NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Sai da sha ɗaya ta wuce sannan Neehal ta tashi daga baccin. Toilet kawai take je ta yi uzurinta ta kuskure baki ta fito ta cewa Aunty A’isha ta kai ta gurin Mama. Aunty A’isha ta ce ta bari a basu sallama mana, amma ta ƙi yarda harda kukanta, ganin haka yasa Aunty A’ishan ta raka ta. Suna shiga ɗakin ta tafi da gudu ta rungume Mama dake kwance idanunta a lumshe. Mama ta buɗe ido ta ce. “Daughter, Ya jikin naki?” Cikin sanyin murya tana duban yanda Maman ta zabge lokaci ɗaya ta ce. “Da sauqi Mama, ya naki?” Mama ta ce. “Alhamdulillah.” Sai kuma ta fara kuka. Aunty Sadiya ta ce mata. “Kukan na mene ne kuma Neehal?” Bata yi magana ta cigaba da kukanta. Mama ta ce. “Me ya faru?” Cikin kuka ta ce. “Ki yi haquri Mama, na san ni ce sanadin wannan ciwon naki, saboda…….” Cikin sauri Mama ta katse ta da faɗin. “Wanne irin shirme ne wannan Neehal, bana hana ki irin waɗannan maganganun ba, ciwo Ubangiji ne ke ɗora shi kuma shi ya ɗora mun. Ki bar kukan hakan kin ji ƴar albarka, ke ba lafiya karki ƙarawa kanki wani ciwon.” Ta gyaɗa mata kai tana share hawayenta. A ranar aka sallami Neehal duk da dama already ta sallami kanta, sai magungunanta da zata cigaba da sha. Ranar haka aka dinga zuwa duba Mama, ƴan’uwa da abokan arzik’i ko ta ina, ana kuma yi musu murnar bayyanar Neehal. Da yawan mutane sun ɗauka damuwar ɓatan Neehal ce ta sakawa Mama ciwo har ta kwanta a asibiti. Kwanan Mama huɗu aka sallame ta daga asibitin, Alhamdulillahi jikin nata ya yi sauƙi, amma cikin zuciyarta cike take fal da damuwar abun da mijinta ya aikata da zullumin makomar rayuwarsa, duk da dai har yanzu abun da ya faɗa na sharad’in ƙungiyarsu akan kisan duk wanda ya fallasa sirrinsu har yanzu bai tabbata a kansa ba. Su Uncle Ahmad da Abba da Uncle Mahmud suna ta cuku_cuku akan case ɗin Daddy, amma abun ya ci tura ko damar ganin sa basu taɓa samun yi ba. Ameen kuwa ya yi busy suna ta aikin ganin sun kamo sauran ƴan ƙungiyarsu Daddy. Duk inda Daddy yake tunanin za’a ga wani daga cikin ƴan ƙungiyar an je duk ba’a same su ba, gaba-d’aya sun ɓace bat tamkar aljanu, da alama su ma suna can suna shirin ko ta kwana akan farautar su da suka fahimci ana yi. Babu wanda yasan halin da Daddy yake ciki sai ƴan’uwa na jiki_jiki da ya zama dole, ko ƴan dubiya sun tambaye shi idan an zo su Mama sukan san abun da zasu faɗa na rashin ganin shi da ba’a yi ba, wanda zai saka baza a yi tunanin ko da akwai wata matsalar ba………✍️

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

7️⃣1️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

Barkanmu da Sallah, fatan an yi Sallah lafiya? Allah ya maimaita mana, Amin.

………Aunty Sadiya ta yi kanta tana kiran sunanta tare da jijjigata. Neehal ta faɗa jikinta ta rungume ta tana faɗin. “Please Mama wake up, karki mutu ki bar ni, dan Allah Mama ki tashi karki tafi ki bar ni., Mama! Mama!…” Aunty A’isha ta zo ta janye ta tare da rungume ta, ta shiga rarrashinta cikin dauriya. Dan itama hankalinta ba a ƙaramin tashe yake ba na ganin halin da Maman take ciki, ta umarci Zulai dake tsaye ta ɗauko ruwa mai sanyi a shafawa Maman ko Allah zai sa ta farfaɗo. Hajiya kuwa bata motsa ba, dan bata jin idan ta tashi ƙafafunta zasu iya ɗaukar gangar jikinta balle har su yi tafiya, sai salati take yi tare da duk addu’ar da ta zo bakinta cikin matuƙar gigita na wannan mummunan al’amarin. Aunty Sadiya ta bar jikin Mama ta ɗauko wayarta ta shiga kiran Numbern Ameen, tana shiga amma ba ya ɗauka. Aunty Sadiya ta karɓi ruwan da Zulai ta kawo ta fara shafawa Mama a fuska, amma ko alamar zata motsa ba su gani ba. Hankali a tashe suka ɗauke ta sukay Mota dan kai ta asibiti. Ganin yanda aka ɗauki Mama kamar gawa ya ƙara tayar da hankalin Neehal, stress ɗin sun mata yawa, ga tashin hankalin tafiyar da aka yi da Daddy ga halin da Mama take ciki ga kuma dunbin damuwar dake cunkushe a cikin zuciyarta, hakan yasa ta sume itama. Sai daukar ta aka yi aka haɗa da Mama aka kai su asibitin.

AFTER TWO HOURS

HOSPITAL

A hankali Neehal ta buɗe idonta tana kallon saman ɗakin da take na wasu sakanni, sannan ta juyo da kanta gefen damanta domin fahimtar gurin take. Aunty A’isha dake zaune a kujerar gaban gadon marasa lafiya ta rafka tagumi ta sauke ajiyar zuciya tare da tashi tsaye cikin sauri ta ƙarasa kusa da Neehal ta kama hannunta ta ce. “Sannu Neehal, kin tashi? Bari a kira Doctor.” Neehal ta d’aga mata kanta dak’yar, tana so ta tambaye ta ina Mama amma kuma ta kasa motsa bakinta da niyyar magana, ga wani irin ciwon kai da kanta ke yi mata. Aunty A’isha ta fice daga ɗakin, Hajiya dake zaune akan sallaya ta taso ta shiga yiwa Neehal sannu, Neehal ta gyaɗa mata kai kawai tare da mayar da idanunta ta lumshe. Har lokacin tana jin nauyin da ƙirjinta da yay mata gami da zafin zuciya. Bayan mintuna kaɗan Aunty A’isha suka dawo tare da wani likita, ya dudduba Neehal ɗin tare da yi mata ƴan tambayoyi, ta amsa masa da kai kawai ta nuna masa kanta da ƙirjinta a matsayin inda yake yi mata ciwo. Ya cire mata drip ɗin hannunta sannan ya cewa Aunty A’isha ta bata magungunan da suka siyo mata, amma su bata ko da tea ne ta fara sha. Zai je ya haɗo allura ya dawo yay mata. Sukay masa godiya shi kuma yay mata addu’ar samun sauƙi. Aunty A’isha ta taimaka mata ta tashi zaune ta kuskure mata baki, sannan ta haɗa mata tea ɗin ta bata ta sha. Da ƙyar Neehal take had’iye tea ɗin saboda ɗacin da take jin yay mata a bakinta, kaɗan ta sha ta ɗauke kanta. Aunty A’isha ta bata magungunanta ta sha sannan ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Ta dubi Aunty A’isha cikin muryar marasa lafiya ta ce. “Ina Mama?” Aunty A’isha ta ce. “Tana Emergency na asibitin nan sun bata gado, amma jikin nata da sauƙi yanzu.” K’walla ta taru a idon Neehal, kamar zata yi kuka ta ce. “Ina son na gan ta.” Aunty A’isha ta ce. “Gurin da take ba’a bari a shiga, kin ga Hajiya ma tun d’azu take naci sun hana ta shiga, sun ce sai ta farfaɗo za’a samu ganin ta, amma Sadiya tana gurin, da zarar ta farfaɗo zata kira mu ta sanar mana.” Neehal ta fara hawaye amma bata ce komai ba. Aunty A’isha ta ce. “Mene abun kuka kuma ke da baki da lafiya? Ki kwantar da hankalinki zata samu lafiya Insha Allah, karki saka damuwa a ranki ki ƙarawa kanki ciwo.” Neehal ta gyaɗa mata kai sannan a hankali ta ce. “Ƙarfe nawa? Ina son na yi Sallah Aunty.” Aunty ta ce. “Ƙarfe tara na dare, mu je in kaiki toilet ki yi alwala ko in kawo miki ruwan nan ki yi idan baza ki iya tafiya ba?” Ta taune lip ɗinta sannan ta ce. “Zan iya zuwa toilet ɗin.” Aunty A’isha ta taimaka mata ta tashi da ƙyar ta kai ta toilet ɗin ta yi tsarki sannan ta ɗauro alwala suka dawo ɗakin ta yi Sallar Magriba da isha’in dake kanta a zaune.


Ameen tun bayan da ya kawo Neehal gida ya koma gidansa ya kulle kansa a ɗaki ya cigaba da binkicen da yake hankalinsa a matuƙar tashe. Gabansa na faɗuwa ƙirjinsa na dokawa a million saboda fargaba. Baya son abun da yake zargi ya tabbata. Yana jin Hafsah tana ta yi masa knocking amma bai bi ta kanta ba, Sallar la’asar ce kawai ta fitar da shi daga gidan zuwa masallaci, yana dawowa ya koma ɗakin ya ƙara rufe kansa. Wannan karon sai da ya yi wanka saboda uwar zufar da yake haɗawa. Bayan ya fito ya ɗauki wayarsa ya kira wani suna magana yana lallatsa laptop ɗinsa, da alama tare suke aikin da wanda yake wayar da shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button