NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

7️⃣3️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

………..Washegarin da aka sallamo Mama ya kama Ranar Lahadi. Da safe su Maman suka hallara a part ɗin Mama a Falon sama dan tattaunawa akan al’amarin Daddy. Uncle Mahmud, uncle Ahmad, Kawu Musa, Abba da Mama. Kawu Musa da bai san abun da ya faru da Daddy ba sai a yanzu Abba ya sanar masa da komai. Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un kawai yake maimaitawa cikin tsananin d’imuwa. A ruɗe ya ce. “Subhallahi, wanne irin mugun aboki Alhaji yake tarayya da shi? gaskiya ya cika cikakken mara imani, matsiyaci ne na ƙarshe amma.” Abba ya ce. “Ai Ginyau ba ƙaramar cuta ya yi mana ba, dan ya yi sanadiyar ɓacin sunan zuri’armu.” Mama ta ce. “Hmm, idan bera da sata daddawa ma da wari, da a ce Yaya Tafidan bai bi shi ba ai bai isa ya ɗauke shi ya kai shi ba, ko kuma yana zaune a gida ya saka shi a cikin ƙungiyar ba.” Kawu Musa ya ce. “Kar ki ce haka Hajiya, babu ta yanda za’a yi dan mutum ya ce maka ka zo ku je wani guri ka yi tunanin a wannan mummunar hanyar zai saka ka, ko da zai kaika gurin irin waɗannan mutanen baza ka taɓa kawowa a ranka saka a cikinsu za’a yi ba, kuma idan har gaskiya ne abun da Alhaji Tafida ya faɗa to duk abun da ya aikata a cikin wannan ƙungiya ba’a hayyacinsa ya yi ba, tunda tsaface shi suka yi. Duk abun da ya aikata na saɓon Allah alhakin yana kan waɗanda suka saka shi a ciki ko a gurin Ubangiji, domin ba shi da yanda zai yi ne a dole yake aikatawa, kuma shi ma ya ce abun yana damun sa. Dan haka yanzu dole mu san yanda za’a yi ya fito daga hannun hukuma sannan kuma ya bar cikin wannan ƙungiyar. Ita kuma Neehal wannan abubuwan da suka dinga samun ta sanadiyyar shi Alhaji Tafidan ba laifin kowa ba ne sai mu danginta, domin da mun riƙe ta a hannunmu babu ta yanda za’a yi wannan al’amarin yakasance a gare ta. Watsi da ZUMUNCI da gudun wahala na ƴan’uwan mahaifinta da mahaifiyarta duk shi ya janyo mata, banda haka ta yaya har za’a ce yayar kishiyar mahaifiyarka ce zata riƙe ka banda ma da mutunci sosai a tsakani, alhalin da danginka a raye. Su suna can sun saki baki tunda yarinya ba’a hannunsu take ba babu ruwansu da wahalarta koma me zai faru da ita ya faru basu da asara. Bacin su kuma wahalar da mahaifinta ya yi da su.” Uncle Mahmud ya ce. “Malam Musa da zancenka gaskiya, amma duk da haka Ubangiji ne ya ƙaddara mata hakan zata faru da ita.” Kawu Musa ya ce. “Haka ne, amma komai yana da sanadi a rayuwa, rashin ZUMUNCI ba ƙaramin abu ba ne, wanda bai yi shi a duniya ba fa aka ce zai yi shi a wuta. Yanzu da ace tana hannunmu mu danginta da Alhaji Tafida ya faɗa wannan harkar ai baza su ce ya je har inda take ya cutar da ita ba, tunda kamar yadda suka faɗa ba shi yake ciyar da ita ba da sauransu.” Abba ya ce. “Haka ne Malam Musa zancenka dutse, na fahimci abun da kake nufi da maganar ka da kuma abun da kake son faɗa. Mutane ne yanzu sun mayar da zumunci na ganin ido da kuɗi, zumuncin Allah amma ba’a son yin sa, kuma an mayar da hakan kamar ba komai ba.” Kawu Musa ya ce. “Ƴar guda ɗaya tal a duniya amma su kasa riƙe ta, bacin tarin Alkhairin da mahaifinta yay musu da yana raye. Amma kuma da yake Allah mai ƙudura ne ba ka ga yanda su Salisun suka koma ba yanzu gaba-d’ayansu. (Ƴaƴan Baffa, wanda ya riƙe Umma da Abba.) Sun zama abun tausayi, abun da zasu ci ma gagarar su yake yi, ita ɗin da suka so ta tagayyara gashi Ubangiji sai d’aga ta yake, wannan ƙaddarar data same ta ma Insha Allahu komai ya zo ƙarshe, kuma da ma rayuwar mumuni dole sai da jarrabawa. Wallahi idan kuka ga halin matsin rayuwar da Umar yake ciki sai kun tausaya masa, kuma shi ma duk alhakin marainiyar Allah da ya zalunta ne ya fara kama shi.” Mama ta jinjina kai ta ce. “Na gani tabbas, lokacin bikin Neehal da Sadik kamar ba shi ba, har wani tsufan dole ya yi.” Kawu Musa ya ce. “Ba dole ba, zaluntar Maraya ai ba wasa ba ne, ga kuma watsi da ZUMUNCIN Allah.” Uncle Ahmad ya ce. “Mutanen duniyar nan sai addu’a, ita dai wannan yarinya Allah yasa iya wahalarta kenan duniya da lahira, Allah ya bata miji na gari da zai riƙe ta da amana.” Gaba-ɗaya suka amsa da “Amin ya Allah.” Sannan suka koma hirar Daddy da yanda za’a yi ya fito, inda suka k’ark’are akan matsayar za su nemi abokin Ameen waɗanda suka tafi da Daddy dan su san ya za’a ɓullo wa abun.

Neehal tana kwance a ɗakinta tana tunanin rayuwa da bata rabo da shi Mama ta shigo ɗakin. Ta tashi zaune tana amsa sallamar da ta yi. Mama ta zauna a gefenta ta ce. “Neehal ban ga kin fito kin ci abinci ba.” Kamar zata yi kuka ta ce. “Mama bana jin yunwa ne, wai yaushe Daddy zai dawo?” Mama ta ce. “Ban sani ba Neehal.” Ta fara hawaye ta ce. “Mama dan Allah ki cewa su Abba kar su bari a kashe shi, ko kuma su cewa Yaya yasa waɗanda suka kama shi su sake shi.” Mama ta ce. “Al’amarin ba ƙarami ba ne Neehal, ke dai ki tay masa addu’a kin ji.” Neehal ta d’aga mata kai. Mama ta ce. “To share hawayen mu je ki ci abinci, ai ba zai yiyu ki zauna da yunwa ba.”

Bayan Azhar sai ga Mommy’n Hameedah fakal_fakal ta zo gidan, duk zaman da Mama ta yi a asibiti bata zo ba sai yau, yauma dan ta ji labarin abun da ya faru da Daddy ne a wajen Kawunsu k’anin mahaifinsu. Ta zo tay ta ƴan koke_kokenta akan abun da ya samu Daddy tare da borin kunyar abun da suka yiwa Neehal na mutuwa da samarinta suke yi. Daga Mama har Neehal babu wanda ya kula ta, sai da ta gaji dan kanta ta yi shiru. Da yamma Ahmad ya zo gidan. Lokacin Neehal bacci ma take Mama ta tashe ta. Tunda ta sakko ya ƙura mata ido ganin yanda ta rame ta ƙara haske, idanunta duk sun jeme alamun suna shan kuka. Ta zauna a ƙasa nesa da shi a hankali ta ce. “Ina yini?” Ya ce. “Lafiya k’alau Princess ya jiki? Ashe Mama ma bata da lafiya?” Ta ce. “Da sauqi, ita ma Maman ta ji sauƙi Alhamdulillah.” Ya ce. “Masha Allah, Allah ya ƙara afuwa, wallahi ban sani ba ai da tuni na zo. Su Ummi suna muku ya jiki.” Ta ce. “Amin, ba komai, muna amsawa, ina Yarana?” Ya ce. “Yaranki suna nan k’alau, kullum sai rigimar zasu gurin Aunty suke yi.” Ta yi murmushi kawai. Ya gyara zama sosai cikin kulawa ya ce. “Princess bacin rashin lafiya akwai wani abu da yake damun ki, dan Allah ba dan ni ba ki rage saka samuwa a cikin ranki, ki miƙawa Allah dukkan alamuranki shi zai shige miki gaba, amma damuwa bata haifar da komai sai matsala, Please Princess ki mun wannan alfamar.” Gyaɗa masa kai Neehal ta yi cikin gamsuwa tare da yi masa godiya. Ya ɗan jima a gidan suna hira, anan yake sanar mata next week za kai kayan lefensa, tay masa fatan Alkhairi tare da fatan zaman lafiya a rayuwar auransu. Bayan Magriba su Abba suka gana da Kamal abokin Ameen, suka faɗa masa buƙatarsu da labarin da Daddy ya ba su na shigar sa cikin ƙungiyar. Ya jinjina abun sosai ya kuma yi musu alƙawarin zai yi iya yinsa na ganin hakan ya yiyu duk da hakan da matuƙar wahala, dan case ɗin ya bar hannunsu yana gun manyansu. Daɗin abun da ba’a fito da zancen ba ga al’ummar gari ba, amma dai ya ce su dage da addu’a. Da daddare bayan isha’i Neehal tana kwance a falon ƙasa suna chatting da Haneefah Ameen ya shigo falon, ko sallamarsa bata ji ba sai k’amshin turarensa. Saurin kifa wayar ta yi a ƙirjinta tare da lumshe idonta kamar mai bacci, dan haushin shi take ji akan kama Daddy da ya saka a yi, a ganin ta ya kamata ya yi bincike kafin ya yi saurin zartar da hukunci. Shi kuwa tsayawa ya yi yana kallon ta, ta turo baki domin tana jin idanunsa na yawo a jikinta, tsawon three minutes yana kallon ta sannan ya wuce sama. Ta buɗe ido jin takun sa akan steps tana kallon bayansa. Tana ganin ya haye ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta shige ɗakin su Dije dan kar ya fito su ƙara haɗuwa. Washegari da safe ta je school ta dubo result ɗinsu da aka kafe musu tun week ɗin da ya wuce. Alhamdulillah kamar kodayaushe ya yi kyau successfully. Sai a lokacin ta ji haushin rashin apply ɗin N.Y.S.C da bata yi ba, a lokacin classmates ɗinta suna ta yi ita kuma ta ƙi yi saboda auranta da Sadeek, dan ba zai yiyu daga yin aure ta fara da bautar ƙasa ba. Shine Mama ta ce ta bari sai next year ta yi. A cikin week ɗin nan ta fara bucking karɓar result ɗinta. Sati biyu da sallamo Mama bayan cuku_cuku da shan gwabarmaya su Abba suka samu aka fito da Daddy, dan ma Daddy’n na manya mutane ne a ƙasar shi yasa abun ya ɗan zo musu da sauƙi, amma duk da haka sun sha wahala ba kaɗan ba. Ana i gobe ranar ne kuma jami’an tsaro suka yi nasarar k’one gidan tsafin ƙungiya bisa jagoranci Daddy. Bisa Ikon Allah sai abun da ya zo da tsautsayi ashe duka ƴan ƙungiyar suna cikin gidan suna meeting akan yanda za su yi Daddy ya zo hannunsu a wannan lokacin, tunda Sarauniya ta hana a kashe shi, su kuma jami’an tsaro basu san suna cikin gidan ba, gidan kawai suka zo da niyyar k’onewa aka haɗa da su. Sai da wutar ta mutu sannan aka dinga zak’ulu k’onannun gawarwakinsu. Jami’an tsaro ba su so haka ba, sun so su kama su a hannu. Amma al’ummar gari da labarin ya bazu kowa cewa yake yi gwara haka, dan halin ƙasar nan tsaf za’a kama su a tsare kuma a ƙi yi musu hukuncin komai a yi ta jan abun har a manta da maganar, musamman da ya kasance da wasu daga cikin manyan ƙasa a cikin ƙungiyar. Ranar ƙasar nan da kewaye rud’ewa aka yi da zancen kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Daddy ya yi kuka sosai tare da ƙara godewa Allah da ya bar shi da imaninsa, shigarsa cikin ƙungiyar nan bai ruɗe shi yasa ya manta da Ubangiji ba, ya kuma gode masa akan fitar da shi da ya yi, domin yasan wannan ikonsa ne kawai da rahamarsa yasa ya cece shi. Ranar ji ya yi tamkar an sauke masa wani abu mai nauyi a cikin zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa, ya ji jikinsa da kansa yay masa wasai kamar wanda ya tashi daga doguwar cuta, nutsuwarsa ta dawo cikin jikinsa. Ya ƙudure a ransa yanzu bautar Allah da istigfari kawai zai duk’ufa yi akan abubuwan da ya aikata, duk da bayin kansa ba ne amma ba zai dogara da hakan ya ƙi tunatarwa Allah ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button