mu daga kan abun. Shi yasa muka kasa samun mafita al’amarin ya ƙi ci ya ƙi ƙarewa, sai yanzu da ita kanta Neehal ɗin Allah ya nuna mata shi da idonta. Kuma muna fata Insha Allahu ƙarshen abun ne ya zo.”
Mama ta runtse ido ta buɗe numfashinta na kaiwa da komowa da sauri da sauri ta ce. “Tabbas biri ya yi kama da mutum Sadiya, sai yanzu da kikai waɗannan maganganun sannan wasu abubuwan suke dawo mun kwanyata. Ku san shekaru goma sha biyu kenan da nake lura Tafida kamar baya cikin nutsuwarsa, sai yay ta yin wasu irin abubuwa amma ban taɓa kawo komai a raina ba. Sannan kuma lokuta da dama ana kiransa a waya sai ya dinga ƙin d’agawa a gabana, ko kuma ya d’aga ya ce yana zuwa zai kira daga baya. Na raba shi da Kabir Ginyau saboda ba mutumin k’warai ba ne, amma na lura bai rabu da shi ba, duk da ya ce mun ba mu’amala suke yi kamar ta da ba, gaisawa kawai suke. Sannan kuma lokacin da aka sace Sadik tun a wurin d’aurin Aure Usman ya ce a ɗaurawa Neehal Aure da wani amma ya ce a’a, bayan iyayen Sadik sun ce ba zai auri Neehal ba na same shi a ɗaki ni da shi na ce masa zan aurawa Ameen Neehal mu huta da wannan tashin hankalin, amma ya dinga kawo mun wasu hujjoji da suka akan hakan har na haqura na bar al’amarin, ashe duk kansa yakewa tanadi, ashe da Mushirinki miji nake zaune, me yasa ka aikata haka Tafida? Why? Why? Ko ɗan ɗanka guda ɗaya tilo a duniya bai kamata ka aikata wannan mummunan laifin ba, bai kamata ka ɓata masa suna a Duniya ba. Ka cuce ni ka cuci Ameen, am sorry Ameen ban maka zaɓin Uba na gari ba.” Mama ta ƙarashe zancen cikin sark’ewar numfashi. Aunty Sadiya ta shiga bubbuga bayan ta a hankali tana maimaita mata sunan Allah. Kuka sosai Aunty A’isha da Hajiya suke yi, dan wannan abun ba ƙaramin girgiza zuciyoyinsu ya yi ba. Neehal ta kama hannun Mama tana kuka amma bata ce komai ba, so take tay mata magana amma ta kasa. Mama ta damk’e hannunta cikin dashashshiyar murya ta ce. “Ki yi haquri Neehal, duk wannan abun da ya faru nina jawo miki, da na barki a hannun A’isha ta riƙe ki da ƙila haka baza ta faru da ke ba.” Neehal ta girgiza mata kai tare da rungume ta ta ƙara fashewa da kuka.