NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan ya fito daga wanka ya shirya ya ci lafiyayyen abincin da Mama tay masa da sassayan lemo wanda rabon da ya ci ya manta saboda rashin kwanciyar hankali. Gashi duk ya rame ya yi duhu sakamakon tsaren shin da aka yi. Su Abba sun zo ana ta ƙara jajanta abun tare da murnar kub’utar da shi da Allah ya yi, domin sun san ba iyawarsu da dabararsu ba ce Ubangiji ne ya dubi zuciyar Daddy ya tseratar da shi bai mutu yana aikata wannan mummunan saɓon ba. Abba ya dubi Daddy ya ce. “Toh Alhamdulillah, Masha Allah, komai ya yi farko yana da ƙarshe, Muhammad wannan ita ce taka jarrabawar kai kuma, fatanmu Allah kar ya kuma maimaita mana irin wannan musifa ga zuri’armu da ma dukkan Musulmi baki ɗaya, wannan kuma ya isa ya zama izna ga ƴan baya akan mu’amala da abokai wanda bana gari ba ne. Dan shi aboki kullum burinshi ya ɗora ka akan hanyar da yake, musamman in bata ta gari ba ce.” Daddy ya ce. “Gaskiya ne, ai na yi dana sanin sanin Kabir Ginyau a rayuwata, shi yasa Fateemah tun farko kamar ta sani ta dinga ƙoƙarin raba ni da shi, Allah ya yi dai wannan abun sai ya faru. Amma kuma sanadin haka gashi an yi nasarar kawar da mugun iri daga doran duniya, an rage masu saɓon Allah.” Abba ya ce. “Allah ya kyauta, ya cigaba da tonawa masu irin wannan munanan d’abi’un asiri.” Suka amsa da Amin. Dai-dai lokacin Ameen ya shigo falon. Daddy ya tashi da sauri ya tarye shi tare da rungume shi yana murmushi ya ce. “Da fatan yanzu zuciyar gwarzon ɗana ta yi fari da mahaifinsa akan baƙin da ta yi a da?” Ameen ya yi murmushi cikin wasa ya ce. “Kamar da saura dai Dad.” Daddy ya marairaice fuska, gaba-d’aya Falon suka saka dariya. Neehal kam ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murnar Allah ya fito mata da Dad ɗinta lafiya. Sai Hamdala ga Ubangiji take. Alhamdulillah rayuwar gidan Mama ta koma kamar da ita da Daddy wanda a da ta fitar da ran samun hakan. Suna fatan kuma matsala ta ƙare musu haka daga su har Neehal. Hankalin ƴan’uwa ya kwanta akan problem ɗin Neehal tunda an gano bakin zaren har ma an yi maganin abun, yanzu sai fatan Allah ya kawo miji na gari ta yi auranta. Bayan sati biyu wanda ya kama farkon watan maulud aka yi bikin Ahmad wanda har yanzu bai san an fasa Auran Neehal da Sadik ba, dan Neehal ce masa ta yi d’aga bikin aka yi. Neehal ta je ta yi kwana uku da ita aka sha biki aka rak’ashe. Ƴan’uwan Ahmad sun nuna mata k’auna, kowa ya zo Ummi ta nuna masa ita ta ce ga Aunty’n su Afrah wadda ta tsince su ta riƙe su. Ranar D’aurin Aure da Mama da Daddy suka je ta biyo su suka dawo gida tare. A daren ranar ta ci kukan da bata san dalilinsa ba, ta ji dai kawai tana jin ba daɗi akan Auran da Ahmad ya yi, amma ta daure bata bari kowa ya fuskanci halin da take ciki ba. Ta koma bakin aikinta wanda aka ƙara mata girma bayan karɓar result ɗinta da ta yi. Ameen bai yi magana ba akan yana son Neehal ko wani abu makamancin haka, ko nuna alamar hakan ma bai yi ba. Mama kuma ta zuba masa ido ta ga iya gudun ruwansa da ƙarshen muskilancinsa. Da Daddy yay mata zancen ta ce masa kar ya kuma balle Ameen ɗin ya ji, sai ya zo da kansa ya ce yana son abun, tunda bai isa tay masa tallar ƴarta kota ba shi ita a bagas ba. Daddy ya yi dariya kawai. Mama ta dage da yiwa Neehal addu’ar samun miji na gari tare da neman zaɓin Allah mafi Alkhairi a gare ta. Ita ma ta ce mata ta dage da yin addu’ar hakan………..✍️

Ga Barka da Sallah nan har 3 pages, sai dai ni ban ji nawa ba har yanzu.????????

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

7️⃣4️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.

………Yau ta kama ranar Asabar, da yamma Mama da Daddy suna zaune a falon ƙasa na part ɗin Mama suna hira door beil ta yi ƙara. Neehal bata nan ta je gidan Haneefah tun Azhar. Daddy ya tashi ya je buɗe ƙofar. Kawu Musa ya gani, da fara’a ya tarb’e shi tare da yi masa iso zuwa cikin falon. Ya shigo ya zauna a kujerar dake fuskantar wadda Mama take, Daddy kuma ya koma ya zauna a gefenta. Cikin girmamawa da muntuntuwa Kawu Musa suka gaisa da Mama. Zulai ta shigo falon ta kawo masa drinks a cikin plate tare da gaishe shi. Bayan ya ɗan kurb’i juice ɗin ya dubi Daddy ya ce. “Na ji daɗi dana same ka a gida, dan har na yi tunanin baka nan sai Hajiya kawai.” Daddy ya ce. “Ai yanzu yawanci da yamma ina gida, da rana ne nake ɗan fita idan ta kama.” Kawu Musa ya ce. “Allah sarki, dama wata magana ce mai muhimmanci ke tafe da ni.” Mama ta bayar da duka hankalinta a kansa, Daddy ya ce. “Toh muna sauraren ka Malam Musa.” Malam Musa ya gyara zama ya ce. “Jiya da yamma Ameen ya zo ya same ni har gida mun gaisa, to na zata zuwan nasa kamar na kodayaushe ne da yake zuwa lokaci zuwa lokaci muna gaisawa, sai dai bayan mun gama gaisawar na fuskanci akwai magana a bakinsa sai ce masa, Aminullah kamar akwai magana a bakinka, meke tafe da kai ne? Sai ya sunkuyar da kai ya faɗa mun abun da ke ransa, wato yana son Auran NEEHAL. Shine na ce to bazan yi ƙasa a gwiwa ba yau na taho ƙafa_ƙafa domin sanar da ku wannan abun farincikin, tunda ya ce mun bai sanar muku ba.” Ya ƙarashe zancen cikin murmushin farinciki wanda ke nuni da yana jin daɗin al’amarin sosai. Mama ta kalli Daddy wanda shi ma yake murmushin sannan ta jinjina kai ta mayar da kallonta ga Kawu Musa cikin mamaki ta ce. “Lallai na gaishe da Ameen na jinjinawa halinsa, wato dan ya san idan ya zo ya same ni bazan amince ba ko kuma Dad ɗinsa shi yasa ya je ya same ka, saboda bashi da kunya ba zai faɗa da bakinsa ba sai dai ya turo ka, to bazan amince ba duk da haka.” Kawu Musa ya yi ƴar dariya sannan ya ce. “To ai wannan shine ƙa’ida, abun da ya yi shine dai-dai, idan kana son yarinya ka je ka samu magabatanta ba wai ka je kai ta hure mata kunne kana cika ta da surutun kawai ba.” Daddy ya ce. “Faɗa mata dai, ita tafi son ya zo su yi ta ja masa aji ana ƴank’wana shi.” Kawu Musa yana dariya ya ce. “Ai ɗan nawa ba irin waɗannan mazan da ake yiwa haka ba ne.” Ganin sun mayar da abun wasa cikin seriously Mama ta ce. “Koma yaya ɗan naku yake dole ya ajiye duk wani ji da kai ya zo ya nemi yarda da amincewar yarinya, domin bazan yi mata Aure ba tare dana tabbatar tana so ko bata so ba.” Kawu Musa ya yi murmushi ya ce. “Haba Hajiya, abu na gida abu tuwona maina ai bama buƙatar wani jan abubuwa, yarinyar nan tunda Ubangiji ya kawo mata ƙarshen matsalarta burinmu yanzu kawai mu gan ta a ɗakin mijinta, hankalinmu sai ya fi kwanciya.” Daddy ya ce. “Wannan gaskiya ne Malam Musa.” Mama ta ce. “Nima ban ƙi ta taku ba, hasalima abun da na kasa da addu’a a gaba kenan Allah ya kawo mata miji na gari ta yi auranta. To amma dan Ameen ya ce yana son ta baza mu amince masa ba ba tare da mun ji ra’ayin yarinya ba, idan bata so duk sonmu da abun dole mu haqura.” Kawu Musa ya ce. “Wannan ai duk ba wata matsala ba ce Hajiya, yaron nan kowa ya san halinsa ba shi da wani aibu, kowanne iyaye zasu so ƴarsu ta yi dacen miji da kamar Ameen yaron kirki. Ni dai dan Allah ina nema masa wannan alfarmar a gurinku, domin a ganina koda bata son shi idan aka yi auran zata so shi, za su fuskanci juna, bare ma Insha Allahu na san baza ta ƙi ba. Mu dai kawai mu bi su da addu’ar Allah yasawa abun albarka ya ba su zaman lafiya.” Daddy ya ce. “Amin Amin, mun gode sosai Malam Musa, Allah ya bar zumunci.” Ya ce. “Amin, amma mune da godiya akodayaushe Alhaji, Allah ya raya zuri’a ya ƙara buɗi.” Mama ta sauke numfashi ta ce. “Amin, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi.” Malam Musa ya ce. “Amin, shine kawai dama, ina Neehal ɗin ne ban ga gilmawarta ba ko tana gurin aiki?” Mama ta ce. “Ta je gidan ƙawarta ne, yau ai Asabar bata da aiki.” Malam Musa ya ce. “To Allah ya taimaka, ni zan wuce sai na kuma dawowa, duk abun da ake ciki sai ku sanar mun a waya.” Mama ta ce. “To ka gaida gida da mutanen gidan, mun gode sosai fa, Allah ya bar zumunci.” Ya ce “Gida zai ji.” Tare da miƙewa, Daddy ya tashi ya bi bayansa dan raka shi. Bayan ya dawo Mama ta ce masa. “Ni fa Gen. bana son mu tursasa Neehal akan Auran Ameen, kuma ka san indai muka faɗa mata baza taɓa ƙi ba, ni kuma bazan so hakan ba gaskiya.” Daddy ya yi murmushi ya ce. “Bana jin zata ƙi Ameen Fateemah, a yanda Neehal abubuwa suka faru a baya akan aurarrakinta da Allah bai nufa an yi ba tana buƙatar ace ta samu miji na gari wanda baza ta yi kuka da shi ba ko bayan ba ma raye, ke kika haifi Ameen kin fi kowa sanin halinsa, Ameen ba shi da wata matsala da zata saka a hana shi Aure.” Mama ta ce. “Hmmm, in aura masa ƴa ya cinye mun ita da masifa da faɗa.” Daddy ya yi murmushi ya ce. “Wannan kuma aiba a ƙasa ya ɗauka ba gurinki ya gado, kuma tunda yana k’aunarta ai bazai mata ba. Kin ga Fateemah kamar yadda Malam Musa ya ce mu bi al’amarin nan kawai da addu’a, idan Alkhairi ne Allah ya tabbatar mana, Insha Allahu watarana sai mun yi alfahari da farincikin auransu.” Mama ta ce. “Allah yasa.” Sai kuma ta shiga mitar Ameen dan ya san baza ta iya cewa Malam Musa a’a ba shine ya turo musu shi, zai zo ya same ta ne har inda take.” Daddy dai dariya kawai yake yi mata, zuciyarsa wasai, domin babban burinsa a yanzu Ameen ya auri Neehal, domin ya san bazai taɓa wulaqanta ta ba, ya yarda da ɗansa da irin tarbiyyar da yay masa. Ita kuma Mama anata ɓangaren tana son abun domin idan ya kasance sai ta fi kowa farinciki, amma gani take kamar tursasa Neehal zasu yi, ita kuma baza ta so hakan ba. Sai bayan Magriba Neehal ta dawo gida. Direct ɗakin Mama ta wuce, ta faɗa jikinta cikin shagwab’arta ta ce. “Wash Mama na gaji sosai.” Mama ta ce. “Wani aikin kika yi ne?” Ta ce. “Driving mana.” Mama ta ce. “Daga gidan Haneefah zuwa nan shine zai saka ki gaji saboda lalacinki.” Ta turo baki bata ce komai ba. Mama ta ce. “Ki je ki ci abinci ki huta bayan isha’i Dad yana son ganinki.” Ta ɗan waro Ido ta ce. “Lafiya Mama?” Dan haka kawai ta ji gabanta ya faɗi. Mama ta ce. “Ba wani abu ba ne tambayar ki kawai zai yi.” Ta yi shiru a ranta tana kissima abubuwa da dama, ko kaɗan maganar aure bata zo cikin zuciyarta ba a matsayin abun da Daddy zai yi mata magana akai ba. Ta bar jikin Mama ta tashi ta ɗauki jakarta jikinta duk a sanyaye, Mama ta bi ta da kallo har ta fice. Kayan jikinta ta rage sannan ta shiga toilet ta watsa ruwa ta fito. Ta zira doguwar riga sannan ta ɗauko laptop ɗinta ta zauna ta shiga lallatsawa. Har aka yi sallar isha’i bata tashi ba, da yake tana fashin Sallah ne. Sai wajen tara saura ta kashe system ɗin ta tashi, ta san yanzu Daddy’n ya dawo. Ta zira hijabi ta fice daga ɗakin ta nufi part ɗin Daddy. A dinning area ta same su suna dinner. Da fara’a Daddy ya ce. “Daughter sai yanzu? Na ɗauka ko bacci ya ɗauke ki ma.” Ta ce. “A’a Daddy, aiki na ɗan rage.” Dad ya ce. “Toh Masha Allah, Allah ya taimaka ya yi albarka Daughter.” Cikin jin daɗin addu’arsa a gare ta da baya gajiya da yi mata a kodayaushe ta ce. “Amin Daddyna.” Mama ta dube ta, ta ce. “Ki zauna ki zuba abinci ki ci.” Bata yi musu ba ta ja kujerar kusa da Mama ta zauna ta zuba abincin ta yi Bismillah ta fara ci cikin nutsuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button