NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

To masoya makaranta littafin Neehal, anan zamu dakata sai bayan Sallah idan mai kowa mai komai ya kai mu zamu cigaba da yardar Allah. Allah yasa muga wannan wata na Ramadan lafiya, Allah ya karb’i ibadun da zamu yi yasa muna cikin ‘yantattun bayinsa da zai ƴanta a cikin wannan wata mai albarka. Allah ya bawa dukkan Musulmi lafiyar yin ibada, Amin ya Allah.????

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

7️⃣2️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

……….Cikin dare Mama ta farka, Aunty Sadiya da idanunta biyu har lokacin ta tasa ta a gaba ta tashi da sauri ta kira likita, ya zo ya ƙara duba jikin Maman, Alhamdulillah an samu numfashinta ya daidaita yana fita da kyau, hakan yasa suka cire mata Oxygen ɗin suka yi mata allurar bacci dan ta ƙara samun relief. Sai a lokacin Aunty Sadiya ta ji ta samu nutsuwar zuciya ganin Maman tana numfashi normal. Da Asuba Mama ta kuma farkawa, alhamdulillah ta farka cikin nutsuwarta, kanta ne kawai ta ji yay mata nauyi da ƙirjinta da har yanzu take jin ciwo a cikin zuciyarta. Ta shiga bin inda take da kallo abubuwan da suka faru na dawo mata cikin kwanyarta. Ta runtse ido saboda wani ɗaci da ta ji ya ƙaru a cikin zuciyarta akan na da. Ƙoƙarin tashi zaune ta yi cikin ƙarfin hali da na zuciya duk da yanda take jin jikinta kamar ba nata ba. Jin motsinta Aunty Sadiya dake kan darduma ta juyo ta kalli gadon da take da sauri, miƙewa ta yi ta ƙarasa gaban gadon tana faɗin. “Sannu Yaya.” Mama ta gyaɗa mata kai cikin dauriya tana ƙoƙarin tashi zaune, da sauri Aunty Sadiya ta taimaka mata ta tashi sannan ta saka mata pillow a bayanta. Kanta ta dafe da hannunta tana sassauke numfashi cikin muryar dake fita da ƙyar ta ce. “Sadiya ina Neehal da Ameen?” Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. “Suna gida, anjima kaɗan idan gari ya waye zasu zo.” Ta gyaɗa mata kai sannan ta ce. “Suna lafiya dai ko?” Aunty Sadiya ta ce. “Lafiya k’alau, jiya har wajen ɗaya na dare Ameen yana nan, na san nan da anjima zaki gan shi ya dawo.” Mama ta lumshe idonta ta ce. “Hajiya fa?” Aunty Sadiya ta ce. “Suna tare da Ya A’isha da Neehal.” Mama bata kuma magana ba sai hannunta data ɗora a kan ƙirjinta. Aunty Sadiya ta ce. “Sannu, Ya jikin naki? Bari na Doctor ya ce mun in kin tashi na kira shi.” Mama ta girgiza mata kai, sannan ta d’ago a hankali ta cire drip ɗin hannunta. A hankali ta ce. “Taimaka mun mu je toilet na yi alwala.” Aunty Sadiya ta ce. “Haba Yaya baki da lafiya fa, ki bari idan likita ya duba ki sai ki je, na san yanzu ko tafiya baza ki iya yi ba.” Mama ta girgiza kai ta ce. “Zan iya Sadiya, ki bari na fara yin Sallar tukunna.” Aunty Sadiya bata kuma magana ba ta kama ta, ta sauko daga kan gadon ta raka ta toilet. Ita kanta Maman ta san ƙarfin hali ne kawai irin nata, amma ba ƙaramin jiri take ji ba, tafiyar ma duk da Aunty Sadiya ta riƙe ta amma jinta take kamar zata faɗi. A zaune ta yi sallolin dake kanta da ƙyar, bayan ta idar Aunty Sadiya ta taimaka mata ta koma kan gadon ta kwanta. Sai a lokacin ta fita ta kira likita ya zo ya ƙara dudduba jikin Maman tare da yi mata faɗan ta rage tunane_tunane. Ya cewa Aunty Sadiya ta bata magungunan da ya rubuta mata jiya idan an siyo, amma ta fara shan koda tea ne first. Bayan fitarsa Aunty Sadiya ta dubi Mama ta ce. “Bari na yiwa Ya A’isha waya ta kawo ruwan zafi da kayan tea, jiya ba ma cikin nutsuwarmu babu abun da muka taho da shi, magungunan ma Yaya Rufa’i (Mijin Aunty A’isha) ne ya siyo su da ya zo, ya ce ba zai yiyu ki farka kuma ba’a siyo ba.” Mama ta jinjina mata kai kawai, amma bata jin zata iya saka wani abu a bakinta da sunan ci ko sha. Aunty Sadiya ta ce. “Dan Allah Yaya ki bar wannan tunanin, kin ji dai abun da Doctor ya ce, jininki ya hau sosai a cikin yini ɗaya kacal, inaga kuma kin ɗore da tunanin na kwanaki da yawa? Kuma kin san hakan already a matsayin ki na babbar Likita.” Mama ta buɗe idonta da suka yi kamar na masu shaye_shaye saboda cuta ta ce. “Ta yaya Zuciyata zata bar tunani alhalin an riga an dasa mata baƙin ciki, Sadiya Muhammad fa, Yaya Tafida mijina ne a cikin ƙungiyar matsafa, me….” Sai numfashinta ya sark’e ta fara tari, hakan yasa ta kasa ƙarasa abun da take son faɗa. A ruɗe Aunty Sadiya ta ce. “Dan Allah Yaya ki bar wannan maganar, mu yanzu ta lafiyarki muke, kin ga karki ƙarawa kanki wani ciwon akan wanda yake damun ki already.” Mama ta samu tarin ya lafa mata, cikin dashashshiyar murya ta ce. “Tunani ya zama dole Sadiya, dole in yi tunanin rayuwata ni da ɗana yanda zata kasance mana a gaba babu Muhammad, da kuma yanda baƙin fenti ya barwa rayuwarmu zai mana illa.” Aunty Sadiya ta ce. “Insha Allahu zaku cigaba da rayuwarku tare da Yaya Tafida cikin kwanciyar hankali.” Mama ta juyo idanunta a kanta ta ce. “Ta yaya? Ko kin manta abun da ya faɗa kafin su tafi na sharad’in ƙungiyar su?” Aunty Sadiya ta ce. “Ban manta ba, dan nima jiya da zullumun abun na kwana, amma kuma a yanzu na san babu abun da ya faru da shi, saboda da wani abu ya faru da tuni mun samu labari.” Mama ta ce. “Idan ma ƴan ƙungiyar basu kashe shi ba ai hukuma baza ta taɓa barin shi ba, dole ne a yanke masa hukunci dai-dai da abun da suke aikatawa.” Aunty Sadiya ta ce. “Ni kuma bana tunanin hakan, domin idan kika duba labarin da Yaya Tafida ya bamu gaba-d’aya ba’a cikin son ransa yake zaune a cikin wannan ƙungiyar ba, tun asali saka shi aka yi ba bisa yardar shi ba, hasalima tsaface shi akai yanda ba zai iya barin cikin ta ba.” Mama ta ce. “Hmmmm, ke kika san wannan Sadiya, amma su hukuma basu san haka ba, kuma na shiga ban ɗauka ba bata fitar da b’arawo.” Aunty Sadiya ta ce. “Haka ne, amma Insha Allahu Ubangiji zai fitar da shi, tunda ya ga zuciyarsa.” Mama ta girgiza kanta kawai cikin takaici, tana jin dama Ubangiji ya karb’i ranta kafin zuwan wannan mummunar ranar. Aunty Sadiya ta cigaba da magana. “Yaya Fateemah a da na fiki takaici da baƙin cikin halin Yaya Tafida, har ji na yi na tsatse shi bana son ganin sa, amma a jiya tsanar ta juye zuwa tsantsar tausayi. Na tabbata duk halin damuwa da baƙin cikin da muke ciki ya fi mu, domin shi abun a kansa yake faruwa. Yaya Fateemah akwai ciwo ba ƙarami ba kana aikata abu a rayuwarka amma kuma zuciyarka bata son abun da kake aikatawar, irin wannan abun ba ƙaramin ciwo ne da shi a zuciyar ɗan Adam ba.” Mama zata yi magana suka ga an turo ƙofar ɗakin an shigo. Aunty A’isha ce hannunta ɗauke da tea flaks da leda. Mama ta bita da kallon mamaki ganin har ta zo cikin mintuna ƙalilan bayan yi mata waya. Ta ƙaraso cikin ɗakin suka gaisa da Aunty Sadiya bayan ta ajiye kayan hannunta, sannan ta ƙarasa bakin gado ta zauna a wajen kan Mama, ta yi mata ya ya jiki bayan sun gaisa. Mama ta ce. “A’isha har kin fito kin zo a safiyar nan?” Aunty A’isha ta kalli Aunty Sadiya ta ce. “Dama ina cikin asibitin nan gurin Neehal.” A razane Mama ta ce “Gurin Neehal kuma? Mai ya same ta?” Tana ƙoƙarin tashi ta yi maganar. Aunty A’isha ta taimaka mata ta tashi zaune sannan ta ce. “Ba wani abu ba ne, suma ta yi, lokacin muna ƙoƙarin kawo ki asibiti, shine muka haɗo ku duka muka kawo, amma yanzu jikin nata alhamdulillah da sauƙi, nama tashe ta ta yi Sallah, ina jin allurar da akai mata ce bata sake ta ba sai ta koma baccin, amma zuwa anjima ma muna saka ran su bata sallama.” Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce. “Allah sarki Daughter, Allah ya nuna mun ƙarshen wannan jarrabawar taki.” Aunty A’isha ta ce. “Insha Allahu komai ya zo ƙarshe.” Mama ta ce. “Allah yasa, ina Hajiya fa?” Aunty A’isha ta ce. “Tana can gurin Neehal, ina komawa zaki gan ta, ta zo, dan dake ta kwana a cikin ranta, ta tafi gida ma jiya ta dawo yau ƙi ta yi ta ce anan zata kwana.” Jinjina kai kawai ta yi tare da lumshe idonta. Aunty A’isha bata jima ba ta tafi, ta ɗauki wata Nurse a waje suka tafi tare zata dawo tare da Hajiya. Hajiya data zo taga yanda Mama ta rame ta zabge sai ta saka kuka, da ƙyar Aunty Sadiya ta lallame ta ta bar kukan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button