NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Saura sati biyu biki Mama ta ɗauko mai gyaran jikin data gyarawa Neehal lokacin bikinsu da Sadik ta fara yi mata. Haramar biki fa ta ɗauka sosai, Daddy ya ƙara gyara gidan Mama, duk wani furniture’s dake part ɗinta an canza shi an saka sabo, haka ma cotton’s da carpet’s. Ga contributions da Mama take samu ko ta ina, haka ma Neehal ɗin. A lokacin ne Neehal ta fara nuna damuwarta ta fara k’unci da koke_koke irin wanda ta yi lokacin bikinsu da Sadik, ganin dai da gaske auran nata za’a yi, tafiya zata yi ta bar Mamanta. Ameen ma shirye-shiryen bikinsa kawai yake yi ya ajiye batun wata Hafsat a gefe, ya ce idan ta gaji da zaman gidan nasu ta dawo, dan shi dai ko zata shekara ba zai je wani biko ba. Mama bata san Hafsat ta yi yaji ba dan bai faɗa mata ba, Daddy ma haka. Kuma ko kaɗan ba ya nuna alamar bata gidan nasa. Wannan karon Mama ta ce babu abun da za’a yi na events, Ranar d’aurin Aure kawai zata yi yini da daddare a miƙa Amarya gidanta. Haneefah da sauran mate ɗinsu na Familyn su Mama ba su so hakan ba, sai dai ita Neehal hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, dan bata son taro ko kaɗan. Aunty Sadiya dai ta ce sai sun yi Kamu ranar Alhamis ko a gida ne an kira masu kiɗan ƙwarya sun buga musu sun jajige baza’a yi biki lami ba. Tun ranar Sunday wanda ya kama saura kwana biyar d’aurin Aure Ahmad ya kawo twins, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Neehal ba. Ya kuma bata kuɗi masu kauri a matsayin gudunmawa, wanda sai da ya ɓata rai sannan ta karɓa. Uncle Usman ma ranar ya sauka shi da iyalansa. Ana i jibi biki gidan ya ɗinke da jama’a, dangin Mama dana Daddy da kuma na Neehal, wannan karon sun mata kara babu laifi sun zazzo, wasu ma bata san su ba sai an faɗa mata dangantakarta da su take ganewa, Kawu Musa ne duk ya yi musu tilas suka zo, da kansa ya je har Gabasawan ya kai musu abun gayyata. Matan Ƴaƴan Baffa ma sun zo da ƴaƴansu. Ranar aka yarfawa Neehal ƙunshi a fararen hannunta da ƙafarta, ƙunshin ya yi matuƙar kyau akan fatarta data sha gyara bana wasa ba. Sai walwali take tana hasakawa, ga wani k’amshi mai daɗin gaske dake tashi a jikinta. Ita akaran kanta ta san ta sauya, dan wannan gyaran jikin har ya fi wancan da aka yi mata kyau. Sai ta tsaya a gaban mudubi ta yi ta kallon kanta tana murmushi ita kaɗai……….✍️

Wanga novel yaushe zaka ƙare ne?????????

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

7️⃣9️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.

……….A safiyar ranar Hafsat tana zaune a ɗakinta na gidansu abun duniya duk ya ishe ta, tunda ta zo gidan bata da aiki sai kuka, duk ta rame ta lalace ko abinci sai uwar ta yi yaƙi da ita take tsakura ta ɗan ci. Tana son Ameen kuma baza ta so su rabu ba, amma kuma baza ta iya jure kallon sa da wata macen ba. Gashi kuma Mom ta k’wace duk wayoyinta wai saboda kar ta kira Ameen ta zubar musu da kima a wajensa dan ta san halinta, shi kuma ya ƙi kiran ta balle ya zo, gashi Dad ɗinta baya nan yana London. Abin da yake ƙara d’aga mata hankali idan ta tuna Ameen yana can yana shirin bikinsa da wata ita ya banzatar da ita, ita yanzu burinta ɗaya a duniya ta san wa Ameen zai aura, ta ga me matar ta fita da yasa Ameen ɗin zai aure ta, ƴar waye a ina kuma take? Kamar amsar tambayarta ta ji an turo ƙofar ɗakin, ta d’aga kanta da sauri tana share hawayen fuskarta. Wata ƙawarta ce mai suna Jalilah ta shigo Mom na biye da ita a baya. Ba tare da ƙawarta_ta ta damu da yanayin da ta gan ta a ciki ba ta ce. “Hafsy wannan ba mijinki ba ne Ameen?” Tana miƙa mata wayar hannunta ta yi maganar. Hafsah ta karɓa tare da ƙurawa screen ɗin wayar ido. Katin d’aurin Auren Ameen da Neehal ne irin wanda ake yi a yanzu a waya a saka wak’a, amma ita ba wannan ne damuwarta ba, sunan wadda ta gani a matsayin amaryar shi yasa zuciyarta bugawa da ƙarfi. FATEEMAH MUHAMMAD TAFIDA (NEEHAL). Ta murza idonta a tunaninta idon ne ya ganar mata ba dai-dai ba, amma still dai abun da ta gani shi ta ƙara gani. Wata uwar ƙara ta saki tare da sakin wayar, Jalilah ta yi saurin tare abarta cikin tsoron kar ta faɗi ta fashe. Hafsat ta miƙe tsaye jikinta na bari cikin tashin hankali ta ce. “Mom, kin ga abun da na gani kuwa? Neehal Ameen zai aura, yarinyar da Mamansa take riƙo.” Mom ta ce. “Na gani nima Daughter, auran cin amana zai yi.” Cikin ƙaraji Hafsat ta ce. “Ameen why? Me na yi maka? Ka rasa dawa zaka haɗa ni kishi sai da wannan aljanar yarinyar, yarinyar dana tsana.” Sai ta fashe da kuka ta ce. “Munafuki, komai ya ce Neehal Neehal ashe son ta yake yi, yarinyar ta ƙi auruwa shine shi zai aure ta, in ma wani mugun abun ne da ita ya shafe mu kenan? (Hafsah bata san me ya faru ba akan case ɗin Daddy da Neehal, da yake an ɓoye abun ne babu wanda ya ji sai wanda ƴan’uwa na jiki.) Jalilah ta ce. “Na daɗe da ganin wannan videon tun last week, ina ta kiran wayarki bata shiga, a online ma bana ganin ki kwata_kwata. Shine na ce bari dai na je gidanki na tabbatar da gaske mijin naki ne zai yi aure, na je kuma na tarar bakya nan sai masu aiki, suka ce mun kina gida.” Hafsah ta haɗa kanta da jikin wardrobe tana kuka sosai, tashin hankalinta ya ninku akan na da, Neehal fa, yarinyar data tsana a duniya tun kafin ta gan ta, ita Ameen zai aura, ashe dama son ta yake? Ko kuma ta ce soyayya suke? Da ƙyar Mom da Jalilah suka rarrashe ta. Mom ta kira ƙanwarta Safiya suka haɗu suka zauna suna zagin Ameen da Neehal har Mama ba su ƙyale ba suka dinga cewa ita ce munafuka ita ta haɗa komai. Aunty Safiya ta kwantarwa da Hafsat hankali ta ce ta bar komai a hannunta, ta yi mata alƙawarin Ameen sai ya zo har inda take yana kuka da idonsa tare da begging ɗinta, wannan aure da zai yi kuma sunansa matacce.

Da daddare Neehal tana zaune a cikin ƴan’mata suna ta tsokanarta, wannan ta ce mata daga jibi shikenan zata shiga daga ciki. Su Haneefah ne sakaran sharri, harda cewa yanda ta sha gyaran jikin nan ta yi kyau Allah yasa kar ta zautar musu da Yaya. Ita dai idanunta a lumshe tana tunanin abun da ya dame ta bata su take ba. Damuwarta yanda rayuwar Auranta zata kasance, tana yawan jin ana cewa kowanne Aure yana da tasa matsalar da kuma k’alubale, to ita ko wacce matsalar zata je ta tarar sai Allah? Ta sauke numfashi tana tuna yanayin mijin da zata aura da yanda Auran nasu ya kasance, zuciyarta ta kasa hasaso mata yanda rayuwar auren nasu zata kasance, ga kuma wani ƙarin matsalar kishiya, ta riga ta san Hafsat bata son ta tun a da ballantana kuma yanzu. Ta sauke ajiyar zuciya tana jin zuciyarta babu daɗi ga tarin fargaba a cikinta. Muryar Aunty A’isha ta ji a kanta tana kiran sunanta. Ta buɗe ido tare da amsawa. Aunty ta ce. “Tunanin me kike yi haka inata magana baki ji ba? Ga hayaniya ta cika ɗakin amma ke baki ma san ana yi ba.” Cikin sanyin murya ta ce. “Babu komai Aunty.” Aunty ta ce. “Koma da akwai ki yi addu’a, addu’a makamin mumuni ce, ba wai ki zauna ki yi ta tunani ba.” Ta ce. “Insha Allah Aunty.” Aunty ta ce. “Yawwa, tashi mu je part ɗin Daddy Umma na son ganin ki.” Ta miƙe ba tare da yi magana ba suka fice. A falo suka yi kicibus da Hajiya, ta dubi Neehal ta ce. “Ke wai ya kike abu da sanyin jiki ne kamar kazar da k’wai ya fashewa a ciki? Ko baki da lafiya ne?” Neehal ta turo baki bata ce komai ba. Aunty ta yi murmushi ta ce. “Mood ɗin amarci ne kawai.” Hajiya ta ce. “Mudun amarcin me? Ki zage jiki ki dinga abu cikin kazar_kazar da annashuwa mana, kin wani cukele fuska kamar waccan uwar taki Saratu da bata k’aunar fara’a. Wai ina Aminun ne? Tunda na zo ban gan shi ba, ko ɗan zancen nan ma shi ba ya zuwa ne?” Aunty ta yi murmushi ta ce. “Hajiya gida fal da baƙi ina zaki gan shi?” Hajiya ta tab’e baki ta ce. “Bai ga damar zuwan ba ne, amma Aminu ai ba wata kunya ya cika ba.” Aunty ta kama hannun Neehal suka yi gaba. Umma kaɗai suka tarar a Extra room ɗin dake part ɗin Abba. Neehal ta zauna a ƙasan gado Aunty ta juya ta fita. Faɗa da nasiha sosai Umma ta yiwa Neehal akan zamantakewar aure, ta nusar da ita abubuwan da ba’a so a zaman aure da kuma wanda ake so, ta nuna mata mahimmancin tsafta, addu’a, iya sarrafa girki, ladabi da biyayya da iya kula da miji a rayuwar aure. Sai kuma uwa uba haquri, wanda mutane da dama tun kafin Umman suke ta faɗa mata aure ɗan haquri ne, sai ta yi haquri. Mama ma ta zo ta ɗora mata da nata faɗan. Washegari aka yi Kamu kamar yadda su Aunty Sadiya suka shirya, a harabar gidan Maman aka yi decoration mai kyau na gurin zaman amarya, aka jera fararen kujerun roba na zaman baƙi. K’wararrun masu kiɗan ƙwarya suka zo suka buga kiɗa manyan mata suka cashe, an ci an sha an yi bidiri, kuɗi kamar tsinto shi ake yanda family da k’awayen Mama suka dinga zuba lik’i, Mama ta yi kyau sosai, ta sha kiɗan uwar amarya uwar ango a gurin masu kiɗan ƙwarya. Neehal ma ta yi kyau sosai ta sha make up, tsoffi suka feshe ta da turaruka aka kamata (Kamun amarya). Gidan ya cika ya yi mak’il da jama’a. Amarya dai dauriya kawai take amma k’iris take jira ta fashe da kuka, halin da zuciyarta take ciki ba zai misaltu ba, ita kaɗai ta san me take ji. Ga jama’a sun hana ta sakat da ɗaukar hotuna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button