NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ikon Allah ne kawai ya kai Ameen asibitin dan baya cikin nutsuwarsa ko kaɗan. Aunty Sadiya ya kira ta faɗa masa section ɗin da suke. Ya buɗe Mota da ƙyar ya fito yana jin jikinsa kamar ba nasa ba saboda damuwa. Cikin kulawa da tausayawa Aunty Sadiya ta tarb’e shi, kama hannunsa ta yi ta zaunar da shi sannan ita ma ta zauna. A hankali ta ce. “Ameen! Ka ga yanda ka koma kuwa? Kamar wanda ya yi jinyar shekara guda, ga jikinka na ji shi ya yi wani irin zafi.” Lumshe idonsa ya yi bai ce komai ba. Cikin tausayawa Aunty Sadiya ta ce. “Ka yi haquri Ameen, haka rayuwa take cike da kalubale da jarrabawa, damuwa baza ta taɓa maka maganin abun da ke damun ka ba sai dai addu’a.” Gyaɗa mata kai ya yi a hankali sannan ya motsa labbansa da ƙyar ya ce. “Ina Mum da Miemerh?” Aunty Sadiya ta ce. “Neehal tana cikin asibitin nan amma ba’a nan wajen ba, Ya A’isha da Hajiya suna tare da ita, Yaya Fateemah kuma tana cikin ɗakin nan.” Ta ƙarashe zancen da nuna masa ɗakin da Mama take. Cikin mamaki ya buɗe idonsa yana kallon ɗakin bugun zuciyarsa ƙaruwa. Aunty Sadiya ta ce. “Damuwar data same ta lokacin ɗaya ce yasa har ta suma, amma zuwa yanzu Doctors sun shawo kan matsalar har ta samu bacci, bana son ka ƙara tayar da hankalinka akan tashin hankalin da kake ciki already, shi yasa da muka yi waya ban sanar maka ba.” Bai jira jin ƙarashen zancen Aunty Sadiyan ba ya miƙe ya nufi ɗakin cikin sauri. Ya ƙarasa gaban gadon da take ya ƙura mata ido, cikin zuciyarsa yana jera mata addu’ar samun lafiya. Yayin da tashin hankali da damuwar da yake ciki ya ninku ganin halin da Mama take ciki. Ya san ya rasa Daddy a rayuwarsa dan hukuma baza ta taɓa barin shi ba, koda ba’a kashe shi ba zai ƙare rayuwarsa a prison ne, amma ba zai so ya rasa Mama ba Mace mafi soyuwa a gare sa, Mahaifiyarsa mai tarin alkhairi ga duk wanda ya rabe ta. Ya ɗora hannunsa akan nata a hankali tare da lumshe idonsa da suka yi jajur yana kukan zuci. Daddy bai musu adalci ba, me yasa ya faɗa wannan mummunar harkar da har su koma ga mahaliccinsu tabon abun da ya aikata ba zai bar rayuwarsu ba? Haka ya zauna a gaban Mama yana ta tunane_tunane wanda yake ƙara masa radad’i da k’uncin zuciya. Da wanne ido zai kalli Neehal da ƴan’uwanta? Da wanne ido zai kalli Mama da nata ƴan’uwan? Da wanne ido zai kalli mutanen duniya da dangin Daddy akan abun da Dad ɗin ya aikata? Kunyar kowa yake ji har shi karan kansa, ji yake tamkar shi ya aikata wannan abun kunyar. Wani Doctor ne ya shigo ɗakin yasa shi dole ya fita, dan farko ma faɗa ya kama akan shiga ɗakin da ya yi, Aunty Sadiya ta bashi haquri ta ce ɗanta ne ya zo ganin ta. Ganin yanayin Ameen Aunty Sadiya ta shiga kwantar masa da hankali cikin kalamai masu taushi, da ƙyar ta lallaɓa shi ya koma gida wajen ɗaya saura na dare, dan da cewa ya yi a nan zai kwana, Aunty Sadiya ta ce ya baro Hafsat ita kaɗai ya koma gobe da safe sai ya dawo. Bai je yaga jikin Neehal ba saboda dare da ya yi, idan ya dawo da safen ya je ya duba ta.

Bayan Neehal ta idar da sallolin ta, ta koma kan gado ta kwanta, ba jimawa likitan ya dawo yay mata allurar bacci. Sai dai tashin hankali da damuwar da take ciki ya hana baccin zuwar mata, ko alamun shi bata ji. Ta lumshe idonta dai kawai ta fara tunane_tunane. Rayuwarta ta fara tunowa tun tana ƙarama lokacin iyayenta suna raye, bata iya tuno komai a lokacin sai fuskokinsu da wasu moment ɗinta tare da su kaɗan. Ta tuna yanda Aunty A’isha take bata labarin irin tarin k’aunar da mahaifinta yake mata, ta tuna farkon dawowarta hannunsu Mama da irin riqon gaskiya da amana da sukay mata, gami da tarin k’aunar da suke nuna mata. Mama ta nuna mata son da ko ɗan data haifa albarka, lokuta da dama tana danne farincikinta dana ɗanta domin nata farincikin. Ta tuna wasu lokutan baya lokacin tana ƙarama hankali bai gama isar ta ba, yanda take ɓatawa Ameen abubuwan amfaninsa tana sane, shi kuma babu haquri zuciya a kusa, yana ɗan maketa ta kwanta tay ta birgima tana ihu a ƙasa, Mama ta zo ta ɗauke ta, ta rarrashe ta, shi kuma tay masa faɗa ta ce ya daina dukar mata yarinya ƙarama, yay mata faɗa ko nasiha mana idan ta yi masa abu ba wai duka ba. Sai sun koma ɗaki sannan ita kuma Maman tay mata faɗan ta daina taɓa masa abubuwa. Ta tuna wata rana lokacin tana Jss Mama ta aike ta ta kira shi, ta tarar yana toilet yana wanka, ga laptop ɗinsa a ajiye akan bedside drower a kunne. Ta zauna ta dinga lallatsa masa tay masa barna ba kaɗan ba ta tay masa delete ɗin some important documents ɗinsa. Ranar ta gane Allah ɗaya ne a gurinsa dan tsallen ƙwado ya saka ta, wuni ta yi ranar kuka ƙafa ta ƙi takuwa. Yayin da Mama ta kusa cinye shi ɗanye da masifa. Hakan da Mama take yi ba wai tana yi dan ta saka ta raina Ameen ɗin ba ne, hasali ma bata yi masa faɗa koda wasa a gabanta sai dai wanda Allah ya yi ta ji ko ta gani, kuma kodayaushe cikin nuna mata ta girmama shi take, ita Maman tana yi masa haka ne dan tsoron kar su cutar da marainiyar Allah. Mama ta yi mata tarbiyya irin wacce ake fatan kowacce uwa ta yiwa ƴaƴanta, ta nuna mata respect ɗin na gaba da ita ko waye ne. Hakan yasa ko yaya mutum ya girme mata take girmama shi. Ta tuna Daddy da tarin k’aunar da ya nuna mata a duniyar nan, Daddy ko faɗa baya mata sai dai nasiha, a duk lokacin da zai mata magana cikin fara’a da zolaya yake mata, ko me take so a duniyar nan yana yi mata shi idan bai fi ƙarfin shi ba  kuma abun ba mara kyau ba ne. Ko laifi ta yiwa Mama ta san inta kamata zata yabawa aya zaƙinta gurin Daddy take gudawa ta buya, shi kuma ya bawa Mama haquri ita kuma yay mata faɗan har ta kuma. Tun tana ƙaramarta Mama ta koyar da ita yawaita karatun Alkur’ani da azkar da yin nafilfili wanda zuwa yanzu sun zamar mata jiki, uwa uba ibadah da nusar da ita son lahira fiye da duniya. Ita kuma me zata ce da waɗannan bayin Allah a rayuwarta? Sun zame mata garkuwa, bango, jigo da duk wani abun tunk’aho a rayuwa. Komai za su yi baza ta taɓa ganin baƙin su ba a idonta. Wannan abun da ya faru ta san ƙaddara ce Allah ya ɗora musu su duka. Ta tuna yanda dangin mahaifinta dana mahaifiyarta suka banzartar da ita, k’anin mahaifiyarta uwa ɗaya ya kasa yi mata riqon tsakani da Allah, saboda a ganinsa wahala zata zamar masa. Yanzu gashi da bata hannun nasa ya zama abun tausayi, dan ganin da tay masa lokacin bikinsu da Sadik ya zama kamar wani almajiri, duk ya fita hayyacinsa duniya ta fara koya masa hankali. Ta tuna ƙaddarar rayuwarta da yanda al’amura suka dinga tafiyar mata, ashe ƙaddarar ba ta_ta ba ce ita kaɗai, ta shafi mutane masu girma da daraja mafi soyuwa a gare ta, wadda duk matsayin da ta kai a rayuwar nan su ne sanadi. ‘Ya Allah ka fitar da Daddy daga cikin wannan al’amarin, Allah ka yafe masa dukkan abun da ya aikata maka ka shirya shi ya bar wannan mummunar hanyar, Allah ka saka masa akan sanya shi cikin wannan harka ba tare da yardarsa ba da bara_gurbin abokinsa ya yi sanadin shigar sa. Allah ka tashi kafaɗun Mama ka bata lafiya da ikon cinye wannan jarabawar daka ɗora mana.’ Ta faɗi haka a zuci tana zubar da hawaye. “Yaya…” Ta faɗa can ƙasan mak’oshi, ko yana ina ko a wanne halin yake ciki yanzu sai Allah. Da tunanin Ameen da halin da yake ciki allurar da akay mata ta yi aiki a jikinta bacci ya ɗauke ta wajen ƙarfe uku na dare………✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button