NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Da safe da ta tashi idanunta jajur duk sun kumbura haka ma fuskarta saboda kukan da ta sha, ta shiga toilet ta yi wanka ta dinga dirzar fuskar saboda ta ware, bayan ta fito ta shirya harda ƴar kwalliyarta ta rambad’a kwalli duk dan kar Mama ta gane ta yi kuka. Ƙarfe takwas da ƴan mintuna ta fito ta sauka ƙasa. Ta tarar da Mama a kitchen tana haɗa breakfast. Ta tsaya a bakin ƙofa ta ce. “Barka da safiya Mama.” Mama ta juyo ta ce. “Yawwa, kin tashi lafiya?” Ta ce. “Lafiya k’alau Mama.” Mama ta ce. “Masha Allah.” Tana bin ta da kallo. Ta kirkiro murmushi ta ce. “Bari in taya ki aikin Mama.” Mama bata ce komai ba, ta ƙaraso suka ci-gaba da aikin tare. Dauriya kawai take yi amma ita kaɗai ta san halin da zuciyarta take ciki, gabanta sai faɗuwa yake saboda tunanin kar Mama ta tambaye ta abun da ta yanke akan maganar Auran Ameen. Allah ya taimake ta har suka gama aikin Mama bata ce mata ko ƙala ba. Tare suka yi breakfast da Maman, sai bayan sun gama ta tashi zata tafi Mama ta ce ta koma ta zauna. Ƙirjinta na luguden bugu ta koma ta zauna, dan ta san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi. Mama ta kalle ta na sakanni sannan cikin sanyin murya ta ce. “Kuka kika yi jiya da daddare ko Neehal?” Ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da girgiza mata kai. Mama ta ce. “Hmmm, Neehal bazan taɓa yi miki dole akan abun da ba kya so ba, haka ma Dad ɗinki, ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa, indai ba kya son Auren Ameen babu mai yi miki dole.” Ta d’ago da kanta a hankali tana danne kukan da yake ƙoƙarin kufce mata ta ce. “Da gaske fa Mama ban yi kuka ko na damu ba.” Mama ta ce. “Any way dai, ni dai abun da zan faɗa miki karki saka damuwa a ranki, i know You very well, kuma karki tursasawa zuciyarki karɓar abun da ba kya so, rayuwarki ce bata wani ba karki cuci kanki, ki yi abun da zuciyarki bata so.” Ta yi shiru bata ce komai ba. Mama ta ce. “Yanzu zaki gidan Sadiyan ne? Har ta kira ni a waya tana kin taho, kamar aka ce mata a hanya kika kwana, ita da bata jira.” Ta yi murmushi ta ce. “Auntynah kenan, she missed me that is why.” Mama ta ce. “Ki je ki gaishe da Daddy sai ki tafi, make sure kin dawo gidan nan before Asr, zamu je shopping kin sani.” Ta miƙe ta ce “Insha Allah.” Kafin sha ɗaya ta je gidan Aunty Sadiya. Aunty Sadiya ta tarb’e ta cikin farinciki tare da tsokanar ta da wata sabon gani. Bayan sun gama gaggaisawa suna cikin hira Aunty Sadiya ta ce mata. “What going on Neehal naga kamar kina cikin damuwa?” Ta girgiza kai a hankali tana jin damuwar zuciyarta na ƙaruwa ta ce. “Babu komai Aunty.” Aunty Sadiya ta ce. “Baki iya ƙarya ba Neehal, shi yasa kina yi ake gano ki, faɗa mun mene ne? Yanayin ki ya nuna cikin damuwa” Ta yi shiru k’walla na cika idanunta. Aunty Sadiya ta yi ɗan murmushi saboda ta san dawar garin, Mama ta kira su ta faɗa musu komai ita da Aunty A’isha tun jiyan. Cikin lallami ta ce. “Kin yi shiru Neehal.” Ba tare data d’ago ba ta ce. “Aunty ban san me zan ce miki ba ne.” Aunty Sadiya ta ce. “Abun da yake damunki zaki faɗa mun.” Ta turo baki ta ce. “Daddy ne ya ce wai Yaya zan aura.” Murmushi Aunty Sadiya ta yi ta ce. “Kamar ya? Wanne Yayan?” Ta ce. “Yayana fa, Aunty ki duba abun nan, ta yaya zan iya Auran Yaya?” Ta yi maganar cikin marairaicewa. “Ta yadda kowacce mace take Auran mijinta mana.” Cewar Aunty Sadiya tana dariya. Ta fara hawaye ta ce. “Aunty kin san halin Yaya fa, Ni tsoron shi nake, kuma kuma…. Yana da matarshi fa.” Aunty Sadiya ta ce. “Rigimammiya, wannan rigimar taki ai sai Ameen ɗin.” Bata ce komai ba sai cinno baki data ƙara yi. Aunty Sadiya ta gyara zama tare da dafa ƙafaɗarta, seriously ta ce. “Neehal! Bai kamata Auran Ameen ya dame ki ba ko kuma ya saka ki cikin damuwa ba, kin san Ameen kin san komai nasa fiye da kowacce mace da zai aura a duniya, haka kema ya san komai naki. You know Ameen is a good person, ke zaki faɗi hakan ga wasu ma. To mene abun damuwa dan kin aure shi, mu kanmu sai mun fi jin daɗi da farincikin hakan, hankalinmu sai yafi kwanciya, bamu da fargabar yanda mijinki zai riƙe mana ke ko kuma fargabar wanne irin ƴan’uwan miji zaki haɗu da su. Batun matarsa kuma ba’a kanta zaki zauna ba ita ma ba’a kanki zata zauna ba, hasalima kowaccen ku gidanta daban.” Ta ɓata fuska ta ce. “Ai ita yake so, ni ba ya so na.” Aunty Sadiya ta danne dariyar dake ƙoƙarin k’wace mata dan ta gano mutuniyar tata har da kishi a lamarin nata ta ce. “Wa ya faɗa miki? Yana son ki mana, in ma ba ya son ki sai ki koya masa son naki, sai ka ce ba rainon Yaya Fateemah ba?” Ta juya ido ta ce. “Ai nima bana son shi.” Wannan karon Aunty Sadiya kasa danne dariyarta ta yi saboda yanda Neehal ɗin ta yi maganar. Ta ɗan dara sannan ta ce. “Allah ya shirya ki Neehal.” Nasiha ita ma Aunty Sadiya ta yi mata tare da ƙara nuna mata qualities ɗin Ameen, kamar dai yanda Uncle Usman ya faɗa mata jiya, a ƙarshe dai ita ma ta ce ta dage da addu’a kawai tare da neman zaɓin Allah. Wajen ƙarfe uku ta koma gida, ana yin la’asar suka fita shopping ita da Mama, sai daf da Magriba suka dawo. Bayan Magriba ɗaya daga cikin staff ɗin gidan ya zo ya cewa Mama ta yi baƙo. Ta ce masa ya je ya shigo da shi part ɗinta. Baƙon yana zaune a falon ƙasa ta sauko, mamaki gami da fara’a suka bayyana akan fuskarta ganin Alhaji ne Uban gidan Abban Neehal. Cikin murya mai cike da fara’a ta ce. “Alhaji kai ne a gidan namu yau? Sannu da zuwa.” Alhaji Ali ya yi murmushi yana riƙe da sandar dake taimaka masa gurin tafiya ya ce. “Ni ne Hajiya, da fatan mun same ku lafiya?” Mama ta zauna akan carpet ta ce. “Lafiya k’alau Alhaji, da fatan an zo lafiya? Ya hanya? Ya Iyali? Ya ƙafa?” Alhaji Ali ya ce. “Alhamdulillah, komai lafiya k’alau, ƙafa gata nan sai godiyar Ubangiji, a satin nan ma muka dawo daga Saudiyya na je ganin likita.” Mama ta ce. “Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi, ƙafar tana yin sauki dai ko?” Ya ce. “Alhamdulillah, ana samun cigaba.” Mama ta ce. “Haka ake so, wancan satin nake yiwa Neehal maganar ya kamata ta je ta gaishe ka, sai A’isha ta ce mun itama kwanaki ita ma ta yi zancen hakan a zuciyarta, ta tambaya kuma aka ce baka gari. Ashe kun dawo, Alhaji ka zo da kanka maimakon ka yi waya mu mu zo kai da ba lafiyar ƙafa ba.” Ya yi murmushi ya ce. “Ai wannan shine lafiyar, zumunci shine lafiyar ƙafa, babu komai.” Mama ta ce. “Haka ne, Allah ya saka da Alkhairi, na ji daɗi kuwa sosai, bari na kira Neehal ɗin ku gaisa.” Ya ce. “Toh, Maigidan baya nan ne?” Mama tana miƙewa ta ce. “Yana nan masallacin jikin gida, bari na kira shi a waya na sanar masa zuwanka.” Alhaji ya ce. “To babu laifi.” Sai da Mama ta fara lek’awa ɗakin su Dije ta je su kawowa baƙo abinci sannan ta hau sama ta kira Neehal. Neehal ta sakko da murnarta dan tana k’aunar mutumin a rayuwarta, ta gaishe shi cikin ladabi, ya amsa sannan ya shiga tsokanarta da ina surukinsa? Yaushe zata kai masa shi su gaisa? Ita dai murmushi kawai take kanta a ƙasa. Sai isha’i Alhaji Ali ya tafi, da yake Daddy ya dawo suna ta hira.

Wajen tara da rabi na dare Neehal tana shirin kwanciya saboda ƴar gajiyar fitar da ta yi dake jikinta, kuma tana son ta tashi da wuri gobe fitar safe zata yi zuwa aiki. Mama ta shigo ɗakin, ta kunna light ta ce. “Ko har kin yi bacci ne?” Neehal ta ce. “A’a, ina dai shirin kwanciya.” Mama ta zauna a bakin gado ta ce. “Kin ci abinci kuwa?” Ta ce. “Na ci.” Mama ta yi shiru kawai tana kallon ta, ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa gabanta na fad’uwa.” Mama ta sauke numfashi ta ce. “Shikenan ki yi baccinki, dama zuwa na yi in duba ki.” Ta ce. “Toh Manana sai da safe.” Mama ta ce. “Allah ya kai mu.” Tare da miƙewa ta fice. Neehal ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da lumshe idonta, ta yi tunanin Mama zancen Ameen ta zo yi mata. Ta tashi ta sakawa ƙofar ɗakin key tare da kashe light sannan ta koma ta kwanta. Washegari kafin 8 ta fita, bata dawo gidan ba sai da 2 ta wuce. Bayan ta yi wanka ta fito daga ɗakinta zata sauka ƙasa ta ɗibi abinci ta ci kamar yadda Mama ta umarce ta, tana buɗe ƙofar falon sama da nufin fita suka yi karo da mutum zai shigo. Ta d’ago kanta da sauri bugun zuciyarta na sauyawa saboda k’amshinsa da ya sanar mata da ko waye tun kafin ta kalli fuskarsa……✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button