NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya
Bayan sun gama cin abincin Neehal ta tattara kayan da suka bata ta wanke a kitchen ɗin part ɗin Daddy’n. Sannan ta koma Parlour’n sa ta zauna a ƙasan kujerar da yake kai. Cikin girmamawa ta ce. “Daddy gani, Mama ta ce kana son magana da ni.” Daddy ya gyaɗa kai tare da duban ta cikin sanyin murya ya ce. “Ina son in tambaye ki ne Daughter kuma dan Allah ki faɗa mun gaskiya.” Gabanta na fad’uwa ta ce. “Insha Allahu Daddy, indai na sani zan sanar maka.” Daddy ya ce. “Yawwa d’iyar kirki, tambayar da zan miki akwai wanda kike so ne yanzu? Ma’ana akwai wanda kuke mu’amala ta soyayya wanda kike da burin aurar shi?” Neehal ta yi ƙasa da kanta cikin jin kunya, tun bayan rabuwar su da Sadik bata ƙara saurarar wani ɗa namiji da sunan soyayya ba, mutum ɗaya ne ma ya nuna yana son ta, a gurin aikinsu yake kuma dama shi ya daɗe yana nuna yana son nata, ita ce kawai bai yi mata ba. Daddy ya ce. “Kin yi shiru Daughter.” Ta sauke numfashi cikin ladabi ta ce. “Babu kowa Daddy.” Daddy ya ce. “Kin tabbata?” Ta gyaɗa masa kai. Cikin murmushi ya ce. “Toh Alhamdulillah, dama Yayanki Al’ameen ne ya zo mana da maganar yana son auranki, mun yi farinciki da jin daɗin hakan sosai, amincewarki kawai muke jira mu fara shirye-shiryen biki.” Ai wata irin muguwar fad’uwar gaba ce ta riski Neehal, saboda tsabar firgicin da zuciyarta ta shiga fitar jininta har ƙara gudu ya yi. Tun daga sunan Yayanki Al’ameen yana son auranki da Daddy ya faɗa bata ƙara fuskantar sauran abun da yake cewa ba. ‘Yaya fa, Yayana fa? Impossible, gaskiya ban ji dai-dai ba, ba shi Daddy yake nufi ba.’ Ta faɗi haka a ranta. Mama dake nazartar yanayinta ganin yanda ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa sai ta girgiza kai, dama ta san za’a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Daddy ya cigaba da magana. “Idan ba kya so Daughter ki faɗa babu mai miki dole, sai mu yi fatan Allah yasa haka shi yafi Alkhairi, ya kawo miki wani na gari.” Ta d’ago kanta a hankali cikin ƙoƙarin son mayar da k’wallar data tarar mata a ido cikin rawar murya ta ce. “Daddy ban gane wanne Al’ameen ɗin kake nufi ba?” Dad ya ce. “Ameen dai na gidan nan.” Sai ta ƙurawa fuskar Daddy ido kamar shine Ameen ɗin, ta san mafarki take yi babu ta yadda za’a yi a ce ta auri Yayanta, ta shiga addu’a da fatan Allah ya farkar da ita daga wannan rudad’d’en mafarkin da take. Muryar Daddy data ji yana faɗin. “Daughter!” Shi ya dawo da ita cikin nutsuwarta, ta tabbatar gaske ne ba mafarkin ba. Ta sauke numfashi sannan ta ce. “Na’am Daddy.” Ya ce. “Karki saka kanki a cikin damuwa, it’s your life no body will force you ki yi abun da bakya so kin ji. Yanzu ki tashi ki je ki nutsu ki yi tunanin abun da kike ganin ba zaki takura ba a rayuwarki, abun da yafi miki dai-dai zuciyarki tafi samun nutsuwa a kansa, da safe sai ki faɗawa Mamanki abun da kika yanke.” Kamar wadda k’wai ya fashewa a ciki haka ta miƙe da ƙyar ko sallama bata yi musu ba ta fice daga falon. Mama da bata ce k’ala ba ta bita da kallo. Bayan ta fice ta sauke numfashi ta ce. “Dama na san haka zata faru Gen. Jibi yanda yarinyar nan ta firgice daka faɗa mata zancen nan, na san yanzu zuwa zata yi ta tayar da hankalinta tay ta tunani.” Daddy ya ce. “Nima na san dole zata kaɗu da jin wannan batun, amma wannan ba abun tayar da hankali ba ne Fateemah, I assure you sai kin fi kowa murna da farinciki da Auran Neehal da Ameen bayan Auran Insha Allah. A kullum burinki da addu’arki Allah ya bawa yarinyar miji na gari wanda zai riƙe ta da amana ya samar mata da farinciki a rayuwarta, Ameen rainonki ne bani da haufi a kansa da waɗannan abubuwan kuma kema kin sani.” Mama ta ce. “Duk na san wannan, kuma ni bacin Neehal ma ina duba Matarsa Hafsat, dududu yaushe aka yi auransu har da zai ƙara Aure, yarinyar nan baza ta ji daɗi ba.” Daddy ya yi murmushi ya ce. “Wato kina taya ƴarki kishi kenan?” Mama ta ce. “Ba zancen kishi ba ne gaskiya ce.” Daddy ya ce. “Wannan ai duk ba wata matsala ba ce, tunda Ubangiji ne ya ce a auri mata har huɗu idan mutum yana da halin yi zai kuma yi adalci a tsakaninsu, addu’a kawai zamu yi Allah ya haɗa kansu, shi kuma Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakaninsu.” Mama ta ce. “Haka ne, Amin, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi.”
Da jan ƙafa Neehal ta ƙarasa part ɗin Mama ta shige ɗakinta ta faɗa kan gado, da ƙyar ta iya zare hijabin jikinta saboda uban gumin da take haɗawa. Yaya fa, mijin Hafsah da bata k’aunarta shi su Daddy suke son aura mata, dan ita bata yarda Ameen ne ya ce yana son ta ba tafi tunanin kawai Daddy ya faɗa ne. Ita fa a tsarin rayuwarta sam bata son Auren mai mata, mai matar ma kuma Yayanta mijin Hafsat. Yaya masifaffe ta dinga yi masa magana idan sun yi Auran yana share ta. Ta turo baki kamar yana ganin ta tana hango yanda yake tsare gidan nan nasa. A fili ta ce. “Impossible, tunda Daddy ya ce sai na amince to zan ce masa ban amince ba kawai a bar zancen.” Da wannan kalaman ta sauke ajiyar zuciya ta ji zuciyarta ta samu nutsuwa har ta samu k’warin gwiwar miƙewa ta rage kayan jikinta ta kashe light ɗin ɗakin ta kwanta. Sai dai me? Tana kwanciya wata zuciyar ta ce mata. ‘Kina da hankali kuwa Neehal? Ɗan Mama da Daddy na cikinsu zaki iya kallon idonsu ki ce musu ba kya son shi baza ki iya auran shi ba? Mama da Daddy fa? Wanda ko wani suka kawo miki ba ɗansu ba bai kamata ki bijire musu ba.’ Sai ta tashi zaune cikin sauri ta faɗin Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un. Ita dai gaskiya baza ta iya Auran Ameen ba, ta yaya zata iya kallonsa a matsayin mijinta? Ya zaman Auran nasu zai kasance? Sai ta fara hawaye cikin rashin mafita. Idan har ta bijirewa Daddy ta san bata yiwa kanta adalci ba, duniya ma sai ta zage ta, ita karan kanta ma zata ga baƙin kanta. To amma ita da wani ma suka kawo mata ba Ameen ba da sai ta amince, amma ita dai baza ta iya Auran Ameen ba, Yayanta ne fa. Ta yi 1 hour tana tunanin mafita amma ta kasa samowa, gashi Daddy ya ce da safe Mama zata tambaye ta abun da ta yanke a game da maganar. Wayarta ta lalubo bisa shawarar zuciyarta da ta bata na ta nemi shawarar wani, time ta fara dubawa ta ga sha ɗaya saura, to wa ma zata kira? Tambayar da yiwa kanta kenan. Dama Mama ce abokiyar shawararta, idan kuma ba ita ba sai Haneefah, Haneefah kuma zuwa yanzu ta san ta yi bacci, ko ma bata yi bacci ba ya yi dare ta kira ta a yanzu. Sauran waɗanda zata iya shawara da su kuma a duniya wanda ta san za su faɗa mata gaskiya da abun da zata yi na dai-dai sai Aunty Sadiya da Aunty A’isha. Su kuma Mama ƴar’uwarsu ce, ta yaya zata yi wannan zancen da su? Ta yi tunanin kaf danginta babu wanda zata iya kira dan ya bata shawara, wa ma ta shak’u da shi da zai bata time ɗinsa su yi magana? “Uncle Usman.” Zuciyarta ta bata amsa, tabbas shi kadai ne zai bata shawara ya faɗa mata abun da zata yi na dai-dai. Ta latsa wayar ta lalubo Numbern sa ta yi dialing, duk da wata zuciyar na ce mata kar ta kira shi, ƙila yanzun haka yana tare da iyalinsa, amma duk da haka bata fasa kiran nasa ba because she is in needing solution. Bai ɗauki kiran ba har wayar ta katse. Dafe kanta ta yi hawaye na cigaba da zuba daga idanunta, fuskar Ameen kawai take hangowa a cukule, tana son ta hango shi as her husband amma ta kasa, ko dan ta yiwa Mama da Daddy biyayya sau ɗaya tak a rayuwarta akan abun da suke so wanda ita bata so, idan ta tuna tsantsar farincikin data gani a fuskar Daddy a d’azu da yake mata maganar sai ta yi tunanin ya zai ji idan ta ƙi amincewa, duk farincikin nan zai daina shi ne fa. To amma ita yanda zaman nasu zai kasance da Ameen a matsayin MATA da MIJI kawai take tunani, kuma matsalarta ba iya Ameen ba ne kaɗai har da Hafsat……….✍️