NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A fili Abba ya shiga maimaita “Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un.” Cikin tsananin tashin hankalin jin halin da ɗan’uwansa yake ciki. Neehal ta ƙara volume ɗin kukanta kamar yadda Hajiya ta fashe da matsanancin kuka. Mama ta sunkuyar da kanta ƙasa tana ganin wasu taurari na gilmawa ta cikin idonta, daga baya kuma ta daina ganin komai sai duhu dulum na wasu sakanni. Ta yi tunanin bayanin da Daddy zai yi zai ƙaryata abun da Neehal ta faɗa da kuma zargin da Aunty Sadiya take masa ne, ya ce ba shi Neehal ta gani ba wani mai kama da shi ne, ko kuma sharri akai masa kamar yadda Hajiya ta faɗa. Amma sai ta ji saɓanin hakan, sai ma amsa laifinsa da ya yi, ya tabbatar musu yana cikin ƙungiyar matsafa shi ɗan shan jini ne. Ta shiga tambayar kanta anya kuwa ba mafarki take ba? Anya mijinta adalin miji mutumin kirki zai aikata haka? Ko a mafarki bata taɓa tunanin zata faɗa irin wannan jarrabawar ba, bata taɓa tunanin ƙaddara irin wannan zata riske su ba. Muhammad ɗinta mijinta Mahaifin Ameen shine a cikin wannan mummunar harkar? Zuciyarta ta kasa yarda da wannan al’amarin, yay mata girma baza ta iya ɗauka ba. Ta d’ago kanta ta zubawa Daddy jajayen idanunta da suka rine saboda tashin hankali, ta yi gyaran murya cikin ƙarfin hali saboda muryarta da take a shak’e, cikin dauriyar ciwon da take ji a cikin zuciyarta ta ce masa. “Wannan labarin ƙaryar daka zauna ka tsara shi da kukan munafurcin da kake ba zai saka in yarda da kai ko ina yafe maka ba Muhammad, cuta ce ka riga daka cuce ni babu yanda zan yi. Wallahi da ba dan kai ka faɗa mun wannan maganar da bakinka ba da ba zan taɓa yarda ba inda wani ne ya faɗa mun, ko da kuwa Hajiya ce data tsugunna ta haife ni ta faɗa ba zan yarda ba, dan na maka kyakkyawar shaidar kai mutumin kirki ne. Ka bani mamaki Muhammad, ace shekara da shekaru da matsafi mashayin jini nake rayuwa.” Daddy ya matso ya kama ƙafafunta ya ce. “Allah ne shaidata akan duk abubuwan dana faɗa muku shine gaskiyar al’amarin, dan Allah Fateemah ki yarda da ni, ki karɓi hakan a matsayin ƙaddara kamar yadda na ɗauka wannan ita ce ƙaddarata a rayuwata.” Mama ta watsa masa wani kallo ta ce. “Ƙaddara ko son zuciyarka? Komai ɗan Adam ya aikata sai ya ce ƙaddara ce, saboda ita ƙaddarar ba’a ganin ta bare ta kare kanta ko? Wannan labarin naka shirya shi kawai ka yi ka faɗa mana. Ban da haka ta yaya kana cikin ƙungiya za’a shirya yanda za’a kashe ƴaƴan mutane amma ka ce baka sani ba? Ta yaya hakan zata kasance?” Daddy ya ce. “Wallahi bana sanin lokacin da suke shiryawar, na fi tunanin cikin dare ne da bana zuwa gidan suke shiryawa.” Mama ta ce. “Me yasa ka san dalilin da yasa aka kashe su Jameel amma ka bar Sadik ya nemi Auran Neehal? Ko dan ba ɗanka ba ne ko an kashe shi baka da asara?” Daddy ya ce. “Babu yanda zan yi ne Fateemah, bani da mafita, ko so kike in ce miki Neehal baza tay Aure ba? Ki ce mun akan wanne dalilin in rasa amsar baki? Wacce fassara zaku mun idan na faɗi haka? Wallahi ko Anwar da Jameel dana san za’a kashe su a ranar dana fara ganin su da Neehal zan aura musu ita ba tare da duniya ta sani ba, balle har ƙungiya ta ji su ɗauki matarsu su tafi ba tare da an yi taron bikin komai ba, kinga da tuni na huta da wannan fargabar, da duk abubuwan da suka faru da Neehal ba su faru ba.” Mama ta runtse idanta cikin matsananciyar damuwa ta ce. “Muhammad ka taɓa shan jinin mutum ɗan’uwanka? ka taɓa yin tsafi ta shirka da kanka?” Daddy ya shiga girgiza kai ya ce. “Fateemah tsafi gaskiyar mai shi, wallahi ba yin kaina ba ne tsaface ni suka yi, idan na je gidan duk abubuwan da nake yi ba’a cikin hayyacina nake ba.” Hawaye suka fara shatata daga idon Mama, cikin muryar kuka ta ce. “Fatana da addu’a ta ɗaya ne, Allah yasa kana yin Sallah da azumi Muhammad? Allah yasa baka sadaukar da su saboda san duniya ba?” Daddy ya ce. “Ban daina Sallah ba balle azumi kema zaki bayar da shaidan hakan.” Mama ta buɗe idonta tare da dafe ƙirjinta ta ce. “Na san babu yadda za’a yi ace ana Sallah a gidan matsafa, a ina kake yin Sallar?” Daddy ya ce. “Idan na dawo da yamma nake haɗawa na yi, asuba da isha’i kuma ina yin su akan lokaci, Magriba ma wani lokacin inna dawo da wuri ina yin ta akan lokaci.” Mama ta girgiza kai cikin takaici ta ce. “Da azumi a bakinka kana zuwa gurin shirka mene makomar azumin naka?” Daddy ya ce. “Bana zuwa gidan da azumi, hutu nake ɗauka.” Mama ta yi murmushi mai ciwo ta ce. “Da kuɗin tsafi da shan jini kake ciyar da mu ka tufatar da mu?” Daddy ya ce. “Wallahi ban taɓa ciyar da ku da haram ba, ni akaran kaina ban taɓa cin kuɗin ƙungiyar nan ba, dan na san haram ba ƙaramin bala’i ba ce a jikin ɗan Adam. Fateemah kin san ina da kuɗi tun asalina, Baffa ya rasu ya bar mana kadarori da tarin dukiya, and then my salary is more than 1.5 kin san wannan kuma already, ina business ina da Mall a Abuja da Kano, waɗannan sun isa na ciyar daku nay muku komai na buƙatar rayuwa ba tare da k’azaman kuɗin ƙungiya ba. Ke tsarkakakkiya ce Fateemah, ba zan taɓa yi miki algus da kazanta a rayuwarki ba. Wallahi Fateemah baki san tarin yawan nadamar dake cikin zuciyata ba ne, ina jin dama ban taɓa sanin Kabir ba a rayuwata, dama ban faɗa harkar siyasa ba, da ana dawo da abun da ya wuce baya dana dawo da rayuwata na cire wannan dattin da ya ɓata mun tsaftatacciyar rayuwata.” Mama ta sauke ajiyar zuciya bata kuma cewa komai ba. Ta mayar da idanunta ta lumshe tana jin yanda zuciyarta take bugawa da sauri da sauri gami da wani irin zafi da take mata kamar ana gasa mata nama a cikin ta.
Daddy ya bar jikinta ya koma gaban Neehal, ya d’ago kanta yana hawaye ya ce. Ki yafe mun Daughter ni ne sanadin saka miki baƙin ciki a rayuwarki, dan Allah ki yafe mun ko zan samu sauƙin azabar Ubangiji idan na mutu.” Neehal ta girgiza kai ta ce. “Babu abun da kai mun Daddy sai tarin Alkhairi, ka riƙe ni ba tare da ƙyara ko zangwama ko hantara ba a gidanka, ka bani tarbiyya ka bani ci da sha da sutura, ka bani ilimin addini dana boko ka samar mun aikin yi. Abun da ƴan’uwana na jini wanda Ubangiji ya ɗora musu hak’k’in hakan ba su mun ba, amma duk kai ka yi mun. You Are still my father Daddy, kai na sani a matsayin ubana a duniyar nan, wannan abun da ya faru ƙaddararmu ce gaba-d’ayan mu, amma kai ma ba laifinka ba ne.” Sai ta faɗa jikinsa tana ƙara fashewa da kuka mai ban tausayi tare da faɗin. “You are still my father Daddy.” Daddy ya rungume ta yana kuka sosai ya ce. “I’m Bad father for you Neehal, mahaifinki shine wanda ya yarda aka kashe shi saboda ganin ya kare mutuncinki da martabar ki, ni kuma ni ne nake ƙoƙarin raba ki da su, I’m not good fasher for you, please forgive me Daughter!.” Aunty A’isha ta lumshe idonta hawayen tausayinsu na zuba daga cikin idanun nata, sun bata tausayi ba kaɗan ba, wannan wacce irin ƙaddara ce, gaskiya Kabir ya cuci Daddy, Amma Allah zai masa sakayya. Aunty Sadiya ma duk taurin zuciyarta sai da ta yi kuka. Abba ya jinjina kai ya ce. “Na rasa da sunan da zan kira wannan baƙin al’amarin, Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un. Yanzu Muhammad kai da na sani mai riƙo da addini kai ne a cikin ƙungiyar matsafa fiye da shekara goma? Ya assamadu kasa mu yi kyakkyawan ƙarshe.” Turo ƙofar ɗakin da aka yi yasa suka juya gaba-d’aya suna kallon ƙofar, Neehal ta bar jikin Daddy da sauri. Zulai ce ta fara shigowa sai kuma wasu mutum uku masu sanye da suit a jikinsu. Ɗaya daga cikin su ya yi sallama, babu wanda ya iya amsa masa. Bai damu ba ya ɗauko i.d card a aljihun rigarsa ya nuna musu tare da faɗin. “Ku yi haquri mun shigo muku har bedroom ba da izinin ku ba, mu ma ba’a son ranmu ba ne, mun yi ta knocking baku ji mu ba shiyasa muka shigo. Jami’ai ne mu daga hukumar S.S ta ƙasa.” Ya kalli Daddy sannan ya cigaba da magana da faɗin. “Mun zo ne for arrest you bisa umarnin ɗanka Major col. Al’ameen Muhammad Tafida, akan laifin da in mun je office zaka ji.” Abba ya waro ido cikin tashin hankali amma bai yi magana ba. Daddy ya yi murmushi sannan ya goge hawayen fuskarsa ya tashi ta haɗa tafukan hannayensa ya yi tafi sau uku sannan ya ce. “Wannan ya tabbatar mun da zargin da nake na Ameen ne ke bibiyar wannan al’amarin, sannan kuma shi ya saka a ɗauke Sadik saboda ya tseratar da rayuwar shi. Ko yanzu na faɗi na mutu zan yi farinciki ban yi asarar haihuwar ɗa ɗaya tamkar da dubu ba, na bar ɗan da ƙasa da duniya zata yi alfahari da shi. Duk ɗan da ya kama ubansa da laifi sannan bai yi ƙasa a gwiwa ba ya sanar da hukuma domin a kama shi a hukunta shi hakan ya tabbatar ba zai ƙyale duk wanda ya kama da laifi ba kowa ye. Lallai Ameen ya cika jami’in tsaro na gari wanda ƙasar mu take buƙatar irin su. I’m proud of that, zan mutu da farincikin haka.” Daddy ya dubi su Mama ya ce. “Zan iya ce muku sai watarana, domin ka’idar wannan ƙungiyar da nake ciki ne duk wanda ya fallasa sirrin su ga wasu sai an kashe shi, ni kuma na baku labarinta yanzu, dan haka a daren yau zasu tsotse jinina sai dai a wayi gari aga gawata, dan haka ina neman yafiyar ku gaba-d’aya akan baƙin ciki da damuwar dana saka ku a ciki.” Ya ƙarasa gaban Mama ya yi kneel dawn ya ce. “Ki nema mun yafiya a gurin gwarzon ɗana Ameen.” sannan ya matsar da bakinsa daf da kunnenta cikin raɗa ya ce. “Ina neman alfarmar ki aurawa Ameen Neehal, domin tun kafin ta yi candy ya sanar mun yana son ta, nina nuna masa ba zan ba shi ita ba saboda wani dalilina. Dan Allah ki mun wannan Alfarmar, koda zata kasance alfarma ta ƙarshe da zaki mun a rayuwarki.” Daga haka ya miƙe ya fice daga ɗakin cikin sauri ba tare da kuma kallon kowa ba, mutanen nan suka mara masa baya da sauri. Su Aunty sun shiga cikin tashin hankali ba kaɗan ba da jin furucin Daddy na wai ƴan ƙungiyar su zasu kashe shi, kuka Neehal ta fashe da shi mai ƙarfi tana kiran sunan Daddy. Hajiya kuwa gaba-d’aya bata cikin hayyacinta ta ma daina fahimtar abun da yake faruwa, Aunty A’isha ma kuka take sosai. Abba ya tashi da sauri ya bi bayan su Daddy. Mama ta miƙe tsaye tare da dafa bango ta ce. “Ina wayata in kira Ameen, na san yana can cikin damuwa da baƙin cikin abun da ubansa ya aikata na son zuciya da son duniya, ku kira mun ɗana in ji a halin da yake ciki, kar zuciyarsa ta buga saboda baƙin ciki. Dan Allah ku kirawo mun shi in ji lafiyarsa.” Sai ta tsugunna ta fara laluben wayarta a ƙasan ɗakin cikin fitar hayyaci, ta samu ta ɗauko wayar amma sai wayar ta zubce daga hannunta ta faɗi saboda rawar da jikinta yake yi. Ta miƙe tsaye tana jin kamar ana wujijjigata a cikin iska saboda juyawar da kanta yake mata. Lokaci ɗaya ta ji numfashinta ya tsaya cak, idanunta sun daina ganin komai sai duhu, a hankali ta yi baya luuu ta faɗi ƙasa babu alamar numfashi a jikinta……….✍️