NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A daren Daddy bai jira komai ba ya kira Abba da wasu cousins ɗinsa ya sanar musu abun da yake faruwa, ya kuma faɗa musu a cikin week ɗin nan yake son akai kuɗin Auren Neehal gidan kawunta. Mama ta ce masa saurin me yake har haka? Ya ce mata baza ta gane yanda yake d’okin abun ba ne, a yanzu ba shi da wani sauran buri a rayuwarsa bayan ya ga Auran Neehal da Ameen….. Kamar yadda ya faɗa ranar Asabar wanda ya kama kwana biyar da yin maganar da yamma suka kai kuɗin na gani ina so gidan Kawu Musa. Ranar Neehal ji ta yi gaba-d’aya kamar ba ita ba, ita ce yau aka karb’i kuɗin Auranta da Ameen? Sai ta dinga jin abun kamar a mafarki, ta tabbata dai Auransu za’a yi da Ameen, ɓoye kanta ta yi a ɗaki ta ci kuka ta k’oshi. Su Daddy ba su baro gidan Kawu Musa ba sai da aka tsayar da lokacin biki wata uku masu zuwa, a haka ma da ƙyar Kawu Musa ya yarda, ya ce abun tunda duk na gida ne no need a ja lokaci, in san ransa ne bai ƙi a yi bikin a cikin two weeks masu zuwa ba. Da Daddy ya zo yana faɗawa Mama ta ce, ta san wannan duk shirin Ameen ne, shi yake zuwa yana zubawa Kawu Musa sintiri akan maganar bikin. A ranar bayan Magriba Ameen ya zo gidan kamar kullum, sai dai tun daga ranar da Neehal ta zura masa da gudu bai kuma ganin ta ba, dan b’uya take yi a ɗaki, ana yin Magriba zata shige ɗakinta ta kulle dan ta san shine time ɗin zuwansa gidan, bata fitowa har sai ta tabbatar ya tafi. Shi kuwa yana sane da ita da duk b’uyan da take, kuma ya san duk saboda shi ne, ƙyale ta kawai ya yi ya ga iya gudun ruwanta dan ya san akwai ranar ƙin dillanci. A ranar Mama ta ce masa ya sanar da Hafsat maganar bikin, ya amsa mata duk da bai so hakan ba, da ya so sai abun ya matso daf sannan ya sanar mata, amma yaya zai yi tunda Mama ta bayar da umarni dole ya bi. Bayan isha’i ya koma gidansa, ya tarar da Hafsat Hakimce a falon ƙasa ta ci uwar kwalliya ta tarb’arsa……….✍️

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

7️⃣8️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.

……….Ranar Friday da yamma wanda ya kama bikin Neehal saura 4 weeks cif, tana zaune a ɗakin Mama suna hira dawowarta kenan daga gidan Alhaji Ali da ta je ta gaishe shi. Wayarta dake kan cinyarta ta fara ringing, ta ɗauka ta duba, ganin Sadik ne yake kiranta ta waro Ido cikin mamaki, duk da ta yi loosed wayoyinta a gidan ƙungiya amma Daddy yana fitowa ya siya mata sabbi dal guda biyu, ita kuma ta yi welcome back na Sims ɗinta. Amma da yake a email take sarving Numbers ɗinta tana ɗora shi akan wayar numbobinta suka dawo, that is why Numbern Sadik ta fito a wayarta with saved tunda bata goge ta ba ko bayan sun rabu. Ta d’aga tare yin sallama cikin sanyin muryarta. Sadik ya amsa mata tare da faɗin. “Neehal kwana dubu kin manta da Yayanki ko? Ko ɗan kira na mu gaisa ma ba kya yi.” Ta ɗan murmusa ta ce. “Ka yi haquri Ya Sadik dan Allah, na san bani da bakin da zan kare kaina a gurinka.” Ya ce. “Shikenan ya zan yi tunda kin ce Allah amma da ban yi niyyar haqura ba.” Ta ce. “Toh Na gode, ya su Maamah da Batul?” Ya ce. “Suna nan k’alau, ya Mama da Daddy?” Ta ce. “Duk suna lafiya.” Ya ce. “Masha Allah, ki gaishe su Please.” Ta ce. “Za su ji Insha Allah.” Ya ce. “Na manta lefin naki biyu ne ma a gurina, ashe bikinki ya taho amma babu labari Neehal?” Cikin mamaki ta ce. “A ina ka ji Ya Sadik?” Ya ce. “Zancen duniya yana b’uya ne? Amma dai Neehal baki kyauta mun ba da baki faɗa mun ba sai da abun ya zo daf nake ji.” Ta ce. “To ka yi haquri, wannan ma na karb’i laifina.” Ya ce. “Na ƙi yin haqurin.” Ta shagwab’e ta ce. “Haba Yayana ni ce fa, ka haqura Please.” Ya sauke numfashi ya ce. “Shikenan na haqura, Insha Allahu a cikin satin nan zan zo in gaishe da Mama.” Ta ce. “Toh Shikenan sai ka shigo, Allah ya kawo ka lafiya.” Ya ce. “Amin, sai anjima.” Sai ta ji kamar ta tambaye shi yaushe ne nasa bikin, amma dai ta fasa ta ce. “Allah ya kai mu.” Tare da katse wayar. Ta kalli Mama da hankalinta yake kan wayarta tana latsawa, can ƙasan ranta moment ɗin soyayyarsu da Sadik yana dawo mata. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ta ce. “Mama Ya Sadik ne ya kira ni, ya ce yana gaishe ki.” Mama ta ce. “Ina amsawa.” Da daddare kamar haɗin baki sai ga kiran Ahmad ya shigo wayarta. Sai da gabanta ya faɗi saboda rabon da su yi waya da shi tun satin bikinsa da ya yi mata ban gajiya. Ta d’aga tare da ɗan bata fuska kamar yana ganin ta. Ya yi mata sallama ta amsa can ƙasan mak’oshi. Cikin taushin murya ya ce. “Princess!” Ta lumshe ido a hankali ta ce. “Na’am Uncle.” Ya ce. “How are you?” Ta ce. “Lafiya k’alau.” Ya ce. “Uhm, me Ahmad ya yi aka daina kula shi? babu kira babu magana a chat, sai dai in na je gidan Ummi ta ce mun kun yi waya da yaranki.” Ta turo baki bata ce komai ba, a ranta tana cewa. ‘Kai da ka yi auranka ka manta da ni amma kai kake mun complain.’ Ya ce. “Hello, Princess.” Ta ce. “Na’am.” Ya ce. “Why are you silent?” Ta ce. “Nothing, Ka yi haquri Uncle.” Ya ce. “No prob, na ji wani labari a gurin Ummi.” Ta ce. “Labarin me?” Ya ce. “Na auranki mana.” Ta yi shiru bata ce komai ba. Ya ce. “Hmm, dole ki yi shiru tunda ke ma kin san baki kyauta ba, yanzu Princess ace za’a yi bikinki amma You can’t tell me, sai da Mama ta kira Ummi ta faɗa mata sannan nake ji a gurinta.” Yanda yake maganar ta gane ya ji haushi sosai, kamar zata yi kuka ta ce. “Ka yi haquri Uncle.” Ya ce. “No, ai I’m not your Uncle right? Shi yasa baki faɗa mun bikinki ba” A shagwab’e ta ce. “You Are.” Ya ce. “To me yasa baki faɗa mun ba.” Ta ce. “Babu komai fa da gaske, I’m sorry.” Ya ce. “Ba zan haqura ba, dan na san da ban kira ki ba yanzu baza ki kira ni ba.” Ta ce. “Zan kira ka mana.” Ya ce. “Eh zaki kira ni, amma sai nan da kamar 2 weeks haka ki ce na kawo miki twins ko?” Ta yi murmushi ta ce. “To yanzu tunda ka kira ni ai shikenan my Uncle sai ka yi haquri.” Ya ce. “Na haqura, amma duk da haka I will punish you, punishment ɗin kuma shine bazan kawo miki twins ba.” Ta ce. “Tab’, aikuwa da kiranka zan yi inta maka kuka.” Ya yi murmushi mai sauti ya ce. “Zaki iya ai, cry cry Baby.” Ta ce. “Yanzu na girma na daina kukan ai.” Ya ce. “Na san baki daina ba, zaki dai ki daina.” Ta ce. “Ya Auntynah?” Ya ce. “She is fine.” Ta ce. “My regard please.” Sun daɗe suna hira da shi wadda ta saka su duka su biyun a cikin nishad’i, sai da ta ga goma ta wuce sannan ta yi masa sallama ta kashe wayar ganin ba shi da niyyar barin wayar, ta rungume wayar a ƙirjinta tana jin tsohon tsumin Ahmad na ƙoƙarin tasowa daga cikin zuciyarta, she missed him alot in her life. Ta lumshe idonta da ya ciko da k’walla. Shi kuwa Ahmad bin wayar ya yi da kallo bayan ta kashe kamar zai gan ta a cikin screen ɗin wayar, har yanzu yana son Neehal babu yadda zai yi ne kawai tunda ƙaddara ta raba su. Ya lumshe idonsa yana hango ta a cikin zuciyarsa tana murmushinta mai kyau, ba ya jin akwai macen da zai kalla a duniyar nan ya ga kyawunta kamar yadda nake ganin na Neehal. Ya buɗe ido a hankali yana sauke numfashi sannan ya tashi ya nufi ɗakin da Matarsa take bacci, wadda take fama da laulayin ɗan ƙaramin cikinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button