NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Haka a ka ci gaba da zaman makokin mutuwar Anwar, Neehal kullum su na zuwa gidansu Anwar da safe sai dare suke tafiya har a ka yi sadakar uku, daganan kuma bata ƙara komawa ba saboda ita ma ana zuwa gida yi mata gaisuwa, sai ranar sadakar bakwai suka kuma komawa. Yau Juma’a wanda ya kama kwana goma sha biyu da rasuwar Anwar, zuwa yanzu Neehal ta sakawa zuciyarta dangana game da mutuwar Anwar, Anwar ya riga ya tafi ya zama tarihi addu’ar su kawai yake buƙata, duk da wani lokacin ta na damuwa sosai har ta zauna ta yi ta kuka, Mama,Dad, Haneefah sune ‘yan rarrashin ta da bata baki gami da nasihohi, Ameen ma yanzu wata kulawa yake bata ta musamman saboda tausayi take basa sosai, ta zama wata so silent wannan rigimar da neman magana gurin Mama duk ta daina, Magana ma ba sosai take yinta ba, ga rama da ta yi. Misalin ƙarfe Biyar na yamma Neehal ta na zaune a falon ƙasa ita kaɗai ta na kallon Sunna TV, gani ta yi Dije mai aiki ta fito daga dakinsu da sauri, ashe ƙarar bell ta ji, ita ba ma ta ji ba ta na can duniyar tunani. Dije ta na buɗe door d’in ta ga kanwar Dad ce ta zo tare da ‘yarta, hanya ta ba su ta na musu sannu da zuwa cikin girmamawa, Matar ce kawai ta amsa mata a wulak’ance amma ‘yarta ta ko kallon ta ba ta yi ba, ta wuce ciki ta na taunar cingum ƙas_ƙas ga takalmin ƙafarta mai shegen tsini sai ƙara yake a kan tiles ɗin falon, k’amshin turarenta mai hawa kai ya cika falon, fara ce tass kamar ka tsaga jikinta jini ya fito amma gajeriya ce ta na da madaidaicin jiki, ta na sanye da wata doguwar riga ‘yar kanti, ta yafa mayafi kalar rigar kanta babu ɗankwali sai fuskarta da ta sha uban make up. Neehal ta bita da kallo fuskarta ba yabo babu fallasa, ita kuwa wani matsiyacin kallo take bin Neehal da shi. Neehal ta yi ɗan murmushi ta ce “Sannunku da zuwa Aunty Hamida” kamar ba ta ji ba, ta yi banza da ita, Neehal dama ta san za’a rina, duk da kasancewar Hamida ‘yar gidan k’anwar Dad ce amma ba sa shiri ko kaɗan, ko dan hakan ya samo asali ne daga rashin shirin Mahaifiyar Hamidan da Mama ne?. Neehal ranta ya ɓaci a kan abin da Hamida ta mata, dama shi ya sa bata son shiga sabgarta, Mama ce ke tursa sata dole, ta rasa me ta yi wa Hamidan ta tsane ta over. Hamida ta zauna ta na kar kaɗa ƙafa, Mahaifiyarta wadda suke k’ira da Mumy ta ƙaraso cikin falon ta zauna ita ma ta na huhhura hanci, Neehal ta dube ta ta ce “Sannu da zuwa Mumy ina yini?” Ta mata wani kallo ta ce “Lafiya k’alau, ya hak’uri kuma?” Neehal ta ce “Alhamdulillah.” Daga haka suka yi shiru, Neehal ta maida hankalinta a kan kallon da take, bayan wasu mintuna Mama suka sakko ita da Hajiya da Dije da ta je kiranta. Mama ba yabo ba fallasa ta ce “Sannunku da zuwa” Mumy ta ce “Yawwa” Mama ta ce “Ya gida Suwaiba?” Mumy ta ce “Lafiya k’alau” Mama ta ce “Masha Allah” tare da zama a kan kujera, Hajiya ma ta zauna. Hamida kamar ba ta so ta ce “Ina yini Mama?” Mama tace “lafiya k’alau, Hamida ya aiki” tace “Fine Mama” Hajiya yadda ba su mata magana ba, itama ba ta musu ba, TV kawai take kallo hankalinta kwance. Su Dije suka dawo falon da ruwa da lemo gami da drinks, Zulai ta gaishe su kamar yadda Mumy ta amsa wa Dije haka ta amsa wa Zulai a wulak’ance. Can dai Mumy ko me tuna sai ta dubi Hajiya ta ce “Ina yini Hajiya?” Hajiya ta ce “Lafiya” tana keb’e fuska, Hamida da ke ta latsa wayarta ita ma ta gaishe ta a yangance. Mumy ta gyara zama ta dubi Mama ta ce “Sai muka ji kuma an kashe saurayin Neehal” Mama ta ce “Eh ƙaddara ta riga fata.” Mumy ta ce “To Allah ya ji k’an shi, amma ni fa ina ganin wannan abun kamar da sa hannu, a ce yarinya duk wanda maganar aure ta shiga tsakaninsu sai an kashe shi, sai ka ce firlm ko labaran tatsuniya?” Mama ta yi shiru ba ta ce komai ba, domin da rainin hankali Mumy ta yi maganar. Hamida ta tab’e baki ta ce “Hmmmm gaskiya dai Mumy, dan Ni na ma fi tunanin ko wani baƙin Aljanin ne ya aure ta………✍️
By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:31] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
0️⃣9️⃣
………..Hajiya ta dubi Hamidah ta na mitsi_mitsi da ido ta ce “Ke! Ki iya bakinki, mugun nufinki Insha Allahu ba dai a kan Neehal ba, ato, bakinki ya sari ɗanyen kashi” Hamida za ta kuma magana Mommy ta girgiza mata kai, tab’e baki ta yi ta ci gaba da latsa wayarta a gadarance, Mama kuwa kamar ba ta ji su ba, ta musu banza. Neehal ma ko d’aga kanta ba ta yi ba, balle ta nuna ta san me su ke cewa. Hakan kuwa ba ƙaramin k’ona ran Mommy ya yi ba, domin kuwa ta so Mama ta kula ta su yi ta yi, ko kuma Neehal ta tankawa Hameedah Dad ya dawo ta haɗa mata sharri, sai kuma ba ta samun haɗin kai ba. Mama tashi ma ta yi ta wuce sama abin ta, Neehal ma bin bayanta ta yi dan zaman falon ya ishe ta. Hakan kuwa ya ƙara kona ran Mommy. Ɗakin da suke sauka idan sun zo Mama ta sa su Dije suka gyara musu, da yake daga Abuja suke a can suke da zama, su Dije suka kwasar musu kayansu zuwa d’akin. A gadarance su Mommy da Hameedah suke yin komai a gidan, Mama kuwa ba ta tanka musu haka ma Neehal, Hajiya ce ma sarkin magana, amma Mama ta roƙe ta a kan ko me za su yi kar ta kula su. Ko da Dad ya dawo part d’insa suka je su na hira, har sai da dare ya yi sosai sannan ya ce ya kamata su je su kwanta, Mama kuwa dama ta san hali shi ya sa ba ta je ba, sai da ya kira ta da kansa a waya. Washegari Neehal tun safe ta wuce gurin aiki, dama tun ranar mutuwar Anwar ba ta koma ba sai yau.
Misalin ƙarfe 11 na safe Ameen ya shigo gidan, kamar yadda ya saba part d’in Mama ya nufa direct, da key d’in hannunsa ya yi amfani ya buɗe kofar, da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga. Hameedah ce kwance a kan kujera ta na latsa waya, Mahaifiyarta kuwa ta fice gidan k’awayenta. Da sauri ta tashi zaune jin sallamarsa tare da faɗaɗa fara’arta wadda tun da ta zo gidan ba ta yi kamarta ba. Ameen ya kalle ta sau ɗaya ya kau da kansa, har ya ƙaraso cikin falon kallon sa take kamar za ta lashe shi bakin ta ya ƙi rufuwa dan farin ciki. Cikin kaud’i da iyayi ta ce “Sannu da zuwa Ya Ameen.” Ta ƙarashe zancen tare da mik’ewa ta koma kusa da shi. Ya kalle ta ba yabo ba fallasa ya d’aga mata kai. Hameedah ba ta damu ba ta ce “Yayanah I missed you so much, na manta when last da na ganka, last zuwan da na yi ba mu haɗu ba, gashi kai kuma ba ka zuwa gidanmu.” Ameen ya banzatar da zancen nata ya ce “Yaushe ki ka zo?” Cike da jin daɗin ya biye mata suna hira ta ce “Yesterday, ni da Mommy mun zo gaisuwa ne?” Ameen ya ce “Tun yaushe aka yi rasuwar amma sai yanzu za ku zo?” Hameedah ta ɗan shagwab’e ta ce “To ai Yaya ka ga ina zuwa aiki, sai weekend nake da time.” Ameen ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma can ya ce “Neehal as she is your cousin sis, amma a mata rasuwa ki ce sai kin samu time za ki zo mata gaisuwa?” Hameedah ta tab’e baki tare da ɓata fuska ba ta ce komai ba, sai kuma can ta ce “Kasan Mommy ma ba ta ji dad’i ba time ɗin shi ya sa ba mu zo ba, kuma na ga ita gaisuwa ai ba ta tsufa, tun da mun masa addu’a ai is ok.” Ameen bai kuma ce mata komai ba ya mik’e ya nufi sama gurin Mahaifiyarsa. Mama ta na operating system ya yi knocking k’ofar ɗakin, Mama ta ba da umarnin a shigo. A hankali ya buɗe k’ofar bakin sa ɗauke da sallama. Mama ta d’ago ta na duban sa ta amsa masa, ya ƙaraso ya zauna a gefen ta ya ce “Gud Morning Mum, how are you?.” Mama ta ce “Lafiya, ka zo lafiya? Ya aiki?” Ya ce “Alhamdulillah, ina Neehal fa?” Mama ta ce “Ta je aiki.” Ya gyad’a kai kawai tare da ƙoƙarin mik’ewa. “Koma ka zauna ina son magana da kai.” Muryar Mama ta katse masa hanzarinsa. Ya gyara zama tare da bata duka hankalinsa. Mama ta ture laptop d’in gabanta ta na dubansa da kyau ta ce “Ameen me kake tunani a kan al’amarin Neehal? Ba ka ganin kamar wasu ne suke bibiyar rayuwarta? Duba da a baya an kashe Jameel ma” Shiru ya yi alamun nazari kafin ya sauke Numfashi ya ce “Mum, babu irin tunanin da ban yi ba a kan wannan al’amarin, tun lokacin na ci karo da labarin mutuwar Anwar dake ta yawo a media, amma kuma da na yi wani nazari da lissafi sai na ga kamar kisan Anwar da Jameel ba shi da alaƙa da Neehal.” “Saboda me ka ce haka?” Cewar Mama ta na kallon sa. Ameen ya ce “Idan ba ki manta ba Mum, shi Jameel dama can ya na da ‘yan adawa a rayuwarsa duba da yanayin aikinsa.” Mama ta ce “Hakane, domin kuwa tun a wancan lokacin da aka kashe Jameel ko kaɗan ban yi tunanin kisan ya na da alaƙa da Neehal ba, dan some times Idan ya zo gaishe ni ya na yawan cewa a taya su da addu’a saboda magauta da mahassada, amma kuma kashe Anwar da aka yi ya birgita mun duk wani lissafi na Ameen.” Ameen ya ce “Duk da an kashe Anwar amma ba na tunanin kisan Anwar ya na da alaƙa da na Jameel” Mama ta yi shiru ta na jin dama furucin Ameen zai tabbata da sai tafi kowa farinciki, za ta so a ce ba dan Neehal ake kisan ba, amma kuma abun da kamar wuya musamman idan ta yi duba da……. “Kar ki sa wa ranki damuwa Please Mom, kuma ki cire tunanin wai ko dan Neehal aka kashe Anwar” Ameen ya katsewa Mama tunaninta da faɗin haka. Mama cikin damuwa ta ce “Ameen! Ka na so ka kwantar mini da hankali ne kawai kamar yadda ka saba a kodayaushe idan ka ga ina cikin damuwa, amma ba ni kaɗai ba ma, ko A’isha da Sadiya mun yi maganar da su kuma suma duk tunanin su haka ne.” “To ai dama tunanin ku duk ɗaya ne ku mata.” Cewar Ameen ya na murmushi. Mama ta ɗan harara shi ta ce “Su kuma sauran mazan da muka yi maganar da su fa?” Kamar a ɗan rud’e ya ce “Su wa kenan?” Mama ta masa wani kallo ta ce “To mene na yin hakan kuma, kamar wanda aka zabura?” Ameen ya ɗan lumshe idonsa ya ce “Nothing, kawai ban so ki ka yi maganar da wasu ba” Mama ta ce “Ahmad ɗin Sadiya ne fa sai Mahmud, su kuma ka ga ai duk na gida ne.” Ameen ya ce “Hakane, Insha Allahu ko ma yaya ne Allah zai warware mana, kuma Insha Allahu problem ɗin ba daga wurin Neehal ta ke ba.” Mama ta ce “Ameen ya Allah.” Ameen ya mik’e ya na faɗin “Ina Hajiya fa?” Mama ta ce “Tun safe driver ya kaita gidan Sadiya yau can za ta wuni.” Ya ce “Ok” har ya juya Mama ta ce “Ka ga Hameedah kuwa” ya gyad’a mata kai alamar Eh ba tare daya juyo ba, Mama ta yi murmushi kawai dan tasan tun da ya yi haka ba ya son zancen Hameedan ne.