NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A daren Daddy bai jira komai ba ya kira Abba da wasu cousins ɗinsa ya sanar musu abun da yake faruwa, ya kuma faɗa musu a cikin week ɗin nan yake son akai kuɗin Auren Neehal gidan kawunta. Mama ta ce masa saurin me yake har haka? Ya ce mata baza ta gane yanda yake d’okin abun ba ne, a yanzu ba shi da wani sauran buri a rayuwarsa bayan ya ga Auran Neehal da Ameen….. Kamar yadda ya faɗa ranar Asabar wanda ya kama kwana biyar da yin maganar da yamma suka kai kuɗin na gani ina so gidan Kawu Musa. Ranar Neehal ji ta yi gaba-d’aya kamar ba ita ba, ita ce yau aka karb’i kuɗin Auranta da Ameen? Sai ta dinga jin abun kamar a mafarki, ta tabbata dai Auransu za’a yi da Ameen, ɓoye kanta ta yi a ɗaki ta ci kuka ta k’oshi. Su Daddy ba su baro gidan Kawu Musa ba sai da aka tsayar da lokacin biki wata uku masu zuwa, a haka ma da ƙyar Kawu Musa ya yarda, ya ce abun tunda duk na gida ne no need a ja lokaci, in san ransa ne bai ƙi a yi bikin a cikin two weeks masu zuwa ba. Da Daddy ya zo yana faɗawa Mama ta ce, ta san wannan duk shirin Ameen ne, shi yake zuwa yana zubawa Kawu Musa sintiri akan maganar bikin. A ranar bayan Magriba Ameen ya zo gidan kamar kullum, sai dai tun daga ranar da Neehal ta zura masa da gudu bai kuma ganin ta ba, dan b’uya take yi a ɗaki, ana yin Magriba zata shige ɗakinta ta kulle dan ta san shine time ɗin zuwansa gidan, bata fitowa har sai ta tabbatar ya tafi. Shi kuwa yana sane da ita da duk b’uyan da take, kuma ya san duk saboda shi ne, ƙyale ta kawai ya yi ya ga iya gudun ruwanta dan ya san akwai ranar ƙin dillanci. A ranar Mama ta ce masa ya sanar da Hafsat maganar bikin, ya amsa mata duk da bai so hakan ba, da ya so sai abun ya matso daf sannan ya sanar mata, amma yaya zai yi tunda Mama ta bayar da umarni dole ya bi. Bayan isha’i ya koma gidansa, ya tarar da Hafsat Hakimce a falon ƙasa ta ci uwar kwalliya ta tarb’arsa……….✍️

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

7️⃣5️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.

………Ta ja gwauron numfashi ta sauke tana ƙoƙarin komawa ta kwanta wayarta ta fara vibrate alamar shigowar kira. Ta ɗauki wayar ta duba wake kiran nata, ganin Uncle Usman ne ta sauke ajiyar zuciya a hankali tare da picking kiran ta kara a kunnenta. Cikin muryar dake nuni da damuwa tay masa sallama, ya amsa mata. Ta ce. “Uncle an wuni lafiya?” Ya ce. “Lafiya k’alau Neehal, dafatan kina lafiya?” Ta sauke numfashi ta ce. “Lafiya k’alau Uncle.” Uncle Usman ya ce. “Masha Allah, naga kiran ki, ina wanka ne kika kira ni, Allah yasa dai lafiya dan na ji muryarki wani iri kuma kira a daren nan.” Idonta ya ciko da k’walla, ta daure ta ce. “Dole ce tasa na kira ka yanzu Uncle, da na so na bari sai da safe amma ina buƙatar magana da kai urgently.” Uncle Usman ya ce. “To! Allah yasa lafiya dai?” Ta ce. “Lafiya k’alau, kawai shawararka nake nema akan wani al’amari, Allah yasa bazan takura ka ko Aunty ba?” Uncle Usman ya ce. “Haba babu komai Daughter, Aunty’n ki ta yi bacci ma ita.” Neehal ta gyara zama ta bawa Uncle Usman labarin duk yanda suka yi da su Daddy, ta kuma faɗa masa ita bata son Auren. Uncle Usman ya sauke numfashi ya ce. “Mene abun damuwa anan Neehal? Ai wannan abun farinciki ne mu a gurinmu ba kaɗan ba, Ameen mutumin kirki ne, iyayensa ma haka kuma kin fi kowa sanin hakan.” Ta ce. “Na sani Uncle, amma Yaya fa, ni dai baza iya auransa ba Allah.” Uncle Usman ya yi murmushi ya ce. “Mene da Yayan?” Ta turo baki tana hawaye ta ce. “Kai ma ka san halinsa, kuma yana da mata fa.” Ta ƙarashe maganar hawaye na zuba daga idonta. Uncle Usman ya yi ƴar dariya sannan ya ce. “Ina ruwanki da matarsa, zamanta daban naki daban.” Ta yi shiru bata ce komai ba. Cikin serious ya cigaba da magana. “Neehal, zan faɗa miki gaskiya a matsayina na uba a gare ki, ki cire wani abu mara kyau na Ameen daga cikin zuciyarki, alkhairinsa da na iyayensa a gare ki zaki duba, ki tuna ajiye komai nasa da ya yi ya ɓata lokacinsa da energy ɗinsa dan ganin ya samo miki mafita a rayuwarki, abun da ya yi saboda ke aiki ne na siyar da rai amma duk da haka sai da ya yi duk dan saboda ya ga ya cire ki daga cikin damuwar rayuwar da kike ciki. Alkhairin iyayensa a gare ki kuma ba zai fadu ba saboda tarin yawansu, ki tuna barazana da Daddy ya fuskanta saboda ke, amma duk dan ganin bai ɓata miki rayuwa ko ya bari an ɓata miki ba ya zaɓi duk wata barazana da abun da za’ai masa, kuma duk saboda ke.” Cikin tsananin mamaki ta ce. “Uncle a ina ka san wannan labarin?” Uncle Usman ya ce. “Aunty A’isha ce ta kira ni ta sanar mun tun lokacin da abun ya faru, har ma na kira Daddy da Mama na jajanta musu.” Ta jinjina kai kawai. Uncle Usman ya ce. “Ki ajiye duk waɗan can abubuwan dana lissafa miki, ki duba Ameen ɗin shi karan kansa, mene ne aibunsa daza ki ƙi shi? Ɗan Adam tara yake bai cika goma ba Neehal, ki yi addu’a kawai Allah ya tabbatar muku da Alkhairi ya kau da fitina a tsakaninku, amma ta yaya ma zaki ce baza ki amince ba, ko a fuska karki bari ki nuna damuwar da za su gane bakya so, ɗansu ne fa Neehal na cikinsu, ko da basu furta ba amma baza su taɓa jin daɗi ba idan kika ƙi ɗansu, muma baza mu ji daɗi ba.” Nasiha sosai Uncle Usman yay mata. Ba dan ranta ya so ba ta ce masa ta amince, zata cewa su Maman ta amince. Yay murna sosai ya dinga saka mata albarka. Sai ɗaya suka gama wayar, ta tashi ta shiga toilet ta canza pad ta dawo ta kwanta. Babu bacci ko d’igo a idonta, idan ta tuna gobe fa tana cewa Mama ta amince shikenan kamar yadda Daddy ya ce za’a fara shirye-shiryen bikinsu sai ta ji hawaye sun zob’o mata, shikenan zata zama Matar Yayanta Ameen shi kuma Mijinta? Idan ta tuna ba son ta yake ba sai ta ji hankalinta ya ƙara tashi, ko kuma idan ta tuno Hafsat da dama can ba k’aunarta take ba, ina ga ta aure mata miji? Amma duk da haka dole zata amince kamar yadda Uncle Usman ya ce mata, Mama da Daddy basu cancanci butulci daga gare ta ba. Ta sha kuka sosai kafin bacci ya ɗauke ta ba tare data sani ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button