NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Washegari da safe sai ga Aunty Hauwa matar Uncle Umar ta zo gidan Mama, da tarkadu na kadarorin Neehal da littafi dake ɗauke da record ɗin duk wata dukiya ta Neehal da inda take da yanda ake juya ta. Mama ta yi mata godiya sosai tare da d’unbin Alkhairi. Ta sanarwa Neehal Uncle Umar ba shi da lafiya, cutar hawan jini na damun shi. Mama ta cewa Neehal ta shirya su koma tare da Aunty Hauwa ta dubo jikin nasa. Bayan sun je Neehal tana ganin shi ita sarkin kuka sai da ta yi kuka saboda yanayin jikin nasa da halin da yake ciki. Shi ma kukan ya saka cikin numfarfashi yana roƙon ta gafara akan zaluntar da ya yi a rayuwa. Ta ce ita ta yafe masa dama kuma bata riƙe shi a ranta ba. Ta kira Mama ta sanar mata halin da ake ciki, Mama ta ce ta saka shi a Mota su kay shi asibiti zata je asibitin yanzu ita ma. Suna zuwa aka bashi gado, zuwan su ba jimawa Mama ta ƙarasa asibitin, ita ta biya dukkan wani charges da akay musu. Washegari Sunday da daddare aka kay lefen Neehal gidan Kawu Musa, a daren Kawu Musa yasa aka juyo da kayan zuwa gidan Mama ya ce ai nanne gidan iyayen Neehal mene sai sun wahalar da kansu sun kay gidansa. Kaya masu kyau da tsada na gani na faɗa sune a cikin lefen Neehal, ba ƙaramin tatsar Ameen kuɗi su Aunty su kay ba, dan ma kusan rabin kuɗin Daddy ne ya bayar. Akwatuna goma sha biyar ne cif manya masu tsada, su kansu abun kallo ne. Banda wasu abubuwan da aka zubo a cikin Basket ɗin kaba da kuma wasu manyan jakunkunan leda guda biyu.

Washegari misalin ƙarfe biyu na rana Ameen ya koma gidansa daga gurin aiki, bai shiga cikin gidan ba sai ya kira mai gadi da mai bawa flowers ruwa ya ce musu su shigar masa da akwatunan Hafsat na kayan faɗar kishiya dake cikin Motarsa. Suka amsa masa shi kuma ya shige ciki. Hafsat tana bedroom ɗinta tana shiryawa, fitowarta kenan daga wanka ta ji shigowar Motarsa gidan, a gaggauce take shiryawa dan kar ya shigo bata kammala shirinta ba. Bayan ya hau upstairs ɗin ma bai shiga ɗakin nata ba sai ya zauna a falo yana jiran su mai_gadi su shigo da kayan. Suna kammala shigowa da shi ba jimawa sai ga Hafsat ta fito cikin shirinta tana ta zabga murmushi. Ameen ya d’ago daga danna wayarsa da yake ya kalle ta. Turus ta tsaya murmushin fuskarta na ɗaukewa, da tsantsar mamaki take bin kayan da kallo, set na akwatuna mai shida sai ƙatuwar jakar leda guda ɗaya.

Ta dube shi cikin mamaki ta ce. “Baby wannan kayan fa, na wa ye?” A dake ya ce. “Naki ne, na faɗar kishiya ake cewa ko?” Ta tsaya kawai kamar status tana kallon shi na wasu sakanni, sannan kamar wata sabuwar kamu ta ce. “Wasa kake yi Baby, na san na wani ne ya kawo maka ajiya shine kake mun wasa.” Ta ƙarashe zancen tana nufar kayan. Ya yi ɗan murmushi ya ce. “My dearest wife uwar gidan Ameen, babu maganar wasa anan, aure zan yi nan da three weeks da kwanaki, so waɗannan kayan naki ne, and kuma ki faɗi me kike so na canza miki a gidan nan, kafin lokacin bikin sai a canza.” Ta saki baki tana kallon shi ganin yanda yake maganar babu alamar wasa a fuskarka. Wata irin bugawa ta ji ƙirjinta ya yi mata. Cikin raunin murya ta ce. “Dan Allah da gaske Al’ameen Aure zaka ƙara? Baka ce mun ka fasa ba?” Ya yi mata wani kallo bai ce komai ba. Sai kuma ya miƙe ya yi ƙoƙarin janyo ta jikinsa ya rarrashe ta ganin ta fara hawaye. Ta yi baya cikin sauri a tsawace ta ce masa. “Karka kuskura ka taɓa ni, munafuki kawai macuci azzalumi.” Sai kuma ta fashe da kuka. Ya tsaya kawai yana kallon ta cikin mamaki da ɓacin ran sunayen data kira shi da su. Ta juya ta shige ɗakinta da gudu tana kuka. Ya lumshe idonsa ya buɗe sannan ya ɗauki mukullin Motarsa dake kan kujerar da ya zauna ya juya ya fice daga gidan. Ba ya son ya cigaba da zama a gidan Hafsah ta yi masa abun da ba zai jure ba, ya ɗauki hukunci a kanta a zo a samu matsala. Yana fita Hafsat ta fito daga ɗaki kamar mahaukaciya tana kuka ta shiga bubbud’e akwatunan tana cilli da kayan ciki a tsakiyar falon. Tana yi tana faɗin. “Wallahi Ameen baka isa ba, ka yi kaɗan ka yi mini kishiya, zan ga ta yanda za’a yi auran nan ina raye.” Sai da ta gama watsar da fiye da rabin kayan sannan ta sauka ƙasa a matuƙar fusace ta shiga kitchen, su Harirah suka bi ta da kallon mamaki ganin ta a haka babu maraba da mahaukaciya yanda take huci tana zazzaro ido. Taɓarya ta lalubo ta ɗauko ta fito falon ta fara faffasa abubuwa, ai da gudu su Harirah suka yi ɗakinsu suka banko ƙofa. Harirah ta dubi Baraka ta ce. “Mun shiga uku, Hajiya ko ta haukace ne?” Baraka ta ce. “Ko kuma dai ta tayar da aljanu ba, dan wannan aikin sai dai su.” Dai-dai lokacin Hafsah ta rantab’awa show glass taɓarya, ji kake tassss gurin da ta dokawa taɓaryar ya yi ƙasa a dagargaje. Ai cikin rige_rigen gudu su Harirah har faɗuwa suke suka banka toilet suka rufo cikin tsoro tare da fargabar har Hafsat ta gama da falon ta dawo kansu. Duk wani abun fasawa a falon sai da Hafsat ta yi masa illa, sannan ta hau sama ta yiwa na saman ma. Tana zuba uban gumi da haki ta zaɓi jaka ta zira takalmi ta yi gidansu tana kuka. Su Harirah dai suna toilet rungume da bango ba su san ma ta fice ba, suna tsoron kar su fito aljanun su haɗa da su. Sai zazzare ido suke cikinsu na ƙugi.

Hafsah ce zaune a falon gidansu tana ta rusa kuka, tunda ta je gidan kusan minti talatin kukan kawai take yi, Mom har ta gaji da tambayar ta abun da ya faru. A harzuk’e Mom ta ce. “Daughter wai ba tambayarki nake yi abun da ya faru ba, kin taho a hargitse kamar wata korarriya kin zo sai kuka kike mun kin ƙi yin magana.” Ta ɗan tsayar da kukan ta ce. “Mom ashe Ameen yaudarata ya yi bai fasa Auran da ya ce zai yi ba.” Mom ta ce. “Kamar yaya kenan?” Cikin kuka ta ce. “D’azu ya kawo mun wasu tsinannun kaya wai kayan faɗar kishiya, wai saura 3 weeks bikinsa.” Sai ta kuma fashewa da kuka. Mom ta ce. “Kan uban nan, lallai ma yaron nan ɗan iska ne, mu zai yiwa haka? To wallahi bai isa ba, zai zo gidan ya same ni ne, sai dai ya zaɓa ko ke ko auran da zai ƙara. Ki daina kukan nan haka da’alla, har wani shid’ewa kike kamar wadda aka cewa na mutu, yanzu zan kira Alhaji in sanar masa halin da ake ciki, dan yana dawowa ya san matakin ɗauka cikin gaggawa. Shi kuma mara kunyar zai zo ya same ni har inda nake, na san zai kwaso jiki zalalo_zalalo ya zo biko, anan zan masa wankin babban bargo in ci masa mutunci. Yaro da ana ganin ka kamar na Allah ashe ka ce na shaid’an ne kai, banda ƙaddara mai zai haɗaki aure da wannan ai kin fi ƙarfin ajin shi.” Ita dai Hafsah kukanta kawai take yi, bata ma saurarar sababin Mom.

Ameen bai koma gidansa sai bayan Magriba, a lokacin ya ga aika_aikar da Hafsah ta yi. Da farko gani ya yi kamar ba Falon gidansa da ya saba gani ba ne kodayaushe tsaf, ya tsaya yana kallon Falon kamar wanda aka yi yaƙi a cikinsa cikin mamaki. Ya tsallake abubuwan ya haura sama dan jin ba’asin faruwar hakan a gurin Hafsah. Sai ya tarar falon saman ya ci uban na ƙasa a haukacewa. Yanda aka yi da kayan da ya kawowa Hafsah shi ya tabbatar masa gaba-ɗaya wannan aikin nata ne. Ransa ya yi matuƙar ɓaci ba kaɗan ba, saboda kawai ya ce zai ƙara Aure? Mene matsalar mata da ƙara Auren Namiji ne? Ubangiji ne fa ya halatta a yi, da wannan haukan ba gwara ki dage da Sallah kina addu’a da kai kukanki gurin mai duka akan Allah ya baki kishiyar ta gari ba, idan mai sharri ce ki roƙi sharrin ya ƙare a kanta ke kuma ya tsare ki daga sharrin. Amma sai sabon jahilci da hauka zaki tsiro. Cikin tsantsar ɓacin rai ya nufi ɗakinsa ya yi wanka ya fito. Kamar yadda ya zata bata gidan, ya sauka ƙasa ya tarar su Harirah wanda jin shigowarsa yasa suka fito falon, amma duk da haka a tsorace suke. Fuska a cukule ya ba su umarnin gyara gidan sannan ya fice. A gurin gyaran ne su Harirah suka gane dawar garin, wato dalilin da yasa Hafsah ta yi wannan haukan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button