NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL
NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ban yi editi ba, a yi haquri da typing errors.
By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡
By
Zeey Kumurya
8️⃣0️⃣
……….Kamar yadda yau ta kasance ranar farin ciki ga su Mama da duk wani masoyinsu haka ta kasance rana mafi muni da baƙin ciki a gurin Hafsah. Daren jiya ko bacci bata iya yi ba saboda wani abu da yay mata cunkus a cikin zuciya. Tunda ta tashi yau da safe kuwa take ta aikin kuka, ta ƙi ci ta ƙi shan komai. Da rana ta samu Mom ta bata ɗaya daga cikin wayoyinta daƙyar, jikinta har rawa yake yi gurin azarɓaɓi da zumuɗin shiga yanar gizo, aiko cikin lokacin ƙanƙani ta ci karo da abun da take nema. Pics ɗin Neehal kala_kala tun daga na ranar kamu har na ranar ɗaurin Aure wanda bai jima da sauka ba ta yi katari da shi, sai kuma na Ameen a gurin ɗaurin Aure, wasu shi kaɗai wasu kuma da jama’a yana ta murmurshinsa mai kyau wanda ya tabbatar mata yana cikin tsananin farin ciki. Ya yi kyau sosai cikin milk ɗin dakakkiyar shadda ya sha babbar riga wadda ta ci aiki mai kyau. Bata san lokacin data yarda wayar ta_ta ba tare da kurma wani uban ihu, shikenan Ameen ya zama nasu su biyu, yau ita ce da kishiya? Abar da bata taɓa kawo ta ba a cikin rayuwarta ko a mafarki da sunan za’ai mata, gaskiya Ameen ya cuce ta, zata iya cewa tunda ta zo duniya bata taɓa ganin ranar baƙin ciki irin wannan ba, ita ƴar gata ce bata taɓa neman abu ta rasa a rayuwarta ba, kome take so iyayenta suna yi mata. Ameen ne mutum na farko da ya fara bata ciwon kai a rayuwarta, yanzu kuma yana ƙoƙarin saka mata na zuciya. Ihun data kurma ya yi dai-dai da shigowar Aunty Jamila cikin falon wadda zuwanta gidan kenan, Aunty Jamila ta ƙarasa gare ta da sauri cikin damuwa ta ce. “Subhanallahi, Hafsah lafiya? Me ya faru?” Cikin kuka ta ce. “Aunty na kaɗe har ganyena, ta tabbata Ameen ya ƙara aure ya mun kishiya, na shiga uku ni Hafsat.” Aunty Jamila ta zauna a gefenta ta ce. “Haba Hafsah, dan an yi miki kishiyar kike wannan kukan da ihun? Me hakan zai haifar miki? A kanki aka fara kishiyar ne? Ko kanki farau ne? Kishiya ai abokiyar zama ce ba abar tashin hankali ba, da har zaki zauna kina wannan abun.” Hafsah ta ce. “Aunty ce mun fa ya yi ya fasa auren, ashe munafiki bai fasa ba.” Aunty Jamila ta kama haɓa ta ce. “Hafsah! Mijin naki kike cewa munafiki dan ya ƙara aure sunnar ma’aiki da Ubangiji ya halatta masa ya yi? To akul kar na ƙara jin kin kuma jifan mijinki da wannan kalmar.” Hafsah ta yi shiru a ranta tana takaicin yanda bata kula kowa a familyn Ameen da matan abokansa, may be da suna hulɗa da wani ko wata zata samu labarin bikin tun kafin lokaci ya ƙure, may be da ta yi ƙoƙarin hana yin auren, amma yanzu lokaci ya ƙure mata tunda an yi an gama, amma duk da haka baza ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen bin duk abun da Aunty Safiyya ta ce mata ba dan ganin auran Neehal da Ameen ya zama matacce……..
Neehal tana zaune naɗe cikin mayafi tana kukanta ta ji ana sallar ishai, ta miƙe daƙyar saboda kanta dake mugun sara mata ta yi ta_ta Sallar da yake tana da alwalarta. Sai a lokacin ta ɗaga kanta ta shiga bin madaidaicin ɗakin da take ciki da kallo, ya matuƙar yi mata kyau da burgewa. Ta lumshe idonta a hankali tana jin ta kamar mai cuta, bata fi ten minutes da idar da sallar ba ta ji ƙarar buɗe ƙofa daga waje, tana can tana tunanin da ya aure ta ko shigowar Mota gidan bata ji ba, ta miƙe da sauri ƙirjinta na tsananta bugu ta koma kan gadon ta zauna ta ƙudundune jikinta guri guda da mayafin jikinta. A hankali ta ji an turo ƙofar ɗakin da take, gabanta ya yanke ya faɗi, sallamarsa cikin kamilalliyar muryarsa da kuma daddaɗan ƙamshinsa suka ziyarci hancinta a lokaci ɗaya. Ya tsaya a jikin ƙofa bayan ya mayar ya rufe tare da harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallon ta, hakan ba ƙaramin ƙarawa Neehal saurin bugun zuciyarta ya yi ba. Ya tako a hankali ya ƙaraso bakin gadon tare da tsugunnawa a gabanta, fuskarsa na fitar da wani irin annuri gami da sihirtaccen murmushi. A hankali ya saka hannun damansa ya shiga ƙoƙarin buɗe fuskarta, jin hakan ita kuma ta ƙara ƙanƙame mayafinta a jikinta, kukan data daina na ƴan mintunan da suka gabata ya dawo sabo ta hanyar fara zubar hawaye daga idonta, jikinta har ƴar rawa ya fara saboda tsoro da fargaba, duk guje masan da take yau gashi daga ita sai shi a gida ɗaya a ɗaki ɗaya, sai dai ita ba wannan ne ya fi damunta ba, damuwarta yanzu ya zo mata ne a matsayin miji, kuma bata san irin zama da rayuwar da ya shirya musu ba. Ya yi nasarar yaye mayafin, fuskarta da ta yi jajur saboda kuka ta bayyana, saboda tsorata a ƙoƙarinta na ƙara riƙe mayafin bata san ma hanyar da zai cire cikin sauƙi ta samar masa. A hankali ya kama hannunta dake kan cinyarta ya riƙe tare da sakin wata sassanyar ajiyar zuciya, ƙamshin jikinta ya fara tasiri a gare sa, riƙe hannunta da ya yi ya zo mata a bazata har ƴar zabura ta yi tare da ƙara yin ƙasa da kanta. Ya damƙe hannun nata sosai a cikin nasa jin tana ƙoƙarin zare shi, cikin wata sassanyar murya mai daɗin amo mai kama da raɗa ya ce. “Welcome home my bride.” Ta turo baki a hankali maganarsa na yi mata yawo a cikin zuciyarta da kwanyarta, kalmar my Bride ɗin da ya furta ta fi komai bata mamaki, da kuma yanda ya yi mata magana cikin sanyi da wani irin salo. Ya yi murmushi mai sauti tare da kai ɗayan hannun nasa ya ɗago haɓarta, ta yi saurin lumshe idonta tana jin zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito saboda bugu, yanayin da take jin kanta da zuciyarta ba zai misaltu ba, ita kanta ta kasa tantance yanayin da take ciki, kafin ya shigo ta san tsoro da fargabar ganinsa da kasancewar da za su yi a gida ɗaya take, amma yanzu da ya shigo inda take yake tsugunne a gabanta sai ta ji wani baƙon al’amari a game da shi a cikin zuciyarta. Tana jin yanda ya ƙurawa fuskarta ido yana kallon ta ko kiftawa babu a jikinta, sai ta ji ita ma zuciyarta tana azalzalarta da ta buɗe idonta ta kalle shi, duk yanda ta so bijirewa daga umarnin zuciyarta amma zuciyar ta ƙi bata goyon baya, bata ma san lokacin data buɗe kumburarrun idonta da suka ci kuka suka ƙoshi ba ta zuba su akan kyakkyawar fuskarsa da gangar jikinsa a lokaci ɗaya, amma bata bari sun haɗa ido ba. Sanye yake cikin wani tsadadden yadi milk colour, kansa sanye da hula, duk da bai fiya sakawa ba amma ta yi masa kyau sosai. Yanda ya kafe ta da ido yasa ta kallon nasa idon ita ma, hakan ya ƙara mata jin abun da take ji a cikin ranta, ta yi saurin janye nata idon saboda wasu abubuwa da take gani suna shiga nata idon daga nasa masu kaifi suna ƙoƙarin fasa mata zuciya. Ta lumshe idonta a hankali hawaye ya zubo daga cikinsu tare da ƙoƙarin cire hannunsa daga kan fuskarta saboda yanda ta ga yana yi mata wani irin kallo da ya kashe mata jiki. Ya shafi kuncinta cikin sanyin murya ya ce. “Cry cry baby, kukan barin gidan Mama ne ko na zuwa gidan Ameen?” Ta turo baki tare da cire hannunsa daga fuskarta, amma ko 2 second ba’a yi ba ta ji hannun nasa a gefen wuyanta yana shafawa cikin wani irin salo, hakan yasa ta ji tsigar jikinta ta fara tashi, wani abu da bata san ko mene ma yana yawo a cikin jikinta, kawai sai ta saka kuka tare da ja baya, yanayin da zuciyarta da gangar jikinta suke ciki bazai misaltu ba, ta rasa ya zata yi, ta rasa ina zata saka kanta. A hankali ya ce. “God! Kukan dai miemerh, Please ki daina kukan nan, na ji jikinki da zafi kar zazzaɓi ya rufe ki, kuma na san wannan kukan da kika sha kanki sai ya miki ciwo.” Cikin shagwabarta ta ce. “Ni bacci nake ji.” Ya ɗan yi murmushi sannan ya miƙe ya ce. “Ni kuma na hana ki ko? To ki bar kukan haka, indai ni ne na tashi, amma kafin ki kwanta ya kamata ki ci wani abu ki sha magani.” Ta turo baki ta ce. “Ni na ƙoshi bacci kawai zan yi.” Bai ce komai ya matsa daf da ita sannan ya ɗora goshinsa akan nata ya ɗora hannunsa a ƙirjinta saitin zuciyarta ya ce. “Wannan bugun zuciyar duk na tsoron mene ne?” Ta ja wani gwauron numfashi ta sauke tana jin abun da bata taɓa ji ba a tsahon rayuwarta a dalilin kusancin da suka samu, ga ƙamshinsa dake ƙarawa zuciyarta hauhawar yanayin da take ciki. Ta runtse idonta numfashinta na fita da sauri da sauri. Ya janye fuskarsa daga ta_ta, yana kallon tsoro ɓaro_ɓaro akan fuskarta_ta, ajiyar zuciya ya saki a hankali tare da jan gwauron numfashi. Ta ƙara jan mayafinta ta lullub’e jikinta. Ya yi murmushi kawai wanda ya kasa b’acewa daga fuskarsa tunda ya shigo ɗakin sannan ya juya ya fice. Ta sauke ajiyar zuciya tare buɗe fuskarta ta bi ƙofa da kallo, a ranta tana mamakinsa yanda yake mata magana da wasu abubuwan. Bayan kamar 15 minutes ya dawo ɗakin, saurin rufe idonta ta yi tana keɓe fuska, ya ajiye ledodin hannunsa sannan ya juya ya ƙara fita, bai jima ba ya dawo hannunsa ɗauke da tire da glass cup da fork. Ya d’auko kaza ɗaya dake cikin ɗaya daga cikin ledodi biyun da ya ajiye ya saka a cikin tiren sannan ya kalle ta ya ce. “Oya come and eat.” Ta mak’e kafaɗa alamar a’a. Ya miƙe ya ce. “Okay, idan baki sauko ba kin san dai baza ki gagare ni ɗauka ba ko?” Jin haka yasa ta buɗe idonta da sauri tare da ja baya, kamar zata yi kuka ta ce. “Ni fa Yaya na ƙoshi Allah.” Ya kalle ta na wasu sakanni ba tare da ya yi magana ba ya tunkari gadon, da sauri ta sauko tana cize lip saboda ciwon kai idonta cike fal da hawaye. Ta zauna a gaban tiren tana turo baki gaba. Ya dawo ya zauna shi ma a kusa da ita, ba tare da ya yi magana ba ya saka fork ya gutsiro naman ya kai bakinta, ta kawar da kanta gefe, ya saka hannu ya juyo da fuskarta tare da haɗe da rai yana yi mata kallon warning. Ganin babu wasa a fuskarsa ta buɗe bakinta ya saka mata tare da fara hawaye. A kausashe ya ce mata. “Ki haɗiye mun wannan kukan naki, karki bari hawaye ya ƙara zubowa daga idonki.” Ba shiri ta haɗiye kukan amma cikin ranta ji take kamar ta fasa ihu. Duk yanda take ɓata fuska da turo baki bai saka ya daina ya bata ba sai da ya tabbatar ta ƙoshi, ita kanta ta san tana jin yunwa, amma yanda take jin kanta na sara mata babu abun da take buƙata a yanzu sama da bacci. Fresh milk ɗin da ya zo da ita a ɗayar leda ya d’auko ya tsiyaya ya bata, ta kurb’i kaɗan ta ajiye, yay mata wani kallo alamar ta d’auka ta ƙara sha. Ta saka kuka ta ce. “Yaya cikina fa zai fashe.” Ya yi murmushi tare da kai hannu saitin cikin ya ce. “Mu ji ta inda zai fashe ɗin.” Ta ture hannun nasa tana cigaba da kukan nata. Ya janyo ta jikinsa a hankali tare da kwantar kanta akan kafaɗarsa ya ce. “Kuka, kuka dai Miemerh? I know baki ci wani abincin kirki ba yau saboda hada_hada, ta yaya zan barki ki kwana da yunwa? ko so kike Mamanki ta sab’ar mun? Baki san warning ɗin data ja mun a kanki ba ne shi yasa.” Ta yi shiru bata ce komai ba sai ƙoƙarin tashi da ta yi daga jikinsa, bai hana ta ba har ta miƙe ta haye kan gado. Tana ƙoƙarin kwanciya ya miƙe ya ce. “Ta so mu je ki ga gidan naki kafin ki yi bacci.” Ba musu ta miƙe ta ja mayafinta ta yafa ta sauko daga kan gadon saboda ita ma bata so daga cin abincinta ta kwanta ba, shima kuma nasa nufin kenan.” Ya kama hannunta ta k’wace, ya ƙara riƙewa, ta kalli fuskarsa ya harare ta, ta ɗauke idonta da sauri tare turo baki. Ko ina a gidan sai da ya kai ta ya nuna mata, tsarin gidan ya yi mata kyau sosai kuma ya burge ta. Sannan ya raka ta, ta koma nata ɗakin. Suna shiga ta nufi kan gado. Ya ce. “Kin yi Sallah ne?” Ta gyaɗa masa kai. Ya ce. “Wanka fa?” Ta ce. “Na yi shi ma.” Ya ce. “Ki sake wani, sai ki fi jin daɗin baccin.” Bai jira amsarta ba ya d’auki tiren da ta ci kaza da sauran kayan gurin ya juya ya fice. Ta turo baki ta yi kwanciyarta. Mintuna kaɗan sai gashi ya dawo ɗakin, bai ce mata komai ba ya shige toilet hannunsa ɗauke da soap da soso, ya ajiye su sannan ya kunna mata heater. Ya fito yana duban ta ya ce. “Ki tashi ki yi wankan kar bacci ya ɗauke ki.” Ta tashi tana babbata fuska ta shiga toilet ɗin. Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juya ya fita……….✍️