NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
A hargitse Daddy ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi cikin matuƙar tashin hankalin da Mama zata iya cewa tunda suka yi aure bata taɓa ganin shi a cikin irinsa ba, Abba na biye da shi a baya shi ma cikin tashin hankali yana tambayar shi abun da yake faruwa ya gan shi duk a birkice. Mama ta janye jikinta daga jikin na Neehal ta miƙe tsaye cikin sauri, ta nuna shi da hannunta cikin muryarta dake fita da ƙyar saboda tsantsar damuwa ta ce. “Me ya kawo ka inda muke, ko ka zo ka ƙara mana wani ciwon zuciyar ne akan wanda ka saka mana ni da marainiyar Allah da bata ji ba bata gani ba? Ko kuma ka zo ne ka aiwatar da mummunan nufinka a kanta a gaban mu?” Daddy ya ƙaraso kusa da ita ya kama hannunta kamar zai yi kuka ya ce. “Dan Allah Fateemah ki tsaya ki saurare ni in miki bayani, na san a yanzu ji kike kamar ki kashe ni saboda tsana, amma dan Allah ki tsaya ki ji mai zan faɗa miki, wallahi ba laifina ba ne nima babu yadda zan yi ne.” Mama ta fizge hannunta ta ce. “Muhammad ko ganin ka bana k’aunar yi balle na ji wannan muryar taka mai ƙara mun k’una da baƙin ciki a cikin raina, dan Allah ka fice daga ɗakin nan ko kuma ni in fita in bar maka gidanka. Ka ba ni mamaki kuma ka bani kunya, ashe dama ba dan Allah kake riƙon Neehal ba? Yanzu duk abubuwan da suke faruwa da ita kai ne sanadi?” Daddy ya ƙara riƙe hannunta ya ce. “Please Doctor, ki mun wannan alfamar ki tsaya ki saurare ni in miki bayani, ko da wannan zata kasance alfarma ta ƙarshe da zaki mun a rayuwata. Please and please, ni kaina a yau na ji tsani kaina da rayuwata.” Mama ta kuma k’wace hannunta ta ce. “Bayanin me zaka mun Tafiya? Bayanin kai ka kashe Jameel da Anwar ko kuma bayanin kana riƙon Neehal ne saboda ka lalata rayuwarta? Ko kuma bayanin da zai ƙara tabbatar mana kana cikin ƙungiyar matsafa kai ɗan shan jini ne?” Abba dake bakin ƙofa yana kallon su cikin tsananin mamaki ya ce. “Subhallahi, Fateemah me kike faɗa haka? Kin san kuwa mai kike cewa? Mijinki ne fa General Muhammad Tafida a gabanki ba wani ba.” Mama tana hawaye ta ce. “Na sani Yaya, Na sani.” Sai ta mayar da duban ta ga Daddy ta ce. “Ka cuce ni, ka cuce ni Muhammad, ka ɓata wayonka, ka ɓata rawarka da tsalle, yanzu duk damuwa da k’aunar da kake nunawa Neehal duk na Ƙarya ne? pretended kawai kake yi saboda kar mu gano mummunan nufinka a kanta? Muhammad why? Me yasa? Mai Ubangiji ya rage ka da shi a rayuwar nan da ka zaɓi saɓa masa da laifin da ba ya yafewa? Shirka fa muham……” Kasa ƙarasa abun da take son faɗa ta yi saboda numfashinta da ba ya fita sosai, sai haki take jikinta na wani irin ƙyarma. Daddy ya yi ƙoƙarin riƙe ta ta yi baya da sauri kamar zata faɗi, da sauri Aunty Sadiya ta tashi ta riƙe ta, ta zaunar da ita a bakin gado. Cikin kuka Hajiya ta ce. “Na shiga uku ni Zainabu, wannan wacce irin masifa ce, Allah ka farkar da ni idan mafarki nake.” Aunty A’isha ta dubi Mama cikin sanyin murya ta ce. “Ki yi haquri mu saurari Yaya Tafida mu ji me yake tafe da shi, ki bi komai a sannu dan Allah, kar wani mummunan ciwon ya kama ki.” Mama zata yi magana amma ta kasa, sai jujjuya kanta kawai take. Abba ya ce. “Ni fa ƙara saka ni a cikin duhu kuke, dan Allah ku fahimtar da ni abun da yake faruwa.” Aunty A’isha ta ce masa. “Ka zauna yanzu zamu ji komai daga bakin Yaya Tafida.” Abba ya ƙaraso ya zauna akan carpet cikin tsananin al’ajabin wannan murdadden al’amarin. Aunty A’isha ta mayar da duban ta ga Daddy dake ta yiwa Mama sannu cikin tsananin tashin hankali, ta ce masa. “Ka zauna ka yi mana bayanin muna sauraren ka.” Daddy ya sauke nannuyar ajiyar zuciya ya goge gumin da ke ta tsalala a fuskarsa sannan ya zauna shi ma ya fara magana kamar haka.
Shekaru goma sha uku da suka wuce baya Abokaina Alhaji Karbir Ginyau da Alhaji Idris suka dame ni akan na shiga harkar siyasa, tunda ina da kuɗi kuma na san manyan mutanen ƙasar nan gani General na sojoji mulki ba zai mun wahala ba. Na nuna musu ni bana son harkar siyasa ko kaɗan kuma ba zan yi ba. Alhaji Kabir abokina ne tun samartaka, zan iya kiran shi ma da aminina. Sai dai halayyar mu k’wata_k’wata ba iri ɗaya ba ce, shi mutum ne mai matuƙar son abun duniya dan zai iya yin komai akan kuɗi, sannan yana harkar bin matan banza. Ina faɗa masa gaskiya a kodayaushe a matsayinsa na abokina amma ko kaɗan ba ya ɗauka. Yakan ce mun idan mutum bai shana ba a gidan duniya mai zai yi? Da na ga ba zai taɓa dena halinsa ba sai na koma bin shi da addu’ar fatan shiriya idan mai shiryuwar ne. Kabir ya dinga mun naci da magiya akan in shiga siyasa harkar akwai samu sosai a cikinta. Na nuna masa ni fa ba zan yi ba, amma ya ishe ni da naci da magiya, har na amince masa zan yi amma na ce sai na yi shawara da iyalina. Na tuntubi Fateemah da maganar, da farko ƙin amincewa ta yi sai daga baya na lallaɓa ta ta yarda da ƙyar ta amince in yi siyasar, bayan ta kafa mun sharad’an yin komai cikin gaskiya da tsoron Allah. Zuwa lokacin nima ina son yin siyasar sosai, Kabir ya ƙwadaita mun yanda ake samun Alkhairi a cikin ta. Ban fara siyasa daga matakin ƙasa ba sai na fito takarar shugaban ƙasa. Na saka kuɗi na mai yawa na siyi Form ɗin takara. A hankali na fara tara mabiya da magoya baya, na samu waɗanda suka daɗe a cikin siyasar ake damawa da su suka d’aga hannuna. Tunda na fara harkar sai na fara shiga busy, yau mu ne nan garin gobe mu ne can. Wannan dalilin yasa Fateemah ta ƙara tsanar harkar, har ta fara mun zancen ko zan haqura in daina. A lokacin ni kuma abun ya shiga raina sosai gaskiya, sai na lallaɓa ta na ce mata da zarar komai ya dai-dai ta zan koma normal kamar da. Ana haka Kabir ya ce mun harkar siyasa fa dole sai an haɗa da taimakon malamai. Ban kawo komai a raina ba nake ba shi kuɗi a matsayin wanda za’a kaiwa malamai suke yin addu’a. A lokacin ni akaran kaina na san idan aka yi Elections ba zan taɓa winning ba, amma sai na saka a raina komai dan dagiya ne wani lokacin zan iya cin zaɓen. Sai na dage da taimakawa jama’a da takalawa, ta hanyar samar da maguda nan ruwa a wuraren da ba su da ruwa, da kuma gina masallatai a ƙauyuka. A hankali sunana ya fara baza ƙasar nan, mutane suka san ni sosai. Watarana ranar da ba zan taɓa iya mantawa da ita ba a rayuwata, ranar baƙin ciki ranar da tsautsayi yasa na faɗa cikin k’azamar ƙungiyar da babu komai a cikinta sai shirka da tsantsar rashin imani. Alhaji Kabir ya zo ya same ni har office ɗina ya ce mun, yanzu na fara yin masoya sosai a ƙasar nan, zata iya yiyuwa in ci zaɓe, dan haka in zo mu je zai kai ni wani guri da za’ai mun aikin da zai saka in ci zaɓen, dan siyasar yanzu dole sai da haka. Na ce masa in dai gurin kaucewa hanya ne baza ni ba, ni babu wanda zan kaiwa kukana sai Allah shi zan roƙa da shi na dogara. Kabir ya dinga nuna mun ba wani abu ba ne ai wannan is common thing, in ma ban yi yanzu ba sai na yi watarana, dan indai na ce kwanciya zan yi a siyasa zan ga kwanciya, za ai komai babu ni. Nan dai ya dinga saka mun san abun a raina yana mun huɗubar banza har kalamansa suka yi tasiri a kaina, sheɗan ya dinga zuga ni tare da ƙawata mun daɗin mulki da cigaban rayuwa da zan samu in har na haye kujerar mulkin shugabancin ƙasar nan. Ni har ga Allah na bi Kabir da niyyar zai kai ni wurin wani malamin, irin malaman soron nan ko masu duba, amma ko kaɗan boka da masu tsibbu ba su zo raina a matsayin wanda Kabir zai kai ni gurin su ba. Amma me? Mun yi tafiya ta kai ta awa uku kafin mu tsaya a wani tangamemen gida dake can wajen gari, babu gida gabansa babu gida bayansa, shi kaɗai a gurin. Muna zuwa ƙofar gidan na ji gabana ya faɗi, na dubi Kabir da ya gaji da mitata da nake ta yi masa tunda na ga muna ta tafiya ta ƙi ƙarewa na ce masa. “Ina ka kawo ni Kabir?” Ba tare da ya kalle ni ba ya ce. “Inda na ce zan kawo ka mana.” Daga haka ya buɗe Motar ya fita, nima ban da zaɓi sai bin bayan nasa.