NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ya k’wank’wasa ƙofar gate ɗin gidan, mintuna kaɗan wani ɗan tsoho ya zo ya buɗe mana, suka yi maganar da ni ban ji me suke cewa ba sannan Kabir ya shige gidan. Na tsaya na ƙi shiga saboda yanda gabana yake ta faɗuwa sosai, sai hasbunallahu’wani’imal’wakil nake maimaita a cikin raina. Kabir ya juyo ganin ban bi shi ba ya ce in shigo mana. Na ƙara tambayar sa Kabir wai inane nan ka kawo Ni? Ni fa hankalina ya ƙi kwanciya da gurin nan, gaskiya gida zan koma. Ya ce, ka zo mu je ka gani mana, haba ka cika garaje matsalata da kai, mu ci wannan uwar tafiyar sannan ta tashi a banza, wannan abun da taimakon ka zan yi ba kaina zan yiwa ba. Na yi tsaki sannan na bi bayan shi. Wani dogon lungu ne a cikin gidan, nan muka bi mu kaita tafiya sannan na ga mun shiga wani ƙaton Parlour, wanda babu komai a cikin sa sai wasu irin abubuwa marasa kyan gani a rarrataye, na shiga bin Parlour’n da kallo tsigar jikina na tashi. Kabir ya buɗe wata ƙofa dake falon ya shiga tare da yi mun alamar in biyo bayan shi. Ban musa ba na bi shi na shiga nima, abun da na tarar a ɗakin ba ƙaramin daga mun hankali ya yi ba ya kuma girgiza tunanina, har na yi tunanin ko mafarki nake. Wata mace hakimce akan kujera ta mulki tsirara haihuwar uwarta, kanta babu gashi a aske yake tal kamar Namiji. Ta ɗaura wani jan k’yalle a hannunta da ƙafarta. Sai zazzare idanu take yi. Gabanta kuma wani tulu ne na zinare wasu k’artan maza guda biyu suma ba kayan kirki a jikinsu suna tsiyayo mata wani jan abu mai kauri a cup tana ƙarba ta sha. A fili na ce A’uzubill…… Amma kafin na ƙarasa na ji an buge mun bakina, na juya dan ganin waye amma ban ga kowa ba. Kabir ya tsugunna yay sujjada ga matar nan wanda hakan ya ƙara tayar mun da hankali. Na sunkuya na d’ago shi cikin fusata na sharara masa mari na ce. Kabir gurin matsafa masu shan jini ka kawo ni gurin mushirikai? To rashin imanina bai kai haka ba, neman duniya ta ba zai saka in ɓata har haka ba. Na juya na fice daga ɗakin cikin tsananin fusata da baƙin ciki ina Allah wadaran halin Kabir. Tafiya nake kamar zan tashi sama ina haɗa hanya har na kai bakin gate ɗin gidan, na dubi mai gadin gidan a fusace na ce masa ya buɗen ƙofa. Amma kafin ya yi wani yunƙiri sai gani na na yi a ɗakin dana bar Kabir da wannan matar yanda na bar su. Na shiga rarraba ido cikin tsananin al’ajabi ina bin ɗakin da kallo tare da tunanin da yanda aka yi na iya dawowa ɗakin cikin kiftawar ido ni da nake a bakin gate. Na bi su da kallo kamar yadda suka tsaya cak suna kallo na su ma, na buɗe baki da niyyar magana ko addu’a amma na ji na kasa. Sai na juya da sauri na ƙara ficewa daga ɗakin, wannan karon da gudu na ƙarasa gate ɗin gidan. Amma nan ma kafin kiftawar ido na ƙara ganin an mayar da ni wannan ɗakin. Sai da muka yi haka har sau uku, ni na ƙi haqura in tsaya a ɗakin kamar yadda suke so, su kuma sun ƙi bari na in fita daga gidan, sai na kai bakin gate sannan su ƙara dawo da ni cikin ɗakin. A na ukun ne matar nan ta shek’e da wata mahaukaciyar dariya tana duba na, ni kuma inata aikin zazzare idanu da numfarfashi. Sai da ta yi dariyarta mai isarta ta gama sannan ta murtuke fuska kamar an aiko mata da saqon mutuwa ta fara magana cikin amon murya da faɗin………✍️
By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
7️⃣0️⃣
Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#
…….”Barka da zuwa Muhammad Tafida, ƙungiya na farin ciki da kasancewar ka a cikinta. A kodayaushe muna san irinku masu tsantsar riƙo da addini a cikin mu, domin mu mun fi son mu ɓata shiryayyu su koma ɓatattu, wannan shine burinmu akodayaushe.” Sannan ta dubi Kabir ta ce masa. “Aikinka yana kyau mai jan kai bawan mai jan kai, a yau za’a ƙara maka matsayi a cikin wannan ƙungiya, sakamakon kawo mana wannan babban mutum cikinta da ka yi. Markus da Jamus suna alfahari da kai.” Na dubi Kabir na dube ta ba tare da na gane inda maganganunta suka dosa ba. Ina son na yi magana amma na kasa koda motsa labbana ne balle na iya sarrafa harshena. Na yi ƙoƙarin juyawa na fice daga ɗakin kamar yadda na yiyyi d’azu amma na kasa, daga nan ma ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi na ganni kwance akan wani irin gado ɗan ƙarami, babu komai a jikina sai jan k’yalle ɗaure a hannuna da kaina da ƙafata. Na yunƙura na tashi sai na ga mutane mata da maza kusan hamsin zagaye da gadon da nake, dukkanin su tsirara haihuwar uwarsu sai ɗan jan k’yallen nan kamar na jikina. Suna watsa mun wani jan abu ajikina wanda na fahimci jini ne, suna kuma yin wani abu da bakinsu kamar wak’a amma da wani irin yare irin nasu na matsafa. Na gaza yin komai sai bin su da ido, Kabir kawai na gane a cikinsu sai wannan ƙatuwar matar dake facing ɗina tana mun wani irin kallo. Sun daɗe suna yin abubuwan su akaina, su shaƙa mun hayak’in wannan, su fesa mun wancan su watsa mun wannan, haka dai sukay ta yi. Sai na ji gaba-ɗaya jikina kamar ba nawa ba, kamar an canza ni, na ji zuciyata da ƙwaƙwalwata kamar ba su taɓa sanin abu a cikin duniyar nan ba sai waɗannan mutanen. A tak’aice dai a ranar na zamto member na wannan ƙungiyar ba dan son raina ba sai sanadiyyar la’anannen abokina, kuma duk abun da suka saka ni in yi bana musu nake yi. Ni ban sani ba ashe har mun kwana a gidan, wannan farkawar da na yi ma tsakar dare ne. Sai washegari da hantsi sannan aka bani kayana na saka muka baro gidan ni da kabir, bayan Sarauniya kamar yadda na ji suna kiran wannan ƙatuwar matar ta kafa mun sharad’an zuwa kullum wannan gidan ana aikin ƙungiya tare da ni. Ta tabbatar mun babu abun da zan nema a duniyar nan in rasa komai girman buƙata_ta da burina zan samu, sannan kuma dole duk aikin da ƙungiya ta saka ni in yi shi komai wahalarsa, kuɗi kuwa idan suna bautawa mutum sai sun bauta mun a duniyar nan saboda yawan kuɗin da zan yi. Ta kuma raɗa mun suna jaririntah, sauran ƴan ƙungiya kuma suna kira na autan ƙungiya. Jikina kamar ba nawa ba muka taho gida ni da Kabir dake ta murmushin farinciki da jin daɗi. Ni dai kawai kallon sa nake ina jin kaina ya mun wani irin nauyi kamar duka mutanen duniyar a kaina suke. Sai da muka shigo cikin gari sannan na fara dawowa nutsuwata, hankalina ya fara dawowa jikina. A fili na ce. “Shikenan na zama matsafi ɗan shan jini kenan?” Na yi tambayar cikin tsananin mamaki da al’ajabi. Kabir ya tuntsure da dariya ya ce. “Harkar akwai samu na gidana, zaka yi bala’in kuɗi nake faɗa maka mutumina, na san inna faɗa maka gaskiya tun kafin mu zo baza ka taɓa amincewa ka biyo ba, shi yasa kawai na kawo ka. Na daɗe ina son saka a cikin wannan harkar dan na san ƙungiya tana buƙatar irinku masu tsoron Allah.” Ban san lokacin da nay masa wata muguwar shak’a ba, ya yi saurin taka burki. Ina huci na ce masa, “ka cuce ni Kabir ka cuci rayuwata, yanzu mai zan ce da Ubangiji na da kuma iyalina akan wannan mummunar harkar daka saka ni a cikin ta? Mene ribarka na mun hakan Kabir? Wanne laifi nay maka a rayuwar nan ka zaɓi sanya ni cikin wannan mummunar harkar? Wacce irin tsana kai mun har haka? Dan wannan ba k’auna ba ce.” Ya k’wace jikinsa dak’yar daga shaƙar da nay masa yana mayar da numfashi ya ce. “Aikin gama ya riga ya gama, duk wani hargagi da zakai baza ka taɓa fita daga cikin ƙungiyar nan ba har abada, ƙungiya ce da in aka shiga ba’a fita, sai dai in mutuwa ka yi.” A hasale na ce masa ƙarya yake, kuma zai sha mamakina, ni da ƙara zuwa wannan gidan har abada. Anan muka rabu da Kabir baram_baram ya fice ya bar mun Motata ina girmama rashin imani da son duniya irin na Kabir, ko kaɗan ban taɓa sanin yana wannan harkar ba, dan ban yi zaton son duniyar tasa har ya kai haka ba. Bayan na koma gida na tarar da Fateemah duk ta tayar da hankalinta akan rashin dawowata gida jiya. Tana gani na ta saka kuka ta ce. Indai har ina son zama da ita daga ranar in bar siyasa, ta gaji da wannan bala’in yawa_yawan, ga wani mummunan mafarki da ta yi a daren jiya a kaina. Na tabbatar mata daga ranar na bar siyasa har abada, dama ko bata faɗa ba na yi niyyar dainawa saboda a sanadinta na faɗa wannan mummunar harka. Saboda tana cikin murnar gani na bata lura da canjin yanayin da nake ciki ba. Amma tay ta tambaya ta inda na je na kwana, na sanar mata wani ƙauye muka je campaign motarmu ta lalace mana a hanya. Tay ta mun wani irin kallo kamar bata yarda da abun da na ce mata. First maganar data fara fitowa daga bakinta a lokacin in rabu da Kabir Ginyau domin ba mutumin arzik’i ba ne, bata son alaƙa ta da shi, dan ta san duk inda na je tare muka je da shi. Na ce mata Insha Allahu na rabu da shi kenan. Daren ranar ban iya runtsawa ba saboda tsananin damuwa, na yi dana sanin, sanin Kabir a rayuwata babu adadi. Na yi kuka, na yi kaico da rayuwata, na tsani kaina, na dinga addu’ar Ubangiji ya ɗauki raina a daren in huta, da dai in cigaba da rayuwa a matsayin ɗan shan jini. Washegari safiya tana yi na ji hankalina gaba-d’aya ya yi gurin matsafan nan, na ji kamar zan mutu idan ban je gurinsu ba. Lokacin ina aiki ban yi retired ba, na shirya da zummar zuwa gurin aiki na fita, ina fita na kira Kabir na ce ya zo ya kai ni gidan jiya dan ba zan iya gane hanya ba. Kabir ya zo ya dinga mun dariya yana faɗin dama ya ce ba zan taɓa iya fita ba daga ƙungiya ba da kaina zan koma, to sun riga sun gama tsaface ni na zama na su. Tun daga wannan rana idan ban je gidan nan ba yau to gobe zan je. Amma ko sau ɗaya ban taɓa kwana a can ba, duk da kowanne member akwai ranar kwanansa a gidan, dan an fi yin aiki cikin tsakiyar dare. Ni kaɗai ne bana kwana saboda ban san me zan faɗawa Fateemah ba idan na je na kwanan, ina zan ce mata ina zuwa? Sarauniyar ƙungiya tana matuƙar sona a cewarta, hakan yasa ko da an ce a yi abu na ƙi yi bata iya hukunta ni, saɓanin sauran members da babu wanda yake iya yi mata musu. Ni kuma ina sane nake ƙin yi wani abun idan ta umarce ni, saboda ta yi zuciya ta kashe ni. Dan wallahi ina cikin ƙungiyar ne kawai amma bana so, ni kaɗai na san baƙin cikin da nake ciki a sanadiyyar kasancewa ta a cikin wannan ƙungiya, kodayaushe cikin yiwa Kabir Allah ya isa nake, tunda shi ya jefani a cikin wannan iftila’in, kuma har abada ba zan yafe masa ba. Babu abun da ake aikatawa a cikin wannan ƙungiyar face zallar rashin imani da shirka da tsantsar tsafi. Zaku sha mamaki idan kuka ji manya da wasu daga cikin masu mulki a ƙasar nan wanda ake musu kallon mutanen kirki amma suna cikin wannan ƙungiya. Lokaci ɗaya na sauya daga aihin Muhammad Tafida na, na koma wani daban, na watsar da duk abokaina saboda tsoron kar su gano mummunar hanyar dana faɗa, ƴan ƙungiyar nan su suka zama aminaina da su kaɗai nake hulɗa. Dole ne ko kuma in ce sharad’i ne na wannan ƙungiya, duk wanda yake cikinta sai ya yi tarayya da ƴarsa ta cikinsa budurwa, idan kuma macece ta yi da ɗanta saurayi wannan tilas ne ga kowa. Amma naga su members ɗin ƙungiyar kamar hakan ba ya damun su, daɗi ma suke ji da murnar hakan, wasu ma ba ƴaƴa ɗaya suke ɓatawa ba, in sun kai goma ƴan’matan da samarin duk sai sun ɓata su, wasu ƴaƴan ma sanadiyyar hakan suke rasa ransu. Iyayen kuma su fi kowa nuna damuwa da zak’ewa akan al’amarin a idon duniya. Wanda ba shi da yar ko ɗan ne kawai ake masa uzuri, amma za’a ba shi wani aikin a madadin wannan ya yi, ko lalata ƙananan yara mata da maza, ko kuma wani babban saɓon ga Ubangiji. Nima hakan ce ta kasance da ni, bani da ƴa mace dan haka aka bani aikin ɓata ƙananan yara mata ta hanyar yi musu fyaɗe. Kai tsaye na ce ba zan iya ba, duk da ina cikin wannan ƙungiya amma imanina bai tafi duka daga cikin zuciyata ba. Manyan ƙungiya suka mun caaa aka da masifar dole sai na yi, ai ba fin su na yi ba da za’a saka ni abu ina ƙin yi, amma Sarauniya ta tsawatar musu ta ce su rabu da ni, ta san ya zata yi da ni. Haka na cigaba da rayuwa cikin takatsantsan da ɓoye abun da nake aikatawa, dan babu wata alama da zata nuna maka ina wannan mummunar harkar idan ka gan ni, ba ma ni kaɗai ba, duka yan ƙungiyar idan suka fito cikin gari haka ne, ko iyalanmu ba su isa sun gane ba.