NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Neehal ta na zaune a office d’inta ta na duba wasu takardu Haneefah ta shigo office d’in bakinta ɗauke da sallama. Neehal ta amsa mata tare da dire da takardun a kan table ɗin gabanta. “Har kun gama editing ɗin?” Neehal ta tambayi Haneefah dake ƙoƙarin zama. Haneefah ta ce “Eh, ai time ɗin labaran ya kusa” Neehal ta ce “Hakane” sannan ta gyara zama ta na duban Haneefah ta ce “Haneefah!” Haneefah ta dube ta da mamaki domin tasan tunda Neehal ta kira ta da sunanta abu mai mahimmanci za ta faɗa mata. Neehal ba ta jira amsar Haneefah ba ta cigaba da magana. “Haneefah zuciyata ta na cikin fargaba gami da zullumi da tsoro a kan kisan Anwar, Ina tsoron a ce ta dalilina aka kashe Anwar” Haneefah ta ce “Me ya sa ki ke cewa haka ne wai Neehal, ta yaya kisan Anwal zai zama saboda ke?” “Saboda an kashe Jameel ma a baya.” Haneefah ta ce “Ki dena tunanin saboda ke aka kashe su, na faɗa miki wannan maganar tun kafin yau amma kin k’i ki daina ta, akan me za’a na kashe miki samari?” Neehal ta ce “Shine ban sani ba Haneefah.” Haneefah ta mik’e ta koma kusa da Neehal ta dafa kafad’arta, cikin son kwantar mata da hankali ta ce “Kin ga Neehal kar ki saka wannan abun a ranki har ya yi tasiri a cikin zuciyarki, Jameel da Anwar lokacin mutuwar su ne ya yi, da lokacin su bai yi ba babu wanda ya isa ya kashe su. Kawai Allah ya yi ajalinsu ya na hannun waɗanda suka kashe sun ne, amma wlh Neehal ni har yanzu zuciyata ba ta yarda saboda ke a ka kashe su Anwar ba.” Neehal ta sauke numfashi ta ce “Amma kuma Haneefah yanayin yanda ake kashe sun ɗaya ne, duk harbe su ake fa.” Haneefah ta ce “Kar ki yi la’akari da wannan, duba da yanda zamani ya sauya, yanzu ai ko barayi ne za su yi sata zai yi wahala ki gansu da wuk’a ko wani makamin, sai dai yara, amma waɗanda suka shahara da bindigu suke zuwa, Dan  haka idan an harbe Anwar da Jameel ba hakan ya na nufin mai kisan ɗaya ba ne.” Neehal ta yi shiru kawai ta na kallon Haneefah tare da auna maganganunta a mizanin nazari. Bayan kamar minti uku ta ce “To Haneefah ko dai aljanu ne?” “Haba Neehal, wanne aljanu kuma? Kar ki ɗauki alhakin bayin Allah, idan aljanu ne kuma sai su dinga harbe mutum, su da suke da hanyoyin cutar da mutane kala_kala.” Haneefah ta katse Neehal da faɗin haka cikin tarar numfashi. Neehal ta runtse idonta kawai tare da dafe kanta cikin kullewar kwanyarta. Haneefah ta saki kafadunta ta koma kujerar da ta taso sannan ta ce “Da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, idan da rabon shan numfashin mutum a duniya ko a na yanka naman jikinsa sai ya rayu, idan kuma kwanan mutum ya ƙare ko da lafiyar sa k’alau dole sai ya amsa kiran mahaliccin sa, ki sa wannan a ranki Allah shine mai yin komai a kuma sanda ya so.” Neehal ta ja wani gwauron numfashi ta ce “Tabbas maganganunki gaskiya ne Haneefah, kuma Insha Allahu zan cire wannan tunanin daga raina, amma zan dage da addu’a a kan Allah ya bayyana gaskiyar al’amari.” Haneefah ta ce “Ko ke fah, su kuma sai ki ta musu addu’ar neman gafara da dacewa a gurin Ubangiji” Neehal ta ce “Insha Allah, Ni kuma tawa ƙaddarar kenan duk wanda na so ba ma kasancewa tare sai mun rabu.” Yanda Neehal ta yi maganar sai da Haneefah ta murmusa ba tare da ta sani ba, Neehal ma murmushin ta yi domin kalaman Haneefah sun fara sanyaya mata zuciya. Ta na murmushin ta ce “Dariya ma na baki ko?” Haneefah ta ce “Ai yanda ki ka yi maganar ne kamar wata sabuwar marainiya.” Neehal ta ce “Me ne marabata da sabuwar marainiyar?” “Marabar ku ki na da iyaye samari kawai ki ka rasa, kuma suma za ki samu wasu nan gaba wanda har za ki manta da na baya.” Neehal ta mata wani kallo ta ce “Hmmmm, ki na tunanin zan iya ƙara son wani ɗa namiji a duniyar nan ne? ai ni da soyayya kuma sai dai na ga a na yi” Haneefah ta yi wani ɗan murmushi ta ce “Zance ma kenan, za ki yi ta zama ne ba ki yi aure ba? Ko kuma za ki yi Aure ba tare da soyayya ba? Ni na faɗa miki ki rubuta ki ajiye sai kin so wani fiye da son da ki ka yi wa Jameel da Anwar.” Neehal ta tab’e baki ba ta ce komai ba, dan ita ba ta ɗauki maganganun Neehal da mahimmanci ba, ban da haka ta yaya za ta so wani fiye da son da ta yi wa Anwar d’inta? Ai tun ranar da Anwar ya rasu ta yi wa kanta alƙawarin ta bar soyayya har abada.

Yau ma gidan Mama Haneefah suka wuce bayan sun tashi daga aiki, suna shiga ta ga Hameedah ita ba ma tasan ta zo ba, dan Neehal ta ma manta da zuwanta ba ta faɗa mata, ita kuma rabonta da gidan tun ranar Alhamis. Suka yi sallama, Hameedah ta d’ago ta musu wani kallo kamar ta ga kashi ta ƙi amsa musu sallamar. Haneefah da ta fi Neehal saurin ɗaukar zafi ta ce “Sai ka ce mutum ba musulmi ba a yi sallama ya na ji ya ƙi amsa wa.” Aiko Hameedah dama kaɗan take jira, dan ta je part d’in Ameen za ta masa shirme ya korota, gashi dama ta tsani Haneefah kamar yadda ta tsani Neehal. Mik’ewa tsaye ta yi kamar wata sabowar kamu ta fara ɗura_ɗuran ashar ta na zagin Haneefah har ma da Neehal da ta bata kula ta ba. Haneefah za ta biye mata Neehal ta ja ta su ka hau sama. Bayan sun shiga daki Neehal ta dube ta ta ce “Mai ya sa ki ka kula ta dan Allah? Kin san halin ta fa.” Haneefah ta na ware rolling d’in kanta ta ce “Amma  dai ai gaskiya na faɗa mata, ita say ta yi ta yi wa mutane kallon banza ta na musu masifa, ni kuma zan mata shiru ne, ai ba tsoron ta nake ba.” Neehal ta ce “Na san bakya tsoron ta dama, amma dan Allah ki dai na kula ta, kome za ta yi.” Haneefah ta ce “Shikenan Insha Allahu haka ba za ta kuma faruwa ba.” Washegari tun safe su Hameedah suka shirya suka wuce Abuja. Mama ta haɗa musu tsaraba kamar yadda take wa kowa idan ya zo gidanta. Hameedah kuwa kamar karta tafi saboda ganin Ameen da take, shi kuwa ko kallo ba ta ishe sa ba. Hameedah ta na bala’in mutuwar son Ameen, shekarun ta kusan 30 amma ta ƙi aure wai jiran shi take, Family kowa ya ɗauka soyayya suke nan kuwa ita kaɗai take haukan ta. Mahaifiyarta kullum ta zo sai ta ce wa Dad ya kamata a saka ranar bikin su, a duk lokacin da ta fadi haka sai Dad ya yi murmushi ya ce “Suwaiba Na fi so Ameen ya yi maganar Hameedah da kansa, ko kuma so ki ke ya raina mini ‘yar tawa ya ga kamar neman kai muke da ita.” Ita kuwa Suwaiba (Momy) sai ta kada baki ta ce “Yoo tunda shi ya ƙi magana ai mu sai mu yi, abu duk na gida ai duk ɗaya ne.”

Da daddare Mama ta na part d’in Dad suna tattaunawa akan maganar Ameen ɗin da Hameedah, ya na faɗa mata yanda Mommy’n Hameedah ta takura masa da zancen ayi_ayi aurensu. Mama ta ce “Ni kaina Gen. na matsu Ameen ya yi aure, na gaji da yawo da hankalin da yake mana.” Dad ya ce “Hakane, nima ina son na ga ya yi auren, amma bari na kirashi na ji ra’ayinsa a kan Hameedan, tunda ni bai taɓa mini batun ta ba da kansa.” Mama ta ce “Toh.” Dad ya kira Ameen a waya ya sanar masa ya na son ganinsa yanzu. Bayan 10 minutes sai gashi ya zo, ya zauna a ƙasa ya na duban Dad ya ce “Ga Ni Dad” Dad ya ce “Dama akan maganar Hameedah ne, tunda auren Neehal ɗin Allah bai nufa ba, dama shi muke jira a yi sai mu yi zancen naka, to yanzu ka na son Hameedan ne?” Ameen ya d’ago ya dubi Dad, cikin nutsuwarsa ya ce “Ni fa Dad ba na son Hameedah, Ina da wadda nake so!” Da sauri Mama da ta k’ura masa ido ta ce “Kamar ya ba ka son ta?” Dad ya d’aga mata hannu ya na ɗan murmushi, sannan ya dubi Ameen ya ce “Wa ce wacce ka ke so ɗin?”……….✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button