NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ƙarfe bakwai saura na safe Ameen ya shigo ɗakin. Lokacin bacci ya fara fizgar Mama sakamakon Magungunanta da ta sha. Hajiya ta bar ɗakin ta koma wajen Neehal saboda Aunty A’isha data je gida dan ɗebo musu abubuwan buƙata na amfani. Aunty Sadiya ta amsa sallamar da ya yi tana kallon sa ganin yanda shima ya fita hayyacinsa a kwana ɗaya, kana ganin sa kaga wanda yake cikin damuwa. Ya gaishe ta, tare da tambayar ta jikin Mama. Kamar Maman ta ji sai ta buɗe idonta dake cike da bacci tana kallon sa. Ya ƙarasa bakin gadon ya zauna tare da kama hannunta yana tambayar ta jikin ta cikin tsananin kulawa. Ta amsa masa da sauƙi. Ya sauke ajiyar zuciya tare da damk’e hannunta a cikin nasa. Duk da baccin da Mama take ji amma haka ta daure ta tashi zaune tana ciccize leb’e, domin tana buƙatar tattaunawa da ɗanta a halin yanzu. Ta yi gyaran murya haɗe da ɗan tari ta ce. “Ameen, ka ji abun da Dad yake yi ko?” Taune lip ɗinsa ya yi da ƙarfi tare da sakin numfashi alamun maganar ta taɓa masa zuciya ba kaɗan ba. A hankali ya ce. “Na daɗe ina zargin shi Mum, a jiya kuma na tabbatar.” Mama ta ce. “Amma mai yasa baka taɓa faɗa mun ba Ameen? Kuma ta yaya ka gane?” Ya ƙara taune lip ɗinsa sannan ya ce. “Na ɓoye miki ne saboda ban tabbatar ba, bana son na faɗi abun da ba shi ba ne. Ta yanda aka yi na gane kuwa tun lokacin da Miemerh ta zo gidana time ɗin da Hafsah ta samu miscarriage aka shigo gidan dan cutar da ita, a vantlation ɗin ɗakin da take na ga wani ƙaramin card, kuma na Daddy ne. A lokacin na shiga ruɗu ba kaɗan ba, amma duk da haka ko kusa ban yi tunanin shi ba ne, na yi tunanin dai wani wanda ya san shi ne ko a cikin abokansa. Sai dai daga baya dana zauna na yi dogon nazarin ta yanda aka shigo gidan an yi amfani da keys ɗin gidan ne, kuma Daddy ne kaɗai yake da su. Tun daga sannan na fara saka ido akan dukkan al’amuransa tare da zurfaffen bincike akan duk waɗanda yake mu’amala da su. A lokacin bana zargin sa, na fi zargin wanda yake mu’amala da su ne suke son cutar da shi ta hanyar Neehal. Sai dai duk yanda naso gano komai hakan ya gagara duk da bani kaɗai nake aikin ba, ni da wasu Freind’s ɗina ne da suke aiki a hukumar SS ta ƙasa. Ba ƙaramin shiri ne da su Daddy ba na ɓoye dukkan sirrinsu, ta yanda ko kana bibiyar su baza ka iya gano su da wuri ba. Daga baya ne wata dabara ta zo mun, lokacin da za’a yi bikin Miemerh da Sadik sai na saka a dinga bibiyar mun al’amarin shi, cikin ikon Allah kuwa haƙana ya cimma ruwa, domin kuwa na yi nasarar gane ana bibiyar rayuwarsa musamman lokacin da aka shiga satin bikin. Da kaina na yi badda kama na dinga bibiyar masu bibiyar rayuwar tasa, ana i gobe za’a sace shi na yi nasarar sace na’urar ɗaya daga cikin masu bibiyar tasa. Lokacin da zai tafi gurin kamu ne, a gurin kamun suka b’uya a wani waje amma sun kakkasu kowa da kafar da ya samu ya buyan. Da wannan damar na shammaci ɗaya daga cikinsu na shak’a masa powder bacci, ko 2 minutes bai yi ba ya langwab’e. Na lalabo aljihunsa na ɗauki wannan na’ura dana lura kowa a cikinsu yana da ita. Da ita na gane dukkan shirinsu akan kashe Sadik ana i gobe d’aurin Auren sa, hankalina ya tashi ba kaɗan ba, daga nan muka ƙara duk’ufa akan bincikar al’amarin. Nina tura yarana suka ɗauke Sadik a lokacin da su kuma suke daf da zuwa kashe shi. A lokacin ne kuma na gane da hannun Daddy a cikin al’amarin, ta yanda ya gigice da ɓatan Sadik ɗin. Da kuma yanda a cikin week ɗin kullum sai ya fita da daddare, ba ya fita da Mota amma yana yin ƴar tafiya daga sai a zo an ɗauke shi a Mota, ina yin ƙoƙarin bin su a baya a daren a kullum idan aka ɗauke shi, amma tafiya kaɗan sai in ga sun ɓace mun bat in neme su in rasa. A jiya bayan na ɗauko Meimerh daga gurin nan na yi tracked Numbers ɗin Daddy, gaba-ɗaya location ɗin da suke nuna mun nesa kaɗan ne da gurin da na ɗauko Meimerh, hakan ya tabbatar mun da zargi na. Dad yana dawowa gida officer Gobir ya kira ni ya sanar mun kamar yadda na ce masa, ni kuma na kira hukumar SS nan da muke aikin tare na ce su je su tafi da shi su tuhume shi.” Ya yi shiru na wasu sakanni yana sauke numfashi idonsa sun kada sun yi jajur. Cikin wata irin murya ya cigaba da magana. “Na yi takaici da baƙin cikin ganin ranar jiya a rayuwata, na ji dama Ubangiji ya ɗauki raina in huta da kunyar duniya a lokacin da halin Dad ya bayyana ga mutanen cikinta, na yi fata da roqon Ubangiji ya ɗauki rana babu a dadi, na yi fatan ace mafarki nake zan farka. Ban taɓa tunanin koda Dad zai yi wannan harkar za’a haɗa baki da shi a cutar da rayuwar Miemerh ba, tare da kisan Mutanen da basu ji ba, ba su gani ba. Na ji kamar in kashe kaina a lokacin da na yi realised Mahaifina matsafi ne, Mahaifina ɗan ƙungiyar asiri ne masu shan jinin…….” Sai ya kasa ƙarasawa numfashinsa ya fara wata irin fizga, hawaye kawai Mama take yi tunda ya fara magana. Hannunta na rawa ta kwantar da kansa akan ƙafaɗarta saboda ganin abun da ta manta rabon da ta gani a tattare da shi, baza ma ita tuna ranar data ganin ba wato hawaye. Dama abun da take gudu kenan damuwar ɗanta, ta san duk duniya babu wanda zai kaishi baƙin ciki da takaicin halin Daddy, ko ita baza ta fi shi ba tunda ita mijinta ne, a duk lokacin data so zata iya sauya miji a rayuwarta, amma shi kuma fa? Mahaifinsa ne, abun da ba’a taɓa iya sauyawa a rayuwa, kuma paint ɗin abun da Daddy ya yi shi zai ta bibiya har ƴaƴa da jikokinsa. Ta ɗora hannunta akan lallausar sumar kansa tana shafawa cikin alamun rarrashi, ɗayan hannun kuma tana goge masa hawayen fuskarsa duk da itama hawayen take yi. Aunty Sadiya dake kallon su ta lumshe idonta cikin ƙoƙarin mayar da hawayen tausayinsu da ya cika mata ido.

Sun yi 5 minutes a haka sannan Mama ta d’aga kanshi daga jikinta, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya share mata hawayen fuskarta ita ma. Murmushin ƙarfin hali Mama ta yi tare da kissing hannun nasa. Cikin sanyin murya sosai ta ce. “Ka yi haquri Ameen, ƙaddara ce Ubangiji ya ɗora mana, shi ma Dad ba son ransa ba ne ƙaddararsa ce a haka. Ka rage wannan damuwar da nake gani a cikin idanunka, kar wani ciwon ya kama mun kai, bana son in rasa ku kai da Neehal, tunda na tabbatar na rasa Daddy har abada. Sannan ina maka godiya da jinjina akan yanda ka sadaukar da lokacin ka gami da lafiyarka akan kare rayuwar marainiyar Allah, Na gode sosai Allah ya biya ka da Aljannah.” Ta ƙarashe zancen da shafar kuncinsa. Ya sauke numfashi tare da gyaɗa mata kai, ya motsa labbansa a hankali ya ce. “Amin.” Aunty Sadiya ta dube shi ta ce. “Ameen ka rage jin zafin Daddy a cikin ranka, domin shi ma ba laifinsa ba ne hakan ta kasance da shi, hasalima jefa shi cikin wannan harkar ba bisa son ransa da yardarsa ba.” Ameen ya kalle ta cikin alamun tambaya amma bai ce komai ba. Aunty Sadiya ta jinjina kai sannan ta bashi kaf labarin da Daddy ya ba su. Ya lumshe idonsa yana sakin ajiyar zuciya, ko ba komai ya ji daɗi da ya kasance mahaifinsa ba bisa son ransa ya faɗa wannan mummunar harkar ba, amma kuma hakan ba zai saka a ce ba shi da laifi ba shi ma. Ya buɗe idonsa ya ce. “Duk da haka Dad ba zai taɓa fita daga cikin wannan case ɗin ba, domin case ne babba ba ƙarami ba, kuma a idon mutane da hukuma duk ɗaya yake da sauran ƴan ƙungiyar, tunda duk abun da suke aikatawa shi ma yana yi kuma a cikinsu yake.” Aunty Sadiya ta ce. “Jikina ya bani Insha Allahu zai fita, ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne.” Mama ta ce. “Ameen ka kira Abokinka waɗanda suka tafi shi ka ji yana lafiya, saboda jiya kafin ya tafi ya ce ƴan ƙungiyar zasu iya kashe shi saboda labarin su da ya sanar mana.” Aunty Sadiya ta yi ɗan murmushi a ranta ta ce. ‘Ashe har yanzu tsohuwar zumar tana nan.” Ameen bai yi musu ba ya ɗauki wayarsa ya kira abokin nasa kamar yadda Mama ta ce amma bai d’aga ba. Ya dube ta ya ce. “Daga nan can zan je, duk halin da ake ciki zan sanar muku.” Mama ta ce. “Allah yasa mu ji Alkhairi.” Suka amsa da Amin, sai dai shi Ameen ko kaɗan ba ya ji a ransa Daddy zai fita daga cikin wannan case ɗin. Har ya tashi zai tafi Mama ta tsayar da shi, ya koma ya zauna dan jin mai zata faɗa masa. Mama ta ce. “Ameen dama kana son Neehal tuntuni mai yasa baka taɓa sanar mun ba?” Ya yi shiru na wasu sakanni kansa a ƙasa sannan ya ce. “Na yi zaton baza ki amince mun ba, shi yasa na fara faɗawa Dad domin ya shawo mun kanki, shi kuma ya ce mun in bar maganar ba zai bani ita ba,ban kuma san dalilinsa na yi hakan ba, shi yasa kawai na haqura.” Mama ta ce. “Me zai saka in ƙi amince maka Son? Komai kake so a duniyar nan idan ina da shi zan baka, da ka faɗa mun da abu ɗaya zai saka bazan baka ita ba, idan ita ta ce baka so.” Ya yi shiru bai ce komai ba. Mama ta ce. “Tashi ka je, Allah ya yi maka albarka, ya jib’anci al’amuranka ya shirya ka.” Ya yi murmushi cikin jin daɗin addu’arta ya ce. “Amin Mum, Allah ya ƙara sauƙi.” Mama ta yi murmushi ta ce. “Ameen, ka biya ka duba Neehal ɗin kafin ka wuce.” Ya amsa mata sannan suka yi sallama da Aunty Sadiya ta yi masa kwatancen inda aka kwantar da Neehal ya tafi, yana jin zuciyarsa na masa sanyi kasancewa da ya yi da Mama, sai ya ji wani kaso na cikin damuwarsa na yayewa. Har lokacin da ya je dakin Neehal bata tashi ba baccinta take. Suka gaisa da Hajiya ta shiga tambayar sa ko shi ma cutar yake ne duk ya yi wani iri. Bai bi takan ta ba ya ƙarasa bakin gadon da Neehal take ya tsaya yana kallon ta, zuciyarsa na k’issima masa abubuwa da yawa a kanta. Ya yi kusan 10 minutes sannan ya yiwa Hajiya sallama ya tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button