NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Misalin ƙarfe goma da rabi na dare Mama ta na ɗakinta a zaune a kan darduma ta na lazimi, domin babu d’igon bacci ko kaɗan a idonta, bayan tafiyar su Aunty Sadiya gidajensu Dad ya koma part ɗinsa, ita kam Mama yau ko part d’in nasa ba za ta iya zuwa ba, saboda damuwar da take ciki, sosai Mama ta damu da wannan al’amari, domin ba ta k’aunar abin da zai taɓa Neehal ko kaɗan a rayuwar nan, balle abin da zai taɓa farin cikinta, amma tasan ba ta isa ta goge rubutacciyar ƙaddarar da Ubangiji ya zana wa Neehal ɗin ba, a rayuwarta. A hankali ta ji an buɗe ƙofar ɗakinta an shigo, a tunaninta Dad ne, amma jin k’amshin turaren Ameen ya sa ta d’ago kanta da sauri ta kalle shi, kansa a ƙasa ya yi sallama tare da nufo inda take, Mama ta ɗauke kanta daga Kallonsa tare da amsa masa sallamar da ya yi a zuciyarta. Kusa da ita ya zauna kansa na ƙasa still ya ce “Mum!” Mama ta ɗan kallesa ta watsar amma ba ta ce komai ba, ya ƙara faɗin “Ya haƙurinmu?” Mama ba ta amsa masa ba sai cewa ta yi “Me ya samu phones ɗinka?” Ba tare da ya yarda sun haɗa ido ba ya ce “Switch up d’insu na yi” Mama ta ce “Akan wanne dalili” ya ɗan yi shiru na wasu sakanni ita kuma Mama ta tsura masa ido. Cikin dakiyarsa ya ce “Aikin da ya kaini Lagos ne ba ƙarami ba ne, kuma ina so in gama shi a yau gobe kawai sai dai a rabawa masu yi, that is why na katse wayar kar a kira ni a tsayar da ni.” Mama ta yi shiru dan ita ta damuwarta take a halin yanzu, shima shirun ya yi, amma ba ka isa ka gane ko wani abu ya na damunsa ko akasin haka ba a halin yanzu.

Washegari Neehal ta tashi jikin nata da ɗan dama, dan Mama a gurinta ta kwana, tun dare jinin ya ɗauke mata, hakan ya sa da asuba ta yi wanka ta yi sallar ta, ta daɗe ta na wa Anwar addu’ar samun dacewa, da waɗanda kullum da koyaushe cikin yi musu take, da Jameel da ma dukkan Musulman da suka rigamu gidan gaskiya baki ɗaya. Zuwa yanzu zuciyarta ta gama tsinkewa ta haƙura ta fawwalawa Allah komai, Amma kallo ɗaya Mutum zai mata ya hango ramar da ta yi lokaci ɗaya, bayan ta gama addu’o’inta ta janyo wayarta wadda rabonta da ita tun jiya, missed calls d’in da akai mata take dubawa, Numbobin da ta sani da wanda ba ta sani ba gasunan rututu har ta rasa kiranwa ma za ta bi. Aranta ta ce “Da waninta ne ya mutu ba Anwar ba, da har da missed calls d’inshi za ta gani, kuma shi kaɗai za ta iya bin kiranshi, wani abu ta ji ya tokare mata a k’irji, a hankali ta shiga App din free kur’an ta buɗe ta fara karanta Suratul Baƙara, domin ta san shi kaɗai zai mata maganin abun da yake damunta. Ta yi nisa a karatun Ameen ya shigo ɗakin, ba ta ma san ya shigo ba har ya yi sallama, saboda hankalinta gabad’aya ya na kan karatun da take, a ƙoƙarin ta na ganin ba ta ba wa damuwa damar zama a cikin zuciyarta ba, sai dai k’amshin turarensa da baya b’uya ya sanar mata da zuwan nashi, ta d’ago da kanta da sauri cikin mamaki dan ba ta san ya kwana a gidan ba, gabanta ya faɗi haɗa idon da suka yi da shi, ta ɗauke idonta da sauri daga kallon shi bugun zuciyarta na ƙaruwa ba tare da tasan dalili ba, nufar inda take ya yi cikin takunsa na ƙasaita da burgewa……….✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:31] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

0️⃣8️⃣

……….Tsugunnawa ya yi a gabanta ya na kallon ta, ƙasa ta yi da kanta zuciyarta na cigaba da bugawa, lumshe idonta ta yi saboda daddad’an k’amshinsa da ya mamaye mata hanci, numfashi ta ja tare da lumshe idanunta, a hankali ya kama tattausan hannunta da nasa, cikin sanyin murya ya ce “Miemerh! Ya hakurin rashin Anwar?” Cikin muryarta da ta ɗan dashe saboda damuwa ta ce “Alhamdullah” fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce “Allah ya ji k’an shi, ya sa ya huta.” Neehal ta d’ago kanta a hankali tare da buɗe idanunta da suka cika taf da hawaye, ta ce “Amin, amma Yayah me ya sa ba ka zo tun jiya ba?” Ta k’arashe zancen hawaye na zubo mata, ba tare da ya saki hannunta ba ya shiga share mata hawayen fuskarta da ɗayan hannun nasa, cikin murya mai nuni da rarrashi ya ce “Am sorry, ban samu labarin mutuwar da wuri ba ne.” Neehal ba ta ce komai ba, sai hawaye kawai take kamar jira take a taɓa ta dama. Ameen ya ce “Kukan na mene kuma? Kin san dai mamaci ba ya buƙatar kuka ko?” Neehal ta na kuka ta ce “Dole in yi kuka Yaya, me Anwar ya yi aka kashe shi, haka ma fa a ka kashe mun Jameel, shima Anwar d’in ba za su bar mun sh…….” Rungumeta Ameen ya yi tsam a jikinsa cikin tsananin tausayinta, sosai shima al’amarin ya rud’a shi, Ajiyar zuciya Neehal ta shiga saukewa ta yi luf a kirjinshi tare da dena kukan. Shigowar Mama d’akin ya sa ta janye jikinta daga na shi da sauri, Mama ta kalle su ta ce “Me ya faru?” Ameen ya mik’e tsaye ya ce “Babu komai” Sannan ya sa kai ya fice. Mama ta zauna a bakin gado ta na duban Neehal ta ce “Kukan me ki kay?” Neehal ta girgiza mata kai alamun babu, Mama ta ce “Shikenan tashi mu je ki yi breakfast, Haneefah na hanya idan ta zo sai ku wuce gidan su Anwar” Neehal ba ta yi musu ba ta mik’e suka sauka k’asa tare da Mama. Tea kawai tasha kaɗan, shima dan kar Mama ta mata fad’a ne, Mama ta ce “Shikenan abin da zaki sha kuma ki ce kin k’oshi?” Neehal ta ce “Eh Mama ba zan iya ƙara cin komai ba” Mama ta ce “Daurewa za ki, ki ci ko Irish ne kaɗan” Neehal ta ɓata fuska, sannan ta d’ibi Irish d’in kadan ta ci, ta na kokarin barin falon Haneefah ta shigo da sallamarta, suka amsa mata ta gaida Mama, sannan ta dubi Neehal ta ce “Besty ya hak’urinmu?” Neehal ta ce “Alhamdulillah, ya kuka je gida jiya?” Haneefah ta ce “Lafiya k’alau” Sama suka hau tare, suka je d’akin Hajiya suka gaisheta. Neehal ta ɗauki wayoyinta suka fito suka yi wa Mama sallama, sannan suka je part d’in Dad  suka gaisheshi. Yau ma Neehal an zo mata ta’aziyya sosai, Uncle Mahmud da ya koma gida jiya yau ma ya dawo har da matarsa da ‘yarsa budurwa kamar su Neehal, sai dai Neehal ta ɗan girme ta. Ameen da Dad yau da su a ka wuni gurin zaman makoki. Da yamma Police masu fararen kaya suka zo gidan mutuwar domin yin tambayoyi ga ahalin Anwar, bayan sun gama da mutanen waje suka shigo cikin gidan, inda suka ce a kai su gurin Mahaifiyar Anwar. Ammi ta na ɗakinta ta ce su shigo, su su uku ne kuma duk maza ne, ɗaya daga cikin su wanda da alama shine babban su ya dubi Ammi ya ce “Hajiya ina yini, ya ƙarin hak’uri kuma?” Ammi ta ce “Lafiya k’alau Alhamdulillah” Ya ce “Allah ya ji k’an shi ya gafarta masa” mutanen d’akin suka amsa da “Amin” gabatar wa da Ammi kansa ya yi da na abokan aikinsa sannan ya ɗora da faɗin “A daren ranar da ana washegarin Anwar zai mutu, kun zauna da shi? Ma’ana kun yi doguwar hira?” Ammi ta ɗan yi jim na wasu sakonni kafin ta ce “Eh mun yi hira amma ba wata me tsayi ba” Mutumin ya ce “Ko a cikin hirar taku ya faɗa miki sun yi faɗa da wani ko kuma sun samu ɗan sabani haka?” Ammi ta ce “Gaskiya A’a, dan gaba-da’ya  ma hirar a kan kai lefen sa da za’a kai ne washegari” Mutumin ya jinjina kai ya ce “Kuma ba ki ga wata alamar ɓacin rai ko damuwa a tattare da shi ba?” Ammi ta ce ko kaɗan, sai ma tarin farin cikin da ya kasa b’oye shi, abun ma da na san ya faɗa mun wanda ya ɗan dame shi, sai rashin lafiyar da ita yarinyar da zai aura take yi, harma ya ce mun zai je ya gano jikin nata a wannan lokacin” Mutumin ya ce “Daga nan ba ku sake haɗuwa ba a wannan daren?” Ammi ta ce “Eh, sai dai sallama da ya zo ya mun, lokacin wajen 11 na dare” Mutumin ya ce “Kuma a nan ma ba ki ga ya na cikin wani yanayi ba ko kuma damuwa haka?” Ammi ta ce “Gaskiya ko kaɗan ban ga haka ba” Mutumin ya gyara zama ya ce “Ki yi hak’uri da tambayoyi na fa, sha’anin aiki ne” Ammi ta ce “Babu komai, ka ci gaba insha Allah zan faɗa maka duk abin da na sani” Mutumin ya gyad’a kai sannan ya ci gaba da magana “To a baya fa, ya taɓa faɗa miki ya na da wani wanda ba sa shiri da shi, ko a makaranta ko gurin aiki ko unguwa ko wani guri daban?” Ammi ta yi shiru na wani gajeren lokaci ta na tunani, sai kuma can ta girgiza kai ta ce “Gaskiya babu, domin Anwar tunda ya girma ba zan ce ga abokin faɗan sa ba, ko cikin abokansa da ‘yan’uwa da unguwa harma gurin aikin na su, idan ma da akwai bai taɓa faɗa mun ba, kuma gaskiya ba ya b’oye mini duk wani abu nashi, komai zai faɗa mun ya ce Ammi ki ta ya ni da addu’a.” Mutumin ya jinjina kai ya ce “A ranar da zai rasu ya yakasance ya tashi kamar kullum da ya saba ko da wani canji?” Ammi ta sauke Numfashi muryarta na ɗan rawa ta ce “Lafiya k’alau muka tashi kamar kodayaushe, Misalin ƙarfe 7 da k’wata kamar yadda ya saba ya zo nan gurina, muka gaisa k’annensa suka kawo masa abincin kari ya ci, sannan ya mun sallama ya tafi gurin aiki, kuma kamar yadda ya saba da ya ƙarasa wajen aikin ya kira ni ya ce mun ya je lafiya, daga nan sai mummunan labarin da muka j…….” Ta fashe da kuka mai ban tausayi. Mutumin ya jinjina kansa a karo da yawa ya ce “Sai hak’uri Hajiya, Allah ya ji k’an shi, Mun gode da haɗin kai da ki ka ba mu, Insha Allah za mu yi iya ƙoƙarin mu wajen ganin an gano waɗanda su kai kisan kuma an bi muku hakkin ran ɗanku, idan da buƙatar sake zuwa mu miki wasu tambayoyin za mu dawo” Ammi ta gyad’a masa kai ta na share hawayen fuskarta. Mutumin ya dubi ɗaya daga cikin wanda suka zo tare mai rubuce_rubuce ya ce “Ya kamata mu ga yarinyar da zai Aura ita ma” Ɗayan ya ce “Haka ne Sir” Ammi ya tambaya ina Neehal ta ce ta na falo bari a kira masa ita, bayan ta zo sun gaisa ya mata ta’aziyya sannan ya dubeta da kyau ya ce. “Malama Neehal, a zamanku da Anwar ko ya taɓa faɗa miki cewa ya na da wani abokin faɗa ko kuma wanda ba sa jituwa?” Neehal da kanta ke ƙasa cikin sanyin murya ta ce “Gaskiya bai taɓa faɗa mun ba, Ni tunda nake da shi ma bai taɓa ce mun yau sun yi faɗa da wani ba, ko kuma wani ya ɓata masa rai ba” Mutumin ya ce “Ke ce wadda ya yi waya da ke ta ukun ƙarshe kafin rasuwar sa, shin da kuka yi waya kin ji wata alama da take nuni da ba ya cikin wani firgici ko damuwa? duba da a gurin aikinsa har cikin office d’insa a ka je a ka kashe shi, kuma wayar ki da shi ko 2 hour ba’ayi ba hakan ta faru” Neehal ta ce “Ko kaɗan ban ji alamar hakan ba gaskiya” Mutumin ya jinjina kai ya ce “Shikenan Malama Neehal bari na barki haka, next time idan buƙatar mu ƙara tattaunawa da ke ta taso, za mu nemi ki”  Neehal ta gyad’a masa kai kawai, zuciyarta na bugawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button